Jana'iza tareda Binne Hazrat Fatima (S)

Daga wikishia
Wannan labarin yana magana ne game da jana'izar Sayyida Fatima (A.S) da kuma binne ta. Domin neman bayani kan abubuwan da suka shafi wannan batu , duba: Wurin da Aka Binne Hazrat Fatima (S) da kuma Shahadar Hazrat Fatima (S).
Zanen "Lahutiya" tare da fasahar fentin mai, na Hasan Ruhul Amini

Jana’iza da Binne Hazrat Fatima (s) (Larabci:تشييع السيدة فاطمة الزهراء (ع) ودفنها)ishara ce dangane da Rakiya da Binne Jana’izar Hazrat Fatima (S)a boye cikin Dare, a shekara ta 11 hijiri Kamari, Fatima (S) ta yi wasiyya da cewa a binneta a boye kuma cikin dare don gudun kada Abubakar Ibn Abi Kuhafa da Umar Bn Khaddab su yi tarayyya cikin binne Jana’izarta, wannan wasiyya tana nuni fushinta kan abubuwan da suka bayan wafatin Annabi (S.A.W) An rana Jana’izarta cikin dare tareda binneta da rakiyar yan tsirarun mutane misalin Imam Ali (A.S) Imam Husaini (A.S) Akilu Bn Abi Talib, Abbas Bn Abdul-Mutallib, Ammar Bn Yasir, Mikdadu Bn Aswad, Zubairu Bn Awam, Abu Zar Gifari da Salmanul Farisi, ba tareda halartar Abubakar da Umar ba wani boyayyen wuri. Bayan Mutane sun sami labarin binneta da Daddare sai Umar BN Khattab ya nemi a tonata domin su kara yi mata Sallah, sai dai cewa bayan barazanar da Imam Ali (A.S) yayi sun hakura da tonota.

Shahadar Hazrat Fatima (S)

Asalin Makala: Shahadar Hazrat Fatima (S) Fatima (S) diyar Annabi Akram (S.A.W) bayan rashin lafiya ta wani lokaci sakamakon ciwon aka ji mata cikin abubuwan da suka afku bayan wafatin Annabi (S.A.W) a Shekara ta 11 hijiri Kamari [1] dangane da tarihin lokacin da ta yi Shahada akwai maganganu kai tsakanin kwanaki 40 zuwa watanni 8 bayan Wafatin Annabi (S.A.W) [2] wasu ma sun tafi kan kwanaki 95 bayan wafatin Annabi (S.A.W) [3]ma’ana 3 ga watan Jima Sani [4] itace maganar da tafi shahara a wurin `Yan Shi’a [5] amma kuma akwai batun kwanaki 75 bayan wafatin Annabi (S.A.W) ma’ana 13 ga watan Jimada Awwal [6]

Taron Mutane domin Halartar Raka Jana’aiza

Hazrat Fatima (S) ta bar duniya bayan faduwar rana [7] bisa doga da abinda Fattal Naishaburi ya nakalto cikin littafin Raudatul Alwa’izin Mutanen Madina sun je gidan Imam Ali (A.S) sun zauna suna jira su Sallaci gawarta, sai dai cewa Abu Zar ya je wurinsu ya gaya musu cewa an jinkirta Rakiyar Jana’izarta sai kowa ya tafi ya gama gabansa [8] Abbas Baffan Annabi (S.A.W) ya nemi Imam ALI (A.S) ya tara Muhajirun da Ansar domin Rakiyar Jana’iza da sallah, ya gaya masa cewa yin hakan kara kawata addini ne, sai Imam Ali (A.S) ya bashi amsa ba zan iya yin hakan ba saboda Fatima (S) ta yi wasiyya da cewa ayi mata sallaha da binneta a boye [9] kan asasin abinda Sulaimu Bn Kais ya nakalto, a cikin daren da Fatima ta yi shahada Abubakar da Umar sun nemi Imam Ali (A.S) kada ya tara fiye da Mutum biyu a taron Jana’izarta [10]

Wankan Gawa da Sanya Likkafani da Sallah

Aikin zane kan batun jana'izar Sayyida Fatima (AS) na Reza Badar al-Sama.

Talifi da Maudu’in Jana’izar Hazrat Fatima (S) Rida Badrul Sama’ [11] Hakika Fatima (S) ta yi Wasiyya mijinta Imam Ali (A.S) ya Wanke Gawarta [12] sannan ta nemi Asma’u Bint Umaisi ta taimkawa Imam Ali (A.S) cikin wankewa 14 Imam Ali (A.S) da Taimakon Asma’u Bint Umaisi [13] ya zartar da Wasiyya Fatima (S) [14]ya sa mata Likkafani [15] Husaini Bn Abudl-Wahab cikin littafin Uyunul Mu’ujizat [16] da Muhammad Bn Jabir cikin littafin Dala’ilul Imama [17] dukkaninsu Malaman Shi’a a karni na 5 hijiri Kamari sun nakalto cewa Imam Ali (A.S) tare da Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) sune kadai suka sallaci Jana’izar Fatima (S) amma a wasu Masadir din adadin mutane da suka yi mata Sallah ya wuce haka, Fattal Naishaburi Malamin Shi’a a karni na 5-6 cikin littafin Raudatul Wa’izin [18] da Fadlu Bn Hassan Ɗabarasi Malamin Shi’a a karni na 6 cikin LIttafin Elamul Alwara [19] duka sun nakalto cewa Kari kan Imam Ali (A.S) da Imam Hassan da Husaini (A.S) akwai Akilu dan’uwan Imam Ali (A.S), Ammar, Mikdad, Abu Zar, Salmanu, Buraidatu Bn Husaibi da wasu adadin Mutane daga Banu Hashim duka sun halarci Sallar Jana’izarta. Allama Majlisi cikin Biharul-Anwar ya nakalto wata riwaya cewa mutane da suka halarci sallar Jana’izarta sun kasance Salmaul Farisi, Abu Zar Gifari, Abdullahi BN Mas’ud, Abbas Bn Abdul-Mutallib da kuma Zubairu BN Awam [20] cikin littafin Sulaimu Bn Kais ya zo cewa Abbas Baffan Annabi (S.A.W) shima ya halarci Sallar Jana’izar Hazrat Fatima (S) kafin ma a fara sallar [21]

Dalilin Kin Sanar da Mutane

Dalilin boye taron Jana’iza ya kasance ne sakamakon Wassiyar Fatima (S) bisa abinda Fattal Naishaburi ya nakalto, hakika Fatima (S) ta yi wasiyya ga Imam Ali (A.S) cewa kada ya bada izini ga daya daga mutanen da suka zalunce shi suka kwace masa hakkinsa da su halarci sallar Jana’izarta [22] haka kuma ta yi wasiyya a binneta cikin duhun Dare lokacin da mutane suke bacci [23] Shaik Saduk shima ya rawaito cewa lokacin da aka tambayi Imam Ali (A.S) kan dalilin binneta cikin Dare a boye sai ya basu da: hakika Fatima ta yi fushi da wasu mutane kuma bata son su halarci Rakiyar Jana’izarta [24] Ibn Kutaiba Dinawari Malamin Hadisi a bangaren Ahlus-Sunna a karni na 3 hijiri Kamari shima ya nakalto cewa Fatima ta yi wasiyya a binneta da duhun Dare don kada Abubakar ya halarci Jana’izarta [25]

Jana’iza

Bayan Imam Ali (A.S), ya binne Fatima (S) sai ya yi magana da kabarin Manzon Allah (S.A.w):'
“Ya Manzon Allah, saboda rasuwar zababbiyar ‘yarka hakurina ya yi karanci, karfina da karfin jikina sun duk sun tafi... An mayar da wannan ajiyar, wannan amana ta koma wurin mai ita. Bakin ciki ba ya ƙarewa; Ba zan yi barci kullum ba sai Allah Ya ba ni gidan da kuke. Ba da daɗewa ba, 'yarka za ta gaya maka yadda al'ummarka suka taru suka zalunce ta.

[26]

Asalin Makala: Mahallin da aka Binne Hazrat Fatima (S) Tarikh Yakubi daya daga cikin Masadir na tarihi a karni na 3 ya zo cewa an binne Jana’izar Fatima (S.AW) cikin dare, a lokacin Jana’aizarta kadai Salmanu da Abu Zar da Mikdad ne suka halarta [27] Fattal Naishaburi a adadin da ya nakalto kasa da haka ne [28] Ibn Shahre-Ashub cikin littafin Manakib cikin wata riwaya Mursala ya nakalto cewa lokacin da Imam Ali (A.S) ya ajiye Jana’izar Hazrat Zahra (S) kusa da ramin Kabari kwatsam sai ga wani Hannu ya fito daga cikin Kabarin ya karbeta sai kuma ya bace aka dena ganinsa [29] Imam Ali (A.S) ya goge duk wata Alama da zata sa a gane Kabarinta [30] ta yanda hatta wurin da aka binne ta ba za a iya gane shi ba, akwai maganganun mabambanta dangane da wurin da aka binneta [31] daga jumlarsu: Raudatul Annabiyi [32]

Waki’o’in da Suka Faru Bayan Jana’iza

A Duba: gina Kaburbura domin Boye Kabarin Fatima (A.S) Imam Ali (A.S) a yunkurin na cigaba da boye Kabarin Fatima (A.S) da kuma hana gano shi, bayan ya kawar da duk wani Kufai da alama da zata sa a gano Kabarin [38] ya gina Kaburbura har guda bakwai [39] a wani nakali ma an ce sun kai guda Arba’in [40] Cikin littafin Sulaimu Bn Kais ya zo cewa a Safiya bayan kwana daya da binne Fatima (A.S) Abubakar da Umar Bn Khaddab tareda wasu Mutane sun taru sun tafi su yi sallah kan Jana’izar Fatima (S) sai Mikdad ya ce musu an riga an binne ta tun jiya da daddare [41] Bayan Mutane sun samu labarin binne Fatima (S) da kasancewar basu samu damar halarta Jana’izarta ransu yayi masifar baci sun dinga zargin junansu [42] bisa nakalin Sulaimu Bn Kais, Umar Bn Khaddab bayan ya samu labarin yi mata sallah da binneta a boye ya cewa Abubakar: ai na gaya maka za su aikata haka [43] haka kuma Umar Bn Khaddab yayi Jayayya da Abbas Bn Abdul-Mutallib da ya kuma tuhumi Banu Hashim da Hassada, Abbas yana ganin binneta ya faru sakamakon wasiyya da ta yi ya gaya ma Umar cewa wasiyya ce ta yi kada a baku damar ku halarci Jana’izarta [44] bisa abinda ya zo cikin Biharul-Anwar, Umar Bn Khaddab [1] yace wasu a kirawo ba’arin Matan Musulmai domin su tone Kabari a fito da Jana’izar domin mu yi mata sallah karo na biyu mu yi ziyara [45] lokacin da Imam Ali (A.S) yaji wannan yunkuri da Umar yake yi, yayi matukar fushi ya dauki Takobinsa ya tafi Makabartar Baki’i [46] bayan Jayayyar da suka yi da Umar [47] ya gaya Umar idan na fito da Takobina daga Kubenta ba zna komar da ita ba sai bayan na sare maka kai [48] haka ya juya ya gayawa suke yunkurin tone Kabarinta yace musu duk wanda ya `daga dutse daga wannan Kabarin sai na Kashe shi [49] bayan wannan Barazana da yayi sai Umar ya janye ya juya ya tafi [50] kan asasin wasu Nakali bayan wannan tattaunawa, sai Abubakar ya baiwa Imam Ali (A.S) hakuri ya kwantar masa da hankali ya gaya masa cewa ba za ayi abinda baya so ba [51]

Bayanin kula

  1. Tusi, Misbah Al-Mutahjad, 1411 AH, juzu'i na 2 shafi na 793.
  2. Shahidi, Zindigani Fatemeh Zahra, 1363, shafi na 154.
  3. Tabarsi,Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
  4. Tusi, Misbah Al-Mutahjad, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 793.
  5. Shabiri, “Shahadat Fatima (AS)”, shafi na 347.
  6. Kulaini, Al-Kafi, 1363, juzu'i na 1, shafi na 241 da 458.
  7. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 200.
  8. Fatal Nishaburi, Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 151-152.
  9. Sheikh Tusi, al-Amali, 1414H, shafi na 156.
  10. Salim bin Qays, Kitabu Sulaim Bn Qays al-Hilali, 1405H, juzu’i na 2, shafi na 870.
  11. <a class="external text" href="https://rahyafteha.ir/49936/">مجموعه آثار استاد رضا بدرالسماء برای حضرت زهرا(س)</a>
  12. Yaqoubi, Tarikh Yakubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 115.
  13. Ibn Shahr Ashub, Manakib Ale Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 364.
  14. Yaqoubi, Tarikh Yakubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 115.
  15. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 201.
  16. Ibn Abd al-Wahhab, Uyun Al-Mujizat Qum, shafi na 55
  17. Tabari Amoli, Dalai Al-Imama, 1413H, shafi na 136.
  18. Fatal Nishaburi,Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 151-152.
  19. Tabarsi,Ealamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
  20. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 200.
  21. Sulaim bin Qays,Kitabu Sulaim bin Qays al-Hilali, 1405H, juzu’i na 2, shafi na 870.
  22. Fatal Nishaburi,Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 151.
  23. Fatal Nishaburi,Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 151.
  24. Sheikh Sadouq, Amali, 1400 AH, shafi na 658.
  25. Ibn Qutaiba, Tawil Muktalafil Hadis 1999, shafi na 427.
  26. Nahj Al-Balaghah, hadisi na 193, 1377, shafi na 421-420
  27. Yaqoubi, Tarikh Yakubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 115.
  28. Fatal Nishaburi, Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 151-152.
  29. Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 365.
  30. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 193.
  31. Tabarsi,Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
  32. Tabari Amoli, Dala'il Al-Imamah, 1413H, shafi na 136.
  33. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 461.
  34. Ibn Abd al-Wahhab, Uyun Al-Mujizat, Qum, shafi na 55.
  35. Tabari, Tarikh Al-Umam wa-Al-Muluk, 1387H, juzu'i na 11, shafi na 599.
  36. Ibn Sa’ad, Tabaqat Al-Kubra, 1410H, juzu’i na 4, shafi na 33.
  37. Najmi, “ Kabari Fatima (AS) Ya-Kabari Fatima Bint Asad”, shafi na 100.
  38. Fatal Nishaburi, Raudatul Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 152.
  39. Ibn Shahr Ashub, Manaqib al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 363.
  40. Ibn Abd al-Wahhab, Uyun Al-Mujizat, Qum, shafi na 55.
  41. Sulaim bin Qays, Kitabu Sulaim bin Qays al-Hilali, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 870-871.
  42. Ibn Abd Al-Wahhab, Uyun Al-Mujizat, Qum, shafi na 55; Tabari Amoli, Dalai al-Umamah, 1413H, shafi na 136
  43. Sulaim bin Qays, Kitabu Sulaim bin Qays Al-Hilali, 1405H, juzu’i na 2, shafi na 871.
  44. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 304.
  45. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 304.
  46. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 212.
  47. Tabari Amoli, Dala'il Al-Imamah, 1413H, shafi na 137.
  48. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 304.
  49. Tabari Amoli, Dala'il Al-Imamah, 1413H, shafi na 137.
  50. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 304.
  51. Tabari Amoli, Dala'il Al-Imamah, 1413H, shafi na 137.

Nassoshi

  • Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, bincike: Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugun farko, 1410H.
  • Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Manaqib Ale Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), Qum, Allameh Publications, bugu na farko, 1379H.
  • Ibn Abd al-Wahhab, Hossein, Uyoun Al-Mujizat, Kum, Al-Davari School, 1st edition, beta.
  • Ibn Qutaiba Dinuri, Abdullahi bin Muslim, Tawilu Muktalafil hadis, Bija, Al-Ishraq, 1999.
  • Salim bin Qays,Kitabu Sulaim bin Qays Al-Hilali, mai bincike kuma mai karantawa: Muhammad Ansari Zanjani Khoini, Qum, bugun Al-Hadi, bugu na farko, 1405H.
  • Shabiri, Sayyid Mohammad Javad, "Shahadat Fatimah (AS)",Ya- Fatema Bint Asad (A.S) Daneshnameh, Juzu'i na 1, Tehran, Cibiyar Bincike kan Al'adun Musulunci da Tunani, Bugu na 1, 2014.
  • Shahidi, Sayyid Jafar, Rayuwar Fatemeh Zahra, Tehran, Gidan Buga Al'adun Musulunci, 1363.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Mali, al-Alami, Beirut, bugu na biyar, 1400H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Misbah Al-Mutahjad da Selah al-Mutabbad, Beirut, Fiqh al-Shi'a Foundation, bugu na farko, 1411H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Amali, Kum, Darul Taqfah, bugun farko, 1414H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Elamul Al-Wara, Qum, Cibiyar Al-Baiti, bugun farko, 1417H.
  • Tabari Amoli, Muhammad bin Jarir, Dala'il Al-Imamah, Qum, Ba'ath, bugun farko, 1413H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al’umam wa Al-Muluk, bincike: Ibrahim, Muhammad Abulfazl, Beirut, Dar al-Trath, bugu na biyu, 1387H.
  • Fatal Neishabouri, Muhammad bin Ahmad, Raudatul Al-Waaziin da Basira Al-Mutaaziin, Kum, Razi Publications, bugun farko, 1375.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, edita: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
  • «لاهوت در تابوت»، * «

مجموعه آثار استاد رضا بدرالسماء برای حضرت زهرا(س)»

  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • نجمی، محمدصادق، «قبر فاطمه(س) یا قبر فاطمه بنت اسد»، میقات حج، شماره۷: بهار ۱۳۷۳ش.
  • Nahj al-Balagha, wanda Abdul Mohammad Aiti ya fassara, Tehran, bugun Farzan Rooz da bincike, 1377.
  • Yaqoubi, Ahmed bin Abi Yaqoob, Tarikh Yaqoubi, Beirut, Dar Sadir, bugun farko, beta.