Ha Aliyun Basharun Kaifa Basharun
Ga Ali mutum ne amma wane irin mutum? (Larabci: ها عليٌّ بَشَرٌ کَيْفَ بَشَر ) wani yanki ne na waƙar Gadiriyya wace akayi ta kan Imam Ali (A.S), wanda ya yi waƙar shi ne Mulla Mihir Ali Khuyi ɗaya daga cikin mawaƙain Ghadir a ƙarni na sha uku, wannan ƙasida ta zama dalilin ɗaukakarshi.
Wannan waƙa tana dauke da baituka arba'in, an yi ta ne a shekara ta 1216-1240 bayan Hijira, Mirza Muhammad Riza Basira Shirazi ya fassarata cikin tsarin harshen Farisanci, wakar ta kasance abin sha'awa ga mawaƙa da masu wa'azi na shi'a, waɗanda suka kawo baitikanta a cikin hudubobinsu da wakokinsu.
Waƙar
Wakar, Ha Ali Bashr, wana irin mutum ne, waka ce ta Gadiriya,[1]don yabon Imam Ali (A.S) ta mawakinta Mulla Mihru Ali Attabrizi Al-Khuyi.[2] An ruwaito cewa wannan waƙa ce ta ƙunshi baitika ashirin ko arba’in, an yi ta ne a shekara ta 1216-1240– 1216 Hijira,[3] Farhad Mirza wanda ya yi zamani da Mullah Mihr Ali, ya ambaci wannan waƙa a cikin littafinshi Zanbil.[4]
Wakar ta kasance abin sha'awa ga masu wa'azi da mawakan Shi'a, kuma suna nakalto baitukanta a cikin wakokinsu.[5] Mirza Muhammad Rida Basira Shirazi ya fassara wakar cikin tsarin harshen Farisanci, a kan wazaninta da ƙafiyarta.[6]
Mawaƙin
Mullah Mihr Ali Tabrizi AlKhuyi (1182-1262 hijira) yana ɗaya daga cikin mawaƙan ƙarni na sha uku, ya rubuta wakoki a harsuna uku, Farisa, Turkanci, da Larabci.[7] Ana daukar shi ɗaya daga cikin masana, masu hikima, kuma malami mai yawan sanin ilimomin zamaninshi.[8] Mafi yawan shaharar Mullah Mihru Ali tana komawa ga waƙarshi ta Gadiriyya, kuma yana da wata waƙa a cikin baituka 18 game da falalar Annabi (S.A.W) a harshen Farisanci.[9]
Mafarki Da Annabi
Ya zo a cikin littafin wilayat Name ta Ghadiriya inda ya nakalto daga littafin Ulamaye Mu'asirin, Mulla Ali Wa’izi Kiyabani, cewa ya yi: Bayan Mullah Mihru Ali ya yi wakarsa mai suna Ha Ali Basharun, ya ga Annabi (S.A.W) a mafarki, Imam Ali (A.S) yana tare da shi,[10] Sai Annabi (S.A.W) ya ce wa Mullah Mihru Ali: Karanta mana waƙarka wadda ka yabi dan baffana a cikinta Mullah Mihru Ali ya fara rera ta, bayan gama rera baitin farko, sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: wai Ali wane irin mutum, ya maimaita fadin haka har sau uku.[11]
Bayanin kula
- ↑ Molazadeh, "Tabriri Khoei, Mulla Mehr Ali", shafi na 426.
- ↑ Mujahidi, Siri Dar Qalamru, Shi'iru Nabawi, 1387 AH, shafi 698; Malazadeh, “Tabarri Khoyi, Malamehr Ali”, shafi na 425 da 426.
- ↑ Fadwa Khoei, Velaytanama (Ghadiriya), 1376 AH, shafi na 28 da 29; Malazadeh, “Tabarri Khoyi, Malamehr Ali,” shafi na 426.
- ↑ Farhad Mirza, Zanbil, 1367 AH, shafi na 70-72.
- ↑ Malazadeh, “Tabarri Khoyi, Mullla mehr Ali,” shafi na 426; Fadwi Khoei, Velayat namah (Ghadiriyah), 1376 AH, shafi na 28. Don neman sani kan waqoqin: Fadwa Khoei, Velayat namah (Ghadiriyah), 1376 AH, shafi na 37-61.
- ↑ Fadwa Khoi, Velayta nama (Ghadiriya), 1376 AH, shafi 27; Malazadeh, “Tabarri Khoyi, Mulla mehr Ali,” shafi na 426.
- ↑ Farhad Mirza, Zanbil, 1367 AH, shafi 70; Mujahidi, Sairi Dar Qalamru, Shi'iru Nabawi, 1387 AH, shafi 698; Mullla zadeh, “Tabarri Khoyi, Mulla mehr Ali”, shafi na 425 da 426.
- ↑ Mujahideen, Sairi Dar Qalamru, Shi'iri Nabawi, 1387H, shafi 698.
- ↑ Mulla zadeh, “Tabarri Khoyi, Mulla mehri Ali,” shafi na 425 da 426; Mujahideen, Ssiri Dar Qalamru, Shi'iru Nabawi, 1387 AH, shafi na 698-700.
- ↑ Fadwa Khoei, Velaytanama (Ghadiriya), 1376 AH, shafi na 27 da 28.
- ↑ Fadwa Khoei, Velaytanama (Ghadiriya), 1376 AH, shafi na 27 da 28.
Nassoshi
- Fadwi Khoei, Mullah Mar Ali, Wilayat Name (Ghadiriyah), Research and Arrangement by Ali Sadraei Khoei, Qom, Ansarian, First Edition, 1997 AH.
- Farhad Mirza, Motamdaldoleh, Zanbil, Tehran, Padideh, second edition, 1988.
- Mujahedi, Mohammad Ali, Siri Dar Qalsmaru Shi'iru Nabawi, Qom, Al-Alami al-Ahl al-Bayt (AS), first edition, 2008.
- ملازاده، محمدهانی، «تبریری خویی، ملامهرعلی»، در دانشنامه جهان اسلام، ج6، طهران، بنیاد دایرة المعارف اسلامی، الطبعة الثانية، 1388 ش.