Muhaddasa (Laƙabi)

Daga wikishia
Ka da a yi Kuskuren daidai ta shi da mashigar Muhaddis
Kafa Banner ta «اَلسَّلامُ عَلَیکِ اَیَّتُهَا التَّقیةُ النَّقیةُ الْمُحَدَّثَةُ الْعَلیمه» cikin salon rubutu na sulsuJaliyyu

Muhaddasa ɗaya ne daga cikin laƙubban Sayyida Faɗima (S) ma'ana matar da mala'iku suke magana tare da ita. Wannnan laƙabi a cikin riwayoyi an yi amfani kan wasu matan daban misalin Sayyida Maryam (S) da Saratu. Ana cewa mala'iku sun tattauna tare da ita cikin batutuwa misalin jaje da gaisuwa, labarurrukan muminai da abin da zai faru gobe.

Yiwuwar mala'iku su yi magana tare da Imamai da Sayyida Faɗima (A.S) suna daga cikin aƙidun shi'a, da wannan dalili wasu ahlus-sunna suke zargin ƴan shi'a da annbtar da Imamansu. A cewar Allama Amini, marubucin littafin Al-ghadir, yiwuwar mala'iku su yi magana tare da mutanen da ba Annabawa ba magana ce da shi'a da ahlus-sunna suka yi ittifaƙi kanta, kaɗai sun yi saɓani ne cikin misdaƙi da su wane ne waɗanda mala'ikun za su iya magana tare da su.

Muhaddasa, Laƙabin Sayyida Zahra (S)

Kan asasin riwayoyin, laƙabin muhaddasa ɗaya ne daga laƙubban Sayyida Zahra (S)[1] kuma ɗaya ne daga sunayen ta guda tara.[2] na'am daidai da abin da ya zo cikin riwayoyin shi'a ana amfani da wannan laƙabi kan Sayyada Maryam (S), mahaifiyar Annabi Musa (A.S) da kuma Saratu matar Annabi Ibrahim (A.S).[3] Cikin ba'arin riwayoyi da suke da alaƙa da Mus'hafu Faɗima an ishara da ga kasancewar ta muhaddasa.[4] cikin ziyarar Sayyida Faɗima nan an kira ta da «الْمُحَدَّثَةُ الْعَلِیمَةُ» (Al-muhaddasa Al-alima).[5]

Ma'anar Muhaddasa

Muhaddasa yana nufin wanda mala'iku suka yi magana da shi,[6] a cewar Allama Amini marubucin littafin Al-ghadir, isɗilahin muhaddasa ana amfani da shi kan wanda ba Annabi ba; amma tare da haka mala'iku suna magana da shi.[7]

Ba'arin abin da magana da mala'iku ya ƙunsa wanda Sayyida Faɗima ta yi, ya dunƙule a cikin wurare guda biyar : gaisuwa da ta'aziyya, bata labarin Annabi (S.A.W) da matsayinsa a cikin aljanna, labaran abubuwan da za su faru a gobe, labarurrukan masu mulki da labaran muminai da kafirai.[8]

Wasu suna ɗaukar laƙabin muhaddisa da ma'anar mai magana, saboda suna cewa lokacin da ta kasance a cikin mahaifiyarta ta kasance tana magana da mahaifiyarta.[9][Tsokaci 1]

Yiwuwa Zantawar Mala'iku Da Waɗanda Ba Annabawa Ba

Tushen ƙasida: Ilhama

Allama Amini, yana ɗaukar imani da kasancewar Sayyida Faɗima (S) tana magana tare da mala'iku, haka ma Imamai suma suna magana da su yana daga cikin aƙidun ƴan shi'a, a cewarsa yar da cewa mala'iku suna magana tare da waɗanda ba Annabawa batu ne da shi'a da ahlus-sunna suka yi ittifaƙi a kansa.[10] ya bayyana cewa kaɗai dai an samu saɓani cikin wannan batu ne ta fuskacin su wane ne mala'ikun suka yi magana da su. Alal misalin yan shi'a saɓanin ahlus-sunna ba su yarda cewa Umar Ɗan Khaɗɗab yana daga mutanen da mala'iku suka yi magana tare da shi ba.[11]

Abdullahi ƙasimi, marubucin ɗan salafiyya daga ƙasar saudiyya, a cikin littafin "As-sira'u Bainal Al-Islam Wal Al-wasaniyya", sakamakon imani da kasancewar Sayyida Faɗima (S) da Imamai a matsayin wanda mala'iku suka yi magana da su, ya tuhumi shi'a da annabtar da Imamansu da kuma Faɗima (S). Na'am Allama Amini ya bada amsa kan wannan tuhuma.[12] domin tabbatar da zantawar mala'iku tare da mutanen da ba Annabawa ya dogara da ayoyin kur'ani misalin aya ta 42 suratul alu imran, aya ta 71-73 suratul hud da aya ta 7 suratul ƙasas, cikin waɗannan ayoyi an yi ishara kan zantawar tsarkakakkun magabata mata tare da mala'iku.[13]

Bayanin Kula

  1. Sheikh Saduq, Illal al-Shara’i’, 1386 BC, juzu’i na 1, shafi na 182; Tabari, Dala'ilul Al-Imama, shafi na 81, h. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 14, shafi na 23.
  2. Sheikh Saduq, Al-Amali, 1376H, shafi 592.
  3. Majlis, 1403 BC, Bahar al-Anwar, juzu'i na 43, shafi na 79.
  4. Al-Saffar ne ya rawaito shi, Basaer Al-Darajat, 1404H, shafi na 152; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 18, shafi na 34; Mahdavi Rad, "Qur'an of Fatima," shafi na 73.
  5. Qomi, Mafatih al-Jinan, Beta, shafi na 317.
  6. Rahmani Hamdani, Fatima Zahra Fatima Zahra (S) Shadmani del Viamber (S), 1381 AH, shafi 244 (Pawarqi).
  7. Allama Amini, Al-Ghadeer, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 67.
  8. رحمان ستایش، «گفت و گوی ملائکه با حضرت فاطمه(س)»، ص۲۵–۲۶.
  9. Rahmani Hamdani, Fatima Zahra Fatima Zahra (S) Shadmani del Viamber (S), 1381 AH, shafi 244 (Pawarqi).
  10. Allama Amini, Al-Ghadeer, 1416 BC, juzu'i na 5, shafi na 67-68.
  11. Allama Amini, Al-Ghadir, 1416 BC, juzu'i na 5, shafi na 68-70.
  12. Allama Amini, Al-Ghadeer, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 78.
  13. Allama Amini, Al-Ghadeer, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 78.

Tsokaci

  1. Kutubud-dini Rawandi< cikin littafin Ar-rasul Wa Ibratuhu, cikin sashen lakubban Fatima, taken "Munisa Khadijatul Al-kubra fi batniha" ya yi ishara da kasancewar ta tana magana tare da babarta tun tana ciki

Nassoshi

  • Rahman Staish, Muhammad Kadhim, “Guftaguye Mala’ikeh Ba Sayyida Fatima (AS), Hadisi Pajuhi Bahar wa Tabistan, 1391 Hijira.
  • Rahmani Hamedani, Ahmed, Fatima Zahra, (S), Shadmani del Viamber, wanda Sayyed Hassan Iftekharzadeh Sabzwari ya fassara, Tehran, Littafin Binciken Badar da Bugawa, Chapharm, 1381 Hijira.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, Shasham, 1376 Hijira.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Ilal al-Shara’i’, Najaf, Library Al-Haidariyya, 1386 BC.
  • Saffar Qomi, Muhammad bin Hassan bin Faroukh, Basa'ir al-Darajat fi Fada'il al-Muhammad, Gyara da Sharhi: Mirzam Mohsen Kocha Baghi Tabrizi, Qom, Laburare na Ayatullahi Marashi al-Najafi, Littafin Rana, 1404 BC.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir bin Rustam, Dala'ilul Al-Imama, Qum, an aiko ni, babi na farko, 1413 BC.
  • Allama Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir Fi Al-kitabe wa Sunnah wa Adabi, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, 1416 BC.
  • Qomi, Abbas, Mafatih al-jinan, Qum, bugun Aswa, Beta.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bahar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1403 BC.
  • Mahdavi Rad, Muhammad Ali, "Qur'an Fatima", Dar Danshnameh Fatimi (S), juzu'i na 3, Tehran, Sazan Publications of the Islamic Revolution and Islamic Revolution, 1393 AD.