Rahamatan Lil Alamin (Lakabi)
Rahamatan Lil Alamin, (Larabci رحمة للعالمين)Rahama ga dukkanin halittun duniya ɗaya daga cikin laƙubban Hazrat Muhammad bin Abdullah (S.A.W) da aka yi amfani da shi kansa a cikin aya ta 107 suratul Anbiya, haka nan an yi amfani da Kalmar rahama kan Hazrat Muhammad (S.A.W) a cikin wasu ayoyin daban misalin aya ta 128 suratul Tauba da aya ta 159 suratul Alu Imrana, Nabiyyul Rahma shima laƙabi ne na Annabi (S.A.W) da aka ciro shi daga waɗannan jumloli na Alkur'ani. [1]
Jumlar rahama ga dukkanin halittun duniya ya zo cikin riwaya daga Imaman Shi'a game da Manzon Allah (S.A.W), kamar misalin riwaya da ta zo cikin littafin Basa'irul Ad-Darajat [2] ko kuma abin da ya zo cikin Tafsirul Furatul Al-Kufi da aka naƙalto daga daga Imam Hassan Mujtaba (A.S) [3] ko kuma riwayar da aka naƙalto daga Imam Baƙir (A.S) wacce cikin huɗubarsa ta juma'a ya yi amfani da wannan kalma. [4] haka nan kuma akwai wani hadisi daga Imam Kazim (A.S) [5] da kuma wani hadisin da aka naƙalto daga shi kansa Annabin muslunci (S.A.W). [6]
Malaman tafsiri na Shi'a da Ahlus-sunna sun yi bayani dangane da kasancewar Annabi rahama wacce ta kasance Magana kamar haka: sakamakon kasancewar saƙonsa saƙo ne na duk duniya kuma wanzazze har abada, farin ciki da kyakkyawan ƙarshe ga kowa da kowa da kuma kasancewarsa shinge daga faɗawa azabar Allah. [7] a cewar Malaman tafsiri abin da ake nufi da azaba anan shi ne kakkaɓe al'umma da halaka bakiɗayansu. [8] a cewar Mulla Fatahullahi Kashani an yi amfani da wannan ma'ana daga aya ta 33 suratul Anfal wacce cikinta Allah yake cewa Annabi (S.A.W) kasancewarka cikin Al'umma yana hana Allah yi musu azaba, [9] Faizul Kashani cikin tafsirul safi haƙiƙa aminci daga kisfewa da ruftawa cikin ƙarƙashin ƙasa, masak jirkita halitta tare da halakar da bakiɗayan mutane suna daga misdaƙan kasancewar Annabi (S.A.W) rahama. [10]
Bayanin kula
- ↑ Hashemi Shahqabadi, "barasi mafhum rahmtan lil Alamin dar sireh nabawi", shafi na 39.
- ↑ Safar Qomi, Basair Al-Derajat, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 381.
- ↑ Kufi, Tafsir Furat Kufi, 1410H, shafi na 197.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1364, juzu'i na 3, shafi.422.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1364, juzu'i na 4, shafi na 148.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1364, juzu'i na 6, shafi na 395
- ↑ Ghazanfari da Zarei, "Rahma llal al-Alamin Budane Payambar (S.A.W) dar Kur'an az Negahe Tafsir Fariqaini", shafi na 70.
- ↑ Misali, duba Abul Fatuh Razi, Rouz Al-Janan, juzu'i na 13, shafi na 289; Kashani, Manhaj al-Sadeghin, 1371, juzu'i na 6, shafi na 117.
- ↑ Kashani, Manhaj al-Sadeghin, 1371, juzu'i na 6, shafi 117
- ↑ Faiz Kashani, Al-Safi, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 358.
Nassoshi
- Abulfatuh Razi, Hossein bin Ali, Ruz al-Jinnan wa Ruh Al-Jinan, Mashhad, Islamic Research Foundation, 1371.
- Faiz Kashani, Mollah Mohsen, Al-Safi, Tehran, Al-Sadr School, 1373.
- Kashani, Mulla Fethullah, Manhaj al-Sadiqin fi Zazam al-Makhalifiin, Tehran, Islamia, 1378.
- Kufi, Furat bin Ibrahim, Tafsir Furat Al-Kufi, Bincike: Mohammad Al-Kazem, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Shiryar Musulunci, 1410H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1364 ya gyara.
- Safar Qommi, Muhammad bin Hasan, Basa'er al-Derajat fi Fada'il Ale Muhammad, bincike: Mohsen Kochebaghi, Kum, mazhabar Ayatullah al-Marashi, 1404H.
- غضنفری، علی و مصطفی زارعی بلوط بنگان، «رحمة للعالمین بودن پیامبر(ع) در قرآن از نگاه تفاسیر فریقین»، فصلنامه مطالعات تقریبی مذاهب اسلامی، شماره ۴۱، پاییز ۱۳۹۴ش.
- هاشمی شاهقبادی، سید رضا، «بررسی مفهوم رحمة للعالمین در سیره نبوی»، مطالعات اهلبیتشناسی، شماره۱، پاییز و زمستان ۱۳۹۳ش.