Karimu Ahlul-Baiti (Laƙabi)

Daga wikishia
talifin Sayyid Muhammad Taƙi Mudarrasi. littafi ne mai suna Karimu Ahlul-Baiti, kan tarihin rayuwar Imam Hassan (A.S)

Karimu Ahlul-Baiti (Larabci: كريم أهل البيت (لقب)) ma’anarsa shi ne Mai kyautar cikin Ahlul-Baiti, yana daga cikin laƙubban Imam Hassan Mujtaba (A.S) 1 an yi masa wannan laƙabi ne sakamakon yawan kyautarsa da karamcinsa, 2 kalmar (Karim) duk da cewa da farko cikin masadir an yi amfani da ita kan Hassan Bn Ali (A.S) amma cikin tarihin rayuwarsa babu littafin tarihi da ya rawaito ana masa laƙabi da wannan Kalmar in banda litattafan da suka zo daga baya-bayan nan. 4

Shaharar Imam Hassan (A.S) da laƙabin Karimu Ahlul-Baiti ta samu sakamakon wasu ƙissoshi da masu nazarin tarihi suka naƙalto su dangane da karamcinsa da kyautarsa, 5 an ce Imam Hassan (A.S) ba a taɓa ganin wani mutum daga babban gida yana kyauta ga Talakawa da Mabuƙata kamar yanda yake yi ba, 6 Imam Mujtaba (A.S) ya kasance mutum mafi kyauta a zamaninsa, ya kasance wanda ake buga misali da shi cikin yawan kyauta da karamci, shi kaɗai ne ake masa laƙabi da Karimu Ahlul-Baiti. 7

Ibn Jauzi wanda ya rasu shekara ta 654 h ƙamari, daga Malaman Ahlus-Sunna cikin littafinsa Tazkiratu Al-Khawas, ya kasance yana ganin Imamin ƴan Shi’a na biyu cikin manyan mutane da suke da ƙima a idanunsa, cikin ambaton falalolinsa ya rubuta cewa Imam Hassan Bn Ali cikin rayuwarsa karo biyu ya kyautar da bakiɗayan abin da ya mallaka cikin tafarkin Allah, sannan karo uku yana raba dukiyarsa gida biyu ya bada rabinta kyauta ga Talakawa, 8 ta kai ga an naƙalto cewa lokacin da wani Talaka ya roƙeshi taimako sai ya bashi kyautar dirhami dubu ashirin. 9

Baƙir Sharif ƙarashi wanda ya mutu shekara ta 1433 h ƙamari, daga Malaman Shi’a, dangane da laƙabin Karimu Ahlul-Baiti ya naƙalto wata riwaya daga Imam Mujtaba (A.S) da aka tambaye shi me yasa ba a taɓa samu ka bawa Mai roƙon taimako daga gareka haƙuri ba? Sai Imam ya bada amsa ya ce: nima a gaban Allah mutum ne Mabuƙaci talaka da yake neman kada Allah ya haramta masa ni’omominsa, ina jin kunya in cira fata da tsammani daga Talakawa, sannan Allah da ya ƙarfafe ni da taimakonsa yana so na taimaki mutane. 10

A cewar Sayyid Baharul Ulum wanda ya rasu shekara ta 1380 h ƙamari, wanda ya yi tahƙiƙi kan littafin Talkhisul Ash-Shafi, ya bayyana cewa Maudu’in laƙabin Imam Hassan (A.S) ya yaɗu ya faɗaɗa matuƙar gaske fiye da iya Magana a kansa. 11

Shaik Hadi Alu Kashiful Giɗa wanda ya rasu shekara ta 1361 h ƙamari, daga Malaman Shi’a a cikin ƙasidarsa da yake siffanta Imam Hassan (A.S) ya rerawa Imam Hassan Mujtaba (A.S) waƙa tare da ishara zuwa ga laƙabin Karimu Ahlul-Ba

ان الامام الحسن مُهذّبا خَیرُ الوَری جَدّاً و اُمّاً و اَبا

کریمُ اهل البیت اهلُ الکَرَم علیهم بَعد الصَّلاة سلم

Haƙiƙa Imam Hassan ya kasance tsarkakakke* mafi alherin mutane ta fuskani Kaka da Uba da Uwa. Karimu Ahlul-Baiti Ahlin Karamci* ku yi salati gare su bayan sallah. 12 A ƙasar Iran wasu Cibiyoyin taimako da jin ƙai an sanya musu sunan Karimu Ahlul-Baiti. 13

Bayanin kula

Nassoshi