Unguwar Bani Hashim

Daga wikishia
Wannan wani hoto ne da ake danganta shi da gidan Imam Sadik (A.S) a madinatul munawwara, cikin unguwar bani hashim

Unguwar ƙabilar Bani Hashim, (Larabci: محلة بني هاشم) guri ne da ƙabilar Banu Hashim suke rayuwa a cikin shi a garin Madinatul Munawwara, ita wannan unguwa ta na tsakanin Madina da maƙabartar Baƙi'a, kuma a wannan unguwar ne gida Imam Sajjad da gidan Imam Sadiƙ (A.S) yake, wannan uguwa ana ambatanta a wajan zaman makoki na `yan shi'a, saboda abin da ya faru a unguwar Bani Hashim, wanda hakan ne ya kai ga shahadar Faɗima Zahra (S). Kuma wana abu na wannan gida ya yi saura har shekara ta 1364 hajira Shamsi, sai dai kuma abin ban takaici da bakin ciki daga baya wahabiyawa sun ruguje wannan unguwa.

Gurin Da Wannan Unguwar Take

Ita wannan unguwa ta Banu Hashim tana kallon ƙofar Jabara'il da kuma kofar Nisa'u daga masallacin Annabi har zuwa maƙabartar Baƙi'a.[1] kuma wannan unguwar ne gidan Imam Sajjad (A.S) yake,[2] da kuma Imam Sadiƙ (A.S),[3] da Abu Ayub Al-Ansari, kuma Manzon Allah (S.A.W) ya yi rayuwa a wannan unguwa tsawon shekara bakwai bayan hijirarshi zuwa Madina.[4] kuma ya zo a cikin litatafan shi'a ƙarfafa yin sallah a gidan Imam Sajjad da Imam Sadiƙ.[5]

Canje-canje

Canji na farko da ya faru a unguwar Banu Hashim, ya kasance a shekara ta casa'in da ɗaya, a lokacin da aka ruguje gidajan Annabi(S.A.W) da umarni shugaba daga Banu Umayya Walid ɗan Abdul-malik, domin ya faɗaɗa masallacin Annabi, shi wannan aikin ya haɗu da tirjiya rashin yarda daga mutanan Madina, kuma dalilinsu na rashin yarda da wannan aiki shi ne san kiyaye abin da Annabi ya bari (S.A.W) a tsakaninsu domin waɗanda za su zo nan gaba, domin su san yadda Annabi ya yi rayuwa cikin tawali'u.[6]

Kuma a shekara ta 1364-1366 hijira Shmasiyya,Ali Sa'ud suka roshi uguwar Banu Hashim gabaki ɗaya, suka shigagar da filin wannan unguwa da maƙabartar Baƙi'a cikin tsarinsu na faɗaɗa masallacin Annabi.[7] kuma kafin roshe ita wannan unguwar ya shahara cewa akwai gidan imam Sajjad da imam Sadiƙ (A.S).[8]

Abin da Ya faru A Lokon Banu Hashim

Tushen Kasida: Abin da Ya Faru A Lokon Banu Hashim

A cikin wata ruwaya daga Imam Sadiƙ (A.S), bayan Muƙabala tsakanin Sayyida Faɗima (S) da Abubakar a kan gonar Fadak, Faɗima ta koma gurin Abubakar, sai ya rubuta mata wasiƙa a cikin ta ya nuna cewa a mayar mata da gonarta ta Fadak, bayan fitowar Faɗima daga gun Abubakar tana riƙe da wannan wasiƙa a hannunta, kawai sai ta yi kiciɓis da Umar ɗan Khaɗɗabi a cikin layi, sai Umar ya ce mata, wannan wata wasiƙa ce a hannunki? Sai ta ce wasƙa ce wanda Abubakar ya rubuta cewa a dawo min da gonata ta fadak, sai kawai ya ce mata bani ita, sai Faɗima taƙi ba shi, sai kawai ya hauta da duka kuma ya kwace wasiƙar da ƙarfi, ya yaga ta. To bayan haka ne, sai Faɗima ta yi rashin lafiya kuma zauna a gida, bayan haka bata rayu ba fiye da kwana saba'in da biyar ta yi shahada.[9]

A baya-bayannan ne, a Ranakun Faɗimiyya, aka gina wata unguwa ta kwaikwayo irin ta Banu Hashim da kuma gidan Faɗima Azzahara, domin mutane su ziyarta, a wasu garuruwa na Iran, kamar ƙum da Tehran.[10]

Bayanin kula

  1. Shuwagabanni biyu, Tarikh wa Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 229.
  2. Shuwagabanni biyu, Tarikh wa Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 406.
  3. Shuwagabanni biyu, Tarikh wa Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 406.
  4. Shuwagabanni biyu, Tarikh wa Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 407.
  5. Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 97, shafi na 225.
  6. Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 298.
  7. Shugabanni biyu, Tarikh wa Asare Islami Makka wa Madina, shafi na 229; Fayd Gilani, “Shandaniha Safar Hajj,” shafi na 158.
  8. Fayd Gilani, “Shandaniha Safar Hajj,” shafi na 158.
  9. Al-Mufid, Al-Ikhtisas, shafi na 185.
  10. نمایشگاه کوچه‌های بنی‌هاشم، خبرگزاری مهر؛ نمایش کوچه‌های بنی‌هاشم، خبرگزاری جمهوری اسلامی.

Nassoshi

  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, “Bihar Al-Anwar”, Beirut, Darul Ihya'i Turath Arabi, 1403 AH.
  • Al-Mufid, Muhammad bin Muhammad, 'Al-Ikhtisas, Qom, Sheikh Al-Mufid taron shekara-shekara na duniya, bugu na daya, 1413H.
  • Jafar, Rasul, 'Asare Islami Makka wa Madina, Tehran, Buga Mash'ar, bugu na 8, 1386H.
  • Fayd Ghailani, Muhammad Ali, Shandanihay Safre hajji, Mujallar Hajji Miqat, fitowa ta 48, Summer 1383 AH.
  • Ka'idan, Asghar, 'Tarikhi wa Asare Islami Makka wa Madina, Tehran, wanda Mash'ar ya buga, 1386H.