Kazim (Laƙabi)

Daga wikishia
Wannan kasida tana magana ne game da taken Imam Kazim (A.S). Domin sanin halayen Imam (a.s.) duba shigar Imam Musa Kazim (a.s).

Kazim (Larabci: الكاظم (لقب)) yana daga Mafi shaharar laƙubban Imam Musa Bn Jafar (A.S) [1] Dalilin kiran Imami Na Bakwai a wurin ƴan Shi’a da wannan laƙabi ya kasance ne sakamakon haɗiye fushi da danne shi. [2] kishiyar zaluncin Azzalumai sai ya yi haƙuri ya kuma haɗiye fushinsa, [3] cikin litattafan Akhlaƙ ya zo cewa duk Mutumin da yake da Konturol da iko kan fushinsa ana kiransa da Kazimul Gaizi (Mai haɗiye fushi). [4] A cikin littafin Tazkiratul Al-Khawas talifin Sibt Ibn Jauzi wanda ya mutu shekara ta 654 h ƙamari, ya zo cewa Imam Kazim (A.S) ana kiransa Kazim sakamakon duk sanda wani abu ya zo wurinsa ta sanadiyar wani to yana aika ma wannan mutumin da kuɗi [5] Sayyid Hashim Ma’aruf Hasani wanda ya mutu shekara 1984 m, shima cikin littafin Siratul Al-A’imma Al’isna Ashar tare da dogara da naƙalin littafin Tazkiratul Al-Khawas yana cewa ana kiran shi da Kazim ne saboda duk sanda ya fuskanci cutarwa daga wani mutum ko ya ga mummunan abu daga wannnan mutumi sai ya aika ma wannan Mutumin da kuɗaɗe da za su kawar masa da matsala da yake ciki. [6] Rahotannin daban-daban daga litatafai daban-daban sun zo kan cewa Imam Kazim (A.S) ya kasance Mutum Mai haɗiye fushinsa da danne shi gaban Makiyansa da kuma Mutanen da suke cutar da shi. [7] daga jumla ance wani Mutum daga jikokin Umar Bn Khaɗɗab a gaban Imam Kazim (A.S) ya yi rashin ladabi kan Imam Ali (A.S) sai Waɗanda suke tare da Imam Kazim (A.S) suka yi Yunƙurin Afkawa wannan Mutumin, sai dai cewa Imam Kazim (A.S) ya kwaɓe su ya hanasu afka masa, daga baya sai Imam Kazim (A.S) ya tashi ya bi bayan wannan Mutumin ya je har gonarsa, da ganin Imam Kazim (A.S) sai wannan Mutumi ya fara ihu yana ɗaga Murya yana cewa kada ka taka min shuka kada ka taka min shuka, sai Imam ya matsa kusa da shi ya tambaye shi nawa ka kashe cikin shukar taka? Sai Mutumin ya ce: Dinare ɗari! Sannan ya ƙara tambayarsa yanzu nawa kake sa ran zaka samu riba daga abin da zaka girba daga shukar ? sai Mutumin ya ce ni ban san gaibu ba. Imam ya ce: na ce kana yanzu kana fatan zaka samu nawa daga abin da ka shuka? Sai Mutumin ya ce: Dinare ɗari biyu! Sai Imam ya ɗauko Dinare ɗari uku ya bashi ya ce wannan naka ne sannan abin da zaka girba daga abin da ka shuka shima naka ne, sai Imam ya juya ya tafi Masallaci. Sai wannan Mutumin ya yi sauri ya kai kansa Masallaci ya tsaya jiran ƙara haɗuwa da Imam, ya ɗaga murya yana karanta wannan aya

«اللَّه أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِ‌سَالَتَهُ؛

Allah Mafi sanin inda zai ajiye Saƙonsa. [8]

Bayanin kula

  1. Erbali, Kashf al-Ghumma, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 743.
  2. Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 164.
  3. Tabarsi,elamul Alwari, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 32.
  4. Naraghi, Jame Al-Sadat, Al-Alami Press Institute, Juzu'i na 1, shafi na 333; Ghazali, Reɓiɓal of Ulum al-Din, Dar al-Marafa, juzu'i na 3, shafi na 176.
  5. Sabt bin Jozi, Tazkira Al-Khawas, 1418H, shafi na 312.
  6. Al-Hasani,Siratul A'Imama na 12, 1382 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 305.
  7. Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 233; ƙurashi, Hayat al-Imam Musa bin Jafar, 1429 AH, juzu'i na 2, shafi na 162-160.
  8. Baghdadi, Tarikh Bagdad, 1417 AH, juzu'i na 13, shafi na 30.

Nassoshi

  • Al-Hasani, Sayyid Hashem, Siratul A'imama Isna Ashar, Najaf, Al-Maktab Al-Haydariyya, 1382H.
  • Baghdadi, Khatib, Tarikh Bagdad, bincike: Mustafa Abdulƙadir Atta, Beirut, Dar al-Kutb al-Alamiya, 1417 AH.
  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-Ima, ƙom, Razi, 1421 AH.
  • Ghazali, Mohammad bin Mohammad, Ahya Ulum al-Din, Beirut, Dar al-Marafa, Bita.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar al-Sadr, 1385H.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Al-Ershad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
  • Sabat bin Jozi, Yusuf bin Ghazaughli, Tazkira al-khawas min umma fi zikr khaizat al-ayama, ƙom, Manshurat al-Sharif al-Razi, 1418 AH.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Alam Al-Wori Ba-Alam Al-Hadi, ƙum, Al-Bait Institute, 1417H.
  • ƙurashi, Baƙer Sharif, Hayat al-Imam Musa bin Jafar (a.s), Mehr Deldar, 1429H.Naraghi, Mohammad Mahdi, Al-Saadat Jame, Beirut, Al-Alami Institute of Press, B.T.