Batula
Batula (Larabci: البتول) daya daga cikin lakubban Hazrat Fatima (S) ne, ana mata lakabi da Batula sakamakon fifitar da ta yi kan sauran mata a cikin magana, dabi'a, da Ilimi, hakika shima Imam Ali (A.S) ana masa Lakabi da mijin Batula sakamakon aurenta da ya yi, Hazrat Maryam (A.S) ita ma ana mata lakabi da Batuka.
Kalmar Batula A Mahangar Lugga
Batala a cikin harshen larabci tana bada ma'anar: cire wani abu daga jikin wani abu, ko kuma dai yanke shi daga jikinsa, sannan Batula ana amfani da kalmar kan kamammiyar budurwa da ta tsare kanta daga maza ta ki aure, sannan kuma ba ta da wata sha'awa zuwa ga maza[1] Hazrat Maryam Mahaifiyar Isa (A.S) ita ma ana mata lakabi da Batula saboda ta nesanci Maza,[2] haka kuma ana amfani da kalmar kan matar da ta ke yankewa zuwa ga Allah tare da baki dayan zuciyarta.[3]
Annabi Akram (S.A.W) ya ce:
«انما سمیت فاطمه البتول لانها بتلت من الحیض و النفاس؛ Kadai an kira Fatima da Batula saboda ta yanke daga barin yin jinin Haila da Nifasi.
Kandusi cikin littafinsa, Yanabi'ul Al-Muwadda, shekara ta 1416 j 2 sh 322.
Dalilin Sanya Mata Wannan Lakabi
Dalili da illar sanyawa Fatima (S) lakabin Batula, an nakalto maganganun da za su zo a kasa kan bayanin dalilin sanya mata wannan lakabi:
- Kan asasin adadin wasu riwayoyi, an kira yi Fatima (S) da Batula saboda bata ganin Jinin Al'ada,[4] Daga ruwayar da aka samu a cikin Amali na Shaikh al-Saduq daga Ibn Abbas, daga Imam Ali (A.S) a lokacin tafiya zuwa Siffin da isa ƙasar Ninawa, an ambata cewa Annabi Isa (AS) yayin da ya wuce wannan ƙasa, ya annabta shahadar Imam Husaini (A.S) kuma Hawariyyun da ke tare da shi sun yi kuka. A cewar wannan ruwaya, Annabi Isa (A.S) yayin da yake gabatar da Husaini, ya ce shi ɗan mace ce mai 'yanci, tsarki, da kamala, da ta yi kama da mahaifiyarsa Maryam (A.S). (Wannan ƙasar ce inda za a kashe ɗan Manzo Ahmad da ɗan mace mai `yanci, tsarki, mai kamala, da ta yi kama da mahaifiyata Maryam).[Tsokaci 1].
- Ta kasance tana bambanta da kuma fifiko akan sauran mata na zamaninta ta fuskar ayyuka, halaye da kuma sanin Allah, kuma ta kai matakin cikakken nisantar komai da ke waje da Allah.[5]
- Ta kasance tana bambanta da kuma fifiko akan sauran mata ta fuskar kamun kai, addini, falala da asali.[6]
Auren Batula
- Asalin Makala: Mijin Batula
Bayan Sarkin Muminai Ali (A.S) ya auri Fatima (S) sai ya zama ana masa lakabi da Mijin Batula, hakika Hazrat bayan ya dawo daga yakin Naharawan cikin wata huduba da ya yi ya kira kansa da Mijinta Batula.[7]
Tarjama: Tun lokacin da aka yi aure tsakanin Haidar da Batul Wannan aya ta sauka daga Allah ga Manzo Don irin wannan suruki da irin wannan zuri'a Rahamar Allah tana karuwa ko wane lokaci.[8]
Bayanin kula
- ↑ Johri, Al-Sahah, 1410 AH, Juzu'i na 4, shafi na 1630; Al-Ain, Al-Nasher: Dar da Al-Hilal Library, Juzu'i na 8, shafi na 124
- ↑ Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, juzu'i na 11, shafi na 43; Rajeb Esfahani, Al Fardat, 1375, juzu'i na 1, shafi na 240.
- ↑ Johri, Al-Sahah, 1410 AH, Juzu'i na 4, shafi na 1630; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 25, shafi na 179.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 64; Tabari Amoli, Dala'il al-Imamah, 1413 AH, shafi na 54; Erbali, Kashf al-Gahma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi.464; Kundozi, Yanabi Al-Moudah, 1416 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 322.
- ↑ Mazandarani, Sharh Usul al-Kafi, 1421 H, J5, shafi na 228; Turaishi, Majma' al-Bahrain, 1375 H, J5, shafi na 316; Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuna, 1374 H, J25, shafi na 179.
- ↑ Ahmadi Miyanjī, Makatīb al-Rasūl (SAW), Mai bugawa: Dār al-Ḥadīth, J2, shafi na 435.
- ↑ Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403H, shafi na 58.
- ↑ «ناصرخسرو، دیوان اشعا، قصاید»،Shafin ganjur.
Tsokaci
- ↑ Wani lokaci wani abu da ba a saba gani ba ko kuma wani abu mai ban mamaki yana kasancewa wata babbar daraja. Kamar yadda Annabi Isa (A.S) ya yi magana a yana jariri, wanda ba wani abu ne na al'ada ba, amma da izinin Allah ya tsarkake mahaifiyarsa daga zargin makiya. Saboda haka, duk da cewa rashin ganin jinin al'ada ga mata da suke cikin shekaru na al'ada na iya zama wata cuta mai haɗari sosai kuma zai iya haifar musu da matsaloli, amma bisa ga ikon da hikimar Allah Madaukaki wajen kare su daga cutarwa, ga mata da Allah ya nufa su daina ganin wannan jini, wannan wata babbar daraja ce; domin mata a wasu lokuta na musamman saboda wani uzuri (kamar al'ada) ba sa iya yin sallah, azumi, shiga Masallacin Harami da Masallacin Annabi, tsayawa a masallatai, ko taɓa lafuzzan Al-kur'ani. Amma Sayyida Zahra (A.S) saboda kyakkyawar kulawar Allah ba su da waɗannan ƙuntatawa.Saboda haka a riwayoyi an ce dukkan 'ya'yan annabawa suna da wannan hali; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Al'ada ba ta dace da 'ya'yan annabawa ba. Shaikh Saduk, Ilal al-Sharai', Monshorat al-Maktabah al-Haydariyyah, J1, shafi na 181.أَنَّ النَّبِيَّ (ص) سُئِلَ مَا الْبَتُولُ فَإِنَّا سَمِعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ تَقُولُ إِنَّ مَرْيَمَ بَتُولٌ وَ فَاطِمَةَ بَتُولٌ فَقَالَ (ص) الْبَتُولُ الَّتِي لَمْ تَرَ حُمْرَةً قَطُّ أَيْ لَمْ تَحِضْ فَإِنَّ الْحَيْضَ مَكْرُوهٌ فِي بَنَاتِ الْأَنْبِيَاءِ. نگاه کنید به: رحمانی همدانی، فاطمة الزهرا بهجة قلب المصطفی، الناشر : المنير، ص۱۵۹-۱۶۲
Nassoshi
- Ahmadi Mianji, Ali, Makatib Al-Rasoul, Al-Nasher, Dar al-Hadith, Bi Ta, Bi Ja.
- Alameh Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, bincike na Mohammad Baqer Behboodi, Beirut, Al-Wafa Institute, 1403 AH/1983 AD.
- Erbali, Ali bin Isa, Kashf al-Gahma, Tabriz, Bani Hashemi, bugu na farko, 1381H.
- Johari, Al-Sahah, Dar Al-Alam Lal-Mulayin, Beirut, 1410H.
- Kulaini, Kafi, Dar al-Kutb al-Islamiya, Tehran, 1365.
- Kundoozi, Yanabi Al-Mowaddeh Lazvi al-Qorabi, bincike: Seyyed Ali Jamal Ashraf Hosseini, Dar al-Aswa na bugawa da bugawa, 1416H.
- Makarem Shirazi Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyeh, 1374.
- Mazandarani, Mohammad Saleh, sharh Usulul Al-Kafi, bincike na Mirza Abulhasan Shearani, gyara daga Seyyed Ali Ashour, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, 1421 AH/2000 AD.
- Muhaddith Nouri, Mirza Hossein, Mostadrak Al-Wasail, Qom, Al-Bait Institute, 1408 AH.
- Qomi, Sheikh Abbas, Bayt Al-Ahzan, wanda Eshtredi ya fassara, Qum.
- Ragheb Esfahani,Mufradat Alfaz Alkur'an, wanda Seyyed Gholamreza Khosravi Hosseini ya fassara, gidan buga littattafai na Mortazavi, Tehran, 1375.
- Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Dokokin Dokoki, Bincike na Sayyid Mohammad Sadiq Bahrul Uloom, Manuscripts na Al-Maktaba Al-Haydriya, Najaf, 1966/1385.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, Kum, Jamia Madrasin, 1403H.
- Tabari Amoli Saghir, Mohammad Bin Jarir, Dala'il al-Imamah, Qom, Dar al-Zhakhar na manema labarai.
- Tarihi, Fakhreddin, Majma Al-Bahrin, bincike na Sayyid Ahmad Hosseini, Tehran, kantin sayar da littattafai na Mortazavi, bugu na uku, 1375.