Sarallahi (Lakabi)
Sarallahi (Larabci: ثار الله) ma’ana jinin Allah, ɗaya daga laƙubban Imam Husaini (A.S) da ya zo cikin Ziyaratu Ashura da aka yi masa sallama da shi, akwai mabambantan fassarori da aka yi bayaninsu kan ma’anar Sarallahi, daga jumlarsu akwai masu ɗaukar a fansar jini tafarkin Allah.
Laƙabin Imam Husaini (A.S)
Wata gaɓa daga Ziyaratu Ashura:
السَّلاَمُ عَلَیكَ یا ثَارَ اللهِ وَ ابْنَ ثَارِهِ Amincin Allah ya tabbata a gareka ya jinin Allah ɗan jininsa.
Sarallahi ɗaya ne daga laƙubban Imam Husaini (A.S) cikin ba’arin matanan litattafan riwaya daga jumlarsu Ziyaratu Ashura an yi sallama ga Imam Husaini (A.S) cikin taken Sarallahi. [2] a cewar Allama Majlisi a cikin ba’arin wasu kwafin littafin Alkafi [3] an yi amfani da Kalmar “Sa’irullahi”. [4] Sarallahi ya zo cikin daɗaɗɗun waƙoƙin mawaƙa, alal misali Ibn Rumi, Mawaƙin Shi’a wanda ya rasu shekara ta 283 h ƙamari, cikin ƙasidar da ya rera kan makokin Yahaya Bn Umar, ya yi amfani da Kalmar sarallahi, [5] Yahaya Bn Umar ɗaya ne daga jikokin Imam Husaini (A.S) da ya yi fito na fito kan Almuntasir halifan Abbasiyawa, [6]
Ma’ana
Saru an ciro wannan kalma ne daga Sa’aru da take bada ma’anar neman fansar jinin wanda aka kashe, [7] da kuma jini [8] a cikin ba’arin riwayoyi bayan ishara kan kasancewar Imam Husaini ‘Sarallahi Fil Arzi” a bayyana shi matsayin wanda Allah zai nemi fansar jininsa, mutane za su yi kira kan neman fansar jininsa, [9] a cewar Allama Majlisi abin da ake nufi daga Sarallahi shi ne cewa Imam Husaini (A.S) ne da kansa a zamanin Raja’a zai nemi fansar jininsa da na iyalansa. [10]
Fuskoki Biyar
Abu Alfazle Tehrani cikin littafin Shifa’ul As-Suduri wanda ya rubuta sharhi kan Ziyaratu Ashura, ya kawo fuskoki biyar game da ma’anar Sarallahi: 1-kalmar Sarallahi a asali ta kasance “Ahlu Sarallahi”, kan wannan asasi tana da ma’anar mutumin da ya cancanci Allah ya nemi fansar jininsa. 2-wanda aka kashe wanda Allah ne zai nemi fansar jininsa. 3-kalmar Sarallahi a asali ta kasance “Al-Sa’iru lillahi” wacce an samu kuskure ne cikin dawwanata a littafai, kan haka zai zamana tana da ma’anar mutumin da yake neman fansar jini cikin tafarkin Allah. 4-Sarallahi misalin Ainullahi (Idon Allah) da (Yadullahi) hannun Allah take, wacce a ma’anarta ta haƙiƙa ba a nufin jinin Allah a haƙiƙa, bari dai misalin sifface ta Khabar da aka yi amfani da ita cikin ma’ana ta majazi ba ta haƙiƙa ba. 5-Sar da ma’anar jinin da aka nemi fansarsa, sannan jingina Kalmar da Allah ya kasance ne ta fuskar kasancewa a haƙiƙa Allah ne Waliyin wannan jini. [11] Tehrani ya danganta fassara ta farko zuwa ga Allama Majlisi, [12] fassara ta biyu zuwa ga Zamakshari malamin tafsiri na Ahlus-sunna, ma’ana ta uku zuwa ga ɗuraihi marubucin littafin Majma’ul Al-Bahraini, [13] sannan ya karɓi ma’ana ta biyar, sai dai cewa bai danganta ma’ana ta huɗu ga kowa ba, kuma ya nesanta yiwuwar fassara ta huɗu. [14]
Fahimta Ta Zamantakewa
Ali Shariati, ma’abocin sabuwar nazariya, ya kafa alaka tsakanin Sarallhi da nazariyar Saura da gado. A cewarsa sarallahi yana fassara falsafar tarihin dan Adam; Domin kuwa duk rayuwar mutum tun daga Adamu har zuwa ƙarshen zamani ta kasance ne domin neman fansar jinin Habila, wadda take ta zazzagawa daga tsatso zuwa tsatso kuma a cikin wannan zub da jini, an sake zubar da jinin Imam Husaini (A.S), wanda ya kasance salsala kewayan da'ira tun daga Adamu har zuwa ƙarshen duniya magajin wannan jini ne wanda shi kansa Imam Husaini (A.S) ya fito ne da sunan mai neman fansar jinni. [15]
Ayatullahi Jawadi Amoli:
Muna rokon Allah ya bamu damar karbar fansar jinin Hussaini bn Ali (a.s), domin mu 'ya'yan Imam Husaini (a.s) ne, don me? Domin kasancewar Annabi (s.a.w) mai albarka ya bayyana karara cewa: “Ni da Ali uban wannan al’umma ne.” “Ni da Ali ubanni biyu ne na wannan al’umma”. Wannan shi ne sakon Ashura, ba magana ce a kan imamanci da al’umma ba, a’a magana ce na uba da ‘ya’ya, hasali ma shi’a `ya`yan Husaini bin Ali (a.s) ne. Ashura makaranta ce a gare mu ta al’adu da ilimi, kuma mu da muka zama ‘yan Shi’a muka samu wannan takardar shaida muka karba muka zama ‘ya’yan Annabi, Ali da Husaini (s.a.w). Saboda haka, muna neman fansar jininsu.
https://javadi.esra.ir/fa/w/شیعه،-فرزند-حسین-بن-علی-ع-است-و-باید-خونبهای-او-را-ب
Kufaifayi Da Suke Da Alaƙa
Ali Akbar Bn Muhammad Amin Lari, ya rubuta wata Risala a ƙarni na goma sha uku h ƙamari, da sunan Sharhu Hadisi “Ya Sarallahi” asalin maudu’in wannan littafi shi ne tabbatar da tsarkin jinin Imamai, cikin wannan Risala tasa ya kawo bahasi kan Isma, [16] lambar rubutun wannan Risala shi ne lamba 4086 a cikin laburaren (Kitabkhune Ayatullahi Mar'ashi Najafi). [17]
Bayanin kula
- ↑ Ibn ƙolwieh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 176.
- ↑ Misali, duba Ibn ƙolwieh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 176, 195, 196, 199; Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 576.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 576.
- ↑ Majlesi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 154-155.
- ↑ Ibn Rumi, Diwan, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 27,be naƙali az Daneshnameh Jahan Islam, Madkhal Tharullah.
- ↑ Abolfaraj Esfahani, Muƙatil Al-Talbeyin, Dar al-Marifah, shafi na 506.
- ↑ Farahidi, Al-Ain, 1410 AH, Juzu'i na 8, shafi na 236 (Thar kayan)
- ↑ Zubeidi, Taj al-Arus, 1414 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 138.
- ↑ Ibn ƙolwieh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 218.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 151.
- ↑ Tehrani, Shifa al-Sodor, 1376, shafi na 163-164.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 151; Majlisi, Mir'atul Al-Uƙool, 1404H, juzu'i na 18, shafi na 298.
- ↑ Tareehi, Majma Al-Bahraini, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 234-235
- ↑ Tehrani, Shifa'u Al-Sudor, shafi na 163-165.
- ↑ Shariati, Hossein Waris Adam, 2013, shafi na 95-106.
- ↑ Hosseini Ashkuri, Fihrisat Nuskhehaye khaɗɗi Kitabkhune Umumi Hazrat Ayatullahi Uzma Mar'ashi Najafi,1376-1354, juzu'i na 11, shafi na 100-99, an nakalto daga littafin jahan-e-Islam, shigarwar Thar Allah.
- ↑ “Ma'akazshinasi Zioyatart Ashura, farhang Kausar, Zaminstan, 2016, No. 72, aka nakalto daga Jahan Islam Encyclopaedia of Thar Allah.
Nassoshi
- Ibn ƙolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel Al-Ziyarat, revised by: Abdul Hossein Amini, Najaf, Dar al-Mortazawieh, 1356.
- Ibn Rumi, Ali bin Abbas, Diwan, bugun Abdul Amir Ali Mehna, Beirut 1411H/1991 Miladiyya.
- Abol Faraj Esfahani, Muƙatil Al-Talbeyin, Bincike na Seyyed Ahmad Saƙr, Beirut, Dar al-Marafa, B.T.A.
- Hosseini Ashkouri, Ahmed,Fihirisat Nuskhehaye Khaɗɗi KItabkhune Hazrat Ayatullahi Mar'ashi Najafi, ƙom, 1376-1354.
- Zubeidi, Seyyed Mohammad Morteza, Taj al-Arus Man Javaher al-ƙamoos, ya gyara shi: Ali Shiri, Beirut, Dar al-Fikr, 1414H.
- Shariati, Ali, Hossein Waris Adam, Tehran, 2013.
- Tarihi, Fakhreddin, Majma Al-Baharin, bugun Seyyed Ahmad Hosseini, Tehran, kantin sayar da littattafai na Mutzawi, 1416H.
- Tehrani, Abulfazl bin Abulƙasem, Shafaal al-Sudor fi Sharh Ziyarat al-Ashur, Tehran, Mortazavi, 1376.
- Farahidi, Khalil bin Ahmad, Kitab al-Ain, Mahdi Makhzoumi da Ibrahim Samarai suka gyara, Kum, Hijira, 1410H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, gyara: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
- Majlisi, Mohammad Baƙir, Beirut, Dar Ahya Al-Trath Al-Arabi, 1403H.
- Majlisi, Mohammad Baƙir, Miryah al-Aƙool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, edited by Seyyed Hashim Rasouli Mahalati, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1404H.