Mujtaba (Laƙabi)

Daga wikishia

Mujtaba (laƙabi), (Larabci: المجتبى (لقب)) ma’ana zaɓaɓɓe, yana daga cikin laƙubban Imam Hassan (A.S) [1] ana amfani da wannan laƙabi kan Annabi (S.A.W) [2] da ma sauran Imamai (A.S), [3] cikin wata huɗuba daga Imam Sadiƙ (A.S) an naƙalto cewa wannan laƙabi ya zo da unwanin hususiyar Imami (A.S) [4] amma sai dai cewa ya shahara kan Imam Hassan (A.S) [5] cikin wata riwaya da aka naƙalto daga Imaman Shi’a, an ambaci Imam Hassan (A.S) da wannan laƙabi na Mujtaba, [6] haka cikin Du’a’u Tawassul an ambace shi da wannan laƙabi Al-Mujtaba, [7] an ce cikin Hirzin Imam Sajjad (A.S) akwai Kalmar (Alhassan Almujtaba) a samansa [8] Mujtaba yana bada ma’anar zaɓaɓɓe [9] Allama ɗabaɗaba’i a ƙarshen aya ta 121 Suratul Nahal, ya fassara Kalmar Ijtiba’u kamar haka haƙiƙa Allah ya zabi Imami Ma’asumi domin kansa, cikin surar da ya nesantar da shi daga warwatsewa ya kuma shiryar da shi kan Madaidaicin Tafarki. [10] Ance wannan laƙabi duk dacewa yana da kebantaccen Mafhumi sai dai kuma tare da haka ana amfani da shi kan bakiɗayan Imamai, amma kuma Imam Hassan (A.S) kaɗai ne ya shahara da wannan laƙabi, ance wannan laƙabi ya samu tun lokacin rayuwarsa. [11]

Bayanin kula

  1. Ibnshahrashob, Al-Manaƙib, 1379 AH, juzu'i na 4, shafi na 29.
  2. Zarandi Hanafi, Nazme Durar Al-Samatin, 1425 AH, shafi na 27.
  3. Duba Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403H, juzu'i na 25, shafi na 150.
  4. Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 25, shafi na 150.
  5. Nizami Hamdani, Al-Maarif Al-Rafi'a, 2009, shafi na 314.
  6. Paknia Tabrizi, "Ta'ammuli dar Mustanadat wa Mashhurtarin Alkab Ma'sumin , amincin Allah ya tabbata a gare su", shafi na 132.
  7. ƙommi, Mafatih Al-Janan, 1415H, 185.
  8. Attardi Guchani, Masnad Al-Imam al-Sajjad, 1379, juzu'i na 2, shafi na 32.
  9. Montazeri, Durushaye Nahj Al-Balagha, 1395, shafi na 398.
  10. Tabatabaei, Al-Mizan, 1390H, juzu'i na 12, shafi na 368.
  11. Fatahi, Anwar Elahi, 1390, shafi na 274.

Nassoshi

  • Ibnshahrashob, Muhammad bin Ali, Manaƙib Al Abi Talib, Kum, Allameh, 1379H.
  • Paknia Tabrizi, Abdul Karim, "Ta'ammuli dar Mustnadat wa m,ashhurtarin Alkab Ma'asumin , (A.S)", Mahinameh Muballigin , No. 145, Oktoba da Nuwamba 2013.
  • Zarandi, Muhammad bin Yusuf, Nazme Durar Al-Samatin, Beirut, Dar Ihya al-Tarath al-Arabi, 1425H.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, bugu na biyu, 1390H.
  • Attardi ƙochani, Azizullah, Masnad al-Imam al-Sajjad, Tehran, Attard, 1379.
  • Fatahi, Hamid, Anwar Elahi, ƙum, Mirfatah, 1390.
  • ƙomi, Abbas, Mafatih al-Jannan, Beirut, Darul Malak, 1415H.
  • Majlisi, Mohammad Baƙer, Bihar al-Anwar, mawallafi: Mu'assasar Al-Wafa, bugu na biyu, 1403 AH, ba a wurinsa ba.
  • Montazeri, Hossein Ali, Durushaye Az Nahj al-Balagha, Tehran, Saraei, 2015.
  • Nizami Hamdani, Ali, Al-Ma'arif Al-Rafi'a fi al-Ziyarah al-Jama'a, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi, 1389.