Jump to content

Ƙasiɗin

Daga wikishia

Ƙasiɗin, (Larabci: القاسطين) ma'ana gungun ƙungiyar azzalumai,[1] magana kan Mu'awiya da mutanensa bayan Imam Ali (A.S) ya zama halifa, waɗanda suka ƙi yarda su yi masa bai'a, lamarin da ya jawo yaƙin Siffin.[2]

Bisa naƙali daga litattafan tarihi, bayan musulmi sun yi bai'a ga Imam Ali (A.S),[3] Mu'awiya wanda Imam Ali (A.S) ya cire daga gwamnan Sham,[4] ya ƙi yi wa Imam Ali (A.S) bai'a, sannan ya fake da uzurin neman fansar jinin Usman matsayin dalili na haifar da yaƙin Siffin.[5] Bisa rahotannin tarihi, lokacin da sojojin Mu'awiya suke daf da shan kaye a yaƙin Siffin, tare da makircin Amru Bin Asi sai suka soke Kur'ani kan tsinin masu suka ɗaɗɗaga shi sama, da wannan dabara ce suka samu nasarar yaudarar sojojin Imam Ali (A.S) suka buƙaci a dakatar da yaƙi.[6] Imam Ali (A.S) ya jawo hankulan sojojin kan hatsarin wannan dabara ta Amru Bin Asi, sai dai cewa aksarin sojojinsa ba su saurare shi ba, daga ƙarshe sun tilasta masa yarda da tahkim (Sulhu).[7]

Mu'awiya da Amru Bin Asi sune suka kasance jagororin ƙungiyar Ƙasiɗin.[8] A cewar Muhammad Muhammadi Rai Shahri, mabiya Mu'awiya galibinsu sun kasance mutane da ba su da wani tarihi na gabata a Muslunci, kuma ba su samu goyan baya daga Annabi (S.A.W) ba. Bari ma dai wasu daga cikinsu sun ma yaƙi Annabi, kuma sun kasance daga mutanen da ya tsinewa.[9]

Bisa wata riwaya da aka naƙalto a Biharul Al-Anwar, Annabi (S.A.W) ya ba da labari cewa bayansa Imam Ali (A.S) zai yaƙi Nakisin, Ƙasiɗin da Mariƙin.[10] A lokacin da Imam Ali (A.S) ya yi gaba da gaba da sojojin Sham a yaƙin Siffin ya bayyana su matsayin cikakken misali na waɗanda ake kira Ƙasiɗin, ya kuma tabbatar da cewa shi ne mai zartar da umarnin Annabi kan waɗannan mutane.[11]

A cikin Nahjul Balaga, cikin huɗubobi 13 misalin huɗubobin Ƙasi'a da Shiƙshiƙiyya,[12]da kuma wasiƙu guda 17 da ke ƙunshe da batun Ƙasiɗin.[13] Kalmar Ƙasiɗin an yi amfani da ita cikin waƙoƙin Farsi.[14] A cikin Du'a'u Nudba akwai ishara da akayi amfani da wannan game da yaƙin da Imam Ali (A.S) da wannan ƙungiya.[15]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, Lisan al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 7, shafi na 378.
  2. Akhundi da Wasu, Isɗilahat Nizami Dar Fiƙhe Islami, shafi na. 99.
  3. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i. 1, shafi. 230.
  4. Al-Tabari, Tarikhul al-Umam Wa al-Muluk, 1387 H., juzu'i na 4, shafi na 440.
  5. Allameh Amini, Al-Ghadir fi Kitab wa Sunnah wa Adab, 1416 AH, juzu'i. 10, shafi. 440.
  6. Al-Tabari, Tarikh al-Umam Wa al-Muluk, 1387 H., juzu'i na 5, shafi na 48.
  7. Al-Manqari, Waqa'atu Siffin, 1404 AH, shafi. 489.
  8. Mohammadi Rayshahri, Daneshnameh Amirul Muminin (A.S.) Bar Paye Qur'an, Hadis Wa Tarikh, 2007, Mujalladi. 5, shafi na 302-383.
  9. Mohammadi Rayshahri, Daneshnameh Amirul Muminin (A.S.) Bar Paye Qur'an, Hadis Wa Tarikh, 2007, Mujalladi. 5, shafi na 293.
  10. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 30, shafi. 588.
  11. Ibn Atham Kufi, Al-Futuh, 1411H, juzu'i. 3, shafi. 77; Nasr ibn Muzahim, Waqa’atu Siffin, 1382 AH, shafi. 338.
  12. Nahj al-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, Huduba 192, shafi. 300.
  13. Khazali, Nakisin, Ƙasiɗin, Wa Mariƙin Dar Nahjul-Balagha, shafi. 398.
  14. Divan Attar, Ganjur site; Divan Samet Borujerdi, Ganjur site.
  15. Shahidul Awwal, al-Mazar, 1410 Hijiriyya, shafi na. 43; Majlesi, Zad al-Maad, 1423 AH, shafi na 305.

Nassoshi

  • Akhundi, Mustafa da Wasu, Isɗilahate Nizami Dar Fiƙhe Islami, Tehran, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci, Wakilin Jagora, Sashen Rukunan Siyasa da Ilimi, bugun farko, 1378.
  • Ibn Abi al-Hadid, Ezzul-Din Abu Hamid, Sharhu Nahjul al-Balagha, Muhammad Abul-Fadl Ibrahim, Qum, ya inganta shi, Ayatullah Marashi Najafi Public Library, bugun farko, 1404H.
  • Ibn A’tham Kufi, Ahmad Ali, Al-Futuh, Beirut, Darul Adwaa, bugun farko, 1411H.
  • Ibn Manzoor, Muhammad ibn Makram, Lisan al-Arab, Mai bincike: Jamal al-Din Mir Damadi, Beirut, Darul Fikr na Bugawa, Bugawa da Rarraba- Dar Sader, bugu na uku, 1414H.
  • Khazali, Abul-Qasim, Nakisin, 'Ƙasiɗin, Wa Mariƙin Dar Nahjul-Balagha", a cikin tarin kasidu da laccoci a taron Millennium International Congress na Nahjul-Balagha, vol. 1, Bita.
  • «دیوان عطار»،Ganju Site.
  • Sayyid Razi, Muhammad bn Husayn, Nahjul-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, Qum, Hijira, bugun farko, 1414H.
  • Shahidul Awwal, Muhammad bn Makki, Al-Mazar, mai bincike: Muhammad Baqir Movahed Abtahi Isfahani, Qum, Makaranta Imam Mahdi (a.s.), bugu na farko, 1410H.
  • «صامت بروجردی»، Ganju Site.
  • Tabari, Muhammad bn Jarir, Tarihin Al'ummai da Sarakuna, Beirut, Darul-Turaht, bugu na biyu, 1387H.
  • Allamah Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir a cikin Littafin Sunnah da Adabi, Qum, Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Al-Ghadir, bugu na 1, 1416 Hijira.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, mai bincike, kungiyar masu bincike, Beirut, Dar Ihya al-Turaht al-Arab, bugu na biyu, 1403 AH.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Zad al-Ma’ad – Miftah al-Jinan, mai bincike: Ala’addin A’alami, Beirut, Al-A’alami Publishing House, bugu na 1, 1423 AH.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad, Daneshanameh Amirul Muminin (AS) Bar Payae Qur'an, Hadis Wa Tarikh, Mujalladi. 5, Qum, Darul Hadith, bugun farko, 1386H.
  • Nasr bn Muzahim,Waq'atu Siffin, Edited by Abd al-Salam Muhammad Haroon, Qum, Ayatullah al-Mar'ashi al-Najafi Library, bugu na biyu, 1404H.