Aƙilatu Bani Hashim (Laƙabi)

Daga wikishia

Aƙilatu bani hashim, (Larabci: عقيلة بني هاشم) laƙabi ne na Sayyida Zainab (S) ƴar Imam Ali (A.S). kalmar “Aƙilaltu” cikin harshen larabci idan aka yi amfani da ita kan mutane tana da ma'anar babban mutum mai daraja. Cikin mutanensa [1]ba'arin malamai daga jumlarsu Ayatullahi Abdullahi Jawadi Amoli ya tafi kan cewa wannan kalmar ta aƙila siga ce ta mubalaga a harshen larabci da take da ma'anar mutum mai hankali sosai.[2]

Wannan laƙabi bai zobe cikin kutubul arba'a haka cikin Biharul Al-anwar; amma litattafan ada aka wallafa su daga ƙarni na sha huɗu misalin Maƙtale Muƙarram,[3] da Minhajul Al-bara'ati Fi Sharhi Nahjil Al-balaga[4] da Tanƙihul Al-maƙal[5] da zamanin da ya biyo bayan ƙarni na sha huɗu[6] anyi amfani da wannan laƙabi kan Sayyida Zainab, daga cikin sauran laƙubba da ake gaya mata akwai misalin Aƙilatu Bani Hashim Sayyida Zainab (S), Zainabul Kubra Aƙilatu Bani Hashim.[7] wasu lokuta masu huɗuba kan yi amfani da aƙilatu bani hashim maimakon ambaton sunanta na yanka..[8]

Abul Faraj Isfahani ya gabatar da Sayyida Zainab Aƙilatu bani hashim matsayin mahaifiyar Aunu Ɗan Abdullahi Ɗan Jafar, ya naƙalto wannan magana ne daga Ibn Abbas cewa:

«حَدَّثَتْنی عَقیلَتُنا زینب بنتُ علیِّ بنِ ابی‌طالب علیه‌السّلام»

Zainab Aƙilatunmu ƴar Ali Ɗan Abi Ɗalibi amincin Allah ya tabbata a gare shi ta zantar da ni.[9] An ce sakamakon hankali da take da tare da rakiyar Imam Sajjad (A.S) ta jagoranci ayarin fursunonin iyalan Annabi (S.A.W) da aka dinga yawo da su daga karbala zuwa kufa daga kufa zuwa sham daga sham zuwa madina, Sayyida Zainab (S) ta taka muhimmiyar rawa cikin majalisan girmama Imam Husaini (A.S) da kuma tona asirin bani umayya.[10] Sayyid Muhammad Ali Ƙazi Ɗabaɗaba'i (Wafati: 1399. h. ƙ),[11] da Zabihullahi Mahallati (Wafati: 1406. h. ƙ), sun ambaci laƙabi Aƙilatu kan Sayyida Zainab.[12]

Bayanin Kula

  1. A cikin Lisan al-Arab, wutsiyar "aql" ita ce ast: «عَقِیلةُ القومِ: سَیِّدُهم».
  2. «ضرورت بازشناسی شخصیت حضرت زینب کبری(س)»، بنیاد بین‌المللی علوم وحیانی اسراء؛ قزوینی، زینب الکبری من المهد الی اللحد، ۱۴۲۴ق، ص۴۰، پاورقی محقق.
  3. Muqareram, Maktale Al-Husain (AS), 1426 Hijiriyya, shafi na 272 da 290.
  4. Khoei, Minhaj al-Bara'a fi Sharh Nahj al-Balaghah, bugu na 4, juzu'i na 15, shafi na 39.
  5. Mamaqani, Taqnih al-Maqal fi Ilm al-Rijal, babin farko, juzu'i na 3, shafi na 79.
  6. Misali, duba Naqdi, Zainab Al-Kabari, 1362, shafi na 17; Qurashi, Al-Sayyida Zainab, 1422 AH, shafi na 40.
  7. Ansari Qomi, “KItabe shinasi Sayyida Zainab (a.s),” shafi na 169.
  8. برای نمونه نگاه کنید: «مناقب عقیله بنی‌هاشم در کلام اهل بیت(ع)»، خبرگزاری تسنیم؛ «ولادت عقیله بنی هاشم مبارکباد»، دانشگاه علم و صنعت ایران.
  9. Isfahani, Muqatil al-Talibeen, 1385H, shafi na 60.
  10. Isfahani, Muqatil al-Talibeen, 1385H, shafi na 60.
  11. Qazi Tabatabai, Tahkik darbaraye awwale arba'in Hazrat Sayyid Al-Shuhada (amincin Allah ya tabbata a gare shi), 1383H, shafi na 51.
  12. Mahallati, Rayahin Al-Sharia, babi na farko, juzu'i na 3, shafi na 88

Nassoshi

  • Ansari Qomi, Naseruddin, “Kitabeshinasi Hazrat Zainab (AS)”, a cikin Mujallar Shahab Legacy, No. 72 da 73, 1392.
  • Esfahani, Abul Faraj, Muqatil al-Talbiyin, Bincike: Kazem Mozafar, Najaf, Al-Maktab Al-Haydriya, bugu na biyu, 1385H.
  • Khoi, Habibullah, Menhaj al-Baraa'ah fi Sharh Nahj al-Balaghah, bincike: Sayyid Ebrahim Mianji, Mu'assasa Al'adu na Imam Mahdi (AS), bugu na hudu.
  • Mahalati, Zabihullah, Riyahin al-Sharia, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, bugu na farko.
  • Mamqani, Abdullah, bitar al-maqal fi ilm al-rijal, bugu na farko.
  • Mohammadi, Salarwa digaran, Aqilah Bani Hashem: Sayyida Zainab (AS), Qununyar, 1394.
  • Muqram, Abd al-Razzaq, Maktal al-Hussein (a.s.), Beirut, Al-Khursan Institute, 1426H.
  • Qazi Tabatabai, Sayyid Mohammad Ali, Tahkik darbaraye Awwale Arbaeen Hazrat Sayyidul Shuhadah (AS), Tehran, Ministry of Guidance, 2003.
  • Qazvini, Seyyed Mohammad Kazem, Zainab Al-Kubara Min Al-Mahad ila-Lahad, bincike: Sayyid Mustafa Qazvini, Qom, Dar al-Ghadir, bugu na biyu, 1424H.
  • Qureshi, Baqar Sharif, Al-Saidah Zainab, Beirut, Dar Mohjah Al-Bayda wa Dar Al-Rasoul Al-Akram (AS), bugu na farko, 1422H.
  • ولادت عقیله بنی هاشم مبارکباد، وبگاه دانشگاه علم و صنعت ایران، تاریخ بازدید: ۱۷ مرداد ۱۴۰۳ش
  • مناقب عقیله بنی‌هاشم در کلام اهل بیت(ع)»، سایت خبرگزاری تسنیم، تاریخ درج مطلب: ۲۵ بهمن ۱۳۹۴ش، تاریخ بازدید: ۱۷ مرداد ۱۴۰۳ش.
  • «ضرورت بازشناسی شخصیت حضرت زینب کبری(س)»، وبگاه بنیاد بین‌المللی علوم وحیانی اسراء، تاریخ درج مطلب: ۷ بهمن ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۱۷ مرداد ۱۴۰۳ش.
  • نقدی، جعفر، زینب الکبری بنت الامام امیرالمؤمنین علی بن ابی‌طالب(ع)، قم، شریف رضی، ۱۳۶۲ش.

{{end}]