Ahlil-Baiti
- Wannan wata ƙasida ce game da Ahlul-Baiti (AS). Domin sanin Imamai goma sha biyu da ma'asumai goma sha huɗu, duba Imaman shi'a da Imamai ma'asumai goma sha huɗu.
Ahlil-baiti da (arabic: أهل البيت عليهم السلام) larabci ko kuma a ce Ahlul-baiti na nufin Iyalan gidan Annabin Muslunci (S.A.W) a littafan Adabin `Yan Shi’a abin da ake nufi da Kalmar shi ne Ma’asumai Goma sha hudu, haka kuma an yi bayani wasu misdakan na Kalmar misalin Ashabul Kisa'i (Ma’abota Bargo) da kuma Matayen Annabi (S.A.W). An nakalto kebantattun Falaloli ga Ahlil-baiti (A.S) cikin masadir din `Yan Shi’a, hakika Ahlil-baiti sun kasance ma’abotan Isma sun fifici dukkanin Sahabban Annabi (S.A.W) bari ma dai sun fifici dukkanin halittun Ubangiji, Wilaya da Jagorancin al’ummar Musulmai ya kasance a wuyansu, dole dukkanin Musulmai su karbi koyarwar addini daga hannun su kuma su yi musu biyayya. Kan asasin masadir na Shi’a kaunar Ahlil-baiti wajibi ne da yake kan dukkanin Musulmai anyi bayanin hakan cikin riwayoyi matsayin asasi da tushen muslunci, Ayar Tadhir da Ayar Muwadda da kuma Hadisai daga Hadis Saƙlaini, Hadsi Safina da Hadis Aman suna daga jumlar ayoyi da hadisai da suka shahara cikin babin Falalolin Ahlil-baiti. Ahlus-sunna, duk da cewa suna da sabani da Shi’a cikin ayyana misdakan Ahlil-baiti amma tare da sun tafi kan cewa galibin ma’abota Bargo suna cikin misdakan Ahlil-baiti, kuma sun nakalto falaloli gare su, daga ciki akwai wajabcin soyayyarsu da kuma haramcin kiyayyar da su, daraja da fifiko Ma’abota Bargo, Marja’iyyar ilimi da Isma gare su. Hakika Musulmai sun yi wallafe wallafe masu tarin yawa game da Ahlil-baiti cikin yaruka daban daban daga Larabci da Farisanci da Urdu, daga cikin jumlar su akwai littafin (Mausu’atu Siratu Ahli-baiti Alaihim Salam) wanda Baƙir Sharif Karashi ya wallafa cikin mujalladi 40, da kuma Mausu’atu Ahli-baiti Alaihimus Salam, talifin Sayyid Ali Ashur mujalladi 20, Ahlil-baiti Alaihimus Salam Simatuhum Wa-Hukukuhum fi Alkur’anil Al-Karim, talifin Jafar Subhani. Haka kuma akwai Wakoki da rubuce-rubuce Masu tarin yawa dangane da Ahlil-baiti da aka samar haka akwai cibiyoyin ilimi da al’adu da suke dauke da wannan suna na su domin neman Tabarukki.
Matsayi da Muhimmanci
Ance dukkanin Al’ummar Musulmai tun daga farko Muslunci zuwa yau suna son Ahlil-baiti kuma sun yarda da Madaukakin matsayi da suke da shi a ilimi da aiki, in banda wasu tsirarun Nasibawa (Makiya Ahlil-baiti) sai dai cewa cikin Firkokin Musulmi hakika `Yan Shi’a sun shahara a matsayin Mabiya Ahlil-baiti [1] Mazhabar Shi’a sakamakon Imani da biyya gare su ana kiran su da sunan Mazhabar Ahlil-baiti [2] haka ta fuskanin fikhu ana kiran su da Fikhun Ahlil-baiti [3] Hujja da la’akari da Sunnar Annabi shi ne aikinsa maganar sa da Takrir dinsa (tabbatarwarsa), wani abu ne dukkanin Musulmai suka yi ittifaki cikinsa Shi’a da Ahlus-sunna, kuma suna daukar Sunnar Annabi (S.A.W) Matsayin daya daga Tushen Istinbadin Hukunce-hukuncen Shari’a, amma su Shi’a sabanin Ahlus-sunna kari kai bisa dogara da ayoyi da hadisan Annabi, suna ganin Sunnar A’imma da Hazrat Zahra (A.S) ita ma hujja ce kuma daya daga tushen Istinbadin Hukunce-hukuncen Shari’a [4] Yan Shi’a sun yi Imani kan cewa Musluncin da ake bayani cikin Mazhabar Ahlil-baiti shi ne Muslunci na hakika cikakke kuma Kammalalle [5] Cikin Masadir na `Yan Shi’a da Ahlus-sunna akwai tarin riwayoyi cikin babin Darajoji da Falaloli da Husisiya da Hakkokin Ahlil-Baiti (A.S) [6] Annabin Muslunci (S.A.W) a lokuta da dama ya yi wasiyya da Girmamasu da basu Kariya [7] An yi rubucce-rubucen Makaloli da Littafai masu tarin yawa daga bangaren `yan Shi’a da Ahlus-sunna cikin yaruka daban-daban Farisanci Larabci Urdu duka kan Ahlil-baiti (A.S) [8] Musulmai musammam `yan Shi’a sun kasance suna bayyana soyayyarsu da Kauna ga Ahlil-baiti ta hanyoyi daban-daban misalin raya ranakun zaman makoki [9] da ranakun farin ciki da murna [10] Wakoki [11] da zane-zanen nuna kwarewa duk suna yin su domin Ahlil-baiti [12] Daga cikin shahararrun Wakoki game da Ahlil-baiti akwai wakar Firdausi da yake rerawa (nima bawa ne ga iyalan gidan Annabi*Mai yabon Kasar kafar Wasiyyi) [13] haka ma Sa’adi ya rera ta sa wakar: (Sa’adi idan nuna soyayya kake*tofa soyayyar Muhammad da iyalan sa ta isar maka)[14] Shafi’i daga Malaman Fikhun Mazhabobi hudu na Ahlus-sunna ya rera:
Ya iyalan gidan Manzon Allahi hakika Soyayyarku Farilla ce daga Allah da ya saukar da ita cikin Kur’ani.[15] Hakika M usulmai Musammam ma `Yan Shi’a suna da wata alaka ta musammam cikin sanyawa yayan da suka haifa sunayen iyalan gidan Annabi (S.A.W) [16] kari kan haka suna sanyawa cibiyoyin su sunayen Ahlil-Baiti, Manyan Jami’o’in ilimi misalin Jami’atu Ahlil-baiti Tehran [17] ko kuma Jami’atu Ahlil-baiti ta Kasar Jodan [18] sannan mu’assasoshi misalin Majma’u Jahani Ahlil-baiti (A.S) [19] da tarin masallatai [20] duka an sanya musu sunayen Ahlil-baiti, Tutoci da Rundunonin Mazhaba su ma sun kasance suna amfani da sunayen Ahlil-baiti [21]
Sanin Mafhumi
A fadin Aliyu Rabbani Gulfaigani: abin da ake nufi da Ahlil-baiti a cikin Masadir na Shi’a Mudlakan babu wata karina ko kaidi shi ne wasu jama’a daga iyalan Annabi (S.A.W) da suke da wata kebantacciyar martaba da da daraja sannan maganarsu da ayyukansu ma’auni ne na gaskiya da sanin hakika [22] Ragib Isfahani yana cewa idan aka ce Ahlil-baiti cikin surar rashin kaidi ana nufin iyalan gidan Annabi (S.A.W) hakika sun shahara da wannan isdilahi [23] a ra’ayin Hassan Mustafawi Malamin Tafsiri kuma Mai bincike a fagen Ulumul Kur’an da Muhammad RaiShahri Malamin Hadisi: cikakkiyar Mana'a ta hakika da tattaro dukkanin abinda take da alaka da shi ga kalmar Ahli, shine danganewar zuwa ga dangi da ya kasance ta fuskanin karfafa da raunana yana da martabobi, mata da `ya`ya da jikoki da surukai duka ana kirga su a matsayin Ahli [24] haka kuma al’ummar duk wani Annabi ana kiran su da Ahlin sa, haka mazauna wani gida ko gari su ma duka ana lissafa su da Ahlin wannan gida ko wannan gari [25] Ahlil-baiti a Kamus na Lugga ya zo da ma’anar mazauna wani gida [26] sai dai cewa Hassan Musdafawi yatafi kan cewa Kalmar baiti na nufin iyali ba wai gida ba [27]
Misdakai
Dangane da cewa takamaimai wai su wanene Ahlil-baiti, Malaman Shi’a da Ahlus-sunna sun ambaci misdakai daban-daban
Ashabul Kisa'i ko Ma’abota Bargo
Fadlu Bn Hassan Ɗabarasi ya nakalto cewa Musulmai sun yi ijma’i kan cewa wanda ake nufi da Ahlil-baiti cikin Ayar Tadhir sune iyalan gidan Annabi (S.A.W) sannan kan asasin riwayoyi daga bangarori biyu [Tsokaci 1]) a mahangar `Yan Shi’a ayar ta kebanci Annabi da Ali (A.S) da Fatima (S) da Hassan (A.S) da Husaini (A.S) [28] Allama Tabataba’i a karshen ayar Tadhir ya ce Kalmar Ahlil-Baiti a Urfin Kur’ani wani kebantaccen suna ne da ya kebanci Mutane biyar, duk da cewa a gama garin Urfi ta kunshi dukkann Mutanen gidan sa [29] A ra’ayin Hassan Mustafawi Kalmar Ahlil-baiti ta tattaro har da Annabi (S.A.W), sabanin ra’ayin wasu Malaman tafsiri dasuke ganin wai ai ba jingina Kalmar Rasulillahi ba [30]
Ma’asumai Goma Sha Hudu
A ra’ayin Aliyu Rabbani Gulfaigani, a cikin littafan `yan Shi’a duk sanda aka samu Kalmar Ahlil-baiti ta zo ba tare da wata karina ba to tana aiki ne kan wasu kebantattun Mutane daga iyalan Annabi (S.A.W) abin nufi sune wanda suke da Isma kuma misdakin kan asasin ayoyi da hadisai su ne Ma’asumai goma sha hudu [31] a ba’arin wasu riwayoyi baki dayan Imaman Shi’a Misdaki ne na Ahlil-baiti [32] a jumla daga wata riwaya daga Annabi (S.A.W) da aka tambaye shi: su wanene iyalan gidanka? Sai ya ba da amsa: su ne Ali da `ya`yan sa biyu Hassan da Husaini da Imamai guda tara daga tsatson Husaini (A.S) [33] Ance bisa imanin `yan Shi’a Imamiya da kuma wasu Malaman Ahlus-sunna masu tarin yawa sun tafi kan cewa dukkanin Imaman Shi’a suna cikin Ahlil-baiti [34] muhammad RaiShahri ya tafi kan cewa tare da la’akari da siyaki da abin da ayar Tadhir ta kunsa da abubuwa da Annabi (S.A.W) ya gabatar cikin bayanin su waye Ahlil-baiti da kuma shaidu da karinoni babu wani kokwanto kan cewa abin da ake nufi daga Ahlil-baiti cikin wannan aya shi ne wasu jama’a daga iyalan Annabi (S.A.W) wadanda su ne za su ja ragamar shugabanci da shiyar da al’umma bayan Annabi (S.A.W) [35]
Matayen Annabi (S.A.W)
Wasu Malaman Tafsiri daga Ahlus-sunna suna ganin Matayen Annabi (S.A.W) su ne misdakan Ahlil-baiti cikin Ayar Tadhir [36] wasu ba’ari kuma sun ganin mutanen biyar tare da Matayen Annabi (S.A.W) su ne misdakin [37] an nakalto daga Zaidu Bn Ali cewa idan har wanda ake nufi da Ahlil-baiti cikin Ayar Tadhiri su ne Matayen Annabi (S.A.W) maimakon kawo lamirin maza zai zamana ne an kawo lamirin mata[38] haka sun ce akwai dalilai misalin amfani da lamirin maza da kuma wasu adadin riwayoyi tareda banbanci cikin lafazin ayoyi da yake dangantaka da matan Annabi tare da jumla da bayanin Ayar Tadhir duka na tabbatar da cewa wannan aya bata tattaro da Matayen Annabi (S.A.W) ba [39]
Iyalai na Nasaba wadanda Sadaka ta haramata a gare su
Kan asasin ba’arin wasu riwayoyi daga Ahlus-sunna, baki dayan iyalan Annabi (S.A.W) da suke dangane da shi ta jini wadanda cin Sadaka ya haramta gare su, misalin iyalan Aliyu,iyalan Jafar,iyalan Abbas, misdaki ne na Ahlil-baiti [40]
Muminai na gaskiya
Kan asasin ba’arin wasu riwayoyi, Ahlil-baiti suna cikin Musulmai wadanda ko da dangantakar su da Annabi (S.A.W) ko kuma ma babu ita sun kasance masu tabbatattun kafafu da gaskiya cikin biyayyar su ga Annabi (S.A.W) [41] haka kuma kan asasin wasu riwayoyi hakika Annabi (S.A.W) ya kirga Salmanul Farisi [42] da Abu Zar Gifari [43] daga cikin Ahlil-baiti. An nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk mutumin da ya kasance mutumin kirki mai tsoran yana daga cikinmu Ahlil-baiti [44]
Falalolin Ahlul-baiti
Cikin ayoyi da Hadisai Masu tarin yawa anyi bayanin alaloli daban-daban na Ahlil-baiti [45] a mahangar Muhammad RaiShahri a cikin ziyara [46]Ziyaratul Al-Jami’atul Al-Kabira a cikin babin Falaloli da Hususiyoyin Ahlil-baiti an kawo Mafi tattarar Magana da bayanai wasu ba’arin falalolin Ahlil-baiti sun kasance kamar haka:
Ahlul-Baiti cikin bayanin Imam Ali (a.s)
Su ne ginshikin ilimi da halakar jahilci. Bari hakurinsu ya baku labarin iliminsu, kamanninsu kuma ya ba da labarin tsaftar ciki, shirunsu ya ba da labarin hikimar maganarsu. Kada ku yi yãƙi da ãdalci kuma kada ku yi jãyayya a cikinsa. Su ne ginshikan addini da mafakar mutane. Ta hanyarsu ne gaskiya ta koma matsuguninta, aka kori karya aka ruguza. Ahlul Baiti sun san addini kuma sun koyi addini yadda ya dace kuma suka yi aiki da shi.
Nahj al-Balagha, wanda Dashti ya fassara, hadisi na 239, shafi na 475
Isma
- Asalin Makala: Ismar Imamai da Ismar Hazrat Zahra (S)
A cewar Jafar Subhani [47] Malaman Shi’a [48] su kafa dalili da aya ta 33 a suratu Ahzab ayar da akafi sani da Ayar Tadhir kan tsarkaka da Ismar Ahlil-baiti, kan asasin wannan Aya Allah ya yi Irada da ya tsarkake Ahlil-baiti daga dukkanin nau’in Zunubi da miyagun ayyuka, saboda haka wannan aya ta kebantu da bayani kan Ismar Ahlil-baiti [49] Hadis Saƙlaini [50] da ya kasance hadisi Mutawatiri [51] shi ma yana daga dalilai da aka dogara da su kan tabbatar da Ismar Ahlil-baiti, saboda wannan hadisi yana bayani karara kan rashin rabuwar Alkur’ani da Ahlil-baiti da juna, da wannan ne ya zama aikata duk wani sabo da kuskure zai zamana ya sabbaba rabuwar su da Kur’ani [52] haka kuma ance cikin wannan hadisi Manzon Allah (S.A.W) ya yi bayani karara cewa duk wanda ya yi riko da Kur’ani da Ahlil-baiti ba zai taba bacewa ba, saboda idan Ahlil-baiti ba su kasance Ma’asumai ba tofa riko da su da musu biyayya ba tare da kaidi ba da sharadi zai zama sababin bacewa [53] sannan hadis Safina shi ma daya daga cikin hadisai ne da ake kafa dalili da su kan tabbatar da Ismar Ahlil-baiti (A.S) [54]
Fifikon darajar Ahlil-baiti kan sauran Mutane
- Asalin Makala: fifikon Ahlul-Baiti
Shaik Saduk ya ce: `yan Shi’a sun yi Imani Annabi (S.A.W) da iyalan gidansa sune masu fifiko da mafi soyuwa mafi darajar halittun Allah, kuma Allah ya halicci Sama da Kasa Aljanna da Wuta duka Albarkacin su [55] a ra’ayin Allama Majlisi duk wanda ya zurfafa bincike cikin riwaya zai kai ga yakini kan fifikon Annabi (S.A.W) da A’imma (A.S) zai kuma sallama tare da mika wuya, Jahilin hadisai da riwayoyi ne kadai yake inkarin fifikon su [56] Ayar Mubahala ita ma tana cikin dalilai kan fifitar Ashabul Kisa'i (Ma’abota Bargo) kan sauran Sahabbai da sauran mutanen Gidan Annabi (S.A.W) [57] a cewar Malamai misalin Allama Hilli da Fadlu Bn Hassan Ɗabarasi, Malamai Tafsiri sun Ijma’i cewa wannan aya ta sauka kan iya Ma’abota Bargo [58] an nakalto daga Annabi (S.A.W) da ace akwai wasu mutane mafi daraja daga Ali da Fatima da Hassan da Husaini da tabbas Allah ya umarce ni da amfani da taimakon su cikin Mubahala [59] A ra’ayin Muhammad Husaini Muzaffar ayar Muwadda ita ma tana nuni kan fifitar Ahlil-baiti (Ma’abota Bargo) su zababbun Allah ne, saboda koma bayan wannan sura babu wata fuska kan wajabcin kebantuwa da soyayyarsu da kuma kasancewarta ladan sakon Annabi (S.A.W) [60] Akwai tarin riwayoyi da suke bayanin kan fifitar Ahlil-baiti daga cikinsu Hadis ƙ kan asasinsa Annabi (S.A.W) ya ajiye Ahlil-baiti jikin Kur’ani ya kira Kur’ani da Siklul Akbari (nauyayya mafi girma) Ahlil-baiti kuma da Siklul Asgar (karamin nauyaya) kamar da yanda Kur’ani ya kasance mai fifiko kan Musulmi haka su ma Ahlil-baiti suka da fifita kan sauran mutane [61]hadisul Amanu (aminci) shi ma ana kirga cikin hadisai da suka tabbatar da fifikon Ahlil-baiti, saboda amintar da Ahlin doran kasa yana nuni kan fifiko a kansu [62]
Marja’iyya ta Ilimi ga Ahlil-baiti
Annabin Muslunci(s.a.w)
إِنَّمَا مَثَلُ أَهْلِ بَیتِی فِیکُمْ کَمَثَلِ سَفِینَةِ نُوحٍ، مَنْ دَخَلَهَا نَجَی، وَ مَنْ تَخَلَّفَ عَنْهَا غَرِقَ؛ Lallai misalin Ahlin gidana a cikinku kamar Jirgin Nuhu ne. Duk wanda ya shiga cikin wannan jirgi ya tsira, duk wanda ya tsaya a baya ya nutse.
Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi na 349, 482 da 733; Sheikh Sadouk, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 27.
Hadis Sakalaini yana bayanin Marja’iyya ta ilmi ga Ahlil-baiti, saboda kiran Annabi (S.A.W) kan riko da Kur’ani da Ahlil-baiti, bayani ne karara kan cewa Marja’iyyar Ilmi ta iyakantu ga Ahlil-baiti (A.S) wajibi ne dukkanin Musulmai cikin waki’o’i da lamurran addini su koma zuwa ga Ahlil-baiti[63] ance bayan Annabi (S.A.W) hakika sani da ilmi da tabbatattun abubuwa na Kur’ani da sunnar Annabi (S.A.W) babu wanda ya sansu da zurfafa sai Ahlil-Baiti, da wannan ne bayan Annabi (S.A.W) suka kasance Makomar ilmi ta al’ummar Musulmai cikin sanin Hukunce-hukuncen addini da kuma fahimtar sakonninsa dole a koma gare su [64]
Wilaya da Shugabanci
Wilaya da Shugabancin siyasa na Ahlil-baiti (A.S) daya daga Falalolin su, kiran Annabi (S.A.W) da riko da littafin Allah da kuma su cikin hadis Saƙlaini bayani ne karara kan iyakantuwa da togacuwar shugabancin siyasa ga Ahlil-baiti [65] wasu ba’ari daga nakalin hadis Saƙlaini ya zo da lafazin Kalifataini [66] (Halifofi biyu) Maimakon Saƙlaini Ma’ana Kur’ani da Ahlil-baiti su ne Halifofi magadan Annabi cikin al’ummarsa cikin dukkanin bangarorin shugabancin siyasa [67] a ra’ayin Jafar Subhani, Annabi (S.A.W) Waki’ar Ghadir ya ayyana Ali da iyalansa ga jagorancin siyasa [68] wasu ba’ari tare da la’akari da Hususiyar Isma suna ganin imamanci da jagorancin siyasa bayan Annabi (S.A.W) ya kebantu da Ahlil-baiti (A.S) haka kuma ba tare da kaidi da sharadi ba wajabcin biyayya ga Ahlil-baiti suna ganinsa daya daga cikin dalilan jagorancin siyasar su,[69] ya tattaro dukkanin abin da ya shafi rayuwar musulmi daga batutuwan ibada da tattalin arziki da siyasa da ala’ada, da wannan ne cikin mas’alolin siyasa da ya alakantu da al’umma da hukuma wajibi a musu da’a da biyayya [70]
Wilaya Takwiniyya
- Asalin Makala: Wilaya Takwiniyya
A cewar Muhammad Jamil Mahmud daya daga cikin Marubuta kuma Malamin Shi’a a kasar Lubnan yana daga cikin mutanen da samun irinsu ya karanta, Malaman Imamiyya sun yi Ittifaki cewa A’imma (A.S) suna da Wilaya Takwiniyya [71] abin da ake nufi da Wilaya Takwiniyya shi ne mutum karkashin iznin Ubangiji ya yi tasarrufi cikin duniyar halitta, alal misali ya warkar da Mara lafiya da yake fama da ciwon da ba shi da magani, ko kuma ya raya Matacce da iznin Allah [72] riwayoyin da suka zo kan Wilaya Takwiniyyar Ahlil-baiti riwayoyi ne Mutawatirai[73] kuma galibinsu idan an la’akari da isnadi ingantattun riwayoyi ne [74]
Wilaya Tashri’iyya
- Asalin Makala: Wilaya Tashri’iyya
Hakika Wilaya Tashri’iyya ta kunshi ma’anoni guda biyu
- Tana daukar ma’anar wilaya (mafi cancantuwar cikin tasarrufi) kan dukiya da rayukan Mutane [75] ance Annabi (S.A.W) da A’imma (A.S) cikin wannan Wilaya Tashri’iyya da wannan ma’ana babu wani sabani tsakanin Malamai [76] Ayatullahi Safi Gulfaigani yana kirga wannan nau’i na Wilaya Tashri’in A’imma (A.S) daga laruran Addini [77]
- Tana daukar ma’anar wilaya kan hukunce-hukunce da hakkin shar’antawa [78]
Wasu adadi daga Malaman Shi’a suna ganin wilayar Annabi (S.A.W) kan shar’anta ba’arin wasu Hukunce-hukunce wani abu ne da babu jayayya cikinsa [79] amma cikin wilayar Imamai (A.S) cikin shar’antawa akwai sabanin ra’ayi tsakanin Malaman Shi’a, wasu ba’arin Malamai kan asasin hadisai masu tarin yawa koma ace sun kai Haddin Mustafiz [80] suna ganin Imamai (A.S) suna da hakkin shar’antawa [81] sabanin wasu jama’a da suka tafi kan cewa babu wanda yake da hakkin shar’antawa sai Allah shi kadai sun kasance suna Inkarin wilayar Tashri'iyya ga Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S)[82] Sayyid Ali Milani ya ce tabbatar da wilayar Tashri'iyya ga A’imma (A.S) sakamakon tarin dalilai wani abu ne tabbatacce kuma yankakke da babu shakku cikinsa [83]
Hakkokin Ahlil-baiti
Kan asasin ayoyi da riwayoyi, Ahlil-baiti suna hakki kan musulmi kuma kan asason wannan hakkoki akwai wasu wazifofi da ya zamana dole su sauke su, ba’arin wannan hakkokin sun kasance kamar haka:
Wajabcin Da’a ga Ahlil-baiti
- Asalin Makala: Muftaradul ɗa’a
Kan asasin ayar Ulul Amri (ku yi da’a ga Allah da Manzonsa da Ma’abota al’amari) an ajiye da’ar Ulul Amri kusa da da’ar Allah da Manzonsa, sannan da’a ga Ulul Amri ba tare da sharadi da kaidi ba wani abu ne da ya zama wajibi [84] a cewar Fadlu Bn Hassan Ɗabarasi a ra’ayin Malaman Imamiya wanda ake nufi da Ulul Amri su ne A’imma Amincin Allah ya tabbata a Gare su [85] An jingina da Hadis Saƙlaini domin tabbatar wajabcin da’a ga Ahlil-baiti; saboda cikin wannan hadisi an ajiye su kusa da Kur’ani: kamar yanda da’a ga Kur’ani ta zama wajibi kan Musulmai haka zalika da’a ga Ahlil-baiti take wajibi a kansu [86] a cewar Abu Salah Halabi Masanin Fikhu da Kalam a karni na hudu, sakamakon kasancewar zancen Annabi (S.A.W) sake yake babu kaidi da sharadi cikin hadis Saklaini to wajabcin biyayya ga Ahlil-baiti kan Musulmai zai kasance saki babu kaidi da sharadi cikin baki dayan ayyukansu da zantukansu wajibi a yi musu da’a [87] Hadis Safina shi ma yana nuni kan wajabcin da’a ga Ahlil-baiti (A.S) saboda kan asasin wannan Hadisi tsira da kubuta daga halaka yana cikin yi musu da’a [88] cikin wannan Hadisi Annabi (S.A.W) ya kamanta iyalan gidansa da Jirgin Annabi Nuhu (A.S) game da fuskar kamaceceniya da juna ance duk wanda cikin Addininsa ya koma zuwa ga Ahlil-baiti zai samu shiriya da kasancewa Mai gaskiya kuma duk wanda yaki yi musu da’a zai bata [89] a cewar Mir Hamid Husaini kan asasin wannan hadisi wajabcin da’a ga Ahlil-baiti (A.S) zai kasance sake ba tare da sharadi da kaidi ba [90]
Kauna da Soyayya ga Ahlil-baiti
- Asalin Makala: Muwaddat Ahlil-baiti
A Akidar Shi’a Imamiya, kan asasin Ayar Muwadda Kauna da Soyayya ga Ahlil-baiti (A.S) wajibi ne kan dukkanin Musulmi [91] kuma wani abu ne da akayi ittifaki kansa in banda Nasibawa (Makiya Ahlil-baiti) ana kirga shi daga laruran Addini [92] Ayar Muwadda da take bayani kan cewa bana neman ladan kawo sako daga gareku face nuna soyayyarku ga iyalina [93] tana daga cikin dalilai kan wajabcin soyayya gare su [94] a cewar Nasir Mukarim Shirazi daya daga Malaman Tafsiri na Shi’a kuma Maraji’an Taklidi, baki dayan Malaman Tafsirin Shi’a sun fassara wannan aya kan Ahlil-baiti kuma soyayyarsu wani tsani ne na karbar Imamanci da shugabanci A’imma (A.S) [95] a cewar wasu Malamai misalin Muhammad Rida Muzaffar ta hanyar Hadisi Mutawatiri an nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa soyayyar Ahlil-baiti (A.S) alama ce ta Imani kuma kiyayyar su alama ce ta Munafunci, Masoyansu Masoyan Allah da Manzon Allah (S.A.W) ne haka Makiyan su Makiya Allah da Manzonsa ne [96] kan asasin ba’arin wasu riwayoyi soyayyar Ahlil-baiti ita ce tushe da asasin muslunci [97] A ra’ayin Muhammad Rida Muzaffar, babu shakka da kokwanto kan wajabcin Kauna da Soyayya ga Ahlil-baiti (A.S) sakaamakon kusancin su da Allah da matsayi da darajar su a wurin Allah da kuma tsarkakar su daga dukkanin Shirka da Sabo dama dukkanin abin da zai hairfar musu da nesanta da Ubangiji [98] Muhammad Muhammadi Rayyu Shahri, zaman makoki domin Ahlil-baiti (A.S) yana daga cikin hanyoyi nuna soyayya a gare su kuma yana daga cikin mafi muhimmancin misdakan girmama alamomin Allah haka kuma ziyartar Kaburburan su [99] da farin ciki a ranakun farin cikin su [100] ambaton darajojin su [101] sanyawa `ya`yanmu sunayen su duka hanyoyi ne na nuna soyayya gare su [102] Girmama Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a gare su, ambaton falalolin su da musibunsu, ba da Khumusi da sadar da zumunci su ma suna daga cikin hakkokin Ahlil-baiti (A.S) [103]
Ahlil-bait a Mahangar Ahlus-sunna
Ahlus-sunna sun yi tarayya da `yan Shi’a kan kasancewar Ahlil-baiti cikin Ma’abota Bargo, hadisai masu tarin yawa daga masadir na Ahlus-sunna sun nakalto cewa Annabi (S.A.W) a lokuta da daman gaske ya kirayi Ali da Fatima da Hassan da Husaini (A.S) da Ahlil-Baiti [104] haka kuma cikin Masadir na Ahlus-sunna ya zo cewa Manzon Allah (S.A.W) game da Ali da Fatima da Hassan da Husaini (A.S) yana cewa (duk wanda yake son su to yana so na kuma duk wanda baya son su to baya so na) [105] a wata riwayar, sannan kuma a wata riwayar daga Annabi (S.A.W) an nakalto cewa ranar Alkiyama Masoya Ahlil-baiti za su kasance tare da Annabi (S.A.W) cikin darajarsa [106] Fakru Razi daya daga cikin Malaman tafsiri na Ahlus-sunna tare da wannan dalili na cewa Annabi (S.A.W) yana son Ali da Fatima da Hassan da Husaini (A.S) kuma da’a garesu wajibi kan dukkanin Musulmi da wannan ne yake ganin soyayya Ahlil-baiti wajibi ce [107] Ibn Hajar Haitami daya daga cikin Malaman Shafi’iyya a karni na goma shi ma ya ce bisa dogara da hadisai wajibi ne a so Ahlil-baiti kuma haramin kin s, a cewar sa akwai Manyan Malamai misalin Baihaki da Bagawi da suka kasance suna kirga soyayya Ahlil-baiti cikin farillai [108] Shafi'i daya daga cikin Malaman fikhu na Mazhabobi guda hudu na Ahlus-sunna ya rera baitukan yabo ga kan wajabcin son Ahlil-baiti [109]
Ya Ahlin gidan Manzon Allah hakika son ku* Farilla ce da Allah ya saukar cikin Kur’ani. Ya kara rerawa cikin wasu baitukan: [110]
Idan har Soyayyar iyalan Muhammad shi ne Rafidanci…. To Mutane da Aljanu su Shaida ni Rafidi ne Zamakshari Malamin Tafsiri na Ahlus-sunna marubucin tafsirin Al-Kashshafu ya tafi kan cewa ayar mubahala tana daga cikin mafi karfin dalili kan falala da fifitar Ma’abota Bargo [111] a ra’ayin Jafar Subhani, da yawa daga Malaman Ahlus-sunna sun ikirari da fifita ta ilimi da sanin addini ga Ahlil-baiti [112] misali Abu Hanifa wanda ya samar da Mazhabar Hanafiya kuma daya daga Malaman fikhu na Mazhabobi hudu, an nakalto cewa yana fadin (ni banga mafi sanin fikhu daga Jafar Bn Muhammad Sadiƙ (A.S) [113] wannan jumla an nakalto ta daga wurin Muhammad Bn Muslim Bn Shahab Zuhri daya daga cikin Tabi’ai kuma masanin fikhu da hadisi daga bangaren Ahlus-sunna a karni na biyu, haka game da Imam Sajjad (A.S) an nakalto cewa Shafi’i wanda ya kafa Mazhabar Shafi’iyya ya tafi kan cewa Imam Sajjad (A.S) [114] shi ne mafi sanin fikhu a birnin Madina [115] Ibn Hajar Haitami ya ce: da wannan dalili ne Annabi (S.A.W) ya kirayi Kur’ani da Ahlil-baiti da sunan Siklu, ana kiran abu da Siklu idan ya kasance mai daraja da kima da muhimmanci, Kur’ani da Ahlil-baiti sun kasance haka, saboda dukkanin biyun su ma’adanai ne na ilimi da sirrika da hikimomi madaukaka da hukunce-hukuncen shari’a, da wannan dalili ne kan riko da su da neman sani aka shaukantar da Al’umma [116] a Imani Ibn Hajar hadisan da suke nuni kan da’a ga Ahlil-baiti za su cigaba kan haka har zuwa tashin Alkiyama suna karfafar hakan, haka batun yake kan riko da Kur’ani [117] A mahangar Ali Rabbani Gulfaigani, kari kan imanin wasu ba’ari daga Malaman Ahlus-sunna babu ragowar kokwanto cikin Ismar Aklak da aiki ga Ahlil-baiti, abin da ake da sabani akai shi ne Ismar su ta ilimi [118]
Sanin Littafi
- Asalin Ma ƙala: Fihirisar Litattafai da aka rubuta dangane da Ahlil-baiti (A.S)
Hakika an rubuta litattafai daban-daban dangane da Ahlil-baiti ba’arin wasunsu sun kasance kamar haka:
- Manakib Ahli-baiti, wallafar Abu Hassan Ali Bn Muhammad Julabi wanda aka fi sani da Ibn Magazili daga cikin Malaman hadisi na Ahlus-sunna cikinsa ya yi bayani game da Fada'el Imam Ali (A.S) da Fada'el Fatima da Hassan da Husaini (A.S)
- Ahlu-baiti, talifin Sayyid Muhammad Aminu Majma’u Jahani Ahlil-baiti ƙom ta buga.
- Mausu’atu Siratu Ahli-baiti Alaihimu Salam, talifin Baƙir Sharif Karashi, wannan mausu’a ta kunshi mujalladi 40 kan tarihin rayuwar Aklak da zamantakewa da ibada da tarihin rayuwar Annabi da Ahlil-baiti.[119]
- Mausu’atu Ahlil-baiti Alahimu Salam, talifin Sayyid Ali Ashur, bugawa Darul Nazir Abud shekara 1427 mujalladi 20 da ya kunshi tarihin rayuwar Ma’asumai goma sha hudu.
- Ahlil-baiti Alaihimu Salam Simatuhum wa-Hukukuhum fi Kur’anil Karim, rubutawa Jafar Subhani, daukar nauyin bugawa Mua’assasatu Imam Sadiƙ (A.S) shekara 1420 h.
- Ahlil-baiti fil-Al-Kitab was-As-Sunna, talifin Muhammad Muhammadi RaiShahri tare da Sayyid Rasul Musawi, an wallafa asalin littafin cikin harshen larabci sannan aka tarjama zuwa harshen Farisanci da taken (Ahli Baiti dar Kur’an wa-Hadis, asalin tarjama daga mu’assasatu Darul Hadis aka fara yada shi.
- Hukuk Ahli-baiti dar Kur’an wa-Riwayat, talifin Ibrahim Shafi’i Sorastani cibiyar Mau’ud ta buga shi a shekara 1400 sh, wannan littafin ya yi bincike kan hakkoki 20 na Ahlil-baiti.
- Hukuk Ahli-baiti dar Tafsir Ahlu-sunnat, talifin Muhammad Yakub Bashawi, ƙom, Markaz Bainal-Milali Tarjume wa Nashar Almustafa (S.A.W) bugun Farko shekara 1390
- Ahli-baiti Alaihimu Salam dar Tafsir Ahlus-sunnat, talifin Ahmad Abidi da Husaini Kakfur, ƙom, Nasharu Za’ir shekara 1392 sh.
Bayanin kula
- ↑ "Bayani a wajen taron bakin da suke halartar taron Ahlul-Baiti (A.S) karo na hudu", shafin yanar gizon ofishin kula da Ayyukan Ayatullah Khamenei; "Sanarwa a wajen taron mahalarta taron "Masoyan Ahlul Baiti (AS) da kuma batun takfiriyya", shafin yanar gizon ofishin kula da ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ Sobhani, Manshur Akayed Imamiyya, 1376, shafi na 8, 9, da 263; Hashemi Shahroudi, "Maktabat Fikhi Ahlul-Baiti (AS)", cikakkiyar mashigar 'yan Adam.
- ↑ Duba Hashemi Shahroudi, "Maktabat Fikhi Ahlul-Baiti (AS)", porotal Jami ulum insani.
- ↑ Center for Islamic Information and Resources, Usul Fi ƙh Dictionary, 2009, pp. 400-398.
- ↑ Sobhani Manshur Akayid Imamiya 1376 sh shafi na 8 «بیانات در دیدار میهمانان شرکت کننده در چهارمین مجمع جهانی اهل بیت(ع)»، وبگاه دفتر حفظ و
- ↑ Misali, duba Mohammadi Rishahri, Ahlul Baiti, Alaihimu salam dar Kur’an wa-Hadis, 1391, shafi na 1020-181.
- ↑ Misali, duba Mohammadi Rishahri, Ahlul Baiti, Alaihimu salam dar Kur’an wa-Hadis, 1391, shafi na 761-765
- ↑ نگاه کنید به: «کتابشناسی اهلبیت(ع)»، پایگاه اطلاعرسانی حدیث شیعه.
- ↑ Mazaheri, “Azadari”, shafi na 345
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به «کشورهای عربی میلاد پیامبر(ص) را چگونه جشن میگیرند؟»، خبرگزاری ایکنا؛ «برگزاری جشن میلاد امام رضا (ع) در کشورهای مختلف جهان»، خبرگزاری مهر؛ «جشن میلاد حضرت ولی عصر (عج) در کشورهای مختلف جهان برگزار شد»، خبرگزاری تقریب.
- ↑ «در رثای اهل بیت علیهم السلام»،
- ↑ «السلام علیکم یا اهل بیت النبوة»،
- ↑ «شاهنامه، آغاز کتاب بخش ۷، اندر ستایش پیامبر»،
- ↑ «قصیده شماره ۱۶، در ستایش حضرت رسول(ص)»،
- ↑ Shafi'i, Diwan al-Imam al-Shafi'i, Alkahira, shafi na 121.
- ↑ «اسمهایی که مردم ایران از صدسال پیش تا به حال دوست دارند»،
- ↑ «دانشگاه بینالمللی اهلبیت(ع)»،
- ↑ «آشنایی با مراکز اسلامی اردن؛ مؤسسه اندیشه اسلامی آل البیت اردن»، خبرگزاری تقریب؛ «نگاهی به فعالیتهای جهانی مؤسسه فرهنگی آلالبیت»، پایگاه اطلاعرسانی حوزهآشنایی با مراکز علمی اردن: دانشگاه آلالبیت»،
- ↑ «مجمع جهانی اهلالبیت(ع)»
- ↑ نگاه کنید به: «ماجرای ساخت مسجد اهلبیت در ورودی شهر قم»، خبرگزاری رسا؛ «مناجات شعبانیه در مسجد اهلبیت(ع) سمنان طنینانداز میشود»، خبرگزاری شبستان.
- ↑ «پرچم مخمل السلام علیکم یا اهل بیت النبوة»،
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 555.
- ↑ Rajeb Esfahani, Mufrdat Alfaz Al ƙur’an, 1412 Hijira, shafi na 96.
- ↑ Mustafawi, Taha ƙi ƙ fi kalamat al- ƙur'an al-Karim, 1368, juzu'i na 1, shafi na 169 da 170; Mohammadi Rayshahri, Ahlul Baiti (Alaihimu Salam) fi Alkur’an wal-Hadis, 1391, shafi na 11.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 553.
- ↑ Duba Farahidi, Kitab al-Ain, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 89; Ibn Faris, Al-Ma ƙayis al-Lugha, 1404 AH, Juzu'i na 1, shafi na 150; Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 11, shafi na 28.
- ↑ Mustafawi, Taha ƙi ƙ fi kalemat al- ƙur'an al-Karim, 1368, juzu'i na 1, shafi na 170.
- ↑ Tabarsi, A'lam al-Wara ba'alam al-Huda, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 293; Tabarsi,
- ↑ Tabatabaei, al-Mizan fi Tafsiril ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 16, shafi na 312.
- ↑ Mostafa ɓi, Taha ƙi ƙ fi Kalemat al- ƙur'an al-Karim, 1368, juzu'i na 1, shafi na 169 da 170.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 555.
- ↑ Duba Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 423; Khazaz Razi, Kefaya al-Athar, 1401 AH, shafi na 156 da 171; Sheikh Sadou ƙ, Uyun Akhbar al-Reza (AS), Mujalladi na 1, shafi na 229.
- ↑ Khazaz Razi, Kefaya al-Athar, 1401 AH, shafi na 171
- ↑ Zainli, Mafhum shinasi wa-Misdakyabi Ahlul Baiti (AS), 2007, shafi na 24.
- ↑ Mohammadi Rayshahri, Ahlul Baiti (Alaihimu Salam) dar Alkur’an wa-Hadis, 1391, shafi na 13.
- ↑ Misali, duba Tabarani, al-Tafsir al-Kabir, 2008, juzu’i na 5, shafi na 193; Thaalbi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422 AH, Juzu'i na 8, shafi na 35 da 36.
- ↑ Duba Bashoy, Hukuk Ahlul Baiti dar Tafasir Ahlul-Sunnat, 1390, shafi na 35.
- ↑ ƙomi, Tafsirin ƙami, 1363, juzu'i na 2, shafi na 193.
- ↑ Duba Bashoy, Hukuk Ahlul Baiti dar Tafasir Ahlul-Sunnat, 1390, shafi na 35 da 36.
- ↑ Nishaburi, Sahih Muslim, Daru Ihya'u Turas Arabi, Juzu'i na 4, shafi na 1873-1874.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 554.
- ↑ Safar, Basa'ir al-Derajat, 1404 AH, shafi na 17 da 25; Sheikh Sadou ƙ, Uyoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 64.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Amali, 1414H, shafi na 525; Tabarsi, Makarem al-Akhla ƙ, 1392 AH, shafi na 459.
- ↑ Abu Hanifa Maghrib, Da'aim al-Islam, Dar al-Maarif, juzu'i na 1, shafi na 62.
- ↑ Misali, duba Mohammadi Rishahri, Ahlul Baiti, Alaihimu Salam, dar kur’an wa-Hadis, 1391, shafi na 521-246.
- ↑ Misali, duba Mohammadi Rishahri, Ahlul Baiti, Alaihimu Salam, dar kur’an wa-Hadis, 1391, shafi na 505
- ↑ Sobhani, Manshur Ja ɓid, 2003, juzu'i na 4, shafi na 357.
- ↑ Misali, duba Seyed Morteza, al-Shafi fi al-Imamah, 1410 AH, juzu'i na 3, shafi na 134; Tabarsi, A'lam al-Wori ba'alam al-Hadi, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 293-294; Bahrani, Menar al-Huda, 1405 AH, shafi na 646; Sobhani, Al-Elahiyat, 1412 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 125.
- ↑ Duba Tabatabaei, al-Mizan fi Tafsir al- ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 16, shafi na 312-313; Sobhani, Tauhidin Ali Hoda al-Kitab wa Sunnah wa Al-A ƙl, 1412 AH, juzu'i na 4, shafi na 125-129; Sobhani, Manshur Ja ɓid, 2003, juzu'i na 4, shafi na 357-364.
- ↑ Duba Safar, Basa'ir al-Deraj, 1404 AH, shafi na 412-414; Sheikh Sadou ƙ, Ayun Akhbar al-Reza (AS), 1378 AH, Juzu'i na 1, shafi na 229 da Mujalladi na 2, shafi na 30-31, 62.
- ↑ Duba Ibn Attiyah, Abhi al-Madad, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 130; Bahrani, Manar al-Huda, 1405 AH, shafi na 670; Sobhani, Manshur Ja ɓed, 2003, juzu'i na 1, shafi.407.
- ↑ Sheikh Mufid, al-Masal al-Jaroudiyya, 1413 AH, shafi na 42; Ibn Atiyah, Abhi al-Madad, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 131; Bahrani, Manar al-Hadi, 1405H, shafi na 671.
- ↑ Duba Ibn Attiyah, Abhi al-Madad, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 131; Bahrani, Manar al-Hadi, 1405 AH, shafi na 671; Hammoud, Al-Fouad Al-Bahiya, 1421H, Juzu'i na 2, shafi na 94-95.
- ↑ Mir Hamed Hossein, Ab ƙat al-Anwar, 1366, juzu'i na 23, shafi na 975-978, 981.
- ↑ Sheikh Sadou ƙ, Al-Ithi ƙadat, 1414H, shafi na 93.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 297 da 298.
- ↑ Misali, duba Tabarsi, Majmaal Bayan fi Tafsirin Alkur’ani, 1372, juzu’i na 2, shafi na 763 da 764; Muzaffar, Dala'il al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 403 da na 404.
- ↑ Hilli, Nahj al-Ha ƙ wa-Kashf al-Sidki, 1982, shafi na 177; Tabarsi, Majmall Bayan fi Tafsirin ƙur'an, 1372, juzu'i na 2, shafi na 763; Shushtri, Ah ƙa ƙ al-Ha ƙ, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 46.
- ↑ Kundozi, Yanabi al-Mouda, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 266; Shushtri, Ah ƙa ƙ al-Ha ƙ, 1409 AH, juzu'i na 9, shafi na 208, juzu'i na 14, shafi na 145, juzu'i na 34, shafi na 310.
- ↑ Muzaffar, Dala'il al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 389-390.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Baiti”, shafi na 556.
- ↑ Duba Ibn Atiyah, Abhi al-Madad, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 819; Muzaffar, Dala'il al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi na 259.
- ↑ Sobhani, Simayeh Akayid Shia, 2006, shafi na 231 da 232
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Baiti”, shafi na 558.
- ↑ Sobhani, Simayeh Akayed Shia, 2006, shafi na 231 da 232.
- ↑ Sheikh Sadou ƙ, Kamal al-Din wa-Tamamul Al-Neema, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 240; Ibn Hanbal, Musnad Ahmad Ibn Hanbal, 1416 AH, Juzu'i na 35, shafi na 456 da 512; Haythami, Majmaal al-Zawaed, Dar al-Kitab al-Arabi, juzu'i na 9, shafi na 163; Shushtri, Ah ƙa ƙ al-Ha ƙ, 1409 AH, juzu'i na 9, shafi na 375 da juzu'i na 18, shafi na 279-281.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 562.
- ↑ Sobhani, Simayeh Akayed Shia, 2006, shafi na 231.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 561.
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Bait”, shafi na 561.
- ↑ Hamoud, al-Fawa'ed al-Bahiya, 1421H, juzu'i na 2, shafi na 117.
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Al ƙur’an, 1386, juzu’i na 9, shafi na 154; Hamoud, al-Fawa'ed al-Bahiya, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 118; Hosseini Milani, isbatu al-Wolaya al-Amma, 1438H, shafi na 166.
- ↑ Hamoud, al-Fawa'ed al-Bahiya, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 137; Hosseini Milani, Isbatu al-Wolaya al-Amma, 1438H, shafi na 168.
- ↑ Hamoud, al-Fawa'ed al-Bahiya, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 137; Hosseini Milani, Isbatu al-wulaya al-Amma, 1438 AH, shafi na 233.
- ↑ Khoi, Misbah al-Fa ƙaha (al-Makasab), 1417 AH, juzu'i na 5, shafi na 38; Safi Golpayegani, ɓelayat Takwini wa-Tashri'i, 1392, shafi na 133; Hosseini Milani, Isbatu al-Wolaya al-Amma, 1438 AH, shafi na 111; Hamoud, al-Fawa'id al-Bahiya, 1421H, juzu'i na 2, shafi na 112.
- ↑ Khoi, Misbah al-Fa ƙaha (al-Makasab), 1417 AH, juzu'i na 5, shafi na 38; Safi Golpayegani, Welayat Takwini wa-Tashari'i, 1392, shafi 133, 135, 141.
- ↑ Safi Golpayegani, Welayat Takwini wa-Tashri'i, 1392, shafi na 141.
- ↑ Sobhani, Manshur Ja ɓed, 2003, juzu'i 10, shafi 180; Hosseini Milani, Isbatu al-Wolaya al-Aaa, 1438 AH, shafi na 267 da 268; Safi Golpayegani, ɓelayat Takwini wa-Tahsri'i, 1392, shafi na 126; Ja ɓadi Amoli, Shamim ɓelayat, 2003, shafi na 92.
- ↑ Misali, duba: Momin, “Waliya Wali al-Masoom (a.s.)”, shafi na 115; Hosseini Milani, Isbatu al-Wolaya al-Amma, 1438 AH, shafi na 272 da 273.
- ↑ Hosseini Milani, Hujjar al-Wolaya al-Aaa, 1438 AH, shafi na 343; Amili, Alwelaya al-Takwini wa-Tashar'iyya, shafi na 60, 61, 63.
- ↑ Momin, "Waliyah Wali al-Masoom (AS)", shafi na 100, 118; Hosseini Milani, Isbat al-Ulaya al-Ammah, shafi na 356; Aamili, Al-Walaya al-Takwini wa-Tashari'iyya, shafi na 60.
- ↑ Duba Mughniyeh, Al-Jawami'i wal-Al-Fawari ƙ, 1414 AH, shafi na 127, 128; Safi Golpayegani, Welayat Takwini wa-Tashri'iy, 1392, shafi 132-130; Fehri "Welayat Takwini wa-Tashri'iy, shafi na 384-388.
- ↑ Hosseini Milani, Ba Peshwayan Hidayatgar, 2008, shafi na 383.
- ↑ Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi 100; Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 4, shafi na 391
- ↑ Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 100
- ↑ Duba Halabi, Al-Kafi Fi ƙhu, 1403H, shafi na 97
- ↑ Halabi, Al-Kafi Fi ƙhu, 1403H, shafi na 97.
- ↑ Muzaffar, Dala'il al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 6, shafi na 262 da 263.
- ↑ Sobhani, Al-Elahiyyat, 1412 AH, juzu'i na 4, shafi na 108.
- ↑ Mir Hamed Hossein, AKbat al-Anwar, 1366, juzu'i na 23, shafi na 975.
- ↑ Muzaffar, Akayed al-Imamiyyah, 2007, shafi na 72; Mousa ɓi Zanjani, Akayed al-imamiya al-ethni al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181.
- ↑ Muzaffar, A ƙeed al-Amamiyyah, 2007, shafi na 72; Mousa ɓi Zanjani, Akayed al-imamiya al-ethni al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181.
- ↑ Suratul Shura, aya ta:23.
- ↑ Misali, duba: Fazel Mo ƙdad, Al-Lawa’mi'ul Al-Ilahiya, 1422H, shafi na 400; Muzaffar, Akayed al-Imamiyah, 2007, shafi na 72; Mousa ɓi Zanjani, Akayed al-Imamiya al-Ethni al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 27, shafi na 595.
- ↑ Makarem Shirazi, TafsiR namuneh, 1372, juzu'i na 20, shafi na 407. Muzaffar, Akayed al-Imamiyah, 2007, shafi na 72; Mousa ɓi Zanjani, Akayed al-imamiya al-ithne al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181.
- ↑ Misali, duba Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi.46; Sheikh Sadou ƙ, Man Lay Hazara Al-Fa ƙih, 1413 AH, Mujalladi na 4, shafi na 364.
- ↑ Muzaffar, Akayed al-Imamiyah, 2007, shafi na 73.
- ↑ Mohammadi Rayshahri, Farhang Nameh Azadari Saraye Sayyid al-Shohda, 1387, shafi na 11-12.
- ↑ Akbarian, “Mahabbat Ahlul Baiti (AS) Alkur’ani”, shafi na 44
- ↑ Akbarian, “Mahabbat Ahlul Baiti (AS) dar Alkur’an”, shafi na
- ↑ Khademi, “Mahabbat Fayambaran wa-Ahli-Baiti az Didgahe Kur’ani wa hadisai” shafi na 25.
- ↑ Khademi, “Mahabbat Fayambaran wa-Ahli-Baiti az Didgahe Kur’ani wa hadisai” shafi na 26
- ↑ Mohammadi Rayshahri, Ahlul Baiti (Aalihimu Salam) dar kur’an wa Hadis, 1391, shafi na 811-833.
- ↑ Misali, duba Nishaburi, Sahih Muslim, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 4, shafi na 1871; Tirmidhi, Sunan al-Tirmidhi, 1998, juzu'i na 5, shafi na 75, 204, juzu'i na 6, shafi 83, 132, 182; Ibn Asaker, Tariku Damascus, 1415 AH, juzu'i na 14, shafi na 138, 140, 148, juzu'i na 41, shafi na 25, juzu'i na 42, shafi na 112, juzu'i na 67, shafi na 25; Dhahabi, Tarikh al-Islam, 2003, juzu'i na 2, shafi na 627.
- ↑ Misali, duba Ibn Asaker, Tariku Dimashku, 1415 AH, juzu'i na 14, shafi na 154; Dhahabi, Tarikh al-Islam, 2003, juzu'i na 2, shafi na 627.
- ↑ Tirmidhi, Sunan al-Tirmidhi, 1998, juzu'i na 6, shafi 90; Dhahabi, Tarikh al-Islam, 2003, juzu'i na 2, shafi na 627.
- ↑ Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 27, shafi na 595.
- ↑ Ibn Hajar, Al-Sawa'i ƙ al-Muhuri ƙa, 1417 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 506.
- ↑ Shafi'i, Diwan al-Imam al-Shafi'i, Alkahira, shafi na 121.
- ↑ Shafi'i, Diwan al-Imam al-Shafi'i, Alkahira, shafi na 89.
- ↑ Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 370.
- ↑ Sobhani, Simayeh Akayed Shia, 2006, shafi na 234.
- ↑ Dhahabi, "Sir al-alamul Nubala", 1405 AH, juzu'i na 6, shafi na 257.
- ↑ Abu Zar'atu Al-Damash ƙi, Tarik Abi Zara'atu Al-Damash ƙi, Majma Al-Lugha Al-Arabiyyah, shafi na 536.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 15, shafi na 274.
- ↑ Ibn Hajar Hitmi, Al-Sawa’i ƙ al-Muhuri ƙa, 1417 AH, juzu’i na 2, shafi na 442.
- ↑ Ibn Hajar Hitmi, Al-Sawa’i ƙ al-Muhuri ƙa, 1417 AH, juzu’i na 2, shafi na 442
- ↑ Rabbani Golpayegani, “Ahl al-Baiti”, shafi na 556.
- ↑ «موسوعة سیرة اهل البیت(ع)»،
Tsokaci
- ↑ Sayyid Hashem Bahrani a cikin littafinsa Ghayatul al-Maram yana da ruwayoyi 34 daga madogaran Shi'a da ruwayoyi 41 daga Ahlus Sunna (Bahrani, Ghaya al-Maram da Hajja al-Khasam, 1422 H. Mujalladi na 3, shafi na 173-211) da Hakim Haskani. ya ruwaito hadisai sama da 130 daga Ahlul Sunna a cikin hadisin al-Tanzil, ma’ana Ahlul Baiti a cikin ayar tsarkakewa, su ne ma'abota bargo.(Hakim Haskani, Havadat al-Tanzil, 1411H). juzu'i na 2, shafi na 18-139)
Nassoshi
- Alkur'anil Kareem
- «آشنایی با مراکز علمی اردن: دانشگاه آلالبیت»، Kamfanin dillancin labarai na Al-Kareem, kwanan wata: 11 Disamba 2008, ranar ziyarta: 21 ga Mayu, 1402.
- «آشنایی با مراکز اسلامی اردن؛ مؤسسه اندیشه اسلامی آل البیت اردن»، Bikin riko, ranar shigar abun ciki: 19 ga Fabrairu, 2009, ranar ziyarta: 21 Afrilu 1402.
- Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharh Nahj al-Balaghah, ƙum, Maktabatu Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, bugu na farko, 1404H.
- Ibn Hajar Haytami, Al-Sawa'i ƙ al-Muhri ƙa Ali Ahl al-Rafzah wal-Zalal wal-Zinda ƙah, wanda Abd al-Rahman bin Abdullah Al-Turki suka yi bincike da Kamel Muhammad Al-Kharat, Beirut, Cibiyar Risala, 1417 Hijira.
- Ibn Hanbal, Ahmad bin Muhammad, Masnad al-Imam Ahmad bin Hanbal, bincike na Shoaib al-Arnaut da Adel Murshid da sauransu, Beirut, Al-Risala Foundation, 1421H.
- Ibn Asaker, Abu al- ƙasim Ali bin Hasan, Tarihin Damascus, Amr bin Gharama al-Amrowi ya yi bincike a Beirut, Darul Fikr, 1415H/1995 miladiyya.
- Ibn Attiyah, Mu ƙatil, Abhi al-Madad a cikin bayanin taron malaman Bagadaza, bayanin da bincike na Muhammad Jamil Hamoud, Beirut, Cibiyar Al-alami, bugu na farko, 1423H.
- Ibn Faris, Ahmad, Mujam Ma ƙayis al-Laghga, Beirut, Darul Fikr, 1418H.
- Ibn Kathir na Damascus, Ismail bn Umar, Tafsirin Ibn Kathir, Beirut, Darul Andalus, 1416 Hijira.
- Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Lasan al-Arab, Beirut, Dar Sadir, 2000 AD.
- Abu Hanifa Maghrib, Noman bin Muhammad, Da'aim al-Islam, Alkahira, Dar al-Maarif, Bita.
- Abu Zareh Al-Damash ƙi, Abd al-Rahman bin Amr, Abi Zareh Al-Damash ƙi, Damascus, Al-Lugha Al-Arabiyyah, Bita.
- اسمهایی که مردم ایران از صدسال پیش تا به حال دوست دارند»، Khabar online, kwanan watan aikawa: Yuni 3, 1391, kwanan shiga: Mayu 21, 1402.
- Akbar Sayyid Muhammad «محبت اهلبیت(ع) در قرآن»، A cikin mujallar Reh Tosheh, lamba 115, bazara da rani na 2018.
- Bahrani, Seyyed Hashem, Ghayatul al-Maram wa-Hujjatu al-Khasam fi Ta'ayini Imam mIN dariki Amm wa-Kass, wanda Sayyid Ali Ashour, Beirut, Al-Tarikh Al-Arabi Foundation ya yi bincike, bugu na farko, 1422H.
- «برگزاری جشن میلاد امام رضا (ع) در کشورهای مختلف جهان»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr, ranar bugawa: Agusta 14, 1396, kwanan wata: Mayu 30, 1402.
- Bashoi, Mohammad Ya ƙub, Hukuk Ahlul Baiti (a.s.) dar tafasir Ahlul-Sunnat, ƙum, Al-Mustafa International Translation and Publishing Center, 1390.
- «بیانات در دیدار میهمانان شرکت کننده در چهارمین مجمع جهانی اهل بیت(ع)»، Yanar Gizo na Ofishin Kula da Ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 28 ga Agusta, 2006, ranar ziyarta: 20 ga Mayu, 1402.
- «بیانات در دیدار شرکتکنندگان در اجلاس «محبان اهلبیت(ع) و مسئله تکفیریها»، Yanar Gizo na Ofishin Kula da Ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 2 ga Janairu, 1396, ranar ziyarta: 20 Mayu 1402.
- «پرچم مخمل السلام علیکم یا اهل بیت النبوة»، Shahararriyar gidan yanar gizon wallafe-wallafe, ranar ziyarta: Mayu 20, 1402 AH.
- Tirmidhi, Muhammad bin Isa, Sunan al-Tirmidhi, bincike na Bashar Awad Ma'rouf, Beirut, Dar al-Gharb al-Islami, 1998.
- Thaalbi, Ahmed bin Muhammad, Al-Kashf da Al-Bayan (Tafseer al-Thalabi), Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, bugu na farko, 1422H.
- «جشن میلاد حضرت ولی عصر (عج) در کشورهای مختلف جهان برگزار شد»،Kamfanin dillancin labarai na Kaream, ranar bugawa: Maris 27, 1400, kwanan shiga: Mayu 30, 1402.
- Ja ɓadi Amoli, Abdullah, Shamim ɓelayat, wanda Seyyed Mahmoud Sadeghi ya shirya kuma ya shirya shi, ƙom, Israa, bugu na biyu, 2003.
- Hakim Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed Al-Tanzil al- ƙawam Al-Tfadil, Bincike na Mohammad Bagher Mahmoudi, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, bugu na 1, 1411H.
- Hosseini Milani, Sayyid Ali, Isbatu Al-Walaya Al-Ulaya Fayambaran wa-Imaman (AS), ƙum, Wallafar Al-Ha ƙay ƙ, bugu na 1, 1438 bayan hijira.
- Hosseini Milani, Seyyed Ali, Ba Fisbayan Hidayatgar, ƙom, Cibiyar Ha ƙai ƙ ta Musulunci, 2008.
- Halabi, Abul Salah, Al-Kafi Fi Fi ƙh, Bincike na Reza Ostadi, Isfahan, Mazhabar Imam Amirul Momineen (AS), bugu na farko, 1403H.
- Hilli, Hassan bin Yusuf, Nahj al-Ha ƙ da Kashf al-Sadde ƙ, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, bugun farko, 1982.
- Hammoud, Mohammad Jameel, Al-Fowa'ed Al-Bahiya fi Sharh Akayed al-imamiya, Beirut, Al-Alami Institute, bugu na biyu, 1421H.
- Kadimi Ainullahi «محبت به پیامبر و اهلبیت از دیدگاه قرآن و روایات»، A cikin mujallar ci gaban ilimin kur'ani mai lamba 5, 2013.
- «خوشنویسی السلام علیکم یا اهل بیت النبوة»، Gidan yanar gizon Moali, ziyarar kwanan wata: 20 Afrilu 1402.
- Khoi, Seyyed Abul- ƙasim, Misbah al-Fa ƙaha (Al-Makasab), fassarar Muhammad Ali Tawhidi, ƙum, Ansari, 1417H.
- «دانشگاه بینالمللی اهلبیت(ع)»، Yanar Gizo na Jami'ar Ahlul-Bait International Uni ɓersity, ranar ziyarta: 21 Afrilu 1402.
- Dhahabi, Shams al-Din Muhammad bin Ahmad, Siyaru Alamul Nubala, Cibiyar Al-Rasalah, bugu na uku, 1405H.
- Zahabi, Shams al-Din Muhammad bin Ahmad, Tarikh al-Islam da Wafiyat al-Mashahir wa al-Alam, bincike na Bashar Awad Maruf, Beirut, Dar al-Gharb al-Islami, 2003.
- Rabbani Golpaygani, Ali, “Ahl al-Bait”, Encyclopedia of Islamic Kalam, karkashin jagorancin Jafar Sobhani, ƙum, Cibiyar Imam Sadi ƙ (AS), bugu na farko, 1387.
- Rajeb Esfahani, Hossein, Mufradat Alfaz Al ƙur'an, Beirut-Damascus, Dar al- ƙalam-Al-Dar al-Shamia, bugu na farko, 1412H.
- Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Al-Kashaf hakayik alal Ghwamaz al-Tanzil, bugun Mustafa Hossein Ahmad, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na farko, 1407H.
- Zainli, Gholam Hossein, Mafhum shinasi wa misdak yabi Ahlul Baiti (AS), Tehran, Mawallafin Mashaar, bugun farko, 1387.
- Sobhani, Jafar, Elahiyat Alal Hodal Al-Kitab wa Sunnah da Al-A ƙl, ƙum, Cibiyar Al-alami ta Ilimin Musulunci, bugu na uku, 1412H.
- Sobhani, Ja’afar, Akayid Shi’a: fassarar littafin Dilil al-Murshidin al-Ha ƙ al-Yaykin, wanda Ja ɓad Mohhaddi ya fassara, Tehran, Mashaar Publishing House, 2006.
- Sobhani, Jafar, Manshur Ja ɓid, ƙum, Imam Sadi ƙ Institute (AS), bugun farko, 1383.
- Sobhani, Ja’afar, Sharh Akayid Imamiyyah, ƙum, Cibiyar Imam Sadiƙ (AS), bugun farko, 1376.
- Shafi'i, Muhammad bin Idris, Diwan al-Imam al-Shafi'i, Alkahira, Ibn Sina School.