Mala'ika
Mala’ika (Larabci: الملائكة) wata Halitta ce da ba a iya ganinta da take Saman Dabi’a wacce aka umarce ta da zartar da umarnin Allah a Duniya da Lahira, Imani da Samuwar Mala’iku yana daya daga cikin Akidun Musulmai, Malaman Addinin Muslunci sun yi sabani da juna kan hakikar Mala’iku, Malaman Kalam sun tafi kan cewa Mala’iku Halittu ne masu dauke da Gangar Jiki wadanda suke bayyana da surori daban-daban, sai dai cewa Masana Falsafa suna ganinsu a matsayin Halitta Mujarradai Marasa Gangar jiki. A imanin Malaman Shi’a Mala’iku Ma’asumai ne, basa sabawa Umarnin Ubangiji ba kuma sa aikata Zunubi, haka kuma basa yin kasa gwiwa ko gazawa cikin sauke wazifar da take kansu, hakika wazifofinsu sun kasance kamar yanda bayani zai zo: Ibada, Tasbihi Tsarkake Allah, Rubuta Takardar Ayyuka, Kawo Wahayi zuwa ga Annabawa, Kariya ga Mutane, Taimakon Muminai, Kawo Arziki Madi da Ma’anawi, Karbar Rayuka, Shiryar da Zukata da kuma zartar da Azabar Allah. Malla’iku Kashi-Kashi ne da Martabobi daban-daban, Jibrilu, Mika’ilu, Israfilu, Azra’ilu, suna sama da sauran Mala’iku. Fifikon Mala’iku kan Mutane, Ismar Mala’iku, kasancewarsu da Gangar jiki ko rashin Gangar Jiki suna daga cikin Bahasin Ilimin Kalam da Malamai suka bayyanar da ra’ayoyi da Mahanga daban-daban.
Su wanene Mala’iku
Mala’iku wasu Halittu ne da suka kasance `yan tsani tsakanin Allah da Mutane, kuma Allah ya wakilta su kan Duniya [1] Mala’iku Jam’i ne Na Mala’ika [2] Dangane da Hakikar Mala’iku akwai Sabanin ra’ayoyi, Malaman Kalam sun tafi kan cewa Mala’iku suna tare da Tausassan Gangar Jiki da Haske, za su bayyana da Surori da Shakalai daban-daban [3] Allama Majlisi ya danganta wannan ra’ayi ga baki dayan Musulmai in banda wasu tsiraru daga Masana Falsafa, ya kuma kara da cewa Annabawa da Wasiyyai su na ganin Mala’iku [4] na’am wasu Jama’a daga Masana Falsafa suna ganin Mala’iku suna saman gangar jiki da jikkantuwa sun tafi kan cewa suna da wasu Siffofi da jiki baya daukarsu [5] a cewar Allama Tabataba’i Abin da ya zo a riwaya dangane da Mala’iku da ya zo cikin misalin Shakali da Surorin Gangar Jiki ya zo a Mukamin Tamassul (Misaltuwa da Gangar jiki) bawai hakikarsa ba, (Ma’ana wani abu ya zo wa wani mutum cikin wata kebantacciyar Sura) [6] ahaka kuma batun cewa Mala’iku da Aljanu Tausassan jiki ne da suke bayyana da surori da Shakali daban-daban babu wani ingantaccen dalili kan haka [7] kan asasin riwaya da aka Nakalto daga Imam Sadik (A.S) an Halicci Mala’iku daga Haske [8]
Matsayi da Muhimmanci
Imani da Samuwar Mala’iku yana daga Akidun Musulmai [9] Imani da su misalin Imani da Sallah da Azumi ne suna daga Laziman Imani da Annabta [10] Kalmar Mala’ika ta zo a wuri 88 cikin Alkur’ani [11] Imam Ali (A.S) cikin Hudubar Ashbahi ya yi Magana kan Halittar Mala’iku da Rabe-rabensu, Hususiyoyinsu da Siffofinsu [12] a cikin Bihar-Anwar akwai riwayoyi fiye da guda 100 da suka zo kan bayanin Hakikar Mala’iku tare da bayanin wazifofinsu da Isma da Siffofin Mala’iku Makusanta. [13] a cikin Addu’a ta uku a Assahifatus Assajidiyya daga Imam Sajjad (A.S) ya kebance wannan addu’a ne ga Mala’iku Makusanta, cikin wannan addu’a an yi bayani cewa akwai salati da gaisuwar Allah wanda take kara musu tsarkaka [14] Kan asasin riwayoyi, Mala’iku sune suka kowacce Halittu yawan adadi, anyi Magana kan yawansu a cikin riwayoyi [15] ya zo cikin hadisai cewa an halicci Mala’iku bayan Halittar Hasken Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S) [16] Wasu Jama’a daga Mushrikai suna bautawa Mala’iku kuma suna ganinsu matsayin Halittun Allah, amma tare da haka sun yi Imani da su cewa suna da cin gashin kai cikin ayyuka [17] wasu ba’arin Mushrikai suna ganin Mala’iku matsayin `ya`yan Allah daga jinsin Mata [18]
Mala’iku a Mahangar Sauran Addinai
Hakika Magana dangane da Mala’iku ta zo a cikin sauran Addinai, a cikin Addinin Zartosht an bayyana cewa Mala’iku Halittun Ahura Mazda (Ubangiji) kuma dukkan Amshasipand (Lakabi ne na Manyan Mala’iku) Mazhari ne na daya daga cikin Siffofinsa, a Addinin Yahudawa Mala’iku suna Matsayin Bayin Allah ne da suke zartar da umarninsa a doran Kasa, kuma suke isar da Wahayi zuwa ga Mutum, kan asasin abin da ya zo a LIttafi Mai Tsarki wurin Kiristoci, an halicci Mala’iku kafin halittar `Dan Adam kuma suna gadinsa ne, yin salati da bautar Mala’iku wanu abu ne da ya yadu sosai cikin Majami’un Kirictoci [19]
Wazifofi
A cikin Alkur’ani an ambaci wasu wazifofin Mala’iku: sune Wasidar Saukar Wahayi, isar da sakon Allah zuwa ga Annabawa [20] gudanar da al’amuran duniya, sadar da Failar Allah zuwa ga halittu [21] Istigfari [22] ceto ga Muminai [23] Taimakon Muminai [24] La’antar Kafirai [25] Tabbatar da ayyuka Bayi [26] da karbar Rai [27] wasu Jama’a daga Mala’iku sun kasance a koda yaushe cikin Ibada da Tasbihi ba su da aiki da ya wuce wannan [28] Hakika Mala’iku suna hallara a duniyar Barzahu [29] da Lahira, wasu Jama’a daga cikinsu suna da Hallara cikin Aljanna [30] wasu kuma kula da Wuta [31]
Martabobi
A cewar Allama Tabataba’i Mala’iku suna da Martabpbi da Mukamai daban-daban, Mukaman wasu ba’arinsu ya fifita kan na wasu ba’ari [32] saboda haka kan asasin bayanin da ayoyin Alkur’ani suka kawo wasu ba’arin Mala’iku sun kasance masu saukar da wahayi, Jibrilu [33] wasu ba’ari kuma suna aiki cire Ruhi kamar Azra’ilu [34] Mulla Sadra ya rarraba Mala’iku da Makusantan Mala’iku sune Arwahu Mahaiyima, sannan Mala’ikun da aka wakilta kan halittun Sama sune Mala’ukun da kuma Mala’ikun da aka wakilta a Kasa [35] Imam Khomaini ya karkasa Mala’ikun da basu da Tasarrufi kan Jikkuna da Mala’iku Muhaiyima, Mala’iku Ahalin Duniyar Jabrut da Mala’ikun da aka wakilta kan Halittu Ma’abota gangar jiki [36] Hususiyoyi Ba’arin Hususiyoyin Mala’aikun sun kasance kamar haka:
Isma
A cewar Allama Majlisi, `Yan Shi’a sun yi Imani da cewa Mala’iku sun katangu ne daga aikata dukkanin Manya-Manyan Zunubai da karaminsa sun kasance Ma’asumai, haka kuma galibin Ahlus-sunna suma sun yi Imani da haka [37] amma tare da haka akwai wasu ba’ari daga Ahlus-sunna da basu yarda da Ismar Mala’iku ba, amma wasu ba’ari daga cikin sun tafi kan cewa kadai wasu kebantattun Mala’iku ne Ma’asumai misalin Makusantan Mala’iku da Masu kawo Sakon wahayi [38] Kan asasin ayar
Basa gabatarsa da zance sun kasance suna aiki da umarninsa. [39]
Basa sabawa Allah abin da ya umarce su. [41] Na’am wasu ba’ari tare da jingina da waki’ar Haruta da Maruta da kuma kin yin Sujjadar Iblisu ga Adam [42] haka da saba umarnin Fitris wasu Ba’arin Malaman Ahlus-sunna sun shakku kan Ismar Mala’iku [43] sai dai cewa Malaman Shi’a sun basu amsa kan wadannan shubuhohi na su: daga Jumlarsu da farko batun saba Umarnin Haruta da Maruta kirkirar Kissa ce da Tatsuniya wacce ba ta zo a cikin Alkur’ani ba [44] haka kuma ance Iblis Bai kasance Mala’ika [45] haka kuma a cewar Murtada Mutahhari na’am akwai yiwuwar samun saba umarni daga wasu ba’arin Mala’iku amma ba dai dukkaninsu ba [46] [yadasht 1]
a cewar Nasir Mukarim Shirazi dangane da abin da ya zo cikin riwaya danganna da ladabtar da wasu ba'arin Mala'iku ya faru ne sakamakon kin yin aiki da Tarkul Aula (barin abin da ya fi cancantuwa) Bawai zunubi ba, kamar yanda ta faru kan ba’arin wasu Annabawa [47] Allama Tabataba’i ya tafi kan cewa suna son dukkanin abin da Allah yake so kuma suna aiki da dukkanin abin da Allah ya yi umarni da shi da wannan dalili ne ya kasance bas a aikata zunubi [48]
Fifita kan `Dan Adam
Wasu ba’arin Malamai tare da jingina da ayar
Hakika mun Karrama `dan Adam kuma un fifita shi daga abubuwan da muka halitta fifitawa. [49] Suna ganin Mala’iku suna da fifita kan `dan Adam, wasu kuma tare da jingina da waki’ar Sujjadar Mala’iku ga Adamu da kuma karbar ilimi daga Adamu, sun tafi kan cewa Mutum ya fifita kan Mala’iku amma da sharadin ya yi amfani da tanadin da Allah ya bashi a inda ya dace [50] A cewar Hassan Zadeh Amoli da Ibn Arabi, Mala’iku Illiyun (Muhaiyimin) sun fifita kan mutane saboda su ba ma wajabta musu yin Sujjada ga Adamu ba [51] muhammad Dawud Kaisari yana ganin Mutanen da suka kai ga Mukamin Halifan Allah sun fifita hatta kan Mala’iku Illiyun [52] Mulla Sadra tare da jingina da aya ta 31 cikin Suratul Bakara da take ishara kan koyar da ilimin da Adamu ya yi ga Mala’iku ya tafi kan cewa wannan aya tana shiryarwa zuwa ga ffitar `Dan Adam kan Mala’iku da suke zauna a Kasa da Sama, banda Mala’iku Muhaiyimin [53]
Fifikon Annabawa kan Mala’iku
Akasarin Musulmai suna ganin fifikon Annabawa a kan Mala’iku dalili kan haka shi ne samuwar Karfin Fushi da Sha’awa cikin Annabawa sabanin Mala’iku [54] haka kuma akwai ayoyi da suke tabbatar da wannan fifiko daga ciki ayar umartar Mala’iku da yin Sujjada ga Annabi Adam da kuma koyar da su da ya yi [55] haka kuma `Yan Shi’a suna ganin Imamansu sun fifita kan Mala’iku [56]
Tamassuli da surar Mutum
Bisa dogara da ayar Alkur’ani [57] Ruhul Amin ya yi Tamassuli ga Maryam [58] ma’ana ya zo wurinta da surar Mutum, haka kuma kan asasin riwayoyi Jibrilu ya zuwa wurin Annabi (S.A.W) da suran wani Saurayi da ake kira da Duhaiyatu Kalabi [59] ya zo a riwaya cewa lokacin da Mala’iku suke karbar Rai suna cire rai da Tamassuli kan asasin Mutum Mumini ne ko Fasiki ne, suna zuwa wurin wannan Mutumi da mabanbanta surori, [60] Tamassuli yana nufin Mala’iku suna bayyana da wata sura sabanin asalin surarsu [61] babu wanda yake ganin Mala’iku da surarsu ta Asali sai Annabi (S.A.W) [62]
Tajarrudi
A bisa abin da Masana Falsafa suka yi Imani kansa Mala’iku Mujarradai ne [63] (wadanda basu da gangar da hususiyoyin gangar misalin Fushi [64]da Sha’awa, sauyi da canji da Kammaluwa [65] da tanadin risker abubuwa da Mariskai biyar) [66] daya daga cikin Dalilan Tajarrudin Mala’iku shi ne koruwa daga wadannan abubuwa da kawo, amma tare da haka Mulla Sadra Sabanin wasu adadin Malaman Tafsiri da suke ganin Mala’iku suna tare da da tabbataccen Mukami [67] Ilimi da Kamalar wasu Jama’a daga cikin Mala’iku yana da tanadin Karuwa [68] Imam Ali (A.S) wasu jama’a daga Mala’iku sun kasance mafi Ilimi da kusanci wurin Allah, idanunsu basa barci, hankalinsu baya rafkana, kuma basa gajiya [69]
Fukafukai
Kan asasin zahirin Ayoyin Alkur’ani [yadasht 2] da Riwayoyi ya nuna cewa Mala’iku suna da Fukafukai [70] sannan dangane da me ake nufi da Fukafukan Mala’iku akwai sabani ra’ayoyi:
- Allama Tabataba’i ya tafi kan cewa abin da ake nufi da Fukafukai ga Mala’iku shi ne cewa an musu tanadi da wani abu wanda da shi ne suke kai kawo daga Sama zuwa Kasa daga Kasa zuwa Sama daga wannan Muhalli zuwa wancan, bawai suna da Fukafukai Irin na Tsuntsaye ba [71]
- Imam Khomaini ya tafi kan cewa Mala’ikun Duniyar Malakut Mujarradai ne basu da Jikkuna kuma basu da Fukafukai, amma Mala’ikun Alamul Misal zai iya yiwuwa ya zamana suna da Fukafukai cike da misali [72]
- Ibn Arabi, yana ganin cewa abin da ake nufi da Fukafukan Mala’iku shi ne awon tasirinsu cikin Malakut din Sama da Kasa [73]
Haka kuma suna ganin adadin Fukafukan Mala’iku alama ce ta saurin zartar da umarnin Allah [74] da kuma alamar kudurar cirata da zartar da aiki [75] kuma alama ce ta banbancin darajoji da martabobin Mala’iku [76]
Sanin Littafi
Anyi rubuce-rubuce cikin Harsuna daban-daban dangane da Mala’iku, ba’arin suna kasance kamar haka:
- Sairi dar Asrar Fareshtegan, littafi ne daka rubuta cikin Uslubin ALkur’ani da Irfani, talifin Muhammad Zaman Rostami da Tahir Alu Buye cikin Harshen Farisanci. Mahiyat Mala’iku, Siffofinsu, Kashe-kashensu, Ayyukansu, da banbance-banbancensu da Mutane suna daga Unwanan wannan littafi [77] cibiyar zurfafa binciken Ilimi da Al’adun Muslunci ta buga wannan littafi a shekarar 1393 h shamsi littafin yana dauke da shafuka 552, [78]
- Al-Maklukat Al-Kafiyyatu fi Alkur’ani: Almala’ikatu, Aljinnu, Iblis. Littafi ne cikin harshen Larabci talifin Sayyid Muhammad Tabataba’i.
Haka kuma akwai littafin Imanu bil-Mala’ikati, talifin Abdullahi Sirajud-Addini. Al-Mala’ika. Talifin Bill Gram, Simaye Fareshtegan dar Kur’an wa-Nahjul Balaga, talifin Laila Hamdullahi, Fareshtegan , talifin Ali Rida Rijali Tahrani, da kuma littafin Mala’ika, talifin Muhammad Shuja’i, duka suna daga rubuce-rubucen da aka yi a wannan fage [79]
Bayanin kula
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 6.
- ↑ Tareehi, Majalisar Al-Bahraini, 1416 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 292.
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Imam Amir al-Mominin, 2007, juzu'i na 1, shafi na 161
- ↑ Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 56, shafi na 202-203.
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Imam Amir al-Mominin, 2007, juzu'i na 1, shafi na 161
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 13.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 13.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 58, shafi na 306, h. 15.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta:285.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 442.
- ↑ Rostami da Alboyeh, Sairi dar Asrar Fareshtegan, 2014, shafi na 47.
- ↑ Nahj al-Balagha, Sobhi Saleh, 1374, shafi na 128-131.
- ↑ Duba Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 56, shafi na 326-144.
- ↑ Sahifa Al-Sajjadiya, 1376, shafi na 40-36.
- ↑ Bahrani, Al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 4, shafi na 535.
- ↑ Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 15, shafi na 8 da juzu'i na 18, shafi na 345 da juzu'i na 24, shafi na 88.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 19, shafi na 38.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 171.
- ↑ The Encyclopedia of Religion, volume1, p:2830, Oxford, New York, (1986 به نقل از مطهرینیا، بازنمایی فرشتگان الهی در رسانه(۱) جبرائیل و میکائیل، ۱۳۹۰ش، ص۵۹.
- ↑ Suratul Nahl, aya ta 2 da ta 102; Suratul Abs, aya ta 16.
- ↑ Suratul Nazaat, aya ta 5; Suratul Ma'arej, aya ta 4.
- ↑ Suratul Mumin, aya ta 7.
- ↑ Suratul Anbiya, aya ta:28.
- ↑ Suratul Alu-Imran, aya ta 124 da ta 125.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta 141; Suratul Ali-Imran, aya ta:87.
- ↑ Suratul Yunus, aya ta 21; Suratul Zakharf, aya ta 80; Suratul Infatar, aya ta 11.
- ↑ Suratul An'am, aya ta 62; Suratul Nisa’i, aya ta:97.
- ↑ Suratul Anbiya, aya ta 19-20.
- ↑ Suratul Nahl aya ta 28 da ta 32.
- ↑ Suratul Zumar, aya ta 72; Suratul Anbiya, aya ta:103.
- ↑ Suratul Mudassir, aya ta:20.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 12.
- ↑ Suratul Takweer, aya ta 21.
- ↑ Suratul Sajdah, aya ta 12; Suratul An'am, aya ta 62.
- ↑ Duba Mulla Sadra, Mufatihul Al-Ghaib, 1363, shafi na 350-351.
- ↑ Imam Khumaini, Ladubban Sallah, 1378, shafi na 342-339.
- ↑ Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 124.
- ↑ Zarakshi, Bahrul Al-Muhit, 1414 AH, juzu'i na 6, shafi na 21.
- ↑ Suratul Anbiya, aya ta:27.
- ↑ Suratul Tahreem, aya ta 6.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 12.
- ↑ Dubi Fayaz Lahiji, Gohar Murad, 2013, shafi na 426.
- ↑ Rastin da Kohensal, Ismat Fareshtegan Shawaheed Muwafik wa Mukalif", shafi na 127 da 128.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 375.
- ↑ Fayaz Lahiji, Gohar Murad, 2003, shafi na 426.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, 2009, juzu'i na 4, shafi 280.
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 1387, juzu'i na 1, shafi na 168.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 12.
- ↑ Suratul Isra, aya ta 70.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 12, shafi na 200-199.
- ↑ Duba Hassanzadeh Amoli, Mammad Elham, 1378, shafi na 367-369.
- ↑ Hassanzadeh Amoli, Mammad Elham, 1378, shafi na 367-369.
- ↑ Mulla Sadra, Tafsirin Kur’an Al-Karim, 1366, juzu’i na 2, shafi na 370.
- ↑ Allameh Hali, Kashf al-Morad, 1413 AH, shafi na 360; Eiji, Sharh al-Mawakif, 1325 AH, juzu'i na 8, shafi na 285.
- ↑ Eiji, Sharh al-Mawakif, 1325 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 283-285
- ↑ Ashqar, Alam Al-Mulaika Al-Abrar, 1421 AH, shafi na 92.
- ↑ Suratul Maryam, aya ta 17
- ↑ Imam Khumaini, Adabus As-Salati, 1378, shafi na 342.
- ↑ Misali, duba: Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 20, shafi na 210.
- ↑ Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 74.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 13.
- ↑ Ashqar, Alam al-Mala'ika Al-Abrar, 1421 AH, shafi na 11.
- ↑ Duba Fayaz Lahiji, Gohar Murad, 2003, shafi na 427.
- ↑ Allameh Hali, Kashf al-Morad, 1413 AH, shafi na 360.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 13.
- ↑ Ashqar, Alam al-Mala'ika al-Abrar, 1421H, shafi na 5.
- ↑ Misali, duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu’i na 17, shafi:176; Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 26, shafi na 362.
- ↑ Mulla Sadra, Tafsirin Kur’an al-Karim, 1366, juzu’i na 2, shafi na 371.
- ↑ Qummi, Tafsirin Qummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 207.
- ↑ Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 8, shafi na 625.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 7.
- ↑ Imam Khumaini, Sharh Cehel Hadis, 1380, shafi na 414
- ↑ Ibn Arabi, Tafsir Ibn Arabi, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 167.
- ↑ Sabzevari, Ershad Al-Azhan, 1419 AH, shafi na 440.
- ↑ Makarem Shirazi, Al-Athl, 1421 Hijira, juzu'i na 14, shafi na 13.
- ↑ Hosseini Hamdani, Anwar Derakhshan, 1404H, shafi na 259
- ↑ Rostami da Alboyeh, Sairi dar Asrar Fareshtegan, 2014, shafi 4., 2014, shafi 4., 2014, shafi 29-5
- ↑ Rostami da Alboyeh,Sairi dar Asrar Fareshtegan , 2014, shafi 4.
- ↑ Rostami da Alboyeh, Sairi dar Asrar Fareshtegan, 2014, shafi na 46.
Nassoshi
- Ibn Arabi, Muhyiddin Muhammad, Tafsir Ibn Arabi, wanda Samir Mustafa Rabab ya yi bincike a Beirut, Dar Ahya al-Trath, 1422H.
- Ashqar, Omar Suleiman, Alam al-Mala'ika al-Abrar, Jordan, Dar al-Nafis, 1421 AH-2000 AD.
- Al-Sahifa Al-Sajjadiya, Qum, Al-Hadi Publishing House, 1376.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Adabus As-Salati, Tehran, Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (a.s), Tehran, 1378.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sharh Cehel Hadis, Qum, Cibiyar Edita da Buga Imam Khumaini, 1380.
- Ayji, Miryyid Sharif, Sharh Al-Mawakif, Badar al-Din Nasani, al-Sharif al-Razi, Qom offset, 1325 AH.
- Bahrani, Sayyid Hashim, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Tehran, Ba'ath Foundation, 1416H.
- Javadi Amoli, Abdullah, Tahrir Tahmhid al-Qasas Ibn Turke, Tehran, Al-Zahra Publications, 1372.
- Hassanzadeh Amoli, Hassan, Mammad Elhamm a cikin bayanin Fuss al-Hakm, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Shiriya, 1378.
- Hosseini Hamdani, Seyyed Mohammad Hossein, Anwar Derakhshan, bincike na Mohammad Baqer Behboodi, Tehran, kantin sayar da littattafai na Lotfi, 1404H.
- Rostami da Alboyeh, Mohammadzaman wa Tahira,Sairi dar Asrar Fareshtegan, Qum, Cibiyar Bincike na Kimiyya da Al'adun Musulunci, 2013.
- Zarkashi, Muhammad bin Abdullah, Al-Baharul al-Muhit fi Usul Fiqh, Dara al-Katbi, 1414 AH 1994 AD.
- Sabzevari Najafi, Muhammad bin Habibullah, Irshad Al-Azhan zuwa Tafsirin Qur'an, Beirut, Dar al-Taraif don bugawa, 1419 Hijira.
- Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Institute, Offset, Qum, Islamic Publications, bugu na biyar, 1417 AH.
- Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma Al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Gabatarwa na Majmad Javad Balaghi, Nasser Khosrow Publications, Tehran, 3rd edition, 1372.
- Tareehi, Fakhreddin, Majma Al-Baharin, Ahmad Hosseini, Tehran, kantin sayar da littattafai na Morteza, 1416H.
- Allameh Hilli, Hassan bin Youssef, Kashf al-Murad fi Sharh Tajrid al-Itqad, Hassan Hassanzadeh Amoli, ya inganta shi, Qom, Al-Nashar al-Islami Est., 1413H.
- Allameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatihul Al-Ghaib, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, 1420 AH.
- Fayaz Lahiji, Abdul Razzaq, Gohar Murad, Gabatarwa na Zain Al Abidine Ghorbani, Tehran, Sayeh, 2008.
- Qummi, Ali bin Ibrahim, Tafsir Qummi, Tayyab Musawi Al-Jaziari, Qum, Darul Kitab, bugun na uku, 1404H.
- Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Darahiya al-Tarath al-Arabi, 1403 AH.
- Motaharinia, Mahmoud, Fareshtegani Ilahi dar Rasaneh (1) (Jibrilu wa Mikael), Qum, Cibiyar Nazarin Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, 1390.
- Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar, Sadra Publishing House, 2009, babu wuri.
- Makarem Shirazi da wasu Marubuta, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kutb al-Islamiya, 1374.
- Makarem Shirazi, Nasser, Al-Athmal fi Tafsir Kitabullah al-Manzil, Qum, Makarantar Imam Ali Ibn Abi Talib, 1421H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Payam Imam Amir al-Mu’minin, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1387.
- Mulla Sadra, Muhammad bin Ibrahim, Tafsirin Kur'an al-Karim, Muhammad Khajawi ya yi bincike, Kum, Bidar, 1366.
- Molla Sadra, Mohammad Bin Ebrahim, Mofatih Al Ghaib, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Ilimi Mai Girma, Hikimar Musulunci da Ƙungiyar Falsafa ta Iran da Cibiyar Nazarin Harkokin Waje da Bincike, 1363.
- Nahj al-Balaghah, Sobhi Saleh, Qum, Center for Al-Pakhuth al-Islamiyya, 1374, ya gyara daga Beirut 1387H.