Jawad
Jawad (Larabci: جواد الأئمة (لقب)) yana daga Mafi shaharar laƙubban Imam Muhammad Taƙiyyu (A.S) Imami na tara ga `yan Shi'a[1] ma'anarsa shi ne Mai Kyauta da Karamci.[2] an naƙalto cewa Imami na tara ya kasance cikin mutanen da aka sansu da yawan kyauta, akai masa laƙabi da Jawad.[3] a cewar Baƙir Sharif ƙarashi wanda ya mutu shekara bta 1433 h ƙamari, Mai binciken tarihin Muslunci cikin littafin Hayatul Al-Imam Muhammad Jawad (A.S), Imam Muhammad Taƙiyyu (A.S) sakamakon yawan kyauta da Ihsani ga Mutane sai mutane suka bashi laƙabin Jawad[4] karamci da kyautar Imam jawad (A.S) ya kai haddin da ya banbanta shi daga sauran Mutane ya zama mutum na daban.[5] Cikin littafin Kashaful Gumma talifin ƙarni na Bakwai tare da Alƙalamin Hafiz Abdul-Aziz Masanin Tarihi da Fiƙihu da Hadisi kuma Mabiyin Mazhabar Hanbaliyya, ya naƙalto cewa Imam Muhammad Jawad shi ne wanda aka yi masa laƙabi da Jawadul A'immma.[6] haka kuma Imam Jawad (A.S) a cikin Du'a'u Tawassul an ambace shi da sunan Jawad.[7] Muhammad Husaini Isfahani Garawi wanda ya mutu shekara ta 1361 h ƙamari, Mawaƙi sannan kuma Mujtahidi ya rerawa Imam Jawad waƙa kamar haka:
Tarjama: Shi ne mai kyauta da bata da ƙarshe kuma kyautarsa ita ce ƙarshen burin dukkanin buri. Shi ne Mai kyauta da kyautarsa ta gudana ko'ina da ina* kuma kyautarsa mabayyanarsa kyautar Allah. Shi ne Mai Kyauta tsantsar kyauta ba iyaka*lallai kyautarsa itace ɗigon farawa da ƙarshe* Dukkanin abin da yake duniya daga failarsa yake* shi kyauta tana cikin zatinsa.[8]
A Duba Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Shushtri, Ahƙaƙ al-Haƙ, 1409 AH, juzu'i na 29, shafi na 7.
- ↑ Firouzabadi, Al-ƙamoos Al-Muhait, juzu'i na 4, shafi na 341.
- ↑ Dhahabi, Tarikhul Islam, 1407H, juzu'i na 15, shafi na 385.
- ↑ ƙurashi, Hayat al-Imam Muhammad al-Jawad (a.s.), 1418 AH, shafi na 23.
- ↑ Khanji Esfahani, Wasilatul Khadim, 1375, shafi na 253.
- ↑ Erbali, Kashf al-Ghumma, Dar al-Azwa, juzu'i na 3, shafi na 137.
- ↑ ƙomi, Mufatih al-Janan, 1415H, 185.
- ↑ Gharaɓi Esfahani, Al-Anwar al-ƙudsiyeh,Mausu'atul Almaref Islamiyya, shafi na 104.
Nassoshi
- Erbali, Ali bin Isa, Kashf al-Ghumma, Beirut, Dar al-Azwa.
- Khanji, Fazullah Roozbahan, Wasilatul Al-Khadim zuwa Al-Mukhdoom a cikin bayanin sallolin Ma'asumai goma sha huɗu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, Kum, Ansari, 1375.
- Dhahabi, Tarikh al-Islam, bincike: Omar Abd al-Salam Tadmari, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1407H.
- Gharaɓi Esfahani, Mohammad Hossein, Al-Anwar Al-ƙudsiyeh, Islamic Encyclopaedia Institute, Beta, Bija.
- Firouzabadi, Muhammad bin Yaƙub, Al-ƙamoos Al-Muhait, Binna, Bija.
- ƙurashi, Baƙer Sharif, Hayat al-Imam Muhammad al-Jawad (a.s.), Amir Publishing House, 1418H.
- ƙomi, Abbas, Mofatih al-Jannan, Beirut, Darul Malak, 1415H.