Fuztu Wa Rabbil-Ka'aba
Fuztu wa Rabbil-Ka'aba (Larabci:فُزْتُ وَرَبِّ الْكَعْبَة) jimla ce daga Imam Ali (A.S) ce, ma'ana "Na rantse da Ubangijin Ka'aba na rabauta,[1] Bayan sara da takobi da akai masa a daran 19 ga watan ramadan shekara ta 40 bayan hijira, ya ambaci wannan jimlar.
Kamar yadda Ibn Ƙutaiba Dinuri, masanin tarihi na Ƙarni na 3 bayan hijira ya ce, Ibn Muljam ya tafi wajen Ali (AS) lokacin da yake Sallah sai ya ce: Hukunci na Allah ne, ba kai ba, anan ne ya ɗaga takobi ya sari kan Imam Ali (A.S) da ita. sai Imam Ali (A.S) ya ce: "Fuztu wa Rabbil-Ka'aba", wato na rantse da ubangijin ka'aba na rabauta[2] Murtada Muɗahhari (kisa: 1358), ya ambaci wannan magana a matsayin shaida da za a iya tabbatar da cewa tabbas a addinin musulunci shahada ita ce nasara ga shahidi, ba zata taɓa zama taɓewa ko faɗuwa ba,[3] Don haka shahada abun farin ciki da murna ce[4] A cikin tafsirin Ayatullah Makarim Shirazi na Nahj al-Balagha, an kuma ambatar wannan magana a matsayin shaida kan lamarin cewa ruhin Imam Ali (A.S) bai ta'allaƙa da abin duniya ba, sai dai yana da alaƙa ne da duniyar sama da mala'iku da Ubangiji; Don haka Imam ya ɗauki bugu da saran da Ibn Muljam ya yi masa matsayin share fage na haɗuwa da Ubangijinsa.[5]
Malaman Shi'a irin su Sayyid Radi[6] Ibn Shahre Ashub[7] da malaman Ahlus-sunna irin su Ibn Asir[8] da Balazuri[9] sun ruwaito hakan, Sai dai wasu majiyoyi da dama daga baya sun naƙalto lafazin "Fuztu bi rabbil-kaaba" a maimakon wannan jimlar da dan canji kadan.[10]
Sai dai Ibn Abdul-Barri masanin tarihi na Ƙarni na 5 bayan hijira ya ce : kafin Imam Ali (A.S) ya faɗi wannan jimlar , Haram bin Malhan ne ya fara faɗi kamar haka "Fuztu wa rabbil- Ka'aba", a lokacin shahadarsa[11]
Bayanin kula
- ↑ Muhaddisi, Farhang Ghadir, 1392, shafi na 465.
- ↑ Ibn Qutaiba, Imamate wa Al-Siyasah, 1410 AH, Juzu'i na 1, shafi na 180.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asare, 1376, juzu'i na 17 shafi na 566-567.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asare, 1376, juzu'i na 24 shafi 471
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Amirul Mominin, 2006, juzu'i na 5, shafi na 717.
- ↑ Sayyid Razi, Khasa'is A'Imma, 1406H, shafi na 63.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 119.
- ↑ Ibn Athir, Usud Al-Ghabah, 1409H, juzu'i na 3, shafi na 618.
- ↑ Ibn Athir, Usud Al-Ghabah, 1409H, juzu'i na 3, shafi na 618.
- ↑ Misali, duba: Mazandarani, Sharh al-Kafi, 2002, juzu'i na 11, shafi na 225.
- ↑ Ibn Abd al-Barr, al-Estiyab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 337.
Nassoshi
- Balazri, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf, bincike: Sohail Zakkar da Riaz Zarkali, Beirut, Darul Fikr, bugu na farko, 1417H.
- Hafez, Shamsuddin Mohammad, Divan Hafez, Beta.
- Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiyab fi Marafah al-Sahhab, bincike: Ali Muhammad al-Bajawi, Beirut, Dar al-Jeel, bugun farko, 1412 Hijira.
- Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Usdul ghabata Fi Marafah Al-Sahaba, Beirut, Darul Fikr, 1409H.
- Ibn Qutaiba Dinuri, Abdullahi bin Muslim, Imamah wa Al-Siyasah, bincike: Ali Shiri, Beirut, Darul Awtah, bugun farko, 1410H.
- Ibnshahr Ashub Mazandarani, Menaqib Al Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare su), Kum, Allameh Publications, bugu na farko, 1379H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Pyam Imam Amirul Muminin (a.s.), wanda tarin fadla, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugun farko, 1386 suka shirya kuma suka shirya shi.
- Mazandarani, Muhammad Saleh bin Ahmad, Sharh al-Kafi, Mohagheg Abul Hasan Shearani, Tehran, Al-Maktaba al-Islamiya, 1382.
- Mohaddisi, Javad, Farhang Ghadir, Qom, sanannen bugu, 1392.
- Motahari, Morteza,Majmu'eh Asar Shahid Motahari, Tehran, Sadra, 1376.
- Sayyidi Razi, Muhammad bin Hussain, Khasa'is A'Imma, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su (Halayen Amirul Muminin, Amincin Allah ya tabbata a gare su), bugun: Mohammad Hadi Amini, Mashhad, Astan Quds Razavi, bugun farko, 1406 Hijira. .