Sayyidatu Nisa'il Alamin (Laƙabi)
Sayyidatul Nisa’il Alamin (Larabci:سيدة نساء العالمين) ma’ana shugabar matan duniya, laƙabi ne daga laƙubba da falalar Hazrat Fatima (S). Kan asasin masadir na hadisi na Shi’a [1] da Ahlus-sunna [2] Annabi (S.A.W) da kansa ya sanya mata wannan laƙabi, a cewar Ibn Abil Al-Hadid, wannan kalma an naƙaltota daga Annabi (S.A.W) da surar tawatiri na lafazi ko Ma’anawi. [3] Cikin maganganun Imam Ali (A.S) lokacin binneta wanda aka naƙalto a cikin littafin Al-Kafi ya yi amfani da wannan laƙabi kan Fatima (S) [4] [Tsokaci 1] haka kuma wannan laƙabi ya zo cikin ba’arin ziyarori misalin Ziyatu Imam Ali (A.S) [5] Ziyaratu Hazrat Zahra (S) [6] da Ziyaratu Waris, [7] Ziyaratu Ashura [8] da Ziyaratu Imam Rida (A.S). [9] Cikin wasu riwayoyi daban daga masadir na Ahlus-sunna, Annabi (S.A.W) ya kira Fatima (S) da sunan Shugabar Matan Al’ummar musulmi da Matan Aljanna. [10] Cikin ba’arin riwayoyi kusa da Sunan Fatima (S) an kawo sunayen Maryam ƴar Imrana mahaifiyar hazrat Isa (A.S) Asiya Matar Fir’auna da Khadija Bint Khuwailid, an kuma kira Fatima da laƙabin Sayyidatul Nisa Alami, (shugabar Matan duniya) [11] na’am bisa wata riwaya, an kira Maryam da shugabar Matan zamaninta ita kuma Fatima shugabar matan farko da na ƙarshe, [12] haka kuma domin fifitar Fatima kan sauran mata, an jigina da maganar Annabi (S.A.W) da yake cewa Fatima Gutsiren tsokar jikina ce. [13] ƴan shi’a a duk zagayowar ranar shahadarta Fatima (S) suna amfani da Fastoci da tutoci a majalisansu da suke ɗauke da wannan kalma. [14]
Bayanin kula
- ↑ Sheikh Sadouƙ, Man Lay Hazara Al-Faƙih, 1413 AH, Juzu'i na 4, shafi na 179 da 420; Sheikh Sadouƙ, Al-Amali, 1376, shafi na 26, 113 da 298.
- ↑ Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 170; Ibn Asaker, Tarikh Damashƙ, 1415 Hijira, juzu'i na 14, shafi na 173 da juzu'i na 42, shafi na 134.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 265.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 459.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 741; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 246.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 711; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 78-81.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 719 da 720.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 772 da 773; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 481.
- ↑ Sheikh Sadouƙ, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), 1378 AH, Mujalladi na 2, shafi na 269.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 203, juzu'i na 8, shafi na 64; Muslim Neishabouri, Sahih Muslim, darul Ihya Al-Turath Al-Al-Arabi, Juzu'i na 4, shafi na 1904 da 1905.
- ↑ Hakim Neishaburi, Al-Mustadrak Ali al-Sahiheni, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 205; Ibn Asaker, Tarikh Damashƙ, 1415 Hijira, Juzu'i na 70, shafi na 109 da 112.
- ↑ Tabari Amoli, Dalai'lul Al-Imamah, 1413H, shafi na 149.
- ↑ Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415-1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 149.
- ↑ <a class="external text" href="https://iƙna.ir/fa/news/4030605">«پرچم «یا سیدة نساء العالمین» بر فراز گنبد حرم امام علی(ع) + عکس»</a>
Tsokaci
- ↑ Ya Ma'aikin Allah, hakurina ya kare a cikin rabuwar 'yarka zababbiya, kuma karfina ya yi rauni a cikin rabuwa da shugabar mata.
Nassoshi
- Alousi, Mahmoud bin Abdullah, Ruh al-Ma'ani fi Tafsir al-ƙur'an al-Azeem da Al-Saba al-Mathani, bincike na Ali Abd al-Bari Attiyah, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1415 /1416 AH.
- Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharh Nahj al-Balaghah, bincike da gyara na Muhammad Abulfazl Ibrahim, ƙum, Mazhabar Ayatullahi al-Mar'ashi al-Najafi, bugu na farko, 1404H.
- Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Damashƙ, Amr Ibn Gharamah ya yi bincike a Beirut, Darul Fikr, 1415 AH-1995 miladiyya.
- Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jafar, Al-Mazar al-Kabir, bincike na Javad ƙayyumi Isfahani, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1419H.
- Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahih Bukhari, Bincike na Muhammad Zuhair bin Nasser al-Nasser, Beirut, Dar Touƙ al-Najah, 1422H.
- <a class="external text" href="https://iƙna.ir/fa/news/4030605">«پرچم «یا سیدة نساء العالمین» بر فراز گنبد حرم امام علی(ع) + عکس»</a>
- Hakeem Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheeni, wanda Mustafa Abd al-ƙadir Atta ya yi bincike a Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na farko, 1411H.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), bincike na Mahdi Lajurdi, Tehran, Jahan Publishing House, bugu na 1, 1378H.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, | Al-Mali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Man Laihzara al-Faƙih, bincike na Ali Akbar Ghafari, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyu, 1413 AH.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid, Beirut, Cibiyar Fiƙh al-Shia, bugu na farko, 1411H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-kafi, Tehran, Al-Maktab al-Islamiyya, 1388H.
- Muslim Neishabouri, Muslim bin Hajjaj, Sahih Muslim, bincike na Muhammad Fouad Abdul Baƙi, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Bita.