Huɗubar Muttaƙin

Daga wikishia

Huɗubar muttaƙin ko huɗubar Hammam (Larabci: خطبة المتقين) tana cikin shahararrun huɗubobin cikin littafin nahajul balaga cikin fagen kyawawan halaye da taƙawa. Imam Ali (A.S) ya yi wannan huɗuba sakamakon roƙonsa da ɗaya daga cikin sahabbansa mai suna Hammam ya yi da Imam ya yi masa bayanin siffofin masu taƙawa. Baya ga Hammam ya gama sauraron wannan huɗuba sai ya shiga wani hali ya suma daga ƙarshe dai take ya mutu. Cikin wannan huɗuba an yi bayanin halaye da mu'amaloli ɗaiɗaikun mutane muta da jama'a da ibada. daga jumlolin siffofin da da halayen za a iya ishara da riƙon amana, haɗiye fushi, haƙuri, ƙanƙan da kai cikin ibada.

Wannan huɗuba baya ga nahajul balaga ta zo a cikin wasu madogaran daban misalin Al-tamhis, Amali Shaik Saduƙ da Kanzul Al-fawa'id; da wannan dalili masu zurfafa bincike suka ganin wannan huɗuba ta kai darajar tawatiri. Wasu ba'ari daban sun tafi kan cewa asalin wannan huɗuba ta kasance gajeriya amma bayan shuɗewar zamani sai aka yi ƙare-ƙare cikinta.

ƙari kan tarjamomi da rubuta sharhi daban-daban kan littafin nahajul balaga, wannan huɗuba an ware mata na ta tarjamomin da sharhi mai cin gashin kansa daga jumlarsu za a iya ishara da littafin “Akhlaƙ Islami Dar Nahjil Al-balaga” da kuma “Rahi wa Rasme Parhizkaran wa Ashi'atu Min Khuɗbatil Al-muttaƙin”. Ana cewa ra'ayoyin adabin larabci daga balaga da fasaha da wannan huɗuba ta tattaro suna da yawan gaske.

Gabatarwa Da Matsayi

Huɗubar muttaƙin tana daga cikin sanannun huɗubobin nahajul balaga[1] ana ɗaukarta cikin muhimman huɗubobin Imam (A.S).[2] Nasir Makarim Shirazi daga maraji'an taƙlidi na shi'a, ya lissafa wannan huɗuba cikin huɗubobin littafin nahajul balaga mafi tattarowa batutuwa a fagen kyawawan halaye da taƙawa.[3] cikin ba'arin bincike da aka yi, an bayyana wannan huɗuba matsayin madogara mai kyau cikin sanin kyawawan halaye da tsaftace zuciya.[4] a cewar Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi daga malaman tafsirin kur'ani na shi'a, rawaito wannan huɗuba daga Imam Baƙir (A.S)[5] da Imam Sadiƙ (A.S).[6] wata alama ce da take nuni kan irin muhimmancinta.[7] duk da cewa Sayyid Radiyu bai sanyawa wannan huɗuba suna ba,[8] amma sakamakon abubuwan da aka siffanta daga halayen ma'abota taƙawa sai aka kira wannan huɗuba da suna huɗubar masu taƙawa.[9]

Imam Ali (A.S) ya yi wannan huɗuba sakamakon roƙonsa da ɗaya daga cikin sahabbansa da ake kira da suna Hammam ya yi.[10] wannan huɗuba an rawaito ta a sauran madogarai ƙari kan nahajul balaga, huɗuba game da siffofin masu taƙawa[11] ko siffofin muminai[12] ko siffofin ƴan shi'a.[13] ana cewa Hammam bayan sauraren wannan huɗuba sai ya gigice ya suma ya mutu take a wannan lokaci.[14] Imam Ali (A.S) ya yi bayanin siffofin masu taƙawa a cikin wannan huɗuba ya lissafo kusan siffofi 100 na masu tsoran Allah.[15] a cewar ba'arin masu zurfafa bincike anyi amfani da fannonin adabi cikin wannan huɗuba.[16]

Sunan Kwafi Lamabar Huɗuba
Al-mujama Al-mufahras Li Alfaz Nahjil Al-balaga/ Subhi Saleh 193
Ibn Maisam baharani/Iban Maisam Baharani 184
Habibullahi Khuyi/ Mulla Salihu Ƙazwini 192
Ibn Abil Al-hadid/ Muhammad Abduhu 186
Mulla Fatahullahi Kashani 221
Muhammad Jawad Mugniyya 191

Abubuwan Da Suke Cikin Huɗubar

An yi bayanin mabambantan sasanni cikin huɗubar ma'abota taƙawa daga sashen rayuwar masu tsantseni, halayen ɗaiɗaikun mutane da jama'a da kuma alaƙoƙinsu da ubangiji.[17] cikin zirin jero siffofi da halaye fiye da guda ɗari.[18] wannan huɗuba ta ƙunshi ɓangarori guda bakwai; 1. Farko-farkon huɗuda da farawa da goiya ga Allah 2. Gabatarwa 3. Siffofin masu taƙa a dunƙule 4. Daren masu tsoran Allah 5.yinin masu tsoran Allah 6. Alamomin masu taƙawa 7. ƙarshen ƙissar Hammam.[19] Siffofin Zamantakewa Na Masu Taƙawa:

  • Nesanta daga miyagun maganganu
  • Riƙon amana
  • Haɗiye fushi
  • Yafewa wanda ya zalunce su
  • Mutane suna cikin aminci daga cutarwarsu
  • Mutane suna yin fata daga kyautatawa daga gare su

Siffofi Na ɗaiɗaiku:

  • Shakku ga kawukansu
  • Gudun Yabon mutane
  • Zurfin tunani tare da tausasaw
  • Imani tare da yaƙini
  • Haƙuri da dauriya
  • ƙaranta cin abinci tare da sauƙaƙƙar rayuwa

Alaƙa Da Allah:

  • Sallar dare tare da karatun kur'ani
  • neman waraka daga kur'ani
  • Tasirantuwa da kur'ani
  • Khushu'i ciki ibada.[20]

Inganci

Nasir Makarim shirazi daga maraji'an taƙlidi na shi'a, ya tafi kan ingancin huɗubar muttaƙin da aka naƙalto ta daga madogarai daban-daban.[21] Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi shi ma ya yi imani da kasancewar wannan huɗubar kan tawatiri za kuma a iya dogara da ita.[22] wannan huɗuba an ambace cikin mabambantan madogaran riwayoyi.[23] daga jumlar waɗannan madogarai su ne wannan litattafai kamar haka: Al-kafi talifin Shaik Kulaini,[24]Al-tamhis talifin Ibn Hammam Iskafi,[25] Tuhaful Al-uƙul rubutun Ibn Shu'uba Harrani,[26] Amali Shaik Saduƙ,[27] Kanzul Al-fawa'id talifin Garajiki[28] Raudatul Al-wa'izin na Fattal Naishaburi.[29] madogarai da masadir na farko-farko na wannan huɗuba ba su kasance bai ɗaya ba ta fuskanin zirin lafuzza da girman riwaya.[30] ba'arin marubuta tare da jingina da bambancin kwafi-kwafin wannan huɗuba da kuma gabatar da ba'arin shaidu sun yi da'awar asalin wannan huɗuba wace ta zo daga Imam Ali (A.S) ta kasance gajeriya.[31] sannu-sannu aka yi ƙarin jumloli masu tarin kalmomi cikinta.[32]

Tarjama Da Sharhi

Baya ga sharhi da tarjama da aka yi kan wannan huɗuba cikin tarjama da sharhi da aka yi na bakiɗayan littafin nahajul balaga, akwai gomomin tarjama da sharhi da aka keɓancewa wannan huɗuba ita kaɗai a ware cikin harshen farisanci da larabci.[33] ga bar'in wasu daga cikinsu kamar haka:

  • Akhlaƙ Islami Dar Nahjil Al-balaga, sharhin farisanci na Nasir Makarim Shirazi;
  • Rahi Wa Rasme Parhizkaran, shima na Nasir Makarim Shirazi
  • Sharhe Khuɗbae Muttaƙin (Sharhe Hadis Haftom) talifin Muhammad Taƙiyyu Majlisi;
  • Az Parsayan Barayam Begu, tarjama da ƙarin bayani cikin farisanci talifin Jamalud-dini parwar;
  • Ashi'attu Min Khuɗbatil Al-muttaƙin, shrhin larabci da aka yi kan huɗubar Hammam, tare da alƙalamin Ummu Ali ƙabanji;
  • Muttaƙin, sharhi cikin harshen farisanci kan huɗubar muttaƙin;
  • Ausaf Parsayan: sharhin huɗuba tare da alƙalamin Abdul-karim Sarush;
  • Ausaf Muttaƙin, tarjama da tafsiri cikin harshen farisanci tare da alƙalamin ƙadir Fazili tare da muƙaddimar Muhammad Taƙiyyu Jafari
  • Nagme Ilahi, sharhin waƙa da tarjamar farisanci kan huɗuabar muttaƙin, na Mahadi Ilahi ƙamshe'i;
  • Sifffat Muttaƙin (Khuɗbe Haftom) Maulaye Muttaƙin Amirul muminan Ali (A.S) tarjamar Gulam Riza Yasipur cikin rera waƙa da zuben magana.
  • Masnawi Parsaname, tajamar waƙar daga huɗubar muttaƙin da wasiƙar Imam Ali (A.S) na Abdul-Mahadi Maruf zadeh;
  • Siffatu Muttaƙin dar Kalame Maulaye Muttaƙi, Sharhe waƙar huɗubar Hammam, mai rerawa Muhammad Ali Muhammadi.

Bayanin Kula

  1. Makarem Shirazi, Payame Imam (a.s), 2006, juzu'i na 7, shafi na 527.
  2. Hoshyar, wa Jalil Tajlil, "Parsi Tadbiki Simani, Insan Kamil Dar kutbeh Mutqin's, Nahj al-Balagha wa asare Aziz al-Din Nasafi," shafi na 20.
  3. Makarem Shirazi, Akhlaq Islami dar Nahj al-Balagha, 2005, juzu'i na 1, shafi na 8.
  4. Shafi’i, Imam Shanasi, 1397H, shafi na 145.
  5. Sheikh Saduq, Al-Amali, 1376H, shafi na 570-574.
  6. Kulayni, Kafi, 1407 BC, juzu'i na 2, 224-230.
  7. Misbah Yazdi, “Semai Perhizkaran dar kutbeh Muttaqin Amirul Muminin (a.s),” shafi na 6.
  8. Nahj al-Balagha,Tashihu Sobhi Saleh, hadisi na 193, shafi na 303.
  9. Soleimani Rahimi, "Namguzari Kutbehaye Nahj al-Balagha"; Yek pishnahad, shafi na 206.
  10. Nahj al-Balagha, Tashihu Subhi Saleh, 1414 AH, Huduba 193, shafi na 303.
  11. Duba: Ibn Shuba Harrani, Tohf al-Aqool, 1404 AH, shafi 159; Nahj al-Balagha, Tashihu Sobhi Saleh, 1414 AH, huduba 193, shafi na 303.
  12. Kulayni, Kafi, 1407 BC, juzu'i 2, 226.
  13. Karajki, Kanz al-Fawa'id, 1410 AH, juzu'i na 1, shafi na 89.
  14. Nahj al-Balagha,Tashihu Subhi Saleh, 1414 AH, Huduba 193, shafi na 306.
  15. Motahhari, Majmueh Athars na Shahid Motahhari, 1372 AH, juzu'i na 16, shafi na 360.
  16. Iqbali, da Mehwish Hassanpour, “Nahahi sabakshnasanah bi Kutbeh muttaqin,” shafi na 125-126.
  17. Makarem Shirazi, Payam Imam (a.s), 1386 AH, juzu'i na 7, shafi na 528-529; Shafi’i, Imam Shanasi, 1397H, shafi na 144.
  18. Nahj al-Balagha, Tashihu Subhi Saleh, 1414 AH, huduba 193, shafi na 303-306.
  19. Ostadi, “Barsi tadbiki matane Kutbeh Muttaqin (Hammam)manabi mutaqaddim”, shafi na 117.
  20. Shafi’i, Imam Shanasi, 1397H, shafi na 145.
  21. Makarem Shirazi, Payam Imam, 1386H, juzu'i na 7, shafi na 527.
  22. Misbah Yazdi, “Semai Perhizkaran dar kutbae Muttaqin Amirul Muminin (a.s),” shafi na 6.
  23. Don ganin tushen wannan huduba, duba: Dashti, Madariku Nahj al-Balagha, 1378, shafi 251-253; Ostadi, "Shanasayi Guyande Kutbeh Mashhur be muttaqin", shafi na 118-120.
  24. Kulayni, Kafi, 1407 BC, juzu'i na 2, 224-230.
  25. Ibn Hammam Iskafi, Al-Tahmhis, 1404 BC, shafi na 70-73.
  26. Ibn Shu`bah Harrani, Tuhaf al-Uqul, 1404 BC, shafi na 159-162.
  27. Sheikh Saduq, Al-Amali, 1376H, shafi na 570-574.
  28. Karajki, Kanz al-Fawaid, 1410 BC, juzu'i na 1, shafi na 89-92.
  29. Fattal Nayshaburi, Rawdat al-Wa’izin, 1375 AH, juzu’i na 2, shafi na 438-439.
  30. Ustadi, “Barsi Tadbiki matane kutbeh Muttaqin (Hammam)dar manabi mutaqaddim,” shafi na 140.
  31. Ustadi, “Barsi Tadbiki matane kutbeh Muttaqin (Hammam)dar manabi mutaqaddim,” shafi na 14
  32. Ustadi, “Shanasayee Gowindeh, Mashhur beh muttaqin,” shafi na 44-48.
  33. Alawi, Sharhin Kutbeh Muttaqin dar Nahj al-Balagha, 1371H, shafi na 21.

Nassoshi

  • Fatal Nishabouri, Muhammad bin Ahmad, Rawda al-Wa'zin da Basira al-Mu'ta'zin, Kum, Razi Publications, 1375.
  • Ibn Hammam Askafi, Muhammad, al-Tamhis, Qum, mazhabar Imam Mahdi (a.s), 1404H.
  • Ibn Shuba Harrani, Hasan bin Ali, Tohf al-Uqoolan Ale -Rasul (SAW), Qum, Islamic Publications Office, 1404H.
  • Karajki, Muhammad bin Ali, Kanz al-Fawadee, Qum, Dar al-Zakhaer, 1410H.
  • Kilini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Darul-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Majlisi, Mohammad Taqi, Sharh Khutbah Mutaqin (Sharh Hadith Hammam), proofread by: Joya Jahanbakhsh, Tehran, Asatir, 2005.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Ladubban Musulunci a Nahj al-Balaghe, Qom, Zaman Matasa, 1385.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Sakon Imam Amirul Momineen (AS), Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 2006.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, "Siffar Masu Taqawa a Wa'azin Amirul Muminin (AS)", a cikin Mujallar Marafet, lamba 217, Disamba 2014.
  • Mohammadi, Seyyed Kazem, Dashti, Mohammad, Al-Mu'ajm Al-Mufars Lalfaz Nahj al-Balagheh, Kum, Imam Ali (a.s.), 1369.
  • Motahari, Morteza, Shahid Motahari tarin ayyuka, Tehran, Sadra, 1372.
  • Sayyed Razi, Muhammad bin Hossein, Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Kum, Hijira, 1414 H.
  • Shafi'i, Mohammad Hassan, Imamology, Qum, Gadar Annabci, 1397.
  • Sheikh Sadouq, Mohammad Bin Ali, Amali, Tehran, Kitabchi, 1376.
  • استادی، کاظم، «بررسی تطبیقی متن خطبۀ متقین (همام) در منابع متقدم»، در مجله معارف اهل‌بیت(ع)، شماره ۲، تابستان ۱۴۰۱ش.
  • استادی، کاظم، «شناسایی گوینده خطبه مشهور به متقین»، در مجله مطالعات ادبیات شیعی، شماره ۲، بهار ۱۴۰۱ش.
  • اقبالی، و مهوش حسن‌پور، «نگاهی سبک‌شناسانه به خطبۀ متقین»، در مجله پژوهش‌های نهج البلاغه، شماره ۱۴، تابستان ۱۳۹۵ش.
  • دشتی، محمد، اسناد و مدارک نهج البلاغه، قم، مؤسسه فرهنگی تحقیقاتی امیر‌المؤمنین(ع)، ۱۳۷۸ش.
  • سلیمانی رحیمی، امیر، «نامگذاری خطبه‌های نهج البلاغه؛ یک پیشنهاد»، در مجله مشکات، شماره ۶۸ و ۶۹، پاییز و زمستان ۱۳۷۹ش.
  • هوشیار، یاسر، و جلیل تجلیل، «بررسی تطبیقی سیمانی انسان کامل در خطبۀ متقین نهج البلاغه و آثار عزیز‌الدین نسفی»، در مجله پژوهش‌های نهج البلاغه، شماره ۴۶، پاییز ۱۳۹۴ش
  • Alavi, Seyyed Mojtabi, Sharhin Khudubar Taqawa a cikin Nahj al-Balagheh, Qom, Hijira, 1371..