Kausar

Daga wikishia

Kausar (Larabci: الكوثر) kalma ce ta Kur'ani kuma tana daga Lakubban Hazrat Zahra(A.S)[1] wannan kalma cikin Kamus tana da ma'anar alheri mai tarin yawa,[2] wannan kalma guri daya rak ta zo cikin Kur'ani Mai girma cikin suratul Kausar.[3] Dangane da tafsiri da misdakinta akwai sabani da mahanga daban-daban sannan akwai maganganu masu tarin yawa a kanta,[4] wasu ba'arin daga tafsirorin Kausar sun zo kamar haka: Korama a cikin Aljanna, muslunci, Annabta, Kur'ani, ilimi da hikima, Tafkin Kausara, ceto, yawan Mataimaka da Mabiya da kuma tsatso da `ya`yansa.[5] Kamar yanda Mawallafin littafin Majma'ul Albayan yake cewa dukkanin fuskokin daidai ne; saboda shi lafazin Kausar ya tattaro alheri mai yawa a duniya da lahira da zai iya daukar dukkanin fuskokin da aka kawo,[6] Malam Fakrul Razi yana cewa Tafsirin Kausar wata Korama ce a cikin Aljanna wannan shi ne ya fi shahara kuma shi akafi rawaita.[7] Allama Taba'taba'i ya ce: abinda ake nufi da Kausar shi ne yawaitar zuriyar Annabi (S.A.W), domin zahirin Kalmar (Abtar) da ya zo a karshen suratu Kausar ya na nufin mai yankakken baya, saboda haka Kausar ma'anarta ta yawan zuriya tafi dacewa da martanin da akai kan kalmar Abtar mara zuriya.[8] A mahangar Malaman Tafsiri na Shi'a abinda ake nufi da Kausar a suratu Kausar shine Hazrat Zahra (S) saboda sabanin abin da Asu Ibn Wa'ilu ya kirayi Annabi (S.A.W)[9] da shi da cewa mutum mai yankakken baya, sai Allah ya yawaita zuriyarsa ta hanyar diyarsa Fatima (S).[10]

Yawaitar Tsatson Fatima (S) a Duniya

A yau a wannan zamani cikin kasashe masu yawa a duniya zaka samu Sharifai masu tarin yawa , alal misali a kasashen Iran da sauran kasashen Larabawa, kasar Marokko da Tunisiya akwai tsatson Idris Ibn Abdullahi Ibn Hassan wanda ya kafa Daular Shi'a ta Idrisawa har zuwa yau din akwai tsatsonsa birjik, haka a kasar Indunisiya akwai gidajen Habashawa, da Alawiyya masu tarin yawa, a kasar Yaman akwai tarin gidajen Sharifai daga tsatson Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) a garin Aswanu da yake a kasar Masar akwai wani babban gida da ake kiransu da Ja'afira da nasabar su take tikewa ga Imam Sadiƙ (A.S), sannan a kasashen Indiya da Fakistan akwai Sharifai Ridawi jinin Imam Rida da Nakawi Imam Aliyu Takiyu (A.S),[11] wasu Malamai tafisiri sun kawo wata fuska kan tafsirin Kalmar Kausar sune: ilimi da aiki, Annabta, Kur'ani, da daukaka duniya da lahira da tsarkaka zuriya daga Hazrat Fatima Zahara (S) sun kara da cewa bayan shahadar Shugaban Shahidai amincin Allah ya tabbata a gare shi, babu Namiji wanda ya rage daga Ahlil-baiti sai Imam Sajjad (A.S) kadai ya rage , sai Allah ya cika alkawarin sa ya cika duniya da zuriyar sa.[12]

Bayanin kula

  1. Ansari Zanjani, Al-Musaw'at al-Kabri an Fatimah al-Zahra', 1428 AH, juzu'i na 22, shafi na 9 da
  2. Fakhrazi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 32, shafi na 313; Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 370.
  3. suratu kausar aya ta 1
  4. Duba: Fakhrazi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 32, shafi na 313-316; Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 370.
  5. Duba: Fakhrazi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 32, shafi na 313-316; Tabarsi, Majma Al Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 836; Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 370.
  6. Tabarsi, Majma Al Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 837.
  7. Fakhrazi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 32, shafi na 313.
  8. Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 370.
  9. Ibnul Arabi, Tafsiri Ibn Arabi, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 424.
  10. Duba: Khorramshahi, Daneshnameh Quran wa Quran Fajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi 1269; Ehsanifar, Ulum Hadith, 2003, shafi na 69-53 (Shaidai da nassosin tafsirin Kausar ga zuriyar Annabi).
  11. Dagher, masadir dirasatul Adabiyya, 1983AD, Sashe na 4, shafi 364-366.
  12. Hosseini Shah Abdul Azimi, Hossein, Tafsir Ezni Ashari, 1363, juzu'i na 14, shafi na 363.

Nassoshi

  • Ibn al-Arabi, Mohiuddin, Tafseer Ibn Arabi, Tahqiq, Tasahih da Gabatarwa: Shaykh Abdul Warith Mohammed Ali, Buga: Sunnah ta Farko Buga: 1422 - 2001 AD, Buga: Lebanon/Beirut - Dar al-Kitb al-Ilmiyah, Mawallafi: Dar al-Kitb al-Ilmiyah
  • Ehsani Far Langroudi, Mohammad,[http://ensani.ir/file/download/article/20120426135705-3094-174.pdf
  • Ansari Zanjani, Ismail, Al-Musaw'at al-Kabri an Fatimah al-Zahra', Qom, Dalil Ma, 1428q.
  • Hosseini Shah Abdul Azeimi, Tafseer Atsni Ashri, Tehran, Miqat Publishing House, Bugu na Farko, 1984.
  • Khorramshahi, Bahauddin, Quran and Quran Pazhvi Encyclopedia, Tehran, Dostan and Nahid, 1998.
  • Dagher, Yousef Asad, Tushen Nazarin Adabi na Labarai na Renaissance, Beirut, Laburaren Gabas, 1983m.
  • Tabatbaei, Sayyid Mohammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir al-Quran, Beirut, Scientific Foundation, bugu na 2, 2011.
  • Tabarsi, Fazl ibn Hassan, Majma' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Naser Khosrow, Chap Sum, 1993.
  • Fakhrrazi, Muhammad ibn Omar, Al-Tafseer al-Kabir (maɓallan gaibi), Beirut, Dar-e-Ahya al-Tarath al-Arabi, Chapter Sum, 1420 q.