Aba Salih
Aba Salih (Larabci: أبا صالح) Alkunya ce da ake nuna Imam mahadi da ita tun daga ƙarni na 11 hijira, wannan kalma da ire'irenta kamar "Salihu" da "Aba Salihu" a cikin hadisai, amma a cikin hadisi ba a faɗi cewa alkunyar Imam Mahadi (A.S) ce ba. kazalika malaman aƙida da masu sharhi kan hadisi ba sun ɗauki wannan kalma a matsayin alkunya ga Imam Mahadi ba. ya zo a cikin wasu hadisai cewa idan ku ka ɓata, to ku nemi ɗaukin ku kira "Salihu" ko "Aba Salihu" ko :"ba Salih" har sai an kawo mu ɗauki.
Aba Salih Alkunya ce ta Imam Mahadi
Kalmar "Aba Salihu" alkunya ce sananniya ta Imam Mahadi (A.S).[1] a daidai lokacin da babu abin da yake nuna haka a cikin ruwayoyi da tarihi waɗanda suka daɗe sai da cewa kawai an san wannan kalmar alkunyar Imam Mahadi ce[2] kuma ba a kira Imam Mahadi da Aba Salihu ba a tarihi sai a litatafan da aka rubuta a baya-baya nan, misali Mirza Husaini Nuri ɗaya daga cikin malaman Shi'a a ƙarni na 13 da 14 na hijira ya ce, su larabawa a waƙoƙinsu da waƙoƙin da suke yi a lokacin bakin ciki suna kiran Imam Mahadi da Aba Salihu.[3]
Tarihin Fara Amfani Da Wannan Alkunya
Bisa abin da ya zo a Mausu'atu Imam Mahadi (A.S) cewa alkunyar Aba Salihu ana anfani da ita tun daga ƙarni na 11, amma kafin nan babu wani abu da yake nuna cewa an yi anfani da wannan alkunya kan Imam Mahadi.[4] Allama Majlisi wanda ya yi rayuwa daga shekara 1037 zuwa 1110 ya ji daga mahaifinshi cewa wani mutum mai suna Amir Is'haƙ al'istir'abadi ya ɓata yayin da yake kan hanyar shi ta zuwa hajji, sai ya ce Ya Aba Salihu ka nusar da ni hanya, kawai sai ya samu wani mutum ya nuna mishi hanya, to bayan sun rabu ne kawai sai ya gane cewa Imam Mahadi ne, sai ya yi nadamar rabuwa da shi.[5] Muhaddisul Nuri ya na rinjayar da cewa amfani da wannan alkunyar kan Imam Mahadi ta samo asali ne daga wannan ƙissar ta wannann mutumin da ya ɓata yayin da yake kan hanyar shi ta zuwa aikin haji, wanda ya sami ceto san da ya nemi ɗauki ta hanyar kiran Aba Salihu.[6] a cikin Mausu'atu Imam Mahadi an faɗi cewa sanadiyar jingina alkunyar Aba Salih ga Imam Mahadi Allah ya gaggauta bayyanar shi da kuma yaɗuwar wannan alkunya da ire-iransu su ne ƙissosi waɗanda suka yi kama da ƙissar wanda ya ɓata yayin da yake kan hanyar shi ta zuwa aikin hajji.[7]
Anfani Da Alkunyar Aba Salih A Hadisi
Kalmar "Ba Salih" da Aba "Salihu" sun zo a wasu hadisai na Shi'a, amma masu rawaito hadisi da masu sharhi kan hadisai ba su ce abin da ake nufi da wannan kalmomin guda biyu shi ne Imam Mahadi (A.S) ba, misali Ahmad ɗan Muhammad ɗan Khalid Albarƙi wanda ya rayu daga shekara ta 274 ko 280 na hijira ya anbaci wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S), ya na cewa, idan ka ɓata a kan hanya, to ka kira Ya Salih da Ya Aba Salih ka nuna mi ni hanya Allah ya yi maka rahama.[8] Shaik Saduƙ ya kawo wata ruwaya da ta yi kama da ruwayar da Albarƙi ya kawo kawai dai akwai banbanaci kaɗan a tsakaninsu, ruwaya da take cewa idan kana tafiya a kan hanya ka ɓata, to Aba Salih ka kira Ya Aba Salih ka nusar da ni hanya Allah ya yi maka rahama.[9] kuma ya ƙara kawo wata ruwayar a bayanta wadda take cewa Doran ƙasa yana hannun Salihu, kogi yana hannun Hamza.[10] kuma ya zo a cikin Mausu'atu Imam Mahadi cewa Shaik Saduƙ ba kuma wani daga cikin masu sharhin littafin Manla yahdurhul Faƙih da ya yarda cewa wannan Laƙabin ko Alkunya ana amfani ne da shi kan Imam Mahadi (A.F).[11] a wata ruwaya a cikin littafin Almahasin na Albarƙi ya ce shi Salihu Aljani ne ba mutum ba, kuma shi aikinshi shi ne taimako da kawo ɗauki ga wanda ya ɓata yayin da yake tafiya a kan hanya.[12]
Bayanin kula
- ↑ Al-Rishahri, Danishnameh Imam Mahdi, 1393 AH, juzu'i na 2, shafi na 322.
- ↑ Al-Rishahri, Danishnameh Imam Mahdi, 1393 AH, juzu'i na 2, shafi na 322.
- ↑ Al-Nuri, Aljannar Maawa, 1427 AH, shafi 136; Al-Nuri, Al-Najm Al-Thaqib, 1410H, shafi na 45.
- ↑ Al-Rishahri, Danishnameh Imam Mahdi, 1393 AH, juzu'i na 2, shafi na 322.
- ↑ Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 175-176..
- ↑ Al-Nuri, Al-Najm Al-Thaqib, 1410H, shafi na 571.
- ↑ Al-Rishahri, Danishnameh Imam Mahdi, 1393 AH, juzu'i na 2, shafi na 322-323.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, 1371 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 362-363.
- ↑ Al-Saduq, Min La Yahdrahu Al-Faqih, 1413H, juzu’i na 2, shafi na 298.
- ↑ Al-Saduq, Min La Yahdrahu Al-Faqih, 1413H, juzu’i na 2, shafi na 298.
- ↑ Al-Rishahri, Mausu'atu Imam Mahdi, 1393 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 322.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, 1371 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 380.
Nassoshi
- Al-Barqi, Ahmad bin Muhammad bin Khalid, Al-Mahasin, Al-Muhaddith Al-Armawi, Qum, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1371H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar Al-Jami’ah Lidur Al-Akhbar Al-Akhbar, Beirut, Larabawa Heritage Revival House, bugu na biyu, 1403H.
- Al-Nuri, Mirza Hussein, Aljannatul Ma'awa fi zikri man faza biliqa'i Hujja, Cibiyar Nazari Na Musamman akan Imam Mahdi, Allah Ta'ala Ya Gaggauta bayyanarsa Mai Girma, Qum, Lady Masoumeh Foundation, Wassalamu Alaikum. gare ta, 1427H.
- Al-Saduq, Muhammad bin Ali, Man La Yahdurah Al-Faqih, Kum, Kum, Kungiyan Malamai na Seminary, bugu na biyu, 1413H.
- Al-Nuri, Mirza Hussein, Al-Najm Al-Thaqib, Qum, Wallafar Masallacin Jamkaran, 1410H.
- Al-Rishahri, Muhammad Muhammadi da sauransu, Danishnameh Imam Mahdi Bar Bayyah, Qur’an, Hadith and History, Qum, bugun Darul-Hadith, 1393H.