Muhaddasa (Laƙabi)
- Ka da a yi Kuskuren daidai ta shi da Shafin Muhaddis

Muhaddasa (Larabci: المُحَدَّثة) ɗaya ne daga cikin laƙubban Sayyida Faɗima (S) ma'ana matar da mala'iku suke magana tare da ita. Wannnan laƙabi a cikin riwayoyi an yi da amfani da shi kan wasu matan daban misalin Sayyida Maryam (S) da Saratu. Ana cewa Mala'iku sun magana tare da ita cikin batutuwa misalin jaje da ta'aziyya, labarurrukan muminai da abin da zai faru gobe.
Yiwuwar mala'iku su yi magana tare da Imamai da Sayyida Faɗima (A.S) suna daga cikin aƙidun shi'a, da wannan dalili wasu Ahlus-sunna suke zargin ƴanShi'a da annbtar da Imamansu. A cewar Allama Amini, marubucin littafin Al-Ghadir, yiwuwar Mala'iku su yi magana tare da mutanen da ba Annabawa ba magana ce da Shi'a da Ahlus-sunna suka yi ittifaƙi kanta, kaɗai sun yi saɓani ne cikin misdaƙi da su wane ne waɗanda mala'ikun za su iya magana tare da su.
Muhaddasa, Laƙabin Sayyida Zahra (S)
Kan asasin riwayoyi, laƙabin muhaddasa ɗaya ne daga laƙubban Sayyida Zahra (S)[1] kuma ɗaya ne daga sunayenta guda tara.[2] na'am daidai da abin da ya zo cikin riwayoyin shi'a ana amfani da wannan laƙabi kan Sayyada Maryam (S), mahaifiyar Annabi Musa (A.S) da kuma Saratu matar Annabi Ibrahim (A.S).[3] Cikin wasu riwayoyi da suke da alaƙa da Mus'hafu Faɗima an ishara da ga kasancewar ta muhaddasa.[4] cikin ziyarar Sayyida Faɗima nan an kira ta da «الْمُحَدَّثَةُ الْعَلِیمَةُ» (Al-muhaddasa Al-alima).[5]
Ma'anar Muhaddasa
Muhaddasa yana nufin wanda mala'iku suka yi magana da shi,[6] a cewar Allama Amini marubucin littafin Al-Ghadir, isɗilahin muhaddasa ana amfani da shi kan wanda ba Annabi ba; amma tare da haka Mala'iku suna magana da shi.[7]
Ba'arin abin da magana da Mala'iku ya ƙunsa wanda Sayyida Faɗima ta yi, ya dunƙule a cikin wurare guda biyar : gaisuwa da ta'aziyya, ba ta labarin Annabi (S.A.W) da matsayinsa a cikin aljanna, labaran abubuwan da za su faru a gobe, labarurrukan masu mulki da labaran muminai da kafirai.[8]
Wasu suna ɗaukar laƙabin muhaddisa da ma'anar mai magana, saboda suna cewa lokacin da ta kasance a cikin mahaifiyarta ta kasance tana magana da mahaifiyarta.[9][Tsokaci 1]
Yiwuwa Zantawar Mala'iku Da Waɗanda Ba Annabawa Ba
Allama Amini, yana ɗaukar imani da kasancewar Sayyida Faɗima (S) tana magana tare da mala'iku, haka ma Imamai suma suna magana da su yana daga cikin aƙidun ƴanShi'a, a cewarsa yarda da cewa mala'iku suna magana tare da waɗanda ba Annabawa batu ne da shi'a da Ahlus-sunna suka yi ittifaƙi a kansa.[10] Ya bayyana cewa kaɗai dai an samu saɓani cikin wannan batu ne ta fuskacin su wane ne mala'ikun suka yi magana da su. Alal misalin ƴanShi'a saɓanin Ahlus-sunna ba su yarda cewa Umar Ɗan Khaɗɗab yana daga mutanen da Mala'iku suka yi magana tare da shi ba.[11]
Abdullahi Ƙasimi, marubuci mai bin tafarkin salafiyya daga ƙasar Saudiyya, a cikin littafin As-sira'u Bainal Islam Wal Wasaniyya, sakamakon imani da kasancewar Sayyida Faɗima (S) da Imamai a matsayin wanda Mala'iku suka yi magana da su, ya tuhumi shi'a da ƙoƙarin annabtar da Imamansu da kuma Faɗima (S). Na'am Allama Amini ya bada amsa kan wannan tuhuma.[12] domin tabbatar da zantawar Mala'iku tare da mutanen da ba Annabawa ya dogara da ayoyin Alƙur'ani misalin aya ta 42 Suratu Ali Imran, aya ta 71-73 Suratul Hud da aya ta 7 Suratul Ƙasas, cikin waɗannan ayoyi an yi ishara kan zantawar tsarkakakkun magabata mata tare da Mala'iku.[13]
Bayanin Kula
- ↑ Saduƙ, Illalush Shara'i, juzu'i na 1, shafi na 182; Ɗabari, Dala'ilull Imama, shafi na 81, h. Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 14, shafi na 23.
- ↑ Saduƙ, Al-Amali, shafi 592.
- ↑ Majlis, Bihar al-Anwar, juzu'i na 43, shafi na 79.
- ↑ Ku duba Saffar, Basa'irud Darajat, shafi na 152; Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 18, shafi na 34; Mahdawi Rad, «مصحف فاطمه», shafi na 73.
- ↑ Ƙummi, Mafatihul Jinan, shafi na 317.
- ↑ Rahmani Hamdani, Fatima Zahra (S) Shadmani Dele Payambar (S.A.W), shafi 244 (Ƙarin bayani a ƙasan shafi).
- ↑ Allama Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 5, shafi na 67.
- ↑ Rahman Satayesh، «گفت و گوی ملائکه با حضرت فاطمه(س)»، Shafi na 25-26.
- ↑ Rahmani Hamdani, Fatima Zahra (S) Shadmani Dele Payambar (S.A.W), shafi 244 (Ƙarin bayani a ƙasan shafi).
- ↑ Allama Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 5, shafi na 67-68.
- ↑ Allama Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 5, shafi na 68-70.
- ↑ Allama Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 5, shafi na 78.
- ↑ Allama Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 5, shafi na 78.
Tsokaci
- ↑ Kuɗubud-Din Rawandi, cikin littafin Al-Ƙabu Ar-rasul Wa Ibratuhu, cikin sashen lakubban Fatima, taken "Munisa Khadijatul Al-kubra fi batniha" ya yi ishara da kasancewar ta tana magana tare da babarta tun tana ciki
Nassoshi
- Rahman Satayesh, Muhammad Kadhim, گفت-و-گوی-ملایکه-با-حضرت-فاطمه-س» گفتوگوی ملائکه با حضرت فاطمه(س)»، (Hirar Mala'iku Da Sayyida Fatima (A.S),) Hadis Pajuhi Bahar wa Tabistan, 2001M.
- Rahmani Hamadani, Ahmad, Fatima Zahra, (S), Shadmani Dele Payambar, wanda Sayyid Hassan Iftekharzadeh Sabzwari ya fassara, Tehran, Ofishin Tahƙiƙat da Intisharate Badar, Chapharm, 1381Sh.
- Sheikh Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, Shasham, 1376Sh.
- Sheikh Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Ilalush Shara'i', Najaf, Al-Maktabat Al-Haidariyya, 1386H.
- Saffar Ƙummi, Muhammad Bin Hassan Bin Faroukh, Basa'irud Darajat fi Fada'il Ali Muhammad, Gyara da Sharhi: Mirzam Muhsin Kocha Baghi Tabrizi, Qom, Maktabat Ayatullahi Mar'ashi Al-Najafi, bugu na biyu, 1404H.
- Ɗabari, Muhammad Bin Jarir Bin Rostam, Dala'ilul Imama, Qum, Bi'isat, bugu na farko, 1413H.
- Allama Amini, Abdul-Husaini, Al-Ghadir Fil Kitab Was Sunna Wal Adab, Qum, Cibiyar Al-Ghadir Lil Dirasatil Islamiyya, 1416H.
- Ƙummi, Abbas, Mafatihul Jinan, Qum, bugun Aswa, babu kwanan wata.
- Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Cibiyar Al-Wafa, 1403H.
- Mahdawi Rad, Muhammad Ali, «مصحف فاطمه», (Mus'hafu Fatima) Cikin Danshnameh Fatimi (S), Tehran, Sazimane Intisharate Pajuheshga Farhnag Wa Andishe Islami, 2014M.