Zainul-Abidin (Laƙabi)

Daga wikishia
Wannan labarin yana magana ne akan lakabin Zainul al-Abidin. Don neman bayani kan Imamin Shi'a na hudu, duba Imam Sajjad ( A.S).

Zainul-Abidin, (Larabci: زين العابدين) Wanda ake nufi da adon masu ibada, yana daga ciki fitattun laƙabin Imam Sajjad (A.S), Imamin Shi'a na huɗu. Ana yi wa Imam Sajjad (A.S) laƙabi da Zainul Abidin saboda yawan ibadarsa.[1] An karɓo daga Malik Ibn Anas masanin fiƙihu kuma muhaddisi cewa: Imam zainul Abidin yana sallah raka’a dubu dare da rana, kuma saboda yawan ibadarsa ana kiransa da sunan Zainul Abidin.[2] Haka nan kuma a cikin ruwayoyin hadisi an ambace shi da Sayyidul-Abidin.[3] An ce a tarihin Musulunci babu wanda aka taɓa kira da wannan sunan gabaninsa, Imam Ali bin Husaini (A.S) mai laƙabin Zainul Abidin.[4] Bisa wani hadisi da aka ruwaito a cikin littafin Ilalul Ash-Shara'ii daga ƙarni na biyu bayan hijira, aka fara kiran Imam Sajjad (A.S) da wannan suna.[5] Ibn Shahab Zohari masanin fiƙihu kuma muhaddasi na Ahlus-Sunna.A duk lokacin da ya ruwaito hadisi daga Ali Ibn Husaini (A.S), yana kiransa da laƙabin Zainul Al-Abidin, Sufyan bin Uyaina wanda ya rayu tsakanin shekaru 107-198H qamari, ya ce me ya sa kuke kiransa da Zainul Abidin? sai ya mayar masa da martanin, sai Zohri ya ambaci wata ruwaya daga Annabi (S.A.W) cewa a ranar Alƙiyama idan mai bushara zai yi kira da ƙarfi ina Zainul Abidin yake, sai na ga ɗana Ali bin Husaini (A.S) yana ɓullowa daga cikin sahu mutane.[6] A cikin littafin Kashful-Ghumma, ya zo cikin wata ruwaya mara sanadi,a kan ambatar laƙabin Imami na huɗu “Zainul Abidin” cewa, a wata rana ya shagaltu da tahajjud a mihrabin ibada, sai ya ji wata murya tana kiransa. sau uku: “Kai ne Zainul Abadin’’; kai ne adon masu bauta”, daga nan ya shahara da wannan laƙabi a tsakanin mutane.[7]

Bayanin kula

  1. Qurashi, Hayat al-Imam Zainul-Abdin, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 145 da 146.
  2. Dhahabi, Al-Abar, Dar al-Kitab al-Ulamiya, juzu'i na 1, shafi na 83.
  3. Misali, duba: Sadouq, Ilalul Al-Shara'i, 1385, juzu'i na 1, shafi na 132.
  4. Qurashi, Hayat al-Imam Zain al-Abdin, 1409, juzu'i na 1, shafi na 187
  5. Sadouq, Ilalul Al-Shara'i, 1385, juzu'i na 1, shafi na 229-230.
  6. Sadouq, Ilalul Al-Shara'i, 1385, juzu'i na 1, shafi na 229-230.
  7. Erbali, Kashf al-Ghamma, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 619.

Nassoshi

  • Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Al-Abar fi Khabar Man Ghabar, bincike na Abu Hajar Muhammad Saeed bin Basiuni Zaghloul, Beirut, Dar al-Kitab Al-Alamiya, Beta.
  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, Razi, 1421 AH.
  • Qurashi, Baqir Sharif, Hayat al-Imam Zain al-Abidin, Beirut, Darul-Azwa, 1409H.
  • Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ilalul Al-Shara'i, Kum, Kantin sayar da littattafai na Davari, 1966/1385.