Mubahalar Annabi Tare da Kiristocin Najran

Daga wikishia
Wannan wata ƙasida ce game da labarin mubahala. Domin neman sanin mubahala a cikin kur'ani ku duba mashigar Ayar Mubahala.
Zanen Waki'ar Mubahala da Aka dora shi kan bangon littafin Asarul Al-bakiya na Abu Raihan Biruni

Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da kiristocin najran,(Larabci: وَاقِعَة المُباهلة) ɗaya ne daga abubuwa da suka faru a farko-farkon muslunci da yake nuni zuwa ga gaskiyar da'awar Annabi (S.A.W), haka kuma wannan waƙi'a tana shiryarwa kan falalar Annabi (S.A.W) da yan rakiyarsa ma'ana Imam Ali (A.S), Faɗima (S), Hassan (A.S) da Husaini (A.S). Aya ta 61 suratul alu Imran ta yi magana game da waƙi'ar mubahala haka nan wannan aya ta shahara da ayar mubahala.

ƴan shi'a sun yi amanna cewa a cikin wannan Imam Ali (A.S) ya kasance a matsayin nafsu wanda yake misalta Annabi (S.A.W) da ransa, da wannan dalili ne ake lissafa wannan aya ɗaya daga cikin falalolin Imam Ali (A.S). an naƙalto wannan waƙi'a cikin madogaran shi'a da ahlus-sunna. Kan asasin abin da ya zo daga madogarai, Annabi (S.A.W) bayan gama munazara tare da kiristocin najran da ƙin yin Imani da suka yi, sai ya bada shawarar yin mubahala sai suka karɓi wannan shawara ta sa, sai dai cewa kuma ranar da aka yi alƙawarin yin mubahalar lokacin da kiristocin najran suka ga mutanen da Annabi (S.A.W) da su daga iyalansa, sai suka gudu basu tsaya an yi mubahalar ba, ma'anar mubahala shi ne a nemi Allah ya saukar da tsinuwarsa kan maƙaryaci domin tabbatar da gaskiyar mai gaskiya daga ɓangarori biyu masu jayayya da juna da ko wane ɗaya cikinsu yana da'awar shi ne a kan gaskiya.

Akwai mabambantan maganganu game da shekara da ranar da wannan waƙi'a ta faru. Mashhur marubutan tarihi sun tabbatar da cewa ta faru ne shekara 10 hijira ƙamari. Haka nan cikin litattafan addu'a an keɓance wasu ayyuka a ranar 24 ga watan zil hijja matsayin ranar da aka yi mubahala tsakanin Annabi (S.A.W) da kiristocin najran. An yi rubuce-rubuce da ayyukan fasaha daga jumlarsu akwai zanen da aka ɗora shi kan bangon kwafin littafin Asarul Al-baƙiyya na Abu Raihan Biruni wanda aka rubuta shi shekara 707 hijira ƙamari.

Matsayi Da Muhimmanci

Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da kiristocin najran ta kasance cikin abubuwa da ake jingina da su kan tabbatar da gaskiyar da'awar Annabin muslunci (S.A.W).[1] kur'an a cikin suratul alu Imran an yi ishara da wannan batu.[2] haka nan wannan waƙi'a ana lissafa ta cikin falalolin mutane biyar daga Annabi (S.A.W), Ali (A.S), Faɗima (S), Hassan (A.S) da Husaini (A.S).[3] an yi maganar wannan batu cikin madogaran tafsiri[4] da tarihi.[5] an yi rubuce-rubuce da ayyukan fasaha game da wannan waƙi'a.[akwai buƙatar kawo madogara]

Shahin Waƙi'ar

Bishop na Kiristocin Najran A Cikin labarin Mubahla:
Da Muhammad \ba ya kan gaskiya ba zai fito da rakiyar mutane mafi daraja a wurinsa ba, idan muka yi mubahala da shi kafin shekara ta zagayo babu wani kirista guda daya da zai rage a doran kasa. a wata riwayar, ina ganin wasu fuskoki wadanda da za su roki Allah ciratar da dutse daga matsuguninsa lallai zai cirata shi, kuma kuma duk wani addini zai gushe. yanzu za ku yarda ku yi mubahalar halaka kawukanku, babu wani kirista da zai rage a duniya.

Source: Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407-1416 AH, shafi na 368-369.

Annabin muslunci (S.A.W) daidai lokacin da yake rubuta wasiƙu zuwa ga sarakunan hukumomin duniya, ya rubuta wasiƙa zuwa ga babban pasto malamin kiristocin najran tare da kiran mazauna najran zuwa addinin muslunci. Wasu jama'a daga wakilan sun zo madina sun tattauna da Annabi (S.A.W) a masallacin annabi da yake a madina, Annabi cikin gabatar da kansa ya ambaci Sayyidina Isa Almasihu (A.S) da sunan bawan Allah, sai dai cewa waɗannan wakilai na kiristocin najran ba su yarda a kira Isa Almasihu da bawan Allah ba, suna masu Imani da cewa haihuwarsa ba tare da uba ba dalili ne kan allantakarsa.[6]

Bayan kowanne ɓangare ya kafe kan cewa lallai shi ne ke kan gaskiya, sai aka yanke shawara kan wannan batu cikin zaɓar hanyar mubahala domin kawo ƙarshen wannan jayayya[Tsokaci 1] da wannan dalili ne aka cimma yarjejeniya da cewa washegarin wannan rana bakiɗaya za a fita wajen garin madina a je sahara domin shirin yin mubahala, safiyar ranar mubahala, Annabi (S.A.W) tare da rakiyar Imam Ali (A.S), Faɗima (S), Hassan (A.S) da Husaini (A.S) sun fita daga garin madina. Lokacin da kiristocin najran suka ga Annabi ya fito tare da rakiyar mafi darajar mutane a wurinsa sun tsuguna kan gwiwowinsu kamar misalin Annabawa suna shirin mubahala, sai suka janya daga yin mubahalar suka gudu, suka roƙe shi da ayi tattaunawar sulhu a kyale batun mubahala, sai Annabi (S.A.W) ya yarda amma da sharaɗin za su bada jizya. Bayan dawowar kiristocin najran garin najran sai manyan mutane guda biyu daga cikinsu suka zo wurin Annabi tare da kawo masa hadayoyi suka kuma muslunta.[7] Fakhrur Razi malamin tafsiri na ahlus-sunna (Wafati: 606. h. ƙ), an ce malaman tafsiri da malaman hadisi sun yi ittifaƙi kan faruwar wannan waƙi'a.[8]

Kyakkyawan rubutun ayar mubahala (فَمَنْ حَاجَّكَ فِیهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل‌لَّعْنَتَ اللَّـهِ عَلَی الْكَاذِبِینَ)

Ayar Mubahala

Tushen ƙasida: Ayar Mubahala

فَمَنْ حَاجَّكَ فِیهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَ أَبْنَاءَكُمْ وَ نِسَاءَنَا وَ نِسَاءَكُمْ وَ أَنفُسَنَا وَ أَنفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَتَ اللَّـهِ عَلَی الْكَاذِبِینَ﴿۶۱﴾ ﴿۶۱
Saboda Haka duk wanda ya yi jayayya da kai bayan abin da ya zo maka daga ilimi ka ce mu ku zo mu mu kira `ya`yanmu da `ya`yanku da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku, sannan mu yi addu'a da magiya Allah ya saukar da tsinuwarsa kan makaryata..



'


Ayar mubahala aya ce ta 61 suratul alu Imran da take ishara kan waƙi'ar mubahala: A cewar Ƙazi Nurullahu Shushtari, malaman tafsiri sun yi ittifaƙi cewa kalmar «ابنائَنا» (ƴaƴanmu) da ta zo cikin ayar mubahala tana ishara ne zuwa ga Hassan da Husaini, haka «نسائَنا» ishara ce ga Faɗima (S) da kuma «اَنفُسَنا» ishara ce ga Imam Ali (A.S).[9] haka nan Allama Majlisi ya yi Imani da cewa hadisai da suke nuni shiryarwa kan cewa wannan aya ta sauka ne kan ma'abota abaya hadisai ne matawatirai.[10] cikin littafin Ihƙaƙul Al-haƙƙi (Rubutawa: 1014. h. ƙ), ya ambaci madogara kusan guda 60 daga madogaran ahlus-sunna da suka kawo bayani ƙarara a fili kan cewa ayar mubahala ta sauka ne kan mutane biyar ma'ana ma'abota bargo.[11] Imaman shi'a[12] da ba'arin sahabban Annabi[13] su ma sun dogara da wannan waƙi'a kan tabbatar da falalolin Imam Ali (A.S).

Wuri Da Lokaci

Bisa dogara da madogaran tarihim waƙi'ar mubahala ta faru ne bayan hijirar Annabi zuwa madina;[14] amma game da wace rana da shekara ce ta faru akwai mabambantan maganganu. Shaik Mufid (Wafati: 413. h. ƙ) ya tafi kan cewa wannan waƙi'a ta faru bayan fatahu makka shekara 8 bayan hijira.[15] cikin Tarikh Ɗabari (Rubatawa: 303. h. ƙ) ya ambaci cewa ta faru ne a shakera ta 10 hijira ƙamari.[16] a cewar Muhammad Muhammadi Rai Shahari (Wafati: 1401. h. shamsi) a cikin littafin Farhange Nameh Mubahala, ya na ganin cewa wannan abu ya faru cikin jerin abubuwa da suka faru a shekara ta goma hijira ƙamari ko shekara ta 9 hijira ƙamari.[17]

Game da ranar da mubahala ta afku nan ma akwai saɓanin ra'ayoyi, misalin akwai magana cewa ta faru ne a ranar 21,[18] 24[19] da 25 ga watan zil hijja,[20] Shaik Ansari, ya ce ranar 24 ga watan zil hijja ita ce maganar da ta shahara.[21] haka nan cikin littafan addu'a an ambaci ayyuka da ake yi ranar 24 ga watan zil hijja.[22] Shaik Abbasi ƙummi, a cikin Mafatihul Al-jinan ya kawo ayyukan daga jumlarsu akwai wanka da azumi da ake yi a wannan rana.[23]

Annabi (S.A.W):
“Na rantse da Allah wanda raina ke cikin ikonsa, cewa halaka mutanen Najran ya kusa, Idan kuma suka yi mubahalatare da ni za su koma birai da aladu, Kuma wannan kwarin gaba ɗaya ya zama wuta a gare su, za su kone, Allah ta'ala zai halaka bakidayan mutanen najran, hatta tsuntsaye ba za su rage a kan bishiyoyinsu sai sun halaka, kafi zagayowar shekara bakidayan kiristoci sai sun mutu babu wanda zai rage a duniya.

Source: Mufid, Al-Arshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 166-171.

Wuri

Waƙi'ar mubahala ta faru ne a garin madina amma a wane unguwa ce ko wani wuri a cikin madina babu cikakken rahoto, a kusa da maƙabartar baƙi'a akwai wani masallaci da ake kira da suna masjidul mubahala wanda aka fi sani da sunan masjidul al-ijaba.[24] wanda maziyarta suna ziyartarsa matsayin wurin da anannne aka yi mubahala.[25] amma ana cewa babu wani masallaci mai wannan suna da ya zo cikin madogaran tarihi.[26] Muhammad Sadiƙ Najami (Wafati: 1390. h. shamsi) marubuci kuma ɗan shi'a, ya tabbatar da cewa wannan masallaci bashi da alaƙa da wurin da aka yi mubahala, batun jingina shi da mubahala kuskure da ya faru sakamakon kamanceceniya cikin ma'anar mubahala da ijaba da kuma maganar da malam Ibn Mashhadi ya yi game da wasiyya da yin sallah cikin masjidu mubahala.[27]

Ibn Mashhadi (Wafati: 610. h. ƙ) cikin littafin Al-mazar, ya ambaci masjidu mubahala tare da wasiyya da yin sallah cikin wannan masallaci.[28] a cewar Muhammad Sadiƙ Najami, dalilin ya sa babu wani masallaci da aka gina a wannan wuri shi ne kasancewar Annabi (S.A.W) bai yi sallah a wannan wuri ba, sannan musulmi duk wurin da suka samu yaƙini cewa Annabi (S.A.W) ya yi sallah a wurin suna gina masallaci a wurin.[29]

Zanen waki'ar mubahala da yake kan bangon littafin Asarul Al-bakiya na Abu Raihan Biruni da aka rubuta shekara 707 hijira kamari.[30]

Litattafai Da Ayyukan Fasaha

An rubutua litattafai game da waƙia'ar mubahala. ba'arinsu su ne:

  • Manabi'u Shinasi Waƙi'eh Mubahala, na Muhammad Ali Asgari da Muhammad Ali Najafi: wannan littafi da aka buga shi shekarar 2022 m. ya gabatar da adadin litattafai da aka rubutu kan wani batu kusan guda 80 da risaloli 25 da ƙasidu guda 100 cikin mabambantan harsuna.[31]
  • Farhange Nameh Mubahala (Hanyar Mu'amala da mabambantan tunani) wanda Muhammad Muhammadi Rai Shahari ya rubuta. Wannan littafi rahoto ne game da waƙi'ar mubahala kan asasin naƙalin Fakhrur Razi (Wafati: 606. h. ƙ) malamin tafsiri ahlus-sunna da kuma Shaik Mufid (Wafati: 413. h. ƙ) mutakallim ɗan shi'a shima ya kawo bayanin wannan rahoto. Haka nan kafa hujjar da Ahlul-baiti (A.S) suka yi da kuma ladubban wannan rana, Intisharat Darul Hadis su ne suka buga wannan littafi a shekarar 2016 m. littafin yana shafuka 154.[32]
  • Mubahala Dar Madina, na Louis Massignon: a shekarar 1378 hijira shamsi aka buga wannan littafi haɗe da tarjama da muƙaddima ta hannun Mahmud IFtikhar Zadeh. Kamfanin Intisharat ƙalam ta buga shi.
  • Mubahale Sadiƙin, na Sayyid Muhammad Alawi, ƙum kamfanin Nagmat suka buga shi shekarar 1383 hijira shamsi.
  • Asare Muntkhab Jasheneware Adabi Mubahale: littafi mai cin gashin kansa na farki da aka aka yi talifi a kan batun mubahala, kuma wannan littafi ya kasance littafin da aka zaɓa a bikin adabi na mubahala, wannan littafi ya ƙunshi sashe biyu "waƙa"da "zube".[33]

Ayyukan Fasaha

Game da waƙi'ar mubahala an gabatar da ayyukan fasaha misalin zane-zane, animeshin (Animation) da sauran ayyukan fasaha. daga cikin daɗaɗɗun ayyuka na zane akwai zane da aka sanya a bangon kwafin littafin asarul al-baƙiya na Abu Raihan Biruni. Wannan kwafi an yi tun shekarar 707 hijira ƙamari sannan yana nan an ajiye shi a ɗakin ajiye kayan tarihi na ƙasar faransa.[34] a cewar Rasul Jafariyan mai nazarin tarihi, akwai tsammanin wannan zane ƙari ne aka manna shi jikin [35].[35]

Bayanin kula

  1. Paknia, "Mubahala, Rushentrin Bowerhai Shi'a," shafi na 51.
  2. Suratul Ali-Imran, aya ta 61.
  3. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1415, juzu’i na 2, shafi na 310; Fakhrazi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1420H, juzu'i na 8, shafi na 247. Marashi, Ihqaq al-Haqq, 1409 Q, juzu'i na 3, shafi na 46.
  4. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1415, juzu’i na 2, shafi na 310; Fakhrazi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1420H, juzu’i na 8, shafi na 247
  5. Ibn Atheer, Al-Kamil fi Al-Tarikh, 1385 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 293-294.
  6. Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1373-1374 AH, juzu'i na 2, shafi 578
  7. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1415 BC, juzu’i na 2, shafi na 310; Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, V1, 1414H, shafi na 392.
  8. Fakhr Razi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1420 BC. Sashe na 8, shafi na 247.
  9. Marashi, Ihqaq al-Haqq, 1409 BC, juzu'i na 3, shafi na 46
  10. Majlisi, Haqq al-Yaqin, littattafan Islama, juzu'i na 1, shafi na 67.
  11. Marashi, Ihqaq al-Haqq, 1409 Q.C., juzu'i na 3, shafi na 46-72.
  12. Al-Fusul Al-Mukhtara, 1414H, shafi na 38; Tabatabai, Al-Mizan, 1351/1352, juzu'i na 3, shafi na 230-229.
  13. Tabatabai, Al-Mizan, 1351-1352, juzu'i na 3, shafi na 232.
  14. Mufid, Al-Irshad, 1413 BC, juzu'i na 1, shafi na 166-171.
  15. Mufid, Al-Irshad, 1413 BC, juzu'i na 1, shafi na 166-171.
  16. Tabari, Tarikh al-Umm wa al-Muluk, 1387, juzu'i na 3, shafi na 139.
  17. Muhammad Rayshahri, Farhangnameh Mubahlah, 1395 AH, shafi na 83-87.
  18. Mobdi, Kashf Al-Asrar, 1371 AH, juzu'i na 2, shafi 147.
  19. Ibn Shahr Ashub, Manaqib, 1376 BC, juzu'i na 3, shafi na 144; Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411, juzu'i na 2, shafi na 759.
  20. Duba Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411H, juzu'i na 2, shafi na 759.
  21. Ansari, Kitabe Tahara, Kangareh Jahani Bazragdasht Sheikh Azam Ansari, juzu'i na 3, shafi na 48-49.
  22. Sheikh Tusi, Misbah al-Muhtajjud, 1411, juzu’i na 2, shafi na 764.
  23. Qomi, Mufatih al-Janan, 2004, Babi na biyu (Ayyukan Sheakara), Ayyukan Ranar Mubahalah, shafi na 451-458.
  24. Duba Fazel Lankarani, Manasik, 1373, shafi na 242.
  25. Najmi, "Masjid al-Ajaba ya Masjid Mubahalah", shafi na 123.
  26. Najmi, "Masjid al-Ajaba ya Masjid Mubahlah", shafi na 124. ↑
  27. Najmi, “Masjid al-Ajaba ya Masjid Mubahlah”, shafi na 122.
  28. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 102.
  29. Najmi, “Masjid al-Ajaba ya Masjid Mubahlah”, shafi na 126.
  30. «دو نقاشی بی نظیر از روز غدیر و مباهله در نسخه‌ای از الاثار الباقیه ابوریحان بیرونی»، سایت کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام.
  31. «منبع‌شناسی واقعه مباهله وارد بازار نشر شد.»، خبرگزاری رسمی حوزه.
  32. فرهنگ‌نامه مباهله (روشی در رویارویی با دگراندیشان)، حدیث‌نت.
  33. «آثار منتخب جشنواره ادبی مباهله»، حدیث‌نت.
  34. «دو نقاشی بی نظیر از روز غدیر و مباهله در نسخه‌ای از الاثار الباقیه ابوریحان بیرونی»، سایت کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام.
  35. «دو نقاشی بی نظیر از روز غدیر و مباهله در نسخه‌ای از الاثار الباقیه ابوریحان بیرونی»، سایت کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام.

Tsokaci

  1. lokacin da wasu mutane suke tattauna game da wata mas'ala ta addini mai muhimmanaci, hujjoji hankali da suka kafa basu amfanar ba, suna yanke shawrar haduwa wani wuri su roki Allah ya saukar da stinuwarsa kan makaryaci ya kuma tina masa asiri tare da kunyata shi, an ce wannan ake kira da mubahala(Makarim shirazi Payame Kur'an, 1386, shamsi, j 9 shafi na 230.

Nassoshi

  • Ibn Athir, Ali bin Abi Karam, Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir - Dar Beirut, 1385/1965 miladiyya.
  • Ibn Sa'ad, Muhammad bin Sa'd, Tabaqat al-Kubra (Al-Taqabat al-Kabri), bincike na Muhammad bin Samil al-Salami, Al-Taif, School of Al-Sadiq, 1993 AD/1414 AH.
  • Ibnshahrashob, Muhammad bin Ali, Manaqib Al Abi Talib, Najaf: Al-Haydriya Press, 1376H.
  • Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jafar, Al-Mazar al-Kabir, edita ta Javad Qayoumi Isfahani, Qum, ofishin yada labaran Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, bugu na farko, 1419 Hijira.
  • Ansari, Morteza, Kitab al-Tahara, Qom, Majalisar Dinkin Duniya ta karrama Sheikh Azam Ansari.
  • Johari, Ismail bin Hamad, Al-Sihah (Taj al-Lugha wa Sihah al-Arabiya), Ahmad Abd al-Ghafoor Attar, Beirut, Dar-e-Alam Lal-Mulayin, bugu na hudu, 1407H ya yi bincike.
  • Hazin Lahiji, Muhammad Ali bin Abi-Talib, Diwan Hazin Lahiji, edited by Zabihullah Sahibkar, Tehran, Sayeh Publishing House, 2004.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Umar, Al-Kashaf an haqa'iq Ghawamaz al-Tanzil wa uyun al-Aghawil fi wujuhil tawili, bugun Mustafa Hossein Ahmad, Beirut, Darul Kitab al-Arabi, 1407-1416 Hijira.
  • Shushtri, Qazi Noorullah, Ihqaq al-Haq wa Izhaq al-Batil, Kum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, bugu na farko, 1409H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Misbah al-Mutahajjid wa Selah al-Muta'abbid, Beirut, Fiqh al-Shi'a Foundation, bugu na farko, 1411H.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1351/1352.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut: Al-Alami Foundation for Publications, bugu na farko, 1415 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jafar, Tarikh Al-umam wa Al-Muluk, wanda Muhammad Abulfazl Ibrahim ya yi bincike a Beirut, Darul Trath, bugu na biyu, 1387/1967 Miladiyya.
  • Atar Neishabouri, Mohammad bin Ibrahim, Johar al-Zat, editan Timur Burhan Limodehi, Sanai, Tehran, 2003.
  • Fazel Lankarani, Muhammad, manasiku Hajji, Kum, Mehr, bugu na uku, 1373.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Umar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H/1999 Miladiyya.
  • Qommi, Shaykh Abbas, Kulliat Mufatih al-Jinan, Qum, Press Religious, bugun 2, 2004.
  • Majlisi, Mohammad Baqer, Haq Al-yaqin, Islamic Publications.
  • Mohammadi Rishahri, Mohammad, Farhangenameh Mubahlah (hanyar magance masu sabani), Qum, Dar al-Hadith, bugun farko, 1395.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad, Research of Al-Bait (AS) Lahiya Al-Trath Foundation, Qum: Al-Congres Al-Alami Lalfiya Al-Sheikh Al-Mofid, 1413H.
  • Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Fusul al-Mukhtara, Tahaqiq: Al-Sayyid Mir Ali Sharifi, Beirut: Dar Al-Mufid, Al-Taaba al-Thaniyyah, 1414H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Payame Kur’ani, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 9, 1386.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuna, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1374-1374.
  • Meybodi, Ahmed bin Mohammad, Kashf al-Asrar da Kit al-Abrar, Tehran, Amir Kabir, 1371
  • پاک‌نیا، عبدالکریم، مباهله روشن‌ترین دلیل باورهای شیعه، مبلغان، ش۵۰.
  • «آثار منتخب جشنواره ادبی مباهله»، حدیث‌نت، مشاهده ۲ خرداد ۱۴۰۲ش.
  • «دو نقاشی بی‌نظیر از روز غدیر و مباهله در نسخه‌ای از الاثار الباقیه ابوریحان بیرونی»، سایت کتابخانه تخصصی تاریخ اسلام، درج مطلب ۲۵ مهر ۱۳۹۳ش، مشاهده ۲ خرداد ۱۴۰۲ش.
  • فرهنگ‌نامه مباهله (روشی در رویارویی با دگراندیشان)، حدیث‌نت، مشاهده ۲۱ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • «منبع‌شناسی واقعه مباهله وارد بازار نشر شد.» خبرگزاری حوزه، درج مطلب ۵ مرداد ۱۴۰۱ش، مشاهده ۲۱ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • نجمی، محمدصادق، «مسجدالاجابه یا مسجد مباهله»، میقات حج، ش۴۱، زمستان و پاییز ۱۳۸۱ش.