Khatamul Annabiyin (Laƙabi)

Daga wikishia
Masallacin Annabi (S.A.W) da yake a Madina

Khatamul Annabiyun (Larabci: خاتم الأنبياء (لقب)) cikamakin annabawa yana daga cikin laƙubban Hazrat Muhammad bin Abdullah Annabin Muslunci (S.A.W) laƙabi ne da yake bayanin matsayinsa Annabin Allah (S.A.W) na ƙarshe, jumlar Khatamul Anbiya ta zo cikin aya ta 40 suratul Ahzab ayar da tafi shahara da sunan ayar Khatimiya, ɗaya daga cikin dalilan imanin Musulmai da Khatimiyar Annabta ƙarshen Annabta, ita ce dai wannan ayar. [1]

Wannan jumloli biyu an naƙalto su cikin Matanin hadisai da kalmomin A'imma (A.S) misalin Addu'a ta 17 daga Sahifa Sajjadiyya, da ba'arin Huɗubobin Imam Ali (A.S) a lokacin Yaƙin Siffin [2] a cikin wani hadisi daga Imam Ali (A.S) daga littafin ƙurbul isnad [3] da kuma cikin riwayar da ta zo a littafin Usulul Alkafi [4] nan ma anyi amfani da kalmar Khatamul Anbiya.

Baha'iyyawa a cikin ƙarni na biyu h ƙamari, sun yi da'awar bayyanar sabon addini, wani lokaci zaka same su suna da'awar cewa ma'anar Khatamul Anbiya shi ne Adon da yake jikin Zobe [5] wanda yake nuni zuwa ga muƙami na musamnman ga Annabi (S.A.W) shi Ado ne na Annabawa bawai cikamakinsu ba, Annabi da babu wani Annabi da zai zo a bayansa ba, [6] wasu ba'arinsu sun ce ai Alkur'ani da jumlar Khamatun Annabiyin ya yi amfani bawai Khatamul Mursalin ba da take da ma'anar cikamakin Manzanni, saboda haka shi Annabi ne na ƙarshe bawai Manzo na ƙarshe ba, zai iya yiwuwa bayansa a aiko da sabon Manzo. [7] Malaman muslunci cikin bada amsa kan waɗannan shubuhohi na `Yan Baha'iyya sun ce Khatam a asalin kalmar tana da ma'anar tsani da wasila ta khatma da cika abu, kuma shi Zobe da wannan dalili ne ma ake kiransa da Hatimi saboda a zamanin da can da zobe ake buga tambarin kammala wasiƙa, saboda haka amfani da lafazin Khatam kan ma'anar Ado ya saɓawa ma'ana da take zuwa kwakwalwa, [8] haka kuma kamar yanda a cikin tafsirul al-amsal ya zo cewa martabar Manzanci tana sama da muƙamin Annabta duk wanda aka aiko shi da Manzanci to yana nuni cewa tuntuni shi Annabi ne, a natija zai zama lokacin da Annabci ya zo ƙarshe to da hanyar mafi cancanta zai zamana Manzanci shima ya zo ƙarshe. [9] A cikin ƙasar Iran da sauran ƙasashen Muslunci ana sanyawa wasu ba'arin masallatai, makarantu da Jami'o'i sunan Khatamun Anbiya. [10] haka ana sanya sunan Kalmar da ka ciro daga wannan suna misalin (Assalamu Ala Khatamul Annabiyin) a kan saman Zobe

Bayanin kula

  1. Duba Ɗabarasi, Majma Al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 8, shafi na 166.
  2. Nasr bin Mozahem, Waƙ'atu Al-Siffin, 1404 Hijira, shafi na 224 da 236.
  3. Himyari, ƙarb al-Asnad, 1413 AH, shafi na 9.
  4. Kulaini, Al-kafi, cafe Islamiyya, juzu'i na 2, shafi na 585.
  5. Mirza Hossein Ali Baha, Abƙan, shafi na 136; Az Arefi, Khatamit, 2006, shafi na 65.
  6. Hosseini Tabatabai, Majaraye Bab wa Baha, shafi na 163: Arefi, Khatamit, ya nakalto, 2006, shafi na 62..
  7. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 17, shafi na 338.
  8. Mesbah, Rahe Rahnamashinasi, 1376, shafi na 180..
  9. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 17, shafi na 338.
  10. <a class="eɗternal teɗt" href="http://aytmohseni.com/topic/1">«حوزه علمیه خاتم النبیین(ص)»</a>

Nassoshi

  • Arefi Shirdaghi, Mohammad Ishaƙ, Khatamiyat wa Furseshhayae No, Mashhad, Daneshgahe ulumun Islami Razaɓi, 2006.
  • Himyari, Abdullah bin Jafar, ƙurbul Al-Isnad, Al-Bait Foundation, ƙum, 1413 AH.
  • Kulaini, Mohammad bin Yaƙoub, Al-Kafi, Islamia Press, Tehran, 1363.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namunahe, Dar al-Katb al-Islamiya, Tehran, 1374.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taƙi, Tafarki da Shiriya, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, ƙum, 1376.
  • N
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma Al-Bayan, Tahkik Lajna minal Al'Ulama wal Muhakkikin Al-Aksa'iyyin, Mukaddima Seyyed Mohsen Amin, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, bugu na farko, 1415 AH/1995 AD.
  • «حوزه علمیه خاتم النبیین(ص)»، سایت رسمی حضرت آیت الله العظمی محسنی (ره)، بازدید: ۲۷ آبان ۱۴۰۲ش.asr bin Muzahim, Waƙ'atu Al-Siffin, edita: Abdussalam Mohammad Haroun, Ayatullah Murashi Najafi Library, ƙum, 1404 AH