Hadis Wisaya

Daga wikishia
Kar ku ruɗe da Hadis Wasiyya.
Haramin Imam Ali (A.S)

Hadis Wasiyyatu (arabic: حديث الوصاية) wani hadisi ne daga Annabi (S.A.W) wanda cikinsa ya gabatar da Imam Ali (A.S) maysatin Wasiyyinsa kuma Magajinsa, wannan hadisi ya zo da mabanbantan lafuzza cikin litattafan hadisi na Shi’a da Ahlus-sunna, riwayar :

كُلِّ نَبِيٍّ وَصِيٌّ وَ وَارِثٌ وَ إِنَّ عَلِيّاً وَصِيِّي وَ وَارِثِي

Tana daga cikin mafi shaharar riwayar da Buraidatu Bn Husaibu ya nakalto daga Annabi (S.A.W)

Matanin Hadisin

عنه صلی الله عليه و آله : لِكُلِّ نَبِيٍّ وَصِيٌّ وَ وَارِثٌ وَ إِنَّ عَلِيّاً وَصِيِّي وَ وَارِثِي

Annabi (S.A.W) yace kowanne Annabi yana da Wasiyyi da Magaji kuma hakika tabbas Ali ne Wasiyyina kuma Magajina. [1]

Hadisin Wisaya a cikin Litattafan Riwaya

Wannan hadisin ya zo cikin litattafan riwaya na Shi’a na Ahlus-sunna misalin littafin fada’el Sahaba na Ibn Hanbal [2] da Almanakib na Ibn Magazili [3] Almujam Alkabir na Tabarani [4] Tarikh Madinatu Damashk [5] Almanakib Khawarzimi [6] Alkamil na Jurjani [7] tazkiratul kawwas [8] Kifayatul Al-asar [9] Man la yahduruhu Alfakihu [10]Dala’il Imama [11] Manakib Ibn shahriAshub [12] da Bihar-Anwar [13]ya zo daga Buraidatu Bn Husaibu Annabi (S.A.W) yace: (kowanne Annabi yana da wasiyyi da Magaji hakika Ali shine Wasiyyina kuma Magajina [14] Cikin amsar da Annabi (S.A.W) ya bawa Salmanul Farisi lokacin da ya tambaye shi game da Magajinsa, Manzon Allah (S.A.W) yace: Magajina kuma wasiyyina shine wanda zai biya min bashi zai kuma tabvbata da alkawurran da na yi shi ne Ali Bn Abu Talib [15] [yadasht] Haka kuma kan asasin wani hadisi da aka nakalto shi Ali bn Ali Hilali cikin Maganar Annabi (S.A.W) zuwa ga Fatima (S) yace:

َ وَصِيِّي خَيْرُ الْأَوْصِيَاءِ وَ أَحَبُّهُمْ إِلَى اللَه وَ هُوَ بَعْلُكِ؛

Wasiyyina shine mafi alherin Wasiyyai kuma Mafi soyuwarsu a wurin Allah shine Mjinnki [16]

Abin da hadisin ya tattara a kansa

Wannan hadisi na Wasiyyat ya tattara kan Mas’alar Magaji da Halifancin Imam Ali (A.S) Malaman Shi’a sun tafi kan cewa wannan hadisi daya ne daga cikin dalilai kan Imamancin Ali Bn Abu Talib (A.S) sun fassara Wasiyya da ma’anar Magaji kuma sun tafi kan cewa Annabi (S.A.W) kan asasin wannan hadisi ne ya ayyana Hazrat Ali (A.S) a matsayin Halifansa Magajinsa [17] amma wasu ba'arin Malaman Ahlus-sunna sun tafi kan cewa wannan hadisi baya bada ma’anar Halifanci, bari dai kadai dai Annabi (S.A.W) ya ajiye amanar Iyalansa a hannun Ali (A.S) cikin amsar da Malaman Shi’a suka bayar kan wannan Magana sunce Annabi (S.A.W) ya bayyana Hazrat Ali (A.S) [18] a Wasiyyinsa da sura Mudlaka ba tareda kowanne irin kaidi da togaciya ba, babu inda ya kayyade cewa a irin da’airar al’amuran iyalansa ya bayyana shi Wasiyyi [19] Hammadi Bn Abdul-Majid Assalafi cikin Nuskar bincike da tahkiki kan littafin Almujam Alkabir yace idan isnadin hadisin ya inganyta to lallai yana shiryarwa ne zuwa Halifanci da gadon Kujerar Annabi (S.A.W) [20]

Isnadi

Hadisin wasiyyat ya zo da isnadi daban-daban daga Buraidati Bn Husaibu [21] Salmanu [22] Abu Ayyubul Ansari da Anas Bn Malik [23] duka an rawaito ta hanyoyinsu daga litattafan Ahlus-sunna, Sibt Ibn Jauzi Marubucin Littafin Tazkiratul Al-Khawwas ya rawaito daga Salmanu da Isnadi guda biyu, yana ganin ingancin Isnadin da aka rawaito cikin littafin Fada’el Sahaba na Ahmad Bn Hanbal [24] Wasu ba’arin Malaman Ahlus-sunna misalin Ibn Jauzi [25]Jalalud-Addini Suyuti [26] da Haitami [27] sakamakon zuwan Muhammad bn Hamid Razi ko kuma Ali Bn Mujahid a cikin Isnadin sun yi Shakku kan Ingancinsa sun kuma yi watsi da shi, a daidai lokacin da acewar Sayyid Ali Milani Hakika Muhammad Bn Hamid Razi yana daga Marawaitan da aka rawaito Hadisansu cikin Sihahu Sitta, sannan ba’arin Malaman Rijal daga Jumlarsu Yahaya Bn Ma’in sun Wassaka shi [28] haka kuma Tirmizi daya daga cikin Marubatan Sihahu Sitta da Ahmad Bn Hanbal sun nakalto Riwayoyi daga Ali Bn Mujahid [29]

Bayanin kula

  1. Ibn Maghazali, Manaƙib Ali bin Abi Talib, 1426H, shafi na 167; Ibn Asaker, Tarikh Madinati na Damashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 392; Khwarazmi, al-Manaƙib, 1414 AH, shafi na 85; Jurjani, Al-Kamel, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 14; Ibn Shahr Ashub, Manaƙib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 188, juzu'i na 3, shafi na 66; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 38, shafi na 154-339.
  2. Duba: Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khwas, 1418H, shafi na 48.
  3. Ibn Maghazali, Manaƙib Ali bin Abi Talib, 1426H, shafi na 167.
  4. Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, 1405 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 221.
  5. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415 Hijira, juzu'i na 42, shafi na 392.
  6. Khwarazmi, Al-Manaƙib, 1414H, shafi na 85.
  7. Jurjani, Al-Kamel, 1409 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 14.
  8. Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, 1418H, shafi na 48.
  9. Khazaz Razi, Kefayat Athar, 1401 AH, shafi 80
  10. Sadouƙ, Man la Yahdrah al-Faƙih, 1413 AH, juzu'i na 4, shafi na 180.
  11. Tabari Amoli, Dalai al-Imamah, 1413H, shafi na 9
  12. Ibn Shahr Ashub, Manaƙib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 188, juzu'i na 3, shafi na 66.
  13. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 38, shafi na 154-339.
  14. Ibn Maghazali, Manaƙib Ali bin Abi Talib, 1426H, shafi na 167; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 392; Khwarazmi, al-Manaƙib, 1414 AH, shafi na 85; Jurjani, Al-Kamel, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 14; Ibn Shahr Ashub, Manaƙib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 188, juzu'i na 3, shafi na 66; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 38, shafi na 154-339.
  15. Tabarani, al-Mu'jam al-Kabir, 1405 AH, juzu'i na 6, shafi na 221; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 38, shafi na 12.
  16. Haytami, Majma al-Zawaed, 1408 AH, juzu'i na 9, shafi 165; Tabarani, Al-Mu'jam al-Awsat, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 327; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, juzu'i na 42, 1415 AH, shafi na 130; Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, 1404 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 58.
  17. Misali, duba: Estrabadi, Al-Barahin al-ƙata'ah, 2002, juzu'i na 3, shafi na 244.
  18. Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, 1405 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 221.
  19. <a class="eɗternal teɗt" href="http://shamimshia.com/fa/indeɗ.php?option=com_content&view=article&id=373:sanad-vesayat&catid=59:hadess-vesayat&Itemid=35">پایگاه شمیم شیعه، نص حدیث وصایت و بررسی سند آن، بازبینی: ۱۳ تیر ۱۳۹۶.</a>
  20. Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, juzu'i na 6, shafi na 221.
  21. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 392; Khwarazmi, al-Manaƙib, shafi na 85; Jurjani, Al-Kamel, 1409 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 14.
  22. Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, 1405 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 221.
  23. Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, 1418H, shafi na 48.
  24. Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, 1418H, shafi na 48.
  25. Ibn Juzi, al-Ubaat, 1386 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 376.
  26. Siyuti, Al-Lali Al-San'atah fi Hadith Al-Mauduy'a Darul Marafa, Mujalladi na 1, shafi na 358
  27. <a class="eɗternal teɗt" href="http://shamimshia.com/fa/indeɗ.php?option=com_content&view=article&id=373:sanad-vesayat&catid=59:hadess-vesayat&Itemid=35">پایگاه شمیم شیعه، نص حدیث وصایت و بررسی سند آن، بازبینی: ۱۳ تیر ۱۳۹۶.</a>
  28. Milani, Tashyid Muraja'at wa Tafnid al-Makabarat, 1427 AH, juzu'i na 3, shafi na 431-430
  29. <a class="eɗternal teɗt" href="http://shamimshia.com/fa/indeɗ.php?option=com_content&view=article&id=373:sanad-vesayat&catid=59:hadess-vesayat&Itemid=35">پایگاه شمیم شیعه، نص حدیث وصایت و بررسی سند آن، بازبینی: ۱۳ تیر ۱۳۹۶.</a>

Nassoshi

  • Haytami, Majma al-Zawaed, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1408H/1988 miladiyya.
  • Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, bincike: Ali Shiri, Darul Fikr, Beirut, 1415 Hijira.
  • Ibn Juzi, al-Mauda'at, bincike: Abdur Rahman Muhammad Othman, Madina, al-Maktab al-Salfiyyah, 1386/1966 miladiyya.
  • Ibn Maghazali, Manaƙib Ali bin Abi Talib (a.s), Sabat al-Nabi Publications (a.s), 1426 AH-1384 AH.
  • Ibn Shahr Ashub, Muhammad Bin Ali, Menaƙib Al Abi Talib, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allameh, ƙum, 1379H.
  • Jurjani, Abdullah bin Adi, al-Kamel, bincike: Yahya Mukhtar Ghazawi, Dar al-Fikr, Beirut, 1409 AH/1988 miladiyya.
  • Khazaz Razi, Ali bin Muhammad, cancantar athar a cikin nassin Imamai na goma sha biyu, wanda Abdul Latif Hosseini Kohkamari ya yi bincike a kansa, ƙum, bugun Bidar, 1401H.
  • Khwarazmi, Mawafaƙ, al-Manaƙib, bincike: Malik Mahmoudi, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1414 AH.
  • Majlesi, Mohammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, 1403H.
  • Milani, Sayyid Ali, Tasheed al-Muraja'at wa Tafnid al-Makabarat, ƙum, Al-Haƙaƙeeƙ al-Islamiya Center, 1427H.
  • Sabbat bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, ƙum, Al-Sharif al-Razi's handscripts, 1418H.
  • Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdara al-Faƙih, Ali Akbar Ghafari, ƙum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Kum, 1413 AH.
  • Tabarani, Al-Mu'jam al-Awsat, bincike: binciken Badarul Haramameen, Darul-Harameen na bugawa da rarrabawa, 1415 AH/1995 miladiyya.
  • Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir (Juzu'i na 3), bincike: Hamdi Abdul Majid Salafi, Darahiya al-Tarath al-Arabi, 1404 AH/1984 miladiyya.
  • Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir (Juzu'i na 6), bincike: Hamdi Abdul Majid Salafi, Darahiya Al-Tarath al-Arabi, 1405 AH/1985 miladiyya.
  • Tabari Amoli Saghir, Muhammad bin Jarir bin Rostam, Dala'il al-Imamah, ƙum, bugun Ba'ath, bugu na farko, 1413H.
  • Astarabadi, Mohammad Jaafar, Al-Barahin al-ƙata'ah a cikin bayanin abstraction na al-Aƙeed al-Sati'ah, research: Center for Islamic Studies and Research, ƙum, School of Islamic Studies, 1382.