Jump to content

Nakisin

Daga wikishia

Nakisin (Larabci: الناكثين) ma'ana masu karya alƙawari, ishara zuwa ga mutanen da suka yi wa Imam Ali (A.S) ba'ia a farkon gwamnatinSa, amma kuma daga baya sai suka karya bai'ar da suka yi masa kuma suka afkar da yaƙin Jamal.[1] mafi shahara cikin waɗannan mutane shi ne Ɗalha da Zubairu[2] kamar yadda litattafai suka kawo bayanai, waɗannan mutane guda biyu sakamakon rashin cimma burukansu na neman ƙarfin iko[3] misalin tarayya cikin gwamnatin Imam Ali (A.S) sun yi wa Imam Ali (A.S), sai suka janye jikinsu daga gare shi[4] Suka koma wurin Ai'sha tare da fakewa da neman fansar jinin Usman, suka shirya rundunar mayaƙa da kuma afkar da yaƙin Jamal.[5]

A cewar Muhammadi Rai Shahri (Rasuwa: 2022m) manazarcin hadisi a Shi'a, halayen wannan mutane ya janyo ba'arin gama-garin mutane da suke neman gaske a wurin shahararrun mutane, su yi shakku da kokwanto; Imam Ali (A.S) faɗakar da waɗannan gama-garin mutane da shahararriyar maganarSa da yake cewa "Ba a sanin gaskiya da mutane, ka fari sanin gaskiya sai ka gano ma'abotan ta".[6]

Bisa wata riwaya da ta zo a litattafan Shi'a da Ahlus-Sunna, cikin yanayin hasashe Annabi (S.A.W) ya tsinkayar da Imam Ali (A.S) cewa zai yaƙi waɗannan ƙungiyoyi guda uku, maana Nakisin, Ƙasiɗin da Mariƙin.[7] Bisa naƙalin Waƙ'atu Siffin, Imam Ali (A.S) a lokacin yaƙin Siffin yayin arangama da sojojin Sham, ya yi ishara da wannan hasashe na Annabi, ya ce bisa umarnin Annabi ne na yaƙi Nakisin masu karya alƙawari.[8] A cikin Nahjul Balaga a huɗubobi ashirin misalin Shiƙshiƙiyya[9] da huɗuba ta 75[10] da wasiƙu guda uku da hikima guda ɗaya ya yi magana kan Nakisin.[11] A cikin baarin hadisai an yi ishara da tsinuwar Annabi (S.A.W) kan Nakisin.[12] a cikin Du'a'u Nudba nan ma Imam Ali (A.S) ya yi ishara kan Nakisin.[13]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Khatami, Kaweshi Dar Nahjul-Balagha," juzu'i. 1, shafi. 358.
  2. Khatami, Kaweshi Dar Nahjul-Balagha," juzu'i. 1, shafi. 358.
  3. Nahj al-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, Hikmat 202, shafi. 505.
  4. Ibn Qutaiba Dinuri, Al-Imamah Wa Al-Siyasya, 1410H, Mujalladi. 1, shafi. 71.
  5. Mofid, Al-Jamal, 1413, shafi. 229.
  6. Mohammadi Rayshahri, Daneshnameh Amir al-Momenin (A.S), 2007, juzu'i. 4, shafi na 499 da 500.
  7. Allamah Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 30, shafi. 588.
  8. Ibn Atham Kufi, Al-Futuh, 1411H, juzu'i. 3, ku. 77; Nasr ibn Muzahim, Waqqa’ah Siffin, 1382 AH, shafi. 338.
  9. Nahj al-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, Huduba ta 3, shafi. 49.
  10. Nahjul-Balagha, Tas'hihu Subhi Saleh, Huduba ta 75, shafi na. 103.
  11. Khazali, "Nakisin, Qasitin Wa Maiqin Dar Nahjul-Balagha," shafi. 398.
  12. Saduq, Al-Amali, Tehran, 1376H, shafi. 606; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 32, shafi. 127; Kufi, Tafsir al-Furat al-Kufi, 1410 AH, shafi. 141.
  13. Allamah Majlisi, Zad al-Ma'ad, 1423 AH, shafi. 305.

Nassoshi

  • Ibn Atham Kufi, Abu Muhammad Ahmad, Al-Futuh, Research, Shiri, Ali, Beirut, Dar Al-Adwaa, bugun farko, 1411H.
  • Ibn Qutaybah Dinwari, Abdullahi bin Muslim, Al-Imama Was Siyasa, Mai bincike: Ali Shiri, Beirut, Darul-Adwaa, bugun farko, 1410H.
  • Khatami, Sayyid Ahmad, Kaweshi Dar Nahjul-Balagha”, a cikin tarin kasidu da laccoci a taron Millennium International Congress na Nahjul-Balagha, Qum, Nahjul-Balagha Foundation, juzu'i na daya, 1991.
  • Khazali, Abu al-Qasim,Nakisin, Ƙasiɗin Wa Mariƙin Dar Nahjul Balaga, a cikin tarin kasidu da laccoci a Majalisar Millennium International Congress na Nahjul-Balagha, juzu'i na daya, 1991.
  • Sayyid Razi, Muhammad bin Hussein, Nahjul-Balagha, Subhi Saleh, Qum, Hijrat, bugun farko, 1991 ya gyara shi.
  • Sheikh Mufid, Muhammad ibn Muhammad, Al-Jamal Wa Al-Nusra na Sayyid Al-Atra a yakin Basra, mai bincike: Ali Mir Sharifi, Qum, Sheikh Mufid Congress, bugu na farko, 1413H.
  • Sadouq, Muhammad bn Ali, Al-Amali, Tehran, kantin sayar da littattafai, Bugu na shida, 1376 bayan hijira.
  • Allama Majlisi, Muhammad Baqir, Zadul al-Ma’ad- Miftah al-Jinan, Mai bincike: Ala’adin Al-A’lami, Beirut, Al-A’lami Publishing House, Bugu na Farko, 1423 Hijira.
  • Kufi, Furat bn Ibrahim, Tafsir Furat al-Kufi, Mai bincike: Muhammad Kazim, Tehran, Buga da Bugawa a ma'aikatar shiryar da Musulunci, bugu na farko, 1410H.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Mai bincike, kungiyar masu bincike, Beirut, Dar Ihya al-Turaht al-Arab, Bugu na biyu, 1403H.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad, Daneshname Amirul-Muminin (A.S) Bar Paye Qur'an, Hadis Wa Tarikh, Qum, Vol. 4, Darul Hadith, Bugu na Farko, 1386 Hijira.
  • Nasr bin Muzahim, Waki'atu Siffin, Al-Qahira, Al-Mu'assasatul Al-Arabiya Al-Hadithah, Bugu na Biyu, 1382H.