Baƙirul Ulumi (Laƙabi)

Daga wikishia
Wannan ƙasida ce da take magana akan taken Imam Baƙir (A.S). Domin sanin halin Imam (A.S) duba Imam Baƙir (A.S).

Baƙirul Ulumi (arabic: باقر العلوم (لقب)) ko kuma Baƙir [1] shi ne mafi Shaharar Lakabin Imam Muhammad Baƙir (A.S) ya zo cikin littafin Ilalu Shara'i an nakalto daga Jabir Ibn Yazid Ju'ufi cikin amsar da aka bayar kan tambayar cewa me ya sa Imami na biyar ake kiransa da Baƙir? Saboda shi ne wanda ya tsaga hakikar ilimi.[2]

Kamar yanda ya zo cikin littafin Wasilatul Kadim wallafar Fadalu Ibn Rozbahan, Malami daga Malumman Ahlus-sunna a karni na tara zuwa goma, cewa Annabi (S.A.W) shi ne wanda ya sanyawa Imami na biyar wannan Lakabi,[3] a cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa Annabi (S.A.W) ya sanyawa Imam Baƙir (A.S) Imami na biyar wannan Lakabi don falala kebantatta,[4] Annabi (S.A.W) ya bawa Jabir bin Abdullahi Ansari alkawri cewa zai wanzu a raye har sai ka ga `dana Muhammad Ibn Aliyu Ibn Husaini Ibn Abi Talib, wanda ake masa lakabi da Baƙir a cikin Attaura, duk sanda Allah ya sa ka hadu da shi ka isar min da gaisuwa zuwa gare shi.[5] Haka kuma cikin wani nakalin daban a cikin littafin Tazkiratul Kawas wallafar Sibdu Ibn Jauzi wanda ya mutu hijira na da shekara654 ya zo cewa Imam Baƙir sakamakon yawan sujjada ne da ya sanya goshin sa ya bushe ake kiransa da Baƙir.Sani, Uyun al-Akhbar al-Ridha, 1404 juzu'i na 2, shafi na 147.[Tsokaci 1]

Bayanin kula

  1. ƙomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 2, shafi 1263.
  2. Sadouƙ Ilalau al-Sharia, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 233.
  3. Khanji Esfahani, Wasila Khadim, 1375, shafi na 190.
  4. Mofeed, Al-Ikhtisas, 1414 s, shafi na 62.
  5. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1363, juzu'i na 46, shafi na 225.

Tsokaci

  1. ana kiransa da Bakir ne sakamakon yawan sujjadarsa wanda hakan ya tsaga goshinsa ma'ana ya bude shi ya fadada shi.

Nassoshi

  • Alami, Hassan, Ayun al-Akhbar al-Reza, Beirut, Alami Institute, 1404 AH.
  • Khanji Esfahani, Fazlullah, na Al-Khadim zuwa Al-Makhdoom, ƙum, Ansarian Publications, 1375.
  • Majlesi, Mohammad Baƙer, Bihar al-Anwar, Tehran, Islamia, 1363.
  • Mofid, Muhammad bin Nu'man, al-Ikhtasas, bincike na Ali Akbarghafari, Beirut, Dar Al Mofid, 1414 AH.
  • Sabat bin Jozi, Yusuf bin Ghazaughli, Tazkira al-khawas min umma fi zikr khaizat al-ayama, ƙom, Manshurat al-Sharif al-Razi, 1418 AH.
  • Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Ililul Sharayi, Bincike na Mohammad Sadiƙ Bahrul Uloom Najaf Ashraf, Manuscripts na Makarantar Al-Haydariyya, 1385H.
  • ƙomi, Abbas, Mentehi al-Amal, ƙom, Jamia Modaresin, 1379.