Huɗuba Ɗalutiya

Daga wikishia

Huɗuba Ɗalutiya (Larabci: الخطبة الطالوتية) tana cikin huɗubobi Imam Ali (A.S) da ya yi bayan wafatin Annabi (S.A.W), cikin wannan huɗuba ya zargi mutane da sanyi da gazawa cikin taimaka masa cikin batun mas'alar kwacen halifanci, tare a jan kunne game da sakamakon wannan aiki na su, cikin wannan huɗuba Imam ya yi ishara da cewa da ace ya samu mataimaka gwargwadon adadin sahabban Ɗalutu da tabbas zai ceto mutane daga karkacewar suka samun kansu ciki.

Imam Ali (A.S) cikin wannan huɗuba cikin bayanin ba'arin siffofin Allah da shelanta fifikon addinin muslunci kan sauran addinai, ya gabatar da kansa matsayin wasiyyin Annabi wanda ya umarci mutane su yi masa ɗa'a da biyayya. Imam Ali (A.S) cikin wannan huɗuba ya bayyana cewa kyakkyawan ƙarshe da samunb ni'imomin duniya da lahira ya dogara ne da biyayya ga Ahlul-baiti (A.S). kishiyarsa kuwa ba komai bane face shiga duhu da toshewar hanyar ilimi da kuma ɓullar saɓanin tsakankanin mutane.

Kulaini ya naƙalto wannan huɗuba cikin littafinsa Al-kafi daga Ibn Tihan, a ra'ayin Allama Majlisi duk da cewa huɗuba ɗalutiya ta fuskacin ma'aunin ilimin rijal ta kasance hadis da'if amma tare da haka sakamakon balaga da fasahar da take tattare da ita za a iya danganta ta ga Imam Ali (A.S).

Gabatarwa, Lokaci Da Fagen Da Aka Yi Wannan Huɗuba

An ce huɗuba ɗalutiya[1] tana cikin huɗubobi Imam Ali (A.S) da ya yi su bayan wafatin Annabi (S.A.W) a garin madina.[2] dalilin shaharar wannan huɗuba da ɗalutiya ya faru ne sakamakon ishara da Imam ya yi da mataimakan Ɗalutu cikin huɗubar.[3] Imam Ali (A.S) cikin wannan huɗuba ya zargi mutane kan janye masa da ƙin taimaka masa cikin mas'alar kwacen hakifancinsa da wasu suka yi, ya kuma ja kunnensu kan sakamakon da za su iya fuskanta kan ayyukansu.[4] Allama Taharani yana ɗaukar wannan huɗuba matsayin bayyanannen dalilin da ya sanya Imam (A.S) bayan wafatin Annabi (S.A.W) bai miƙe ba ya kwato haƙƙinsa (Wilaya da imamanci kan al'umma) kan asasin wasiyyar Annabi (S.A.W) da ya umarce shi ya yi shiru ka da kuma ya miƙe yana mai zare takobi idan ya rasa mataimaka domin ka da hakan ya cutar da muslunci.[5]

Sanadi

Kulaini, ya kawo wannan huɗuba cikin littafinsa sashen Raudatul Al-kafi ƙarƙashin naƙali daga Abul Haisam Ɗan Tihan daga Imam Ali (A.S).[6] a cewar Allama Majlisi a cikin littafin Mir'atul Al-uƙul, huɗuba ɗalutiya duk da cewa ta fuskacin ilimin rijal ta kasance hadis da'if, amma sakamakon balaga da fasahar wannan huɗuba zai wahala ace wannan huɗuba daga wani mutum take daban wanda ba ma'asumi ba, kuma za a iya danganta wannan huɗuba ga Imam Ali (A.S).[7]

Abin da Yake Cikin Huɗuba ɗalutiya

Imam Ali (A.S) cikin huɗuba ɗalutiya baya ga yabo da godiya ga Allah da bayanin ba'arin sunaye da siffofin Allah,[8] da iƙrari da saƙon Annabi (S.A.W)[9] ya gabatar da kansa matsayin wasiyyin Annabi (S.A.W)kuma masanin wannan al'umma, an kuma umarci mutane da biyayya da miƙa wuya ga jagorancinsa.[10] cikin gaɓoɓin wannan huɗuba ya yi jan kunne ga mutane game da sakamakon juya baya da mutane suka yi ga Ahlul-baiti (A.S).[11] tare kuma da bayanin irin kyakkyawan sakamako da za a samu cikin biyayya ga Imami.[12] sannan ya shiga bayani kan zargin mutane bisa raunana cikin taimaka masa a mas'alar kwacen halifancinsa.[13] daga ƙarshe ya yi ƙarfafa magana kan wannan nukta mai muhimmanci kan cewa da ace ya samu mutane da za su taimaka masa gwargwadon adadin mutanen da suka taimakawa Ɗalutu ko kuma gwargwadon adadin sahabban Annabi (S.A.W) a lokacin yaƙin badar, da tabbas ya dawo da mutane kan madaidaiciyar hanya ta ceto su daga karkacewar da suka samu cikin addini.[14] Darusussukan da suke cikin huɗuba ɗalutiya su ne kamar haka: 1.Siffanta Allah da siffar hayyu (Rayayye) 2.Kasancewar Allah bashi misali kuma bashi da kwatankwaci 3.Dawwamammen mulkin Allah kan duniyakafin halitta da bayan halakar dukkanin halittu 4.Allah bashi da lokaci bashi kuma da bigire (Wuri) 5.Mutum ba zai taɓa iya riskar Allah ba 6.kasancewar Allah mai gani da ai ji da iko kan komai 7.Ba da shaida kan saƙon Annabi (S.A.W) da nasarar muslunci kan bakiɗayan addinai da suka gabata 8.Yaudaruwar musulmai da biyewa son ransu, da kuma ƙin bin bayyananniyar hanya wilaya da imamancin Ahlul-baiti (A.S) 9.Biyayya ga Ahlul-baiti (A.S) sababi ne na samun ni'imomi duniya da lahira da kyakkyawan ƙarshe 10.doɗewar hanyar ilimi ga mutane da nutsewarsu cikin saɓani da nesantar hanya miƙaƙƙa sakamakon rashin biyayya da miƙa wuya ga Ahlul-baiti (A.S).[15]

Abubuwan Da Suka Biyon Bayan Huɗuba Ɗalutiya

Kan asasin riwayar Ibn Tihan, bayan gama huɗuba ɗalutiya da kuma fitowar Imam Ali (A.S) daga masallaci, mutum 360 suka yi masa bai'a cikin dare tare da ɗaukar ma kawikansu alƙawari za su kasance kan tabbatar da gaskiya da tsayuwa kyam har ƙarshen numfashinsu. Imam ya ce musu gobe da safe bakiɗayanku ku aske kawukansu ku yi salsali ku taru a wani wuri a geffan madina da ake kira da suna Ahjarul Zaiti, sai dai cewa babu wanda ya je wannan wuri face ƴan tsiraru daga Abu Zar, Miƙdad, Huzaifa Ɗan Yaman, Ammar Yasir da Salman, sune kaɗai suka je wurin da aka yi alƙawari za a tar, kamar yadda mai riwaya ya faɗa, Imam sakamakon ganin abin da ya faru daga juya bayan da mutane suka yi masa sai ya kai kuka wurin Allah ya ƙarfafa cewa zai yi haƙuri da abin da musulmi suka yi masa sakamakon umarnin da Annabi (S.A.W) ya yi masa.[16]

Bayanin kula

  1. Hosseini Tehrani, Imam Shanasi, 1426, juzu'i na 10, shafi na 151-152.
  2. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 31-33.
  3. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 11, shafi na 270.
  4. Hosseini Tehrani, Imam Shanasi, 1426H, juzu'i na 10, shafi na 151-152; Pakniya, “Abu Haitham Ibn Tihan Ansari,” shafi na 83.
  5. Hosseini Tehrani, Imam Shanasi, 1426, juzu'i na 10, shafi na 157.
  6. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 31-33.
  7. Majlisi, Mirat Al-Uqul, 1404 BC, juzu'i na 25, shafi na 70
  8. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 BC, juzu'i na 11, shafi na 271-274.
  9. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 11, shafi na 274.
  10. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 11, shafi na 279.
  11. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 BC, juzu'i na 11, shafi na 275-276.
  12. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 BC, juzu'i na 11, shafi na 274-278.
  13. Hosseini Tehrani, Imam Shanasi, 1426, juzu'i na 10, shafi na 151-152. ↑
  14. Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 BC, juzu'i na 11, shafi na 279-280.
  15. Majlisi, Mir'atul Al-ukul, 1404 BC, shafi na 70-76; Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 BC, juzu'i na 11, shafi na 274-278; Ibn Qariyaghdi, Albaza'atu Al-Muzjatu, 1429 AH, juzu'i na 1, shafi na 358-380.
  16. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 33.

Nassoshi

  • Hosseini Tehrani, Mohammad Hossein, Imam Shanasi, Mashhad, bugun Allameh Tabatabai, 1426H.
  • Ibn Qariaghdi, Muhammad Hussein, Al-Bada'a al-Mazjaat ( Sharhin Littafin Rouda daga al-Kafi), Tahqiq Hamid Ahmadi Jalfai, Qum, Darul-Hadith, bugun farko, 1429H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Mir'ah al-Aqool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, bincike da: Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, bugu na biyu, 1404H.
  • Mazandarani, Muhammad Saleh bin Ahmad, Sharh al-kafi, wanda Abul Hasan Shearani ya inganta, Tehran, Al-Maktabeh al-Islamiyya, bugun farko, 1382 Hijira.
  • پاک‌نیا، عبدالکریم، «ابوهیثم ابن تیهان انصاری: الگوی رشادت (بخش دوم)»، در نشریه فرهنگ کوثر، شماره ۴۸* ۱۳۷۹ش.