Sajjad

Daga wikishia
Wannan Kasida ce kan lakabin Sajjad . Don neman bayani kan Imamin Shi'a na hudu, duba Imam Sajjad (A.S)
File:قطعه خوشنویسی یا سجاد.jpg
Tambarin "Ya Sajjad" (wanda aka rubuta a 1439 AH), a cikin rubutun Tholt, na Mohammad Al-Mushrafavi.[1]

Sajjad (Larabci: السجاد (لقب)) ma’ana mai yawan Sujjada [2] yana daga cikin mafi shaharar Lakubban Imam Zainul-Abidin (A.S) [3] Imami na hudu cikin jerin Imam Shi’a, an kira shi da Sajjad sakamakon yawan ibada da mika zuciya ga Allah [4] Ka asasin wata riwaya daga Imam Muhammad Bakir (A.S) da ta zo a cikin littafin Ilalu sharayi Imam Sajjada (A.S) ya kasance yana sujjada a wurare kamar haka: idan ya tuna wata ni’ima da Allah ya yi masa, idan aka karanta ayar da ake sujjada sakamakon karantata, idan Allah ya tsallakar da shi daga wani bala’i, idan Allah ya nesanta shi daga Makircin Makirai, bayan Sallah da lokacin da ya samu wani taufiki yin sulhu tsakanin Mutane biyu, a baki dayan gabban Sujjadarsa akwai alamar Sujjada, saboda haka ne ma ake kiransa da sunan Sajjad [5] Ibn Hammad Mawakin Shi’a wanda ya rayu a karni na hudu hijiri Kamari, ya rera waka dangane da yawan Ibada da yawan Sujjadar Imam Sajjad (A.S)

و راهب أهل البیت کان و لم یزل یلقّب بالسجاد حسن تعبد

یقضی بطول الصوم طول نهاره منیباً و یفنی لیله بتهجّد

فأین به من علمه و وفائه و أین به من نسکه و تعبّد

Zahidi Mai tsantseni daga Ahlil-Baiti ya kasance kuma bai gushe ba. Ana masa Lakabi da Sajjad sakamakon yawan Ibada da Ihsaninsa. Ya kasance yana karar da yininsa yana Azumi yana mai komawa ga Allah da dare kuma ya shagaltu da Tahajjudi. Wane ne Kwatankwacinsa cikin iliminsa da cika alkawari. Wane ne misalinsa cikin Ibada da addu’a.

Bayanin kula

  1. یا سجاد»
  2. Khanji, Wasila Alkhadim, 1375, p. 182.
  3. Quraishi, Hayatu Imam Zain al-Abdeen (AS), 1413Q, vol. 1, p.
  4. Quraishi, Hayat Al-Imam Zain al-Abidin (a.s.), 1413 AH, vol.1, pp. 38 and 40.
  5. Sadouq, Ilalu Sharayi, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 233.

Nassoshi

  • Ibn Shahrashob, al-Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 4, shafi na 152.*Ibn Shahr Ashub, Muhammad Bin Ali, Menaqib Al Abi Talib, Kum, Allameh, 1379H.
  • Jazairi, Sayyid Nematullah, Riyadh Al-Abrar, Beirut, Al-Tarikh Al-Arabi Foundation, 1427H.
  • Khanji, Fazullah Roozbehan, Wasila Alkhadim zuwa Al Makhdoom a cikin bayanin falalar bayin Allah goma sha hudu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, Qum, Ansari, 1375.
  • Sadooq, Muhammad bin Ali, Ilalu sharayi, Najaf, Al-Maktab Al-Haydariyya, 1385H.
  • «یا سجاد» Shafi na Mohammad Al-Mushrafavi akan Pintres, ziyarar kwanan wata: Yuni 26, 1401 AH.
  • Qureshi, Baqer Sharif, Hayat al-Imam Zain al-Abidin, Beirut, Darul-Azwa, 1409H.</ref>