Jump to content

Babban shafi

Daga wikishia
Encyclopedia na mazahabar Shi'a, Majma'a Ahlul-baiti (A S) na Dunya
598 Labari / 20,075 gyara cikin Hausa

Maƙalar da aka zaba

Waƙi'ar karbala ko waƙi'ar ashura, (Larabci: واقعة الطف) wani gumurzu ne da Imam Husaini (A.S) da sahabbansa suka yi gaban sojojin Kufa, waƙi'ar karbala ta faru a ranar 10 ga watan muharram shekara ta 61 bayan hijira, waƙi'ar ta faru ne sakamakon Imam Husaini (A.S) ya ƙi yarda ya yi bai'a ga Yazidu ɗan Mu'awiya, lamarin da ta kai ga shahadantar da Imam Husaini (A.S) da sahabbansa, tare da kama iyalansa matsayin fursunonin yaƙi.

Waƙi'ar Karbala waƙi'a ce mai matuƙar tayar da hankali da sosa zuciya a tarihin muslunci, da wannan dalili ne duk shekara a zagayowar wannan rana mai raɗaɗi ƴanshi'a suke shirya mafi girmamar makoki da ta'aziyya domin tunawa da irin ta'addancin da aka aikata kan iyalan Annabi (S.A.W).

Bayan mutuwar Mu'awiya ɗan Abi Sufyan a ranar 15 ga watan rajab shekara ta 60 bayan hijira, farkon fara mulkin Yazid ɗan Mu'awiya ne aka fara wannan waƙi'a, sannan waƙi'ar ta zo ƙarshe tare da dawo da fursunonin da aka kama a Karbala zuwa garin Madina, gwamnan Madina ya yi ƙoƙarin karɓarwa Yazid ɗan Mu'awiya bai'a daga Imam Husaini (A.S); da wannan dalili ne domin gujewa bai'a ga Yazid, sai ya fice daga garin Madina a cikin duhun dare, ya nufi geffan garin Makka, cikin wannan tafiya iyalansa da wasu ba'ari daga Bani Hashim da ƴanshi'arsa sun kasance tare da shi.

Imam Husaini (A.S) ya zauna a garin Makka har tsawon watanni huɗu, cikin wannan lokaci ne wasiƙun gayyata daga mutanen Kufa suka iso hannunsa, domin tabbatar da gaskiya abin da aka rubuta cikin waɗannan wasiƙu na mutanen Kufa sai Imam ya aika da Muslim ɗan Aƙilu garin Kufa, shi kuma Sulaiman ɗan Razin ya aika shi garin Basra, sakamakon cewa akwai tsammanin a kodayaushe yaran Yazid za su iya yuƙurin kashe Imam Husaini (A.S) a cikin garin Makka, a gafe guda kuma ga goran gayyatar da mutanen Kufa suka aiko masa, da wannan dalili ne a ranar 8 ga watan zil hijja Imam Husaini (A.S) tare da ƴanrakiyarsa suka tashi suka nufi garin Kufa.

Full article ...

Other featured articles: Babban shafiNafsu Mudama'innaHusaini daga Gareni Yake

Shin kasani ...
  • ... Ko ka san Mu'ujizozin Annabi (S.A.W) abubuwa ne da suka saɓa da yadda ɗan Adam ya saba rayuwa, Allah yake gudanar da su ta hanyar Manzonsa (S.A.W)?
  • ...Sallar jam'i, sallah ce wace ake yinta cikin tsarin adadin wasu rukunin jama'a?
Labarin da aka Shawarar


  • Fursunonin Karbala «ma'ana mutane da suka rage a raye a waƙi'ar karbala misalin Imam Sajjad (A.S), imami na huɗu a wurin ƴanshi'a da Sayyida Zainab (S) waɗanda sojojin Umar ɗan Sa'ad suka kama su matsayin fursunonin yaƙi.»
  • Sayyidina Abbas (A.S) « wanda ya rayu tsakanin shekaru 26-61 bayan hijira, ya shahara da Abul Fadli na biyar cikin jerin maza ƴaƴan Imam Ali (A.S) farko ɗa ga Ummul banin..»
  • Imam Husaini (A.S) « shi ne Imami na uku a wurin ƴan shi'a, haka nan ana kiransa da Aba Abdillah da Sayyidush Shuhada, ya yi shahada a waƙi'ar karbala»
  • Karbala «ɗaya daga cikin garuruwan ziyara a wurin ƴanshi'a a ƙasar Iraƙi. Shahadar Imam Husaini da sahabbansa lokacin waƙi'ar karbala shekara ta 61 bayan hijira..»
  • Sadakin Sunna «shi ne gwargwadon sadakin da Manzon Allah (S.A.W) ya auri matansa, ya kuma aurar ƴa'yansa mata da shi. Adadin kuɗin ya kai Dirhami 500, kwatankwacin giram 1500 na zallar azurfa...»
  • Gulmar Da Ta Halasta «Larabci: (Larabci: مُستَثنَيات الغيبة) Ma'ana mutanan da ya halasta ayi da su, daga cikin inda ya halasta ayi Gulma, akwai gurin da yin Gulma ya fi rashin yin ta alfanu»
  • Ɗakin Annabi «(Larabci: الحجرة النبوية) ɗakin Annabi wuri ne wanda aka binne Annabi (S.A.W) ɗaki ne wanda ya kasance yana rayuwa tare da A'isha...»
  • Hubbul Waɗani Minal Iman « (Larabci: حُبّ الوطن من الإيمان) wannan jumla ce fitacciya wadda ake jingina ta ga Annabi (S.A.W), wasu masu bincike misalin Shaik Makarim Shirazi cewa wannan jumla babu ita a cikin litattafan asali na hadisi, kai wasu ma suna ganin ƙirƙirarta aka yi..»
  • Sayyidina Abbas (A.S) «wanda ya rayu tsakanin shekaru 26-61 bayan hijira, ya shahara da Abul Fadli na biyar cikin jerin maza ƴaƴan Imam Ali (A.S).»
Babban Rukuni
Category Beliefs‎ not found
Category Culture‎ not found
Category Geography‎ not found
Category History‎ not found
Category People‎ not found
Category Politics‎ not found
Category Religion‎ not found
Category Sciences‎ not found
Category Works‎ not found