Gidan Imam Ali (A.S) A Garin Kufa

Daga wikishia
Hotan Gidan Imam Ali (A.S) da yake a garin Kufa

Gidan Imam Ali (A.S) a garin Kufa, (arabic: بيت الإمام علي (ع) في الكوفة) wani wuri ne da ake danganta shi ga Imam Ali (A.S) wanda ya shahara da cewa a wannan gida ne ya zauna a lokacin halifancinsa, wannan gida yana zawiyyar kudu maso yammacin masallacin Kufa wanda yake manne da jikin Darul Imaratu Kufa, game da ginin cikin gida wanda ya ƙunshi ɗakuna da wurare da aka danganta su gare shi da ƴaƴansa, wurin wankansa, akwai riwayoyi sai da sun samu suka daga ɓangaren Malamai masu dandaƙe bincike kan hadisi da tarihi.

Gabatarwa

Gidan Imam Ali (A.S) yana zawiyyar kudu maso yammacin masallacin Kufa wanda ya kasance haɗe da jikin Darul Imaratul Kufa [1] wannan gida an sake gina shi a lokuta da daman gaske, na ƙarshe-ƙarshe ya faru bayan faɗuwar gwamnatin Saddam. [2] Cikin gidan akwai ɗakuna da wasu wurare da ake danganta su ga Imam Ali (A.S) da ƴaƴansa, [3] a hannun dama na shigowa gidan, akwai ɗakin Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) a hannun hagu kuma akwai wurin wankan Imam Ali (A.S) da inda yake sallah, [4] haka kuma akwai wasu ɗakunan daban da ake danganta su ga Hazrat Zainab (S) da Ummu Kulsum da Ummul Banin. [5] A ƙarshen gida akwai wata rijiya wacce ake cewa Imam Ali (A.S) ne da hannunsa ya haƙata, masu ziyara suna shan ruwan wannan rijiya domin neman albarka. [6]

Kokwanto Dangane Da Ingancin Wannan Gidan

Wasu ba’arin Masu bincike da nazari sun nunma shakkunsu da kokwanto dangane da ingancin danganta wannan gida zuwa ga Imam Ali (A.S), [7] daga jumla duk da cewa cibiyar hukuma da gwamnatin Imam Ali (A.S) a ƙarshe-ƙarshen rayuwarsa ta kasance a Kufa, [8] amma dangane da mahallin da ya zauna ya rayu akwai saɓanin ra’oyin Malamai, [9] duk da cewa wannan gida da yake a yanzu ya shahara da cewa shi ne gidan da Imam Ali (A.S) ya zauna a cikinsa. [10] a gefe guda kuma wannan gida an sabunta gininsa lokuta da daman gaske na ƙarshe-ƙarshe shi ne wanda aka yi bayan faɗuwar gwamnatin Saddam Husaini, wanda hakan yana haifar da kokwanto mai yawan gaske. [11] Haka kuma tare da duba da imanin ƴan Shi’a wand aya ginu kan cewa Hassan da Husaini (A.S) da Imam Ali (A.S) sun kasance suna tare da ilmin Ladunni (ilmi daga Allah) ba sa buƙatar koyan karatu, saboda haka keɓantar da wani wuri da sunan makarantarsu ba ya dacewa da hankali. [12] ko kuma cewa ma’anar dai wannan makaranta shi ne wurin aiki da koyarwa, [13] ba zai samu karɓuwa ba saboda asalin gidan gida ne ɗan ƙarami ba zai yiwu ace an samar da wurin aiki da ko ofishi ba. [14] An kuma lura cewa Imam Hasan (A.S) da Imam Husaini (a.s.) sun kasance masu cin gashin kansu a zamanin mulkin mahaifinsu a Kufa, kuma samun irin wannan makaranta a gidan mahaifinsu ba zai yiwu ba. [15]

Bayanin kula

  1. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 128.
  2. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 129.
  3. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 128.
  4. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 129.
  5. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 129.
  6. Faƙih Bahrul Uloom, Ziyaratgaheye Iraki, 1395, juzu'i na 1, shafi na 129.
  7. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟
  8. Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 259-260.
  9. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟
  10. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">«آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟
  11. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟
  12. Makarem Shirazi, Payam ƙur'an, 1386, juzu'i na 9, shafi na 115-119.
  13. Dehkhoda,LuggatNamehe, Zailu Wajeh Maktab
  14. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟
  15. class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟

Nassoshi

  • class="eɗternal teɗt" href="https://hajj.ir/fa/7544/">آیا خانه منسوب به امام علی در کوفه واقعیت دارد؟</a>
  • Faƙih Bahrul Uloom, Mohammad Mahdi, Ziyaratgahaye Irak, Tehran, Mawallafin Mashaar, 1395.
  • Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed Al-Tanzil liƙawa'idil al-Tafadel, bincike da Mohammad Baƙer Behboodi, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Buga Buga Jagoran Musulunci, 1369.
  • Masoudi, Abdul Hadi, "Wada'u wa Naƙallil Hadis", Tehran, Samit Publications, 2009.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Moruj Al-Dahahab wa Ma'aden Al-Jawhar, Bija, Dar al-Hijrah Publications, 1409 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Al-Arshad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, ƙum, Sheikh Mofid Congress, bugu na farko, 1413H.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Al-Amali, Beirut, Al-Alami Press Institute, 2009.
  • Ibn Maghazali, Ali bin Muhammad Wasiti, Manaƙib Amir Al-Mu’minin, wanda Abi Abdul Rahman Turki bin Abdullah al-Wada’i ya yi bincike, Sana’a, Darl Atar, 2003 miladiyya.