Saratu

Daga wikishia
Makwancin Saratu matar Annabi Ibrahim (A.S) da yake a garin Khalil

Saratu (Larabci: سارة) Matar Annabi Ibrahim (A.S) Mahaifiyar Is’hak (A.S) kan asasin abin da ya zo cikin surori biyu daga Alkur’ani Mai girma, Hakika Mala’iku sun zo masa da Busharar Samun Haihuwar Is’hak a lokacin da yake da Shekaro 90, Sakamakon Mala’iku sun yi Magana da Saratu kamar yanda suka yi da Hazrat Maryam da Hazrat Fatima (S) ana kiranta da sunan Muhaddasa (wacce Mala’iku suka yi Magana da ita) Hakika Saratu ta kasance Baiwar Hajara da ta Baiwa Ibrahim Kyautarta tsawon Shekaru kafin Haihuwar Is’hak ta bada kyautarta ne domin Ibrahim ya samu haihuwa daga gareta, Shaik Saduk ya nakalto wata riwaya da take Ishara kan Hassadar da Saratu ta yiwa Hajara bayan Haihuwar Isma’il, sai dai cewa Malamai masu zurfafa biincike cikin Riwaya sun bayyana shakku kan Isnadin wannan hadisi.

Rayuwa

Aminul Islam Ɗabarasi [1] da Abul Al-Fatuhu Razi [2] Malaman tafsiri na Shi’a a karni na shida hijiri kamari sun tafi kan cewa Saratu `Diya ga Haran Bn Yahur kuma Diya ce ga Baffan Ibrahim (A.S), sai dai cewa a wasu riwayoyi ya zo cewa Diya ce ga Lahiju Annabi kuma Diya ce `Yar uwar Mahaifiyar Ibrahim (A.S) ce [3] a Masadir na Tarihi wasu maganganun daban sun zo daga cikin akwai batun cewa Saratu Diya ce ga Batawilu Bn Nahur [4] wata Maganar Kuma Diya ce ga Labinu Bn Nahur [5] Diya ce ga Maliku Harrran duka an nakalto wadannan maganganu Ibn Kutaiba Marubucin Tarihi daga Ahlus-sunna a karni na uku ya nakalto daga littafin At-Taura cewa Saratu Diyar dan’uwan Ibrahim ce [6] Ibn Kasir Marubucin Tarihi daga Ahlus-sunna wanda yam utu shekara ya 774 hijiri kamari ya yi watsi da wannan Magana ya tafi kan Magana da ta shahara kan cewa Saratu Diyar Baffan Ibrahim ce [7] Abdus-As-Sahib Amili Marubucin Littafin (Al-Anbiya’u wa Kisasuhum ) ya tafi kan cewa Ludu (A.S) ya kasance dan’uwan Mahaifiyar Saratu, bawai dan’waun Mahaifinta ba, saboda haka Saratu ba ta kasance Diyar Yar’uwar Mahaifiyar Ibrahim ba, a cewar Malamin Saratu ta kasance Diyar Baffan Ibrahim [8] [Tsokaci 1] Saratu tareda Ludu sun yi Imani da Ibrahim sun kasance masu bautar Allah shi kadai, [9] sannan ta yi aure da Ibrahim (A.S) [10] Saratu tana cikin kyawawan Mata a zamaninta [11]ta kasance tana Gonakin Noma da Dabbobin kiwo masu tarin yawa sannan ta yi kyauta baki dayan dukiyarta ga Mijinta Ibrahim (A.S) [12]

Hijira zuwa Misra

Bayan Da’awar Ibrahim Zuwa ga bautawa Allah kadai a garin Babul `yan tsiraru daga Mutane suka yi Imani da shi, da wannan dalili ya sanya Ibrahim yin Hijira zuwa Sham tare da matarsa Saratu da Ludu, sai dia sakamakon yaduwar Fari da Yankewar Ruwan Sama da cuta, sai ya kara yin Hijira tareda Matarsa Saratu zuwa kasar Misra [13] tarihin ya kawo cewa Sarkin Misra ya samu Labarin Kyawun Saratu [14] sai Annabi ya gayawa Sarki cewa `yar’uwarsa ce [15] lokacin da Sarki ya tambaye shi wacce dangantaka take tsakaninsu, a cewar Ibn Asir Ibrahim ya san cewa idan yace Saratu Matarsa Sarki zai bada umarnin Kashe shi domin ya kwace Saratu, sai Ibrahim (A.S) ya boye masa dangantakarsu, [16] Sarkin Misra ya sa aka Kira Saratu Fadarsa yayi bakin kokarinsa ya kwace ta sai dai cewa a wannan lokac dai hannunsa ya kama bushewa [17] Sarki Ya roki Saratu ta yi masa addu’a hannunsa ya koma yanda yake zai kyaleta ta tafi, sai dia cewa bayan ta yi masa addu’a ya kuma samu lafiya sai ya kara yunkuri kai mata hannu, wannan lamari ya maimaitu har karo uku [18] daga karshe dai Sarki yayi nadama kan abin da ya yi, sai ya dauko wata Baiwarsa da ake kira Hajara tareda wasu hadiyoyi ya baiwa Saratu kyautarsu ya kuma `yanta ta [19] A cewar Allama Tabataba’i da’awar Bayyana Saratu Matsayin `yar’uwa da aka ce Ibrahim (A.S) ya yi baya dacewa da Mukamin Annabta, yana daga cikin Tufka da warwarar At-Taura ta yanzu da suka gangara litattafan tarihi da hadisi na Ahlus-sunna [20] sannan kan asasin riwayar da Allama Tabataba’i ya nakalto daga littafin Alkafi lokacin da Sarki ya Tambayi Ibrahim wacce dangantaka ce tsakaninsa da Saratu ya bayyanawa Sark cewa matarsa ce, sannan duk sanda hannun sarki ya bushe Ibrahim (A.S) yae addu’a ya warke ya dawo daidai kamar yanda yake [21]

Busharar Samun Haihuwa ga Ibrahim lokacin yana da shekaru 90 a Duniya

Kamar yanda ya zo a Masadir na Tarihi Mala’ikun Allah sun yiwa Saratu Bushara zata haifi `Da Namiji [22] sai tayi dariya da take nuna rashin yarda tace ta yaya matar da take tsohuwa zata dauki ciki? [23] bayan wani lokaci sai ta Dauki cikin Is’hak [24] hakika cikin surori guda biyu a Alkur’ani Mai girma anyi ishara da Busharar Mala’iku ga Saratu kan samun Haihuwa da kuma raddin da ta yi kan wannan Bushara [25] Kafin a yiwa Saratu Busharar samun Haihuwa, sakamakon kasancewarta wacce bata haihuwa sai ta yi Kyautar Baiwar ta Hajara ga mijinta Ibrahim domin ya samu haihuwa daga gareta, bayan wannan kyauta ne aka Haifi Isma’il [26]

Mutuwa

Saratu Matar Ibrahim (A.S) ta yi bankwana da duniya tana da shekaru 127 a wani gari da ake kira Hebron [27] bayan mutuwar Saratu, Ibrahim ya sayi wani wuri a garin Hebron ya binne Saratu a wannan wuri [28] sannan a wannan wuri ne dai aka binne Ibrahim da Is’hak da Yakub [29] ana kiran wannan wuri da sunan Haramin Ibrahim da wannan suna ya shahara yana nan A garin Alkhalil Kudancin Kudus [30]

Hususiyoyi

Kan asasin wasu riwayoyi da aka danganta su ga Imam Ali (A.S) Sakamakon Mala’iku sun yi Magana da Saratu sun mata Bushara da haihuwar Is’hak itama ana kiranta da sunan Muhaddasa [31] kan asasin wannan riwaya dai ake kiran Hazrat Maryam (A.S) da Hazrat Zahara (A.S) da ma Mahaifiyar Hazrat Musa (A.S) da Muhaddasa [32] `Yan Shi’a sun yi Imani da cewa --Mala’iku bawai kadai da iya Annabawa suke Magana ba, bari dai suna Magana da A’imma da Hazrat Fatima, da ma wasu mutane akwai ayoyin Alkur’ani Mai girma da suka tabbatar da haka daga jumlrasu akwai ayoyi na 42-45 cikin Suratul Alu Imran sun ya Magana kan yanda Mala’iku suka yi Magana da Hazrat Maryam wanda haka yake tabbata da abinda suke da’awa [33] A cikin rwaiayar da aka Nakaltota ta hanyar Shaik Saduk da Ali Bn Ibrahim Qummi, anyi ishara kan hassadar Saratu da karkacewa da dan samu a Aklak bayan haihuwar Isma’il da kuma irin hakurin da Ibrahim (A.S) ya yi [34] tare da wasu ba’arin Masu zurfafa bincike na wannan zamani sun yi suka kan Isnadin riwayar da cewa yana da rauni [35] kan asasin abinda ya zo a Attaura Saratu ta nemi Ibrahim (A.S) ya kori Hajara `danta Isma’il daga gidan da suke, sai dai cewa Ibrahim (A.S) ya nuna bacin ransa kan wannan bukata ta Saratu, [36]duk da cewa daga karshe sakamakon Umarnin Allah ya zartar da bukatar Saratu [37] amma tare da haka ya zo a wasu ba’arin riwayoyin cewa an ajiye tarbiyar `Yan Shi’a da yara kanana a Duniyar Barzahu a hannun Saratu da Ibrahim domin su yi musu Tarbiyya sannan a mika su zuwa ga Mahaifansu [38]

Bayanin kula

  1. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 273.
  2. Boal Fattouh Razi, Rouzu Al-Janan, 1408 AH, juzu'i na 10, shafi na 304.
  3. Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 370; Rawandi, Qasses al-Anbiyyah (AS), 1409 AH, shafi na 106.
  4. Masoudi, Moruj al-Dhahab, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 57.
  5. Ibn Habib, Dar al-Afaq al-Jadidah, shafi na 394.
  6. Ibn Qutiba, Al-Maarif, 1992, shafi na 31.
  7. Ibn Kathir, al-Bedaya wa Al-Nehaya, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 150.
  8. Hosseini Ameli, Al-Anbiya Hayutuhum Qesasehum, 1391 AH, shafi na 116 da 129.
  9. Tabari, Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1387H, juzu'i na 1, shafi na 245.
  10. Tabari, Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1387H, juzu'i na 1, shafi na 245.
  11. Ibn Athir, Al-kamel fi Al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 101; Moghdisi, al-Mishada da al-Tarikh, Makarantar Al'adu Al-Diniyeh, juzu'i na 3, shafi na 51.
  12. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 8, shafi na 370.
  13. Daqs, Ashinayi ba-Zanani Kur'ani, 2009, shafi na 110 da 111.
  14. Ibn Kathir, al-Bedaya wa Al-Nehaya, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 150.
  15. Ibn Athir, Al-kamel fi Al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 101.
  16. Ibn Athir, Al-kamel fi Al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 101.
  17. Ibn Athir, Al-kamel fi Al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 101.
  18. Ibn Athir, Al-kamel fi Al-tarikh, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 101.
  19. Moghdisi, Albad'u wa Al-Tarikh, Makarantar Al-Taqfa al-Diniyeh, juzu'i na 3, shafi na 52.
  20. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 7, shafi na 226-229
  21. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 7, shafi na 231-232.
  22. Daqs, Ashinayi ba-Zanani Kur'ani, 2009, shafi na 116-119.
  23. Daqs, Ashinayi ba-Zanani Kur'ani, 2009, shafi na 116-119.
  24. Tabari, Tarikh Al-Uamm wa Al-Muluk, 1375, juzu'i na 1, shafi na 248-249.
  25. Duba: Suratu Hud, aya ta 71-73; Suratu Dhariyat, aya ta 29 da ta 30.
  26. Moghdisi, Albad'u wa Al-Tarikh, Makarantar Al'adu Al-Diniyeh, juzu'i na 3, shafi na 53.
  27. Ibn Khaldun, Diwan al-Mubtada wa Al-Khabar, 1408 AH, juzu'i na 2, shafi na 43.
  28. Ibn Khaldun, Diwan al-Mubtada wa Al-Khabar, 1408 AH, juzu'i na 2, shafi na 43.
  29. Moghdisi, Albad'u wa Al-Tarikh, Makarantar Al'adu Al-Diniyeh, juzu'i na 3, shafi na 52-53
  30. Hosseini Jalali, Mzaratu Ahlul Baiti wa Tarikuha, 1415H, shafi na 254.
  31. Ashur, Mausu'atu Ahlul-Baiti, 1427 Hijira, juzu'i na 7, shafi na 24
  32. Ashur, Mausu'atu Ahlul-Baiti, 1427 Hijira, juzu'i na 7, shafi na 24
  33. Amini, Mus'haf Fatemi, 1382, shafi na 60.
  34. Amini, Mus'haf Fatemi, 1382, shafi na 60.
  35. Sheikh Sadouq, Al-Khasal, 1403 AH, shafi na 307; Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1361, shafi na 128; Qomi, Tafsirin Qami, 1363H, juzu’i na 1, shafi na 60.
  36. Kitabu Mukaddas Kitabu faidayesh, Babi na 21, ayoyi 9-15.
  37. Kitabu Mukaddas Kitabu faidayesh, Babi na 21, ayoyi 9-15.
  38. Sheikh Sadouq, Man Lay Hazara Al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 3, shafi na 490; Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 5, shafi na 293

Tsokaci

  1. Abd al-Sahib Hussaini Ameli ya gaskata cewa uwayen Sarah da Ibrahim, waɗanda 'ya'yan Lahaj ne, sun auri kawun Ibrahim da mahaifin Ibrahim. A cikin waɗannan nau'in aure guda biyu.Aka haifi Saratu da Ibrahim; Saboda haka, Saratu ƙanwar Ibrahim ce ta bangaren kanwar mahaifiyarsa. kuma ƙanwarsa ta bangaren baffansa. Tabbas, a cewarsa, kafin ta auri kawun Ibrahim, mahaifiyar Saratu ta auri kanin Ibrahim kuma ta haifi Annabi Ludu. Domin wannan, Lutu ɗan wan Ibrahim ne kuma ƙaninsa, kuma ɗan’uwan Saratu, ba ɗan’uwan mahaifinta ba. Saboda haka, a cewarsa, kasancewar Saratu da Lutu ’yan’uwa ba ya nufin cewa Saratu ƙanwar Ibrahim daga mahaifansa. (Hosseini Ameli, Al-Anbiya Hayatham Qasseham, 1391 AH, shafi na 116 da 129).

Nassoshi

  • Alqur'ani mai girma.
  • Kitabu Mukaddas.
  • Ibn Athir, Ali bin Abi Al-Karam, al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir, 1385H.
  • Ibn Khaldun, Abd al-Rahman ibn Muhammad, Diwan al-Mubtada wa Al-Khabar fi Tarikh al-Arab wa al-Barbar da Man Aserham Man Dhu al-Shaan al-Akbar, bincike: Khalil Shahada, Beirut, Dar al-Fikr , 1408 AH/1988 Miladiyya.
  • Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, Al-Bedayah da Al-Nehayah, Beirut, Darul Fikr, 1407H/1986 Miladiyya.
  • Ibn Qutaiba, Al-Ma'arif, Abdullah bin Muslim, Binciken dukiyar Akasha, Alkahira, Al-Masriyyah al-Katab, 1992.
  • Ibn Habib, Muhammad bn Habib ibn Hashemi Baghdadi Mohibari, al-Muhabbar, bincike na Ilza Lichten-Schetter, Beirut, Dar al-Afaq al-Jadidah, Bita.
  • Abul Fattouh Razi, Hossein bin Ali, Rauzul Al-Jinnan da Ruh al-Jinan fi Tafsir al-Qur'an, Mohammed Mahdi Naseh da Mohammad Jafar Yahaghi, Mashhad, Astan Quds Razavi, Islamic Research Foundation, 1408 AH.
  • Tehami, Fatemeh, da Azam Farjami, "Sara, Hamsare Ibrahim (A.S) a cikin Alkur'ani da hadisai", a cikin mujallar Sahifa Mobeen, Tehran, Kur'an da Cibiyar Nazarin Atrat: Jami'ar Azad, Mujalladi na 43, Fall. 2007.
  • Hosseini Ameli, Abdul Sahib, The Prophets: Hayatham - Qassem, Beirut, Al-Alami Publishing House, 2002.
  • Hosseini Ameli, Abdulsaheb, The Prophets Hayatham Qasasham, Beirut, Publications of Al-Alami Foundation for Publications, 1391 AH.
  • Hosseini Jalali, Mohammad Hossein,Mazaratu Ahlul Baiti wa Tarikuhu, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1415H/1995 Miladiyya.
  • Daqs, Fouad Hamdo, Ashinayi ba-Zanani Kur'ani, Fatemeh Heydari ta fassara, Tehran, Mashaar, 2009.
  • Ravandi, Qutbuddin Seyed, Qasases Al-Anbiya (AS), Gholamreza Irfanian Yazdi, Mashhad, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1409 H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Khesal, editan Ali Akbar Ghafari, Qum, Qum seminary community, 1403 AH.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ma'ani Al-Akhbar, Qum, Islamic Publishing House, 1361.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Laihdara al-Faqih, gyara daga Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, 1413 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al’umam wa Al-Muluk, bincike: Muhammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, Darul-Tarath, 1387H/1967 Miladiyya.
  • Ashour, Ali, Masu'atu Ahl Al-Bait, Beirut, Dar Nazir Abboud, 1427 AH/2006 AD.
  • Allameh Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Al-Nashar al-Islami School, bugu na biyar, 1417H.
  • Allameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Qummi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsir Qummi, ta qoqarin Sayyid Taib Musawi Al-Jazayari, Qum, Darul Katab, 1363.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, bugun Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Mahalati, Zabihullah, Riyahin al-Shari’a: a cikin fassarar mata musulmi ‘yan Shi’a, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1369.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, da Dagher, Youssef Asad, Moruj Al-Dahaab da Maaden al-Jawhar, Qom, Estado Dar al-Hijrah, 1409H.
  • Moghdisi, Mohammad Bin Tahir, al-Midah da al-Tarikh, Bursa'id, Al-Taqfah Al-Diniyeh School, B.T.A.