Taƙiyyu (Laƙabi)
Taqiyyu (Larabci:تقي) yana daga mafi shaharar laqubban Imam Jawad (A.S) [1] ma’anarsa shi ne Mutum Mai tsantseni da kuma tsoron Allah, [2] Baqir Sharif Qarashi Mai binciken tarihin Muslunci wanda ya mutu shekarar 1433 h qamari, a cikin littafin Hayatu Imam Jawad (A.S) dangane da danganta wannan laqabi ga Imami na tara ga `yan Shi’a yana cewa ya samu wannan laqabi ne kasancewarsa Mutum Mai tsoran Allah, da yawan Tuba da kuma Tawassali kuma bai tava sallamawa son ransa da kuma buqatun Sarki Mamun Abbasi ba. [3] Kan asasin wata riwaya da Shaik Saduq ya naqaltota cikin littafin Ma’ani Akhbar, Imam Jawad (A.S) ya samun wannan laqabi na taqiyyu sakamakon koda yaushe yana gabatar da tsoron Allah a hallararsa, sai Ubangiji ya kare shi daga sharri da makircin Halifa Mamun lokacin da ya shirya Makircin kashe shi. [4] [Tsokaci 1]
Bayanin kula
Tsokaci
- ↑ anaa kiran shi da MUhammad bin Ali Sani (A.S) da taqiyyu sabida tsoron Allah azza wa jalla sai ALlah ya kare shi daga sharrin sarki mamun
Nassoshi
- Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Lasan Al-Arab, Kum, Adab al-Hawza, 1405H.
- Qurashi, Baqer Sharif, Hayat Al-Imam Muhammad al-Jawad (a.s.), Amir Publishing House, 1418H.
- Sadouq, Muhammad bin Ali, Ma'ani Al-Akhbar, Kum, Jamia Modaresin, 1379H.
- Majlesi, Mohammad Baqer, Jala,ul Al-Ayoun, Qom, Sarwar, 2002.