Ummul Muminin
| Khadija Ƴar Khuwailid | (Aure:25 Shekarar Giwa) |
| Saudatu Ƴar Zam'a | (Aure: Kafin Hijira) |
| A'isha Ƴar Abubakar | (Aure:Shekara 2 Hijira) |
| Hafsa Ƴar Umar Bin Khaɗɗab | (Aure: Shekara 3 Hijira) |
| Zainab Ƴar Khuzaima | (Aure: Shekara 3 Hijira) |
| Ummu SalamaƳar Abu Umayya | (Aure: Shekara 4 Hijira) |
| Zainab Ƴar Jahash | (Aure: Shakara 5 Hijirta) |
| Juwairiyya Ƴar Haris | (Aure: Shekara 5 ko 6 Hijira) |
| Ummu Habiba Ƴar Abu Sufyan | (Aure: Shekara 6 ko 7 Hijira) |
| Mariya Ƴar Sham'un | (Aure:Shekara 7 Hijira) |
| Safiyya Ƴar Hayyu | (Aure: Shekara 7 Hijira) |
| Maimauna Ƴar Haris | (Aure: Shekara 7 Hijira) |
Ummul muminin ko ummahatul muminin (Larabci: اُمُّالْمُؤْمِنين) yana da ma'anar uwayen muminai kuma laƙabi ne da ya zo a Kur'ani kan matan Annabi (S.A.W).[1]
Wannan laƙabi an ciro shi daga «النَّبِيُّ أَوْلَىٰ بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ وَ أَزْوَاجُهُ أُمَّهَاتُهُمْ؛; (Annabi shi ne mafi cancantuwa ga muminai daga kawukansu kuma matansa uwayen muminai ne)[2] A cewar malaman tafsiri wannan aya tana da ma'anar cewa bayan wafatin Annabi (S.A.W) haramun wani ya auri matansa, kuma wajibi ne a mutunta su.[3] Hukuncin haramcin auren matan Annabi ya zo a aya ta 53 suratul Ahzab.[4]
A imanin malaman tafsiri na Shi'a. Wajabcin kiyaye alfarmar matan Annabi ya dogara ne da riƙonsu da umarnin ubangiji da kuma biyayye ga Imami Ma'asumi, idan suka tsallake wannan asali to za su rasa muƙamin girmama su, amma aurarsu yana nan a haramun har tashin alƙiyama, kuma alfarmarsu tana nan yadda take.[5]
Murtada Muɗahhari (Rayuwa: 1919-1980m) ya ganin cewa hikimar wannan hukunci shi ne hana mummunan amfani da su a fagen siyasa da zamantakewa cikin matsayinsu na matan Annabi (S.A.W).[6]
Bayanin kula
- ↑ Suratul Ahzab, aya ta 6.
- ↑ Suratul Ahzab, aya ta 6.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1415 AH, juzu'i. 8, shafi. 122; Tabataba'i, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i. 16, shafi. 277; Makarem Shirazi, Tafsir Numno, 1374 AH, juzu'i. 17, shafi. 205.
- ↑ Shahid Thani, Masalikul al-Afham, 1413 AH, juzu'i. 7, shafi na 79-80.
- ↑ Fayz Kashani, Al-Tafsir Al-Safi, 1416 AH, juzu'i. 6, shafi. 14; Thaqafi, Rawan Javid, 1398 AH, juzu'i. 4, shafi. 304.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, 2011, juzu'i. 19, shafi. 431.
Nassoshi
- Alqur'ani mai girma
- Thaqafi, Muhammad, Rawan Javid, Burhan Publications, bugu na uku, 1398 AH.
- Fayz Kashani, Mohsen, Tafsir Safi, Mawallafi: Dar Al-Kutb Al-Islamiyya - Iran - Tehran, 1416H.
- Tabatabaei, Sayyid Muhammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir Al-Quran, Ismailiyan, Beirut, 1393H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan, Majma’ al-Bayan, Beirut, Al-Alami Publishing House, bugu na daya, 1415H.
- Shahid Thani, Zainul-Din ibn Ali, Masalekul al-Afham IlaTanqih Shara’i al-Islam, Qum, Mu’assasa Al-Ma’arif Al-Islamiyya, 1413H.
- Motahari, Morteza, Tarin Ayyuka, Sadra, Tehran, 1384H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namune, Dar Al-Kutb Al-Islamiyya, Tehran, 1374H.
