Sadiƙ (Laƙabi)

Daga wikishia

Sadiƙ (Larabci: الصادق (لقب)) mafi shahara cikin laƙubban Imam Sadiƙ (A.S) [1] ya samu wannan laƙabi sakamakon kasancewarsa mai gaskiya cikin zancensa da aikinsa. [2] haka kuma an ce an masa wannan laƙabi saboda ba a taɓa ganin kuskurensa ba. [3] Kan asasin wata riwaya daga Imam Sajjad (A.S) ana kiran Imami na shida da laƙabin Sadiƙ domin banbance shi daga Jafar Kazzab, [4] kan asasin riwayar da aka ambata, an tambayi Ali Bn Husaini Imami Na huɗu mene ne ya sanya Mutanen Sama suke kiran Imami na shi da laƙabin Sadiƙ, alhali baki ɗayanku Imamai Ma’asumai kun kasance Masu gaskiya da faɗin gaskiya? Sai ya bada amsa: Mahaifina ya bada labari daga Kakana Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan an haifi ɗana Jafar Bn Muhammad Bn Ali ku yi masa laƙabi da Sadiƙ, saboda na biyar cikin jikokinsa za a sa masa suna Jafar zai kasance Maƙaryaci da kuma da’awar Imamanci, haƙiƙa ya kasance Jafar Kazzab a wurin Allah (Mai ƙagar ƙarya kan Allah) [5] a cikin littafin Ilalul As-Shara’i ma an yi ishara kan wannan batu. [6] Wasu ba’ari sun ce Imam Sadiƙ (A.S) ya samu laƙabin Sadiƙ sakamakon kin yarda ya shiga duk wani Miƙewa da yunƙurin kifar da hukuma mai ci a lokacin, sabida a wancan zamani duk wanda ya tara Mutane don miƙewa a kifar da gwamnati ana kiran wannan mutumi da Kazzab (Maƙaryaci). [7] Abul Farajul Isfahani wanda ya rayu tsakanin shekara ta 286-356 ya nakalto wata riwaya cikin littafin Maƙatil Aɗ-ɗalibin cewa Mansur Abbasi wanda ya yi Mulki tsakakin shekaru 136-158 lokacin da ya hau karagar Mulki ya kira yi Imam Sadiƙ (A.S) da Sadiƙ sakamakon tabbatuwar abin da ya yi labarin da ya bayar daga kashe Muhammad Bn Abdullahi Bn Hassan wanda ya fi shahara da sunan Nafsuz Zakiyya. [8] Kan asasin wani rahoto da Ibn ShahreAshub Mazandarani ya naƙalto shi a cikin Al-Manaƙib cewa Mansur Abbasi shin ne ya sanya Imam Sadiƙ (A.S) Sadiƙ bayan tabbatuwar labarin da ya bayar kan bayyanar ƙabarin Imam Ali (A.S). [9]

Bayanin kula

 1. Majlisi, Jala Al-Ayoun, 2002, shafi na 869.
 2. Muzaffar, Al-Imam al-Sadiƙ, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 190.
 3. Muzaffar, Al-Imam al-Sadiƙ, 1421H, juzu'i na 2, shafi na 190.
 4. ƙommi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 2, shafi na 1336
 5. ƙommi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 2, shafi 1336.
 6. Sadouƙ, Ilalaul Shara'i, 1408 AH, Juzu'i na 1, shafi na 274.
 7. Paktachi, “Jafar Sadiƙ (AS), Imam”, shafi na 181.
 8. Abul Faraj Esfahani, Muƙatil al-Talbeyin, 1385H, shafi na 173.
 9. Ibn Shahrashob, Manaƙib, 1379 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 273.

Nassoshi

 • Ibn Shahr Ashub, Muhammad Bin Ali, Menaƙib Al Abi Talib, Kum, Allameh, bugun farko, 1379.
 • Abul Faraj Esfahani, Ali bin Hossein, Muƙatil al-Talbeyin, Gabatarwa na Kazem Al-Muzaffar, ƙum, Darul Katab Lalprinta da Al-Nashar, 1385H/1965 miladiyya.
 • Paktachi, Ahmad, "Ja'afar Sadiƙ (a.s.), Imam", Tehran, Big Islamic Encyclopaedia, ɓolume 18, Center of Big Islamic Encyclopedia, 1389.
 • Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ilalaul Shara'i, Beirut, Al-Alami Publications, 1408H.
 • ƙommi, Sheikh Abbas, Mantehi al-Amal fi Tawarikh al-Nabi wa al-Al, ƙom, Dilil Ma, 1379.
 • Majlesi, Mohammad Baƙer, Bihar al-Anwar, Tehran, Islamia, 1363.
 • Majlesi, Mohammad Baƙer, Jala Al-Ayoun, ƙom, Sarwar, 2002.
 • Muzaffar, Mohammad Hossein, Imam al-Sadiƙ (a.s.), ƙum, Madrasin community, 1421 AH.