Aba Abdillah (Alkunya)

Daga wikishia

Aba Abdillah أبو عبد الله (كنية) Alkunya ce ta Imam Husaini (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S) ana amfani da Alkunya a Al’adun Larabawa don girmamawa ga Mutum, cikin riwayoyi an kawo sunayen Imaman Shi’a da Alkunyoyinsu, cikin litattafan riwaya duk sanda ka ga an yi amfani da tsuran Alkunyar Aba Abdillah ba tare da Asalin suna ba to Imam Sadiƙ (A.S) ake nufi ba.

Alkunya cikin Al’adar Larabawa

Ku duba: Alkunya.

Cikin Al’adun larabawa Alkunya wani suna ne da ake amfani da shi domin girmamawa. [1] galibi Alkunya ta na kasancewa da lafazin Abu, Aba da Abi da take da ma’anar Baban, Ummu da ma’anar Babar, misalin Abu Hassan (baban Hassan) Abu Qasim (Baban Qasim) Abi Bakar da Ummu Kulsum (Babar Kulsum). [2]

Alkunyoyi Da Imamai Suka yi Tarayya a Cikinsu

Cikin mafi yawa yawan Hadisai ana kiran Imamai ne da Alkunyoyinsu, [3] yawancin Alkunyoyinsu sun yi tarayya cikinsu. [4] alal misali Alkunyar Abu Jafar ana amfani da ita kan Imam Baƙir (A.S) da Imam Jawad (A.S), haka kuma Imamai biyar sun yi tarayya cikin Alkunyar Abu Hassan, sune: Imam Ali (A.S) Imam Sajjad (A.S) Imam Kazim (A.S) Imam Rida (A.S) da Imam Hadi (A.S). [5]

Amfani Da Kalmar

Aba Abdillah a harshen Larabci tana zuwa da surorin Abu Abdillah da Abi Abdilla, Alkunya ce da Imam Sadiƙ (A.S) da Imam Husaini (A.S) suka yi tarayya cikinta. [6] kan asasin rahotan littafin Tazallumil Az-Zahra, Annabi (S.A.W) ya sanya Imam Husaini (A.S) sunan Aba Abdillah. [7] haka kuma an yiwa Imam Sadiƙ (A.S) Alkunya da Aba Abdillah sakamakon sunan ɗansa na biyu ya kasance Abdullahi Afɗahu. [8] Cikin litattafan riwaya ba a naqalto hadisai masu yawa ba daga Imam Husaini (A.S). [9] sabaninsa an rawaito aksarin hadisan Shi’a ne daga Imam Sadiƙ (A.S) [10] da wannan dalili ne duk sanda riwaya ta zo da tsuran sunan Aba Abdillah ba tare da jingina wani suna jiinta ba to kai tsaye Imam Sadiƙ (A.S) ake nufi ba. [11]

Bayanin kula

 1. Farhang Omid, a karkashin kalmar "کنیه".
 2. Farhang Omid, a karkashin kalmar "کنیه"
 3. Manager Shanachi, Ilmul al-Hadith, 2013, shafi na 192.
 4. Manager Shanachi, Ilmul al-Hadith, 2013, shafi na 192
 5. Manager Shanachi, Ilmul al-Hadith, 2013, shafi na 192
 6. Manager Shanachi, Ilmul al-Hadith, 2013, shafi na 192
 7. Mausu'atu Kalemat Imam Husaini, 1415 Hijira, shafi na 39.
 8. Paktachi, “Jafar Sadiƙ (AS), Imam”, shafi na 181.
 9. Manager Shanachi, Alam al-Hadith, 2013, shafi na 192.
 10. Shahidi,Zendigani Imam Sadiƙ, 2004, shafi na 61.
 11. Seifi Mazandarani, Miqyasul Al-Rawat, 1422 AH, shafi na 275; Tafarshi, Naqd al-Rajal, 1418 AH, juzu'i na 5, shafi na 317.

Nassoshi

 • Paktachi, Ahmad, "Ja'afar Sadiq (a.s.), Imam", Tehran,markaz dayirat Maref buzurg Islami, 2009.
 • Tafarshi, Mustafa, Naqd al-Rajal, Qum, Al-Bait Institute, 1418 AH.
 • Saifi Mazandarani, Ali Akbar, Maikyasul Al-ruwat fi kulliyat Ilmil Riajal, Cibiyar Al-Nashar Al-Salami, Qom, 1422H.
 • Shahidi, Sayyid Jaafar,Zindigani Imam Sadiq Jafar bin Muhammad (AS), Tehran, Farhang Islami Publishing House, 2004.
 • Tsakanin al'adun Farisa.
 • luggatnameh na Dehkhoda.
 • Manager Shanachi, Kazem, Alam al-Hadith, Qom, Islamic Publications Office, 16th edition, 2013.
 • Bagheral Uloom Research Institute, Encyclopedia of Word Imam Hossein, Qum, Danesh, bugu na biyu, 1415 AH/1374 AH.