Ranar Dauhi

Daga wikishia

Ranar Dauhi (Larabci: يَوم الدَوح) wani suna ne daban na ranar Ghadir; ranar ne Annabi Akram (S.A.W) ya gabatarwa da mutane Ali (A.S) a matsayin Halifansa kuma Waliyinsa a bayansa.

Dalilin Sanya Mata Wannan Suna

Dauhu sigar jam’i ce ta Dauhatu wanda yake nufi ƙatuwar Bishiya mai rassa da ganye mai yawa tare da inuwa, a wurin da Annabi (S.A.W) ya naɗa Ali (A.S) Matsayin Halifansa akwai adadin waɗannan bishiyoyi da suka kasance bihsiyoyin da ake samunsu a Sahara. [yadash1] sun yi Sallar Azuhur a ƙasan inuwar wannan bishiyoyi, ana kiran ranar Ghadir da sunan Ranar Dauhi, kamar dai yanda tsohon Mawaƙin Shi’a Kumaitu Bn Zaid Asadi wanda ya rasu shekara ta 126 bayan hijira, yake faɗa ƙasidarsa wacce aka fi sani da Hashimiyat: [1]

ويَومَ الدَّوحِ دَوحِ غَديرِ خُم‏ أبانَ لَهُ الوَِلايَةَ لَو اُطيعا

Ranar Dauhi, Dauhi Ghadir Khum*ya bayyana da wilyarsa idan da za ayi ɗa’a Haka kuma, Imam Ali cikin wata huɗuba da ya yi cikin ɗaya daga ranakun Juma’a da ta dace da ranar Ghadir Khum ya yi ishara kan ranar Ghadir cikin amfani da sunan (Ranar Dauhi) [2]

Bayanin kula

  1. Hakimi, Hamase Ghadir, 2009, shafi na 67, bayanin kafa.
  2. Duba: Hakimi, Hamase Ghadir, 2009, shafi na 67

Nassoshi

  • Hakimi, Mohammad Reza, Hamaseh Ghadir, Qom, Dalil Ma, 2009