Karramallahu Wajhahu

Daga wikishia

Karramallahu Wajahahu (Larabci: كَرَّمَ اللهُ وَجْهَه)jumla ce ta girmamawa wadda ahlus-sunna suke amfani da ita kan Imamu Ali (A.S) bayan sun ambaci sunansa saboda su banbanceshi kan sauran sahabbai. har ila yau bayan ambatan sunansu suna cewa (Radiya Allah nnhum) wato Allah ya yarda da su, amma shi'a idan suka ambaci sunan Imam Ali suna cewa (Alaihis salam) madadin Karramallahu Wajhahu. Malaman Ahlussunna sun kafa hujja kan keɓantar Imamu Ali (A.S) da wannan jumla wadda take nuna cewa Allah ya ɗaukakashi ya kuma tsarkakeshi daga yin shirka, saboda shi Imam Ali (A.S) bai taɓa yin shirka ba, amma a ɓangare ɗaya Muftin Wahabiyawa Abdul-Aziz bin Baz ya ce keɓantar da wannan jumla ga Imamu Ali (A.S) bidi'ar `yan shi'a ce.

Hafiz Rajab Al-bursi yana ganin keɓantar wannan Jumla ta Karramallahu Wajahahu ga imamu Ali A S daga bakin ahlus-sunna hakan yana nuni kan fifikon da Imam Ali (A.S) kan sauran sahabbai guda uku, daɗi kan wasu masu bincike na shi'a suka yi nuni kan dalilin keɓantar wannan jumla ga Imam Ali (A.S), sun dogara da ayoyi guda biyu, ta farko faɗin Allah

"لَا یَنَالُ عَهْدِی الظَّالِمِینَ"

Ma'ana azzalumai basu rabauta ba da alƙawarina.

Aya ta biyu "فَمِنْهُمْ ظَالِمٌ لِنَفْسِهِ" ma'ana daga cikinsu akwai mai zalintar kan shi.

Sai masu bincike suka ce halifofi guda uku bisa wannan ayoyi guda biyu ba su cancanci matsayin imamanci ba, saboda bisa wannan ayoyi guda biyu duk mai aikata sabo to mai zalintar kansa ne, kuma shi mai zalintar kansa ba zai rabauta da alƙawarin Allah ba.

Ma'ana

tana nufin cewa Imamu Ali (A.S) Allah ya ɗaukakashi kuma ya tsarkakeshi [1] amma idan mukace wannan jumla addu'a ce,[2] to tana nufin girmamawa da kuma ɗaukakar al-amarin shi [3] wannan jumla ce wacce take nufin girmamawa da kuma tsarki wadda Ahlussunna suke ambata bayan faɗar suna Imam Ali (A.S) [4]. Ibn Hajar Haitami da Mumin Shibalanji waɗanda malamai ne na ahlus-sunna suna ganin wannan jumla ta Karramallahu Wajahahu tana nufin Allah ya tsarkake Imamu Ali (A.S) daga bautar wanin shi [5] kazalika ana samin wannan jumlar (Karramallahu Wajahahu fil Janna) a cikin litattafan ahlus-sunna.[6]

Bisa hadisin Rayatu wanda Ahmad ɗan Hanbal ya kawo wanda shi kuma yana daga cikin malamai huɗu na fiƙihu a cikin mazahabobin ahlus-sunna daga Annabi (S.A.W) a lokacin da ya bawa imam Ali (A.S) tuta a yaƙin khaibar, Annabi ya yi amfani da wannan jumlar kan Imamu Ali (A.S) «وَالَّذِي كَرَّمَ وَجْهَ مُحَمَّد».[٧] (wanda ya kare Fuskar Muhammad).[7]

Keɓantar Wannan Jumla Da Imamu Ali (A.S)

Imam Ali (A.S) ya keɓantu da wannan falala ta Karramallahu Wajahahu shi kaɗai a kan sauran sahabbai waɗanda ake rubuta musu Allah ya yarda da su, ana rubuta hakan a cikin ƙubba ta masallacin Muhammad Ali Basha a garin ƙahira.Ibni Kasir da Ibni Hajar Alhaitami suna cikin malaman Ahlussunna suna cewa wannan jumla ta Karrama Allahu Wajahahu malaman Ahlussunna dayawa sun keɓeta ga imamu Ali A S,kuma ba'a taɓa amfani da ita ba kan kalifofi guda uku,kazalika ba'a taɓa amfani da ita ba kan wani ba daga cikin sahabbai.[8]

Kazalika Ahmad ɗan Muhammad Akafaji da Muhammad ɗan Ahmad Assafarini waɗanda suke malamai ne a mazahabin Hanafiyya sukace wannan jumla ta Karrama Allahu Wajihahu ta yaɗu a tsakanin Ahlussunna.[9]

A cikin litattafan da aka rubuta a ƙarni na 15 hijira, an keɓance wannan jumla ga imamu Ali A S shi kaɗai.[10]

Dalilin Keɓance Wannan Jumla (Karramallahu wajahahu) Ga Imam Ali (A.S)

Malaman Ahlussunna sun kafa hujja kan keɓantar wannan jumla Karramallahu wajahahu ga imamu Ali da wasu abubuwa,ga wasu daga cikin: Imam Ali (A.S) bai taɓa yin sujjada ga gunki ba: Ibni Hajar Haitami da Mu'amin Shiblanji sun kafa hujja kan keɓantar wannan jumla ta Karramallahu Wajahahu ga Imam Ali (A.S) saboda shi bai taɓa sujjada ga gunki ba [11] Ibn Hajar ya shigar da Abubakar tare Imam Ali (A.S) cewa shi ma Abubakar bai taɓa yin sujjada ga gunki ba, amma abin da aka yi ittifaƙi a kai shi ne cewa Imam Ali (A.S) ne bai taɓayin sujjada ga gunki ba kwatakwata.[12]

yayin da Ibn Hajar Haitami yake maida martani kan duk masu cewa ai akwai wasu daga cikin sahabbai kamar Abdulahi ɗan Abbas da Abdullahi ɗan Umar, waɗanda suma kwatakwata ba su yiwa gunki sujjada ba, ya ce ai su waɗanda ba su yiwa gunki sujjada ba ai an haife su ne bayan kawar da shirka da kawo ƙarshenta, saboda haka akwai banbanci tsakanin waɗannan mutanan guda biyu, wanda ya bar matsalar bautar gunki a lokacin da Mushirikai suka tsananta cutarwa ga duk wanda yaƙi bautawa gumaka, saboda haka ba ta yadda za a kamanta wannan da yake a lokacin shirka da kuma wancan wanda ya zo daga bayan kawo ƙarshan shirka.[13]

Girmama Annabi kafin haihuwar shi: Jalalud Dini Addawani masanin aƙida da Falsafa a Musulinci ya ce, a lokacin da Fatima bintu Asad take ɗauke da cikin Imam Ali (A.S) duk lokacin ta ta ga Annabi Muhammad (S.A.W) sai kawai ta ga ta mike tsaye daga gurin da take zaune ba tare da son ran ta ba, jaririn da yake cikinta yake motsawa ta yadda mahaifiyarshi za ta fahimta cewa ta tashi domin girmamawa ga annabi (S.A.W). To bisa ra'ayin Addawani yana ganin mafi yawancin ahlus-sunna suna dangana wannan falala ga Imam Ali (A.S) ne saboda wannan hadisin.[14]

Rashin Amincewar Wahabiyawa Kan Keɓance Imam Ali (A.S) Da Wannan Falala

Bisa ra'ayin Mahadi Farmaniyan mai bincike kan mazhabobin musulinci ya ce Wahabiyawa ba su yarda da wannan falala ga Imam Ali (A.S) ba [15], bisa wani bincike da Ƙasim Uf shi mai bincike ne kan Wahabiyawa ya ce Ibn Taimiyya yaƙi yin amfani da jumlar Karramallahu Wajhahu ga Imamu Ali (A.S) a cikin dukkan litattafansa.[16]

Bisa ra'ayin Abdul-Aziz Ibn Baz Mufti na Wahabiyawa, yana ganin amfani da wannan jumla kan imamu Ali (A.S) makircin `yan shi'ane [17] kuma bidi'arsu ce[18] haka nan Muhammad Salihu Al-munajjid ɗaya daga cikin ɗaliban Ibni Baz ya yi imani cewa farkon waɗanda suka yi amfani da wannan jumla su ne `yan Shi'a, sai marubuta jahilai suka yi koyi da su.[19] kamar yadda suka saba babu wanda wanda ya bada wani dalili kan ra'ayin shi da abin da ya tafi akai.[20]

Kamar yadda masanin Adabin larabci Durra Assufi malami kuma ɗan Shi'a a ƙarni na 13 ya ce `yan Shi'a sun kasance suna faɗar wannan jumla "Aminci ya tabbata a gareshi" da kuma "tsiran Allah ya tabbata a gareshi" bayan sun faɗi sunan Imam Ali (A.S).[21] amam a gefe ɗaya Muhammad Asif Al-muhsini malami ɗan ƙasar Afganistan, yana ganin wannan jumla ta Karramallahu Wajhahu ahlus-sunna ne kaɗai suke faɗarta ga Imamu Ali (A.S).[22]

Dalilin fifikon Imam Ali (A.S)

Malam Hafiz Rajab Al-bursi malamin aƙida kuma malamin shi'a a ƙarni na 8 hijira yana ganin keɓance wannan jumla ta Karramallahu wajhahu ga Imamu Ali (A.S) da `yan Ahlussunna suke yi, dalili ne a bayyane kan fifikon Imam Ali (A.S) kan sauran sahabbai.[23]

Amam shi kuma Muhammad Assaƙafi Aɗɗahirani yana ganin keɓance wannan jumla ga Imamu Ali (A.S) tana nuni kan cewa Imam Ali (A.S) shi kaɗai ne bai bautawa gunki ba kwata-kwata, idan aka ƙiyasta shi da sauran kalifofi, kuma ta hakane ya kai ga wannan sakamako cewa Imamu Ali (A.S) yana da haƙƙi ya zama shugaba na wannan al'umma idan ka ƙiyasta shi da sauran kalifofi.[24]

Sayyid Muhammada Jawad Al-husaini Aljalali mai bincike kan shi'anci bayan ya yi nuni kan dalilin keɓance wannan jumla ta Karramallahu Wajhahu ga Imamu Ali (A.S), ya dogara da wannan ayoyin guda biyu, «لا يَنالُ عَهدِي الظَالِمينَ»؛[٢٥] و«فَمِنهُمْ ظَالِمٌ لِنَفسِهِ» Cewa kalifofi guda uku basu cancata su zamo kalifofi ba, saboda bisa abin da ya zo a wannan ayoyi duk wani mai zunubi da wanda ya zalinci kanshi da dukkan azzalimai alƙawarin (Imamanci) Allah ba zai kai gare su ba.[27]