Ghadir Khum

Daga wikishia
Samfurin Taswirar Ghadir Khom

Ghadir Khum (arabic: غدير خم) wani wuri ne da yake tsakanin hanyar Makka zuwa Madina sannan kuma kusa da Miqati guda biyar wanda a ranar 18 ga watan Zul Hijja shekara goma bayan hijirar Annabi (S.A.W) a wannan wuri ne ya shelantawa Musulmi cewa Ali (A.S) shi ne zai zama Halifansa kuma Magajinsa a bayansa. Ghadir Khum sunan wata qoramar ruwa ce [1] da take da nisan kilomita 4 tsakaninta da Juhufa, Juhufa tana da nisan kilomita 200 tsakaninta da Arewa maso yammacin garin Makka, Juhufa xaya daga cikin Miqatai biyar ce. [2] wannan wuri na Ghadir sakamon samuwar ruwa da kuma bishiyoyi ya kasance wurin tsayuwa da hutawar Ayarin Matafiya. [3]

Hotan Taswirar Yankin Ghadir Khum

Waki’o’i

Asalin Maqala: Waki’ar Ghadir A ranar 18 ga watan Zul Hijja shekara goma bayan hijirar Annabi (S.A.W) daga Makka zuwa Madina, a wannan wuri da ake kira Ghadir Khum ya naxa Sarkin Muminai (A.S) matsayin Waliyinsa Majivancin lamurran dukkanin Musulmi kuma halifansa, wannan waki’a an fi saninta da sunan Waki’ar Ghadir. [4]


ka duba

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, harshen Larabawa, a karkashin kalmar al-Ghadir
  2. Hamawi, Mujam al-Buldan, 1995, juzu'i na 2, shafi na 111.
  3. Ibn Khalqan, Wafyat Al-Aeyan, 1364, juzu'i na 5, shafi na 231.
  4. Qommi, Tafsirin Qummi, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 179; Ayashi, Tafsir al-Ayashi, 1380 AH, juzu'i na 1, shafi na 332.

Nassoshi

  • Ibn Khalkan, Ahmed Ibn Muhammad, Wafyat Al-Ayan, Mohaghegh Ehsan Abbas, * Ayashi, Muhammad Bin Mas'ud, Tafsirin Al-Ayashi, Hashim Rasouli, Tehran, Makarantar Nazarin Musulunci, 1380H.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Beirut, Dar Sader, Bita.
  • Qommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirin Qummi, Kum, Darul Kitab, 1404H.
  • Yaqut Hamavi, Mujam Al-Buldan, Beirut, Dar Sader, bugu na biyu, 1995.

Qum, Al-Sharif Al-Razi, 1364.