Sayyida Zainab (A.S)
Haramin Sayyida Zainab da yake Dimashƙi | |
| Suna | Zainab |
|---|---|
| Matsayi | Mai isar da saƙo a lokacin Waƙiar Karbala da kuma shugabantar Fursunonin Karbala |
| Alkunya | Ummu Kulsum da Ummul Hassan |
| Laƙabi | Zainabul Kubra,Aƙilatu Bani Hashim, Alima Gairu Mu'allama, Ummu Masaib, Kamila, Fadila da... |
| Ranar haihuwa | Shekara ta 5 ko 6 hijira |
| Mahaifa | Madina |
| Rasuwa | 15 Rajab shekara ta 62 h. |
| Kabari | Dimashƙi/Al-Ƙahira (Akwai saɓani) |
| Mahallin Rayuwa | Madina |
| Mahaifi | Imam Ali (A.S) |
| Mahaifiya | Sayyida Faɗima (S) |
| Mata | Mijinta shi ne Abdullahi Bin Jafar |
| Ƴaƴa | Aunu, Muhammad, Ali, Abbas, Ummu Kulsum |
| Tsawon rayuwa | Shekara 57 (Bisa abin da ya shahara) |
Sayyida Zainab ƴar Ali (A.S) (Larabci: السيدة زينب بنت علي عليها السلام،) mahaifinta shi ne Amirul muminina, mahaifiyarta kuma ita ce Faɗimatuz Zahra (A.S) bisa abin da ya zo a wasu ruwayoyi, kakanta maaikin Allah (S.A.W) shi ne wanda ya raɗa mata suna Zainab, ance ta kasance tana koyar da mata tafsirin Alƙurani a lokacin halifancin Amirul muminina Ali (A.S) a garin Kufa. Ta yi tarayya da ɗan uwanta a lokacin Waƙi'ar Karbala, kuma ta ba da gudunmawa mai yawa kan abin da ya faru a waƙi'ar Ashura, ita da sauran matan da aka kashe mazajansu da marayu bayan goma ga wata Muharram an tafi da da su zuwa Kufa matsayin fursunonin yaƙi, inda ta yi wata shahararriyar huɗuba a can, daga Kufa kuma aka tafi da su zuwa Sham, inda a can ma ta yi wata huɗuba, bisa maganar masu fashin baƙi huɗubar Sayyida Zainab (A.S) ta bada gudunmawa wajan wanzar da gwagwarmayar Imam Husaini (A.S) da wajan cimma burinta da ba da gudunmawa wajan kunyata mahukunta Bani Umayya. Kuma ana mata laƙabi da Ummul Masaib (Uwar musibu) sakamakon musibun da ta gani a rayuwarta.
Sayyida Zainab (A.S) ta yi wafati a shekara ta 62 hijira, kuma an binne ta a Dimashƙi. Akwai raayi guda biyu; na ɗaya yana cewa ta yi wafati ne a Alƙahira, kuma aka binne ta a can. Ra'ayi na biyu kuma yana cewa an binne ta ne a maƙabartar Baƙia a birnin Madina.
Tarihi
Ita ce Zainab ƴar Amirul Muminin Ali ɗan Abi Ɗalib (A.S), mahaifiyarta kuma ita ce Faɗimatuz Azzahara (A.S).[1]
Kalmar Zainab akwai maganganu da yawa kan maanarta, amma masu muhimmaci daga cikinsu sune; suna wata bishiya ce mai kyan gani, mai ƙamshi.[2] ya zo cewa asalin kalmar shi ne Zainu Ab,[3]
Abun nufi shi ne kwalliya da ƙawa ta mahaifi. Ya zo cikin wasu litattafai da aka rubuta na wannan zamanin cewa yayin da aka haifi Sayyida Zainab (A.S) mahaifiyarta Zahara (A.S) ta kaita gurin mahaifinta Amirul Muminina (A.S) ta ce mishi ka raɗa ma wannan jaririyar suna, sai ya ce ba zan gabaci Manzon Allah ba, a lokacin Ma'aikin Allah (S.A.W) ya yi tafiya, lokacin da ya dawo sai Amirul muminina ya tambaye shi da ya raɗa mata suna, sai ya ce, ba zan riga ubangijina ba wajan raɗa mata suna ba, to anan ne Malaika Jibrilu ya sauka ya isar da saƙon gaishe da Annabi (S.A.W) daga Allah maɗaukaki, sai ya ce mishi ka raɗawa wannan jaririyar suna (Zainab) lalle Allah ne ya zaɓa mata wannan sunan.[4]
Laƙubbanta
An yiwa Sayyida Zainab laƙabi da wasu adadin laƙubba waɗanda suke nuna girman wannan baiwar Allah, daga cikinsu akwai; Aƙilatu Bani Hashim, da Alima gairu Muallama, da Arifa, Muwassaƙa da Fadila, da Kamila, da Abidatu Ale Ali, da Maasuma Assugura, da Aminatullahi, da Naibatu Zahra da Naibatul Husaini, da Aƙilatu Nisai, da Sharikatu Shuhada, da Baliga, da Fasiha, da Sharikatul Husaini[5] da Ummul Masaib[6] kuma ana yi mata alkunya da Ummu Kulsum.[7]
Haihuwarta Da wafatinta
An haifi Sayyida Zainab (A.S) a Madinatul munawwara a ranar 5 ga Jimada Ula a shekara ta biyar ko 6 hijirar Annabi[8] ta rasu a ranar 15 ga watan Rajab a shekara ta 62 hijira[9] amma a wani naƙalin ta rasu ne a ranar 14 ga Rajab.[10]
Mijinta Da Ƴayanta
Lokacin da Sayyida Zainab ta zama budurwa an nemi aurenta, daga cikin waɗanda suka nema akwai ɗan ɗan uwan babanta Abdullahi ɗan Jafar ɗan Abi Ɗalib, Imam Amirul Muminina (A.S) ya kasance yana da shaawar aurar da ƴaƴanshi ga ƴaƴan ƴan uwanshi kamar ƴaƴan Aƙil da ƴaƴan Jafar, ta yiwu abin da ya sa hakan shi ne yin aiki da maganar Ma'aikin Allah (S.A.W), lokacin da ya kalli ƴaƴan Imam Ali (A.S) da ƴaƴan Jafar Bin Abi Ɗalib sai ya ce, ƴaƴanmu mata na ƴaƴanmu maza ne, bayan haka sai aka sami dacewa ta yin aure a tsakaninsu.
Sayyida Zainab (A.S) ta haifi Ali da Aunu da Abbas da Muhammad da ƴa mace mai suna Ummu Kulsum.[11]
Halayen Sayyida Zainab Da Falaloli Da Darajoji
Ayyukanta
Huɗubobin da Sayyida Zainab (A.S) ta yi a Kufa da cikin fadar Ubaidullahi Bin Ziyad da fadar Yazidu ɗan Mu'awiya a Shim suna nuna zurfin iliminta cikin ayoyin Alƙurani da ƙari da hadisan da ta rawaito daga mahaifinta Amirul Muminin Ali (A.S) da mahaifiyarta Faɗima Zahara (A.S)[12] ta kasance tana zaman tafsiri ga mata a garin Kufa a lokacin mulkin mahaifinta. [13]
Abdullahi Bin Abbas da Muhammad Bin Amru da Aɗau Bin Saib da Faɗima yar Husaini da sauransu sun rawaito daga gareta[14] ita kuma ta rawaito daga Maasumai (A.S) kan maudui mabambanta, daga ciki akwai hadisan da suke magana kan matsayin ƴanShi'a da masoya iyalan gidan manzo (S.A.W) da hadisan da suke shafi fadak da haƙƙin maƙwabci da kan aiko manzo da sauransu.
Ibadar Sayyida Zainab(A.S)
Sayyida Zainab (A.S) ta kasance tana raya dare da yin sallah da karanta Alƙurani, ta kasance mai ibada cikin matan Musulmi saboda haka aka yi mata laƙabi da mai ibadar iyalan gidan manzo[15] babu wata nafila da akeyi a rana face sai ta yi ta, wasu masu rawaito ruwaya suna cewa, Sayyida Zainab (A.S) ta yi sallar nafila a dare mafi tsanani da wahala, wannan dare shi ne daren 11 ga wata Muharram, Faɗima ƴar Husaini (A.S) ta ce, Amma gwaggona Zainab, ta kasance tsaye a daren nan a mihrabinta tana roƙon Ubangiji. Ba mu sami nutsuwar ido ba, kuma ba mu sami shiru daga kuka ba.[16]
Kamewar Sayyida Zainab (A.S)
Wasu misalai na kame kai da sanya hijabi na Sayyida Zainab (A.S) sun zo cikin wasu litattafai waɗanda suka yi magana kan rayuwarta, idan tana so ta tafi ziyara kabarin kakanta Ma'aikin Allah (S.A.W) ta kasance tana tafiya da mahaifinta Imam Amirul muminin (A.S) da ƴanuwanta Hassan da Husaini (A.S) Hassan a hannun damarta Husaini (A.S) kuma daga hagu, Imam Amirul Muminina Ali (A.S) yana yin sauri ya kashe hasken fitilun da suke kan kabarin, sai Imam Hassan (A.S) ya tambaye shi kan yin hakan, sai ya ce mishi ina jin tsoron wani ya kalli ƴar uwarka Haurau.[17]
Yahaya Mazini ya ce, na kasance maƙwabcin Amirul Muminina (A.S) a cikin garin Madina zuwa shekaru masu yawa, kusa da gidan da Sayyida Zainab (A.S) take rayuwa, ya ce na rantse da Allah, ban taɓa ganin ta ba, kuma ban taɓa jin maganar ta.[18]
Haƙurinta Da Jajircewarta
Sayyida Zainab (A.S) ta zama misali guda ɗaya tilo wajan haƙuri da jajircewa, Sayyida Zainab (A.S) ta yi haƙurin da zai bawa duk wani mahaluƙi mamaki kan dukkan musibun da suka same ta, har lokacin da Sayyida Zainab (A.S) ta tsaya kan gawar ɗan uwanta Imam Husaini (A.S) a wannan yanayi mai wahala wanda yake cike da raɗaɗi, ta buɗa hannunta a ƙarƙashin jikinta mai tsarki ta ɗaga shi zuwa sama ta ce, Allah ka karɓi wannan abin da muka sadaukar [19] kuma Sayyida Zainab (A.S) ta dake a gaban irin waccan guguwar mai tsanani da musiba babba duk da cewa ita aka zalinta da kuma baƙuntarta haƙiƙa ta kasance mai yarda da ƙaddarar Allah da abin da ya hukunta.[20]
Sayyida Zainab (A.S) a lokuta da dama ta ba da babbar gudunmawa wajen tseratar da Imam Sajjad (A.S) da kuɓutar da shi daga mutuwar da take yinƙurin ɗauke shi, daga cikin irin wannan gudunmawa, akwai lokacin da sojojin Kufa suka kaiwa Imam Zainul Abidina (A.S) hari a lokacin da rashin lafiya ta ci ƙarfinshi, to a lokacin ne Shimru Bin Zul Jaushan ya so ya kashe shi, a lokacin ne Aƙila Zainab (A.S) ta gaggauta kai masa ɗauki ta riƙe shi, ta ce ba za a kashe shi ba har sai an kashe ni.[21]
Da lokacin da Imam Sajjad (A.S) ya yi raddi ga Ibn Ziyad san da ya yi fishi a wannan majalisi, sai Ibn Ziyad ya ce, kana da ƙarfin hali kabani amsa, shin kana da wani sauran ƙoƙari ka yi mini raddi? Sai ya umarci da a tafi da shi kuma a datse kanshi. Sayyida Zainab (A.S )ta ƙara riƙe shi, ta ce, ya kai ɗan Ziyad jinin da ka zubar mana ya isheka, sai ta ringume Imam Sajjad(A.S)sai ta ce, wallahi bazan rabu da shi ba, ta ce idan kana so ka kashe shi, to ka kashe ni tare da shi.[22]
Fasaharta Da Balagarta
Sayyida Zainab (A.S) ta kai ƙololuwa a fasaha da balaga, har abin ya kai cewa waɗanda suka ji ta tana huɗuba a Kufa sun siffanta tasirinta da ta haifar sakamakon huɗubobinta da cewa, wallahi ba su taɓa gani wata wadda ta kai ta iya huɗuba ba, sun ce kamar tana magana ne da harshen Amirul Muminina Ali (A.S).[23] Fasaharta da balagarta ta yi kama da fasaha da balagar mahaifinta Amirul Muminina Ali (A.S) yayin da ta yi magana a majalisin Ubaidillahi a Kufa da majalisin Yazid a Sham, kuma ta yi kama da balagar mahaifiyarta a huɗubarta ta Fadak.[24]
Waɗanda suka halarci huɗubarta sun yi bayani yadda mutane suke tasirantuwa da ita, wani ya ce: Na rantse da Allah, na ga mutane a ranar nan cikin rikicewa suna kuka, suna rufe bakinsu da hannayensu. Na ga wani dattijo tsaye a gefena yana kuka har gemunsa ya jike, yana cewa: Ku ne rayuwata da iyayena! Tsofaffanku mafi alheri ne daga tsofaffi, matashanku mafi alheri ne daga matasa, matanku mafi alheri ne daga mata, kuma zuriyarku mafi alheri ce daga zuriyar da ba ta taɓa kunyata ba kuma ba ta taɓa wulakanta ba.[25]
Zainab (A.S) A Waƙi'ar Ashura
Sayyida Zainab (A.S) ta yi tarayya da ɗan uwanta Husaini (A.S) a gwagwarmayarshi, ta halarci waƙi'ar Ashura, bayan shahadar Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi an kama ta tare da sauran fursinonin yaƙi, aka kora su zuwa Sham.
A Daren Ashura
Shaikh Mufid ya rawaito daga Imam Sajjad (A.S) cewa ni na kasance ina zaune a wannan safiyar da aka kashe babana, ina gurin ƴar uwar babana Zainab (A.S) tana jinya ta tana kulawa da ni.
Amma gwaggona Zainab, ta ji abin da na ji, ita mace ce, kuma daga halayen mata akwai taushi da damuwa. Ba ta iya riƙe kanta ba, sai ta tashi tana jan rigarta, ba tare da mayafi ba, har ta kai gare shi ta ce: Wayyo asara! Da mutuwa ta raba ni da rayuwa. Yau ne mahaifiyata Faɗima ta mutu, mahaifina Ali ya mutu, da ɗan uwana Hassan ya mutu. Ya mafaka ga waɗanda suka rage. Sai Husain ya dube ta ya ce: Ya ƙanwata, ka da shaiɗan ya raba ki da hankalinki. Idanunsa suka cika da hawaye, ya ce: Da an bar kurciya, da ta yi barci. Sai ta ce: Wayyo! Shin za a tilasta a kashe ka? Wannan shi ne mafi raɗaɗi a zuciyata kuma mafi nauyi a raina.Sai ta bugi fuskarta, ta kai hannunta ga rigarta, ta yayyaga ta, sannan ta faɗi sume.
sai Husaini (A.S) ya tashi yaje gurinta ya zuba mata ruwa a fuska, sai ya ce mata, yake yar uwata, kiji tsoran Allah, kiyi jimami da jimami irin na Allah, sai Imam ya tafi da ita gurinshi ya zaunar da ita a gurina.[26]
A Ranar Ashura
A ranar Ashura da laasar 10 ga Muharram Shimru Bin Zil Jaushan ya yi umarni da a yiwa Imam Husaini (A.S) ruwan masu, suka yi mishi ruwan masu, Sayyida Zainab (A.S) ta fita zuwa ƙofar rumfa ko tanti zuwa filin yaƙi, ta yi magana da Umar Bin Saad ta ce mishi, ya kai ɗan Saad shin za a kashe Abu Abdullahi alhalin kai kana kallo? ya yi shiru bai ce mata uffan ba.[27]
Yayin data isa zuwa gurin jikin ɗan uwanta wanda yake cikin jini, sai ta sa hannunta ƙarƙashin jikinsa mai tsarki, ta ɗaga shi sama, ta ce, ya Allah ka karɓi wannan abin da muka sadaukar[28] An rawaito cewa Sayyida Zainab (A.S) ta zauna kusa da jikin ɗan uwanta, ta fuskanci Madinatul Munawwara, tana mai kira, Ya muhammad! ƴaƴanka mata an kama su a matsayin bayi, zuriyarka an kashe su, iska tana kadawa a kansu. Ga wannan Husain, an yanke kansa daga baya, an kwace masa rawani da riga.[29] Sai da sanya masoya da maƙiya kuka.[30]
Sayyida Zainab (A.S) A Kufa
- Ku duba: Huɗubar Sayyida Zainab (A.S) A Kufa
Lokacin da yaƙi ya ƙare, sai aka tafi da sauran mata da yara da iyalai a matsayin fursunonin yaƙi zuwa Kufa a wani yanayi mai ban takaici, isar su Kufa keda wuya sai Sayyida Zainab (A.S) ta yi huɗuba mai girma ga mutanen Kufa wace Bashir ɗan Kuzaim Asadi ya siffanta ta da cewa, Na kalli Zainab yar Ali (a.s) a ranar nan, kuma ban taɓa ganin mace mai kunya da ta fi iya magana ba – na rantse da Allah – kamar dai harshen Amirul Muminin Ali ɗan Abi Ɗalib (A.S) ne yake fitowa daga bakinta. Sai ta yi ishara ga mutane da su yi shiru, nan da nan numfashi ya tsaya, karar ƙaho da ƙararrawa ta yi shiru[31] Sai ta ce, godiya ga Allah, aminci ya tabbata ga babana Muhammad da iyalan gidanshi masu tsarki kuma zaɓaɓɓu, bayan haka ya ku mutanan Kufa, ya ku mayaudara, shin kuna kuka ne? hawaye bai bashe ba baa daina kuka ba,.....
Ya zo a cikin huɗubar Sayyida Zainab (A.S) a cikin jawabin ta ga Yazid:
Ko da kuwa musifu sun tilasta ni yin magana da kai, lallai ina ƙasƙantar da darajarka, ina ganin gargaɗinka da yawa, da kuma tsananta tofin ala tsine akanka. Amma idanu sun cika da hawaye, ƙiraje kuma suna da zafi. Abin mamaki, mamaki mai girma, ga yadda aka kashe zaɓaɓɓun Allah, rundunar Allah ta hannun rundunar shaiɗan waɗanda aka saki. Waɗannan hannaye suna ɗigar da jinayenmu, waɗannan bakuna suna nuna maita ga namanmu. Waɗannan jikkunan tsarkaka masu tsarki suna zama abin ci ga namun daji, kuma uwayen kekkeci suna binne su da ƙasa. Kuma idan ka ɗauke mu ganima, za ka same mu nan gaba azaba, a lokacin da ba za ka samu komai ba sai abin da hannuwanka suka aikata. Kuma Ubangijinka ba mai zaluntar bayinsa ba ne.
Quran: Maida: Aya Mausuatul Awalim, shafi na 462
Sai Bashir ya ce, wallahi a wannan rana na ga mutane a ruɗe suna kuka, sun sa hannuwansu cikin bakinsu, mutane sun fashe da kuka, mata sun nuna damuwarsu kuma sun kwance gashin kansu, sun zuba ƙasa a kan fuskarsu, sun jiwa fuskarsu ciwo, sun daki kumatunsu, suna kiran wayyo musiba, maza sun yi kuka sun tsige gashin gemunsu, ba a taɓa ganin yadda mutane suka yi kuka irin wannan ranar ba. Wannan magana ta zo cikin huɗubar da Sayyida Zainab (A.S) ta yi ga Yazid.
Idan wata musiba tasameni saboda nayi magana da kai, to lalle ni zan renaka, kuma zan girmama ganin laifinka kuma zan yawaita jamaka kunne, sai dai cewa idanuwa sun yi kuka kuma ƙiraza sun cika da damuwa, ku saurara, abin da yafi komai ban mamaki shine kashe rundunar Allah kuma zaɓaɓɓu da rundunar Shaiɗan marassa daraja suka yi. Wannan hannaye ne da jininmu yake ɗiga daga garesu, da bakunan da naman jikinmu yake zuba, kuma wannan gawakinmu ne masu tsarki da...
Yayin da Ibn Ziyad ya ji tsoran yi ka da mutane su yi mishi bore da juyin mulki, sai ya yi umarni da a shigar da iyalan Imam Husaini (A.S) cikin fadar gwamnati[32]
Sai a aka shigar da Sayyida Zainab (A.S) da sauran waɗanda suka kamo a matsayin fursunonin yaƙi cikin gidan mulki, amma fa duk da haka Sayyida Zainab (A.S) ba ta yi shiru ba, ta tunkari Ibn Ziyad da maganar da bayyanannun hujjojin da suka rusa nasa suka bayyanar da wautar raayinsa.[33]
Maganar Sayyida Zainab (A.S) da ta Imam Sajjad (A.S) da ta Ummu Kulsum da ta Faɗima ƴar Imam Husaini (A.S) a Kufa da ƙari da boren da Abdullahi Bin Afif Azdi da Zaidu ɗan Arƙam suka yi, ya yi tasiri sosai wajan canja raayin mutanen Kufa da nadamarsu kan abin da suka aikata, a ƙarshe hakan ne ya sa suka fara tinanin ɗaukar fansar Shahidai daga waɗanda suka kashe su, kuma hakan shi ne ya kai ga saka ɗanba na yin hamayya da gwamnati da samar da yanayin yunƙurin da Mukhtar Saƙafi ya jagoranta da samun goyan baya daga alumma.
Tare da Tawagar Fursunoni Zuwa Sham
Ku duba: Huɗubar Sayyida Zainab (A.S) A Sham Ubaidullahi ɗan Ziyad ya gaggauta rubuta rahoto zuwa ga Yazid ɗan Mu'awiya a Sham domin sanar da shi kashe Imam Husaini (A.S) da kuma isowar firsinonin yaƙi da kawukan waɗanda aka kashe zuwa Kufa, sai Yazidu ya amsa da cewa a gaggauta tura firsinonin tare da kawukan zuwa gare shi, sai Ibn Ziyad ya gaggauta tura tawagar firsinonin da kawukan zuwa Sham.[34]
Sai Ubaidullah ya tura kawukan a hannun Zajar ɗan Ƙaisi, su kuma Fursunonin ya tura su tare da Mukhfar ɗan Saalaba Alaizi da Shimru ɗan Zil Jaushan
Mu'awiya ne ya tabbatar da mulkin Umayyawa a Sham, alamura sun kasance suna tafiya daidai gun Yazidu ɗan Mu'awiya saboda ƙarfin da yake da shi wajan watsa labarai, hakan ta bawa Alu Abi Sufuyan damar kawar da hankalin mutane da nuna cewa Banu Ummayya sune waɗanda ya kamata su gaji Annabi (S.A.W),Yazid yana rayuwa cikin kwanciyar hankali na siyasa da tsaro, ba tare da wata barazana mai girma ba, Sahabi Sahal ɗan Saad Saidi ya siffata halin farin ciki a Sham gab da zuwan Fursunonin karbala da cewa; Na fita zuwa Baytul Maqdis har na shiga tsakiyar Sham. Sai na same ni a cikin birni mai yawan rafuka da koguna, mai cike da itatuwa. Sun rataye labule da shinge da kayan alfarma, suna cikin farin ciki da murna. Kuma akwai mata suna wasa da bandiri da ganguna.[35]
Amma cikin sauri alamura suka canza sama zuwa ƙasa bayan shigar tawagar firsinoni zuwa cikin Sham da sakamakon sauraran huɗubar da Imam Sajjad (A.S) ya yi da huɗubar Sayyida Zainab (A.S) wacce ta kunyata Ummayyawa kuma ta bayyana munin abin da suka aikata, ta rage zafin ƙiyayar mutanen Sham ga Ahlul-bait (A.S) ta canza mutane daga maƙiya zuwa masoya da tausayawa iyalan gidan Manzo (S.A.W) a cikin wannan yanayi ne Yazid ɗan Mu'awiya ya shirya zama irin wanda ba a taɓa yin irin shi ba, dukkan shuwagabanni da masu muƙami[36] sun halarta, Yazidu yana cikin yanayi da yake ganin ya yi nasara ya yi furici irin na kafurci da shirka.[37]
Aka kawo masa kan Imam Husaini (A.S) aka ajiye shi a gabansa cikin wata tasa sai ya dinga caccakar wushiryarshi da wata ƴar sanda da take hannunshi[38] yana mai bayyana ƙiyayyarshi wacce ya ɓoye ga Manzon Allah (S.A.W) da saƙon da yake ɗauke dashi, sai fara misali da maganar Ibini Zabaara wanda yake shi Mushiriki ne ya kuma ƙara wasu baituci a kai:
Yayin da ya ke rera waɗannan baitikan cikin maye, sai Sayyida Zainab (A.S) ta tashi ta fara huɗuba, ta buɗe maganarta da godiya ga Allah da tabbatar da aminci ga Annabi (S.A.W) sannan ta ci gaba da huɗubarta tana mai gargaɗi ga Yazidu kan irin siyasar da yake amfani da shi kan iyalan gidan Manzo (S.A.W) ta takurawa, tana mai nuna ƙin gaskiyarshi da girman kanshi da kafiricinshi. Ta ci gaba da cewa wannan sakamakon ƙiyayya da ƙin juna da suka ɓoye kuma suka rage tun daga yaƙin Badr da gwagwarmayar farkon Musulunci. Sannan ta yi masa gargadi kan abin da ya aikata na keta hurumin Shugaban matasan Aljanna. Duk wannan yana a gaban Allah. Ta ce wa Yazid: Zai sauka a kanka fushin Allah, kuma Manzon Allah (S.A.W) zai yi maka ƙara, har ka yi nadama ka ce da ace mahaifiyarka ba ta haife ka ba.[39]
Cikin huɗubarta ta cewa Yazidu ɗan Mu'awiya kayi duk makircinka, ka yi duk ƙoƙarin da zakayi, kayi amfani da duk ƙoƙarin da ake dashi, to narantse da Allah bazaka iya kawar da wantsuwarmu ba kuma zaka iya kawar da wahayinmu ba, ba kuma zaka iya sanin mu suwanene ba, ba zaa kankare maka wannan laifin ba.
Lokacin da Yazidu ya ga cewa wannan laifin da ya aikata na kashe Imam Husaini (A.S) ya bayyanar da abin da ya ɓoyewa mutane ta hanyar huɗubar Sayyida Zainab (A,S) da wasu daga cikin iyalan gidan Imam Husaini (A.S), sai ya fara barranta kanshi daga wannan mummuna aiki, ya fara ɗora alhakin abin da ya faru kan Ubaidullahi ɗan Ziyad.[40]
Sayyida Zainab (A.S) ta yi jawabi ga Yazid ɗan Mu'awiya, tana cewa:
فكِد كَيدَك، وَاسعَ سَعيَك، وناصِب جُهدَك، فَوَاللهِ! لا تَمحُو ذكرَنا، ولا تُميتُ وَحيَنا، ولا تُدرِكُ أَمَدَنا، ولا تَرحَضُ عَنكَ عارُها.
Ka yi makirci naka, ka yi ƙoƙarinka, ka yi iyakar ƙoƙarinka! Amma wallahi, ba za ka iya goge ambaton mu ba, ba za ka iya kashe fitilar hasken wahayinmu ba, ba za kawo ƙarshenmu ba, kuma ba za ka iya wanke abin kunya da yake tattare da kai ba.
- Mausua al-Awalim, Al-Imam Husaini, shafi na 462
Daga nan ne Yazidu ya umarci da a ginawa Fursunonin gida jikin gidanshi, sai mata daga iyalan Abi Sufyan suka kai musu ziyara daga cikinsu akwai Hindu matar Yazidu ɗan Mu'awiya, har suka yi zaman makoki kan Imam Husaini (A.S).[41] Bayaan kwana uku Yazidu ya yi umarni da a mayar da su zuwa Madina.[42]
Kabarin Sayyida Zainab (A.S)
Akwai magana guda uku kan kabarinta da inda aka binne ta: Sham: Abin da ya shahara shi ne cewa kabarin Sayyida Zaina (A.S) yana kudancin babban birnin Siriya Dimashƙi, inda ake kiran yanki da aka binne ta da sunan Zainabiyya.[43] Misra: Wasu malaman tarihi sun kawo cewa kabarin Sayyida Zainab (A.S) yana ƙahira a wani guri da ake kira da yankin Sayyida Zainab (A.S) wannan guri sake ginashi sau da yawa, shi ne gurin da aka fi sani da Maƙamin Sayyida Zainab ko masallacin Sayyida Zainab. Maƙabartar Baƙia: Akwai wasu malaman tarihi da suka yi imani cewa kabarinta yana maƙabartar Baƙia a Madina, daga cikin masu goyan bayan wannan magana akwai Sayyid Muhsin Amin.[44]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Ibn Asakir, Alam an-Nisa, shafi 189–190.
- ↑ Ibn Manzur, Lisan al-Arab, jild 1, shafi 453; Zubaidi, Taj al-Arus, jild 2, shafi 60.
- ↑ Zubaidi, Taj al-Arus, jild 2, shafi 60
- ↑ Baqir Sharif Qurashi, Sayyida Zainab, shafi 39; Hassan al-Hayyi, Zainab al-Kubra Aqilat Bani Hashim, Tehran, Afrinah, shafi 29
- ↑ Nuruddin al-Jazairi, Al-Khasa'is az-Zainabiyya, shafi 52–53
- ↑ Nuruddin al-Jazairi, Al-Khasa'is az-Zainabiyya, shafi 52–53
- ↑ Nuruddin al-Jazai'ri, Al-Khasa'is az-Zainabiyya, shafi 48; Qurashi, Sayyida Zainab, shafi 39
- ↑ Muhallati, Zabihullah, Rayahin ash-Sharia, jild 3, shafi 33; Muhammadi Ishtihardi, Hazrat Zainab Furugh Taban Kawthar, shafi 17
- ↑ Qazwini, Zainab al-Kubra min al-Mahd ila al-Lahd, Dar al-Ghadir, shafi 561
- ↑ Qurashi, Sayyida Zainab Batulat at-Tarikh…, shafi 298.
- ↑ Ibn Asakir, Alam an-Nisa, shafi 190; Rayahin ash-Sharia, jild 3, shafi 41; Tarjamat Zainab Kubra, shafi 89
- ↑ Ibn Asakir, Alam an-Nisa, shafi 189
- ↑ Dalail al-Imama, at-Tabari, jild 3; Zabihullah Muhallati, Rayahin ash-Sharia, shafi 57.
- ↑ Nahj al-Balagha Ibn Abi al-Hadid, jild 16, shafi 210; Wasail ash-Shia, jild 1, shafi 13–14; Bihar al-Anwar, jild 6, shafi 107
- ↑ Jafar an-Naqdi, Zainab al-Kubra bint al-Imam, shafi 61
- ↑ Ahmad Sadiqi Ardestani, Zainab Qahraman Dukhtar Ali, shafi 106.
- ↑ Sayyid Abdul-Husayn Dastghayb, Zindagani Hazrat Zainab (Hayat Sayyida Zainab), Tehran, Kaweh, shafi 19.
- ↑ Muhammad Muhammadi Ishtihardi, Hazrat Zainab Furugh Taban Kawthar, shafi 99.
- ↑ Sayyid Ali Naqi Faydh al-Islam, Khatoon Dosra, shafi 185.
- ↑ Sayyid Nuruddin al-Jazairi, Al-Khasa'is az-Zainabiyya, shafi 24
- ↑ Muqarram, Maqtal al-Husayn (a.s), shafi 316.
- ↑ Muhammad Baqir Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 117
- ↑ Khawarizmi, Maqtal al-Husayn, jild 2, shafi 45.
- ↑ Sayyid Kazim Arfa, Hazrat Zainab (alayha as-salam) Sirah Amali Ahl al-Bayt (Sayyida Zainab alayha as-salam, Sirah Ahl al-Bayt al-Amaliyya), shafi 88.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, al-Luhuf, shafi 179. Muhammad Baqir Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 11
- ↑ Mufid, al-Irshad, jild 2, shafi 93–94.
- ↑ Sayyid Ibn al-Tawus, al-Luhuf, shafi 159 da 161.
- ↑ As-Sadr, Adhwa ala Thawrat al-Husayn, shafi 96.
- ↑ Abu Mikhnaf, Waqat al-Taff, shafi 259; Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 59.
- ↑ Abu Mikhnaf, Waqat al-Taff, shafi 295; Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, jild 5, shafi 348–349; Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 59
- ↑ Ahmad Sadiqi Ardestani, Zainab Qahraman Dukhtar Ali (Zainab al-Batula bint Ali), shafi 227–228
- ↑ Ahmad Sadiqi Ardestani, Zainab Qahraman Dukhtar Ali, shafi 246.
- ↑ Abu Mikhnaf, Waqat al-Taff, shafi 299–300;Shaik Mufid, al-Irshad, Qum, Mutamar Shaik Mufid, 1413, shafi 353; Muhammad Baqir Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 117
- ↑ Sayyid Abdul-Karim Hashimi Najad, Darsi keh Husayn be Insanha Amukht, shafi 326; kuma duba: Salih bin Ibrahim bin Salih Shahrastani, Tarikh an-Niyahah ala al-Imam ash-Shahid al-Husayn bin Ali (a.s), shafi 71
- ↑ Muhammad Muhammadi Ishtihardi, Hazrat Zainab Furugh Taban Kawthar, shafi 327–328.
- ↑ Sayyid Abdul-Karim Hashimi Najad, Darsi keh Husayn be Insanha Amukht, shafi 330.
- ↑ Muhammad Muhammadi Ishtihardi, Hazrat Zainab Furugh Taban Kawthar, shafi 248.
- ↑ Hasan al-Hayyi, Zainab al-Kubra Aqilat Bani Hashim, shafi 208.
- ↑ Muhammad Baqir Majlisi, Bihar al-Anwar, jild 45, shafi 135;
- ↑ Shaik Mufid, al-Irshad, shafi 358; Hasan al-Hayyi, Zainab al-Kubra Aqilat Bani Hashim, shafi 244
- ↑ Abu Mikhnaf, Waqat al-Taff, shafi 311; Shaik Abbas Qummi, Nafas al-Mahmum, shafi 265
- ↑ Ibn Asakir, Alam an-Nisa, shafi 191.
- ↑ Qurashi, Sayyida Zainab Batulat at-Tarikh…, shafi 298–303
- ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, jild 7, shafi 140–141
Nassoshi
- Abbas Qummi, Nafas al-Mahmum, Tehran, Shagon sayar da litattafan Musulunci, 1368 H Sh.
- Abd al-Razzaq Al-Musawi, Maqtal Muqarram, fassara: Aziz Ilahi Karmani, Qum, Nawid, 1381 H Sh, shafi na 192.
- Abu Mikhnaf, Waq'at al-Taff, bincike da gyara: Muhammad Hadi Al-Yusufi Al-Gharawi, Qum, Majma' al-Alami li Ahl al-Bait, bugu na biyu, 1427 H.
- Abu al-Qasim Al-Dibaji, Zainab al-Kubra Batulat al-Hurriyya, bugu na biyu, Beirut, Al-Balag, 1417 H.
- Ahmad Behishti, Zanan Namdar dar Qur'an wa Hadith, Tehran, Hukumar Yaɗa Addinin Musulunci, 1368 H Sh.
- Ahmad Sadiqi Ardastani, Zainab Qahraman Dokhtar Ali, Tehran, Zainab al-Batula Bint Ali, Mawallafar Mutahhar, 1372 H Sh.
- Al-Muhaddith Al-Nuri, Mustadrak al-Wasa'il, Qum, Al al-Bait, 1407 H.
- Ali Nazari Munfarid, Qisstul Karbala, bugu na goma sha uku, Qum, Surur, 1384 H Sh.
- Amin, Sayyid Muhsin, A'ayanush Shi'a, bincike da gyara: Hassan Amin, Beirut, Dar al-Ta'aruf lil-Matbu'at, 1406 H / 1986 M.
- Baqir Sharif Qurashi, Al-Sayyida Zainab, Beirut, Dar al-Mahajja al-Baida, bugu na farko, 1422 H / 2001 M.
- Baqir Sharif Qurashi, Al-Sayyida Zainab, Beirut, Dar al-Ta'aruf, 1419 H.
- Hasan Ilahi, Zainab Kubra Aqila Bani Hashim, Tehran, Afrina, 1375 H Sh.
- Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balagha, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, 1418 H.
- Ibn Asakir, A'lam al-Nisa, bincike da gyara: Muhammad Abd al-Rahim, Beirut, Dar al-Fikr, 1424 H / 2004 M.
- Ibn Jum'a Al-Arusi Al-Huwaizi, Tafsir Nur al-Thaqalain, bincike da gyara: Hashim Rasuli Mahallati, Qum, Isma'iliyan, 1373 H.
- Ibn Manzur, Muhammad bn Mukarram, Lisan al-Arab, Qum, Mawallafar Adab al-Hawza, 1405 H.
- Ja'far Al-Naqdi, Zainab al-Kubra Bint al-Imam, Najaf al-Ashraf, Al-Maktaba al-Haidariyya, 1361 H.
- Jaza'iri, Sayyid Nuruddin, Al-Khasa'is al-Zainabiyya, Qum, Mawallafar al-Maktaba al-Haidariyya, bugu na farko, 1425 H / 1383 H Sh.
- Jibran Mas'ud, Al-Ra'id, fassara: Riza Anzabi, bugu na biyu, Mashhad, Astana Quds Razawi, 1376 H Sh.
- Khwarizmi, Muwaffaq bn Ahmad, Maqtal al-Husain, babu wurin bugawa, Anwar al-Huda, bugu na biyu, 1423 H.
- Mahallati, Zabihullah, Riyahin al-Shari'a, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, babu kwanan wata.
- Muhammad Ashtehardi, Muhammad, Hazrat Zainab Forugh Tabban Kawthar.
- Muhammad Baqir Majlisi, Bihar al-Anwar, Beirut, Cibiyar al-Wafa, bugu na uku, 1403 H / 1983 M.
- Muhammad Muhammadi Ashtehardi, Hazrat Zainab Forugh Tabban Kawthar, bugu na uku, Tehran, Burhan, 1379 H Sh.
- Muhammad bn Jarir Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Qahira, Matba'at al-Istiqama, 1358 H.
- Muhammadi Ri Shahr, da wasu, Daneshnama-yi Imam Husain (Mausu'ar Imam Husain), juzu'i na 10, mai fassara: Muhammad Muradi, Qum: Dar al-Hadith, 1430 H / 1388 H Sh.
- Muqarram, Abd al-Razzaq, Maqtal al-Husain (Alaihis Salam), Beirut, Cibiyar al-Khirsan lil-Matbu'at, 1426 H / 2007 M.
- Nasir Makarim Shirazi da wasu, Tafsir Namuna (Al-Amthal), Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1361 H Sh.
- Qazwini, Muhammad Kazim, Zainab al-Kubra min al-Mahd ila al-Lahd, Beirut, Dar al-Qari, bugu na biyu, 1427 H / 2006 M.
- Qazwini, Muhammad Kazim, Zainab al-Kubra min al-Mahd ila al-Lahd, Qum, Dar al-Ghadir, bugu na biyu, 1424 H / 2003 M.
- Sadr, Sayyid Muhammad Baqir, Adwa' Ala Thawrat al-Husain, bincike da gyara: Kazim Al-Abbadi Al-Nasiri, babu wurin bugawa, babu mawallafi, babu kwanan wata.
- Sayyid Abd al-Husain Dastghaib, Zendagani Hazrat Zainab, Tehran, Kaveh.
- Sayyid Abd al-Karim Hashimi Najad, Darsi ke Husain be Insanha Amukht, bugu na goma sha ɗaya, Mashhad, Hashimi Najad, 1369 H Sh.
- Sayyid Ibn Tawus, Al-Luhuf, fassara: Aqiqi Bakhshayishi, Qum, Daftar Mawallafar Nawid Islam, bugu na biyar, 1378 H Sh.
- Sayyid Kazim Arfa', Hazrat Zainab (Alaihas Salam) Sira-yi Amali Ahl al-Bait, Tehran, Mawallafar Qadir, 1377 H Sh.
- Sayyid Salih bn Ibrahim bn Salih Shahrastani (Allah Ya jiƙansa), Tarikh al-Niyaha Ala al-Imam al-Shahid al-Husain bn Ali (Alaihimassalam), shafi na 71, bincike da shiryawa: Sheikh Nabil Riza Alwan, 1325–1395 H.
- Shahidi, Sayyid Ja'far, Zendagani Fatima Zahra (S), Tehran, Daftar Mawallafar Farhang Islami, 1363 H Sh.
- Shaikh Mufid, Al-Irshad, Qum, mai bugawa: Sa'id bn Jubair, bugu na farko, 1428 H.
- Ubaidali A'raji, Akhbar al-Zainabat, Hukumar Buga Manyan Littattafai, Masar.
- Zubaidi, Muhammad, Taj al-Arus min Jawahir al-Qamus, bincike da gyara: Ali Shiri, Beirut, Dar al-Fikr, 1414 H / 1994 M.
- Sayyid Ali Naqi Faiz al-Islam, Khatun Duwum (Sharhu Hali Zainab) [Sayyidat al-Alamin], bugu na biyu, Tehran, Mawallafar Athar Faiz al-Islam, 1366 H Sh.
- Articles with hatnote templates targeting a nonexistent page
- Sayyida Zainab
- Ƴaƴan Imam Ali
- Fursunonin Waƙi'ar Karbala
- Masu Kawo Rahoton Waƙi'ar Karbala
- Ƴaƴan Imamai Da Aka Binne A Dimashƙi
- Ƴaƴan Sayyida Faɗima
- Matan Sahabbai
- Matan Banu Hashim
- Marawaita Daga Imam Ali
- Marubutan Waƙoƙin Makoki Na Ashura A Ƙarni na 1 (Hijira)