Shahadar Imam Ali (A.S)
Shahadar Imam Ali (A.S)(Larabci:استشهاد الإمام علي عليه السلام،) tana daga cikin abubuwa da suka faru a ƙarni na farko h. ƙ. ta kasance wani ya kasance da tasiri mai yawan gaske cikin halin da ƴan shi'a suka samu kansu. Shahadar Imam Ali (A.S) ta zama sababin kashe kashen ƴan shi'a da cuta musu tare da wargajewar dakarun Imam Ali (A.S), shahadar Imam Ali (A.S) ta haifar da samuwar bayyanar ra'ayoyi da saɓanin mahangu da bayyana da ƙiyayya da gaba daban-daban tsakankanin mutanen garin kufa. Wasu ba'arin sahabban Imam Ali (A.S) sun kamanta sojojin Kufa bayan shahadar Imam Ali (A.S) da misalin garken tumakai da suka rasa makiyayinsu bayan hakan Kuraye suka farma su daga kowacce kusurwa. Bayan aikin hajji an samu wasu jama'a daga Khawarij sun taru tre da kokawa kan halin da musulmi suka tsinci kansu, daga ƙarshe sun yanke shawara tare da zaɓar mutane guda daga cikinsu da suka ɗauki alƙawari za su kashe Imam Ali (A.S), Mu'awiya da Amru ɗan Asi, Ibn Muljam ya ɗauki alƙawarin cewa shi ne zai kashe Imam Ali (A.S), a daren 19 ga watan Ramadan Imam Ali (A.S) ya ziyarci ɗiyarsa Ummu Kulsum, gabanin kiran sallar asubahi sai ya tashi ya tafi masallaci, bayan ya shiga masallaci sai ya dinga tashin waɗanda suke bacci domin su yi sallah, cikinsu kuwa harda Ibn Muljam, bayan haka ya tafi Mihrab (Wurin da yake sallah) ya tsaya a wurin.
Daidai lokacin da Imam Yake halin sujjada ko dai ɗagowa daga sujjada sai Ibn Muljam (L.A) ya zare takobi ya ɗaga ta sama ya sara a kan Imam Ali (A.S), sai aka ɗauki Imam Ali (A.S) aka kai shi gida aka kawo masa wani kwararren likita da ake kira da suna Asiru ɗan Amru ya duba shi. Asiru ya kasance daga tabi'ai gabanin mikin saran da Ibn Muljam ya yi masa ya gangara zuwa kwakawalwa sai wanann likita ya nemi Imam da ya yi wasiyya saboda lallai babu isashshen lokaci a gabansa da zai rayu da tsayi, bayan wannan ɗanye aikin ta'addaci na saransa a ak Imam ya ɗauki dogon lokaci bai dawo hayyacinsa ba, ya kasance yana yin sallaha a tsugune sannan ya faɗawa ƴaƴansa wasiyyarsa. Imam Hassan (A.S), Imam Husaini, Muhammad Hanafiyya da Abdullahi ɗan Jafar su ne suka yi wa Imam Ali (A.S) wanka bayan shahadarsa, sannan Imam Hassan (A.S) ne ya yi masa sallar jana'iza, an binne Imam cikin duhun dare, an ɓoye ƙabarin Imam Ali (A.S) don gujewa tone shi daga Khawarijawa da sauran maƙiyansa daga Banu Umayya, kabarinsa ya cigaba da kasancewa a ɓoye har zamanin gwamnatin Banu Abbas bayan Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyanar da shi.
Tasirin da Shahadar Imam Ali (A.S) cikin Halin ƴan shi'a
Imam Ali (A.S) ya yi shahada a watan Ramadan shekara ta 40 bayan hijira ƙ.[1] shahadar Imam ta kasance a lokacin ake fama da matsaloli masu tarin yawa, sojojinsa basu kasance masu kammalalliyar ɗa'a da miƙa wuya ga umarninsa ba, haƙiƙa sun kasance masu rauni da sakaci cikin kasancewarsu tare da shi, saɓanin sojojin Sham ƙarƙashin jagorancin Mu'awiya sun kasance masu ƙarfi.[2] a wannan lokaci tare da tsinkayen da Mu'awiya yake da shi kan halin sojojin Imam ya yi amfani da wannan dama cikin kan gwamnatin Imam Ali (A.S) daga kowacce fuska yana ta kashe mabiya da sojojin Imam Ali (A.S)[3]
Imam Ali (A.S) ya kasance cikin shirya sojojin domin yaƙar sojojin Sham a daidai wannan lokaci ne Ibn Muljam (L.A) ya afka masa ya sare shi.[4] shahadar Imam Ali (A.S) ta haifar da rauni cikin sojojin kufa, kamar yadda Naufu Bakali ɗaya daga cikin sahabban Imam (A.S) yake naƙaltowa cewa sojoin kufa sun kasance cikin shirin tafiyar yaƙar sojojinn sham kwatsam sai Ibn Muljam (L.A) ya afkawa Imam Ali (A.S) da sara lamarin da ya sanya sojojin kufa dawowa gida. Naufa a wannan zamani ya kamanta halin da sojojin kufa suka kasance da misalin garke tumaki waɗanda makiyayinsu ya ɓace sannan kuraye suka afka musu ta kowacce kusurwa.[5]
Bayan shahadar Imam Ali (A.S) mutanen kufa sun yi wa babban ɗansa Imam Hassan (A.S) bai'a. Sai dai cewa kamar yadda ba'arin malamai suke cewa haƙiƙanin mutanen kufa bai canja daga yadda yake ba daga sassauyawa fahima da ra'ayoyi da kuma bayyana ƙiyayya tsakanin mutane, da wannan dalili ne sojojin Imam Hassan (A.S) suka rasa ƙarfin gwiwar tsayawa gaban sojojin sham,[6] Ayatullah Subhani masanin tarihi na daga shi'a ya tafi kan cewa shahadar Imam Ali (A.S) ya bayyana cewa shahadar Imam Ali (A.S) ta kasance wani kakkausan naushi kan al'ummar musulmi, ta kuma zama sababin buɗe babin kisa da takurawa ƴan shi'a daga ɓangaren maƙiya,[7] tare da shahadar Imam da kuma bayan taƙaitaccen Halifancin Imam Hassan (A.S) mulkin Bani Umayya ya fara wanda ya kasance mafi tsanani lokaci ga ƴan shi'a.[8] ƴan shi'a sun faɗa cikin mummunan tsanani a lokaci mulkin Mu'awiya, Ibn Abil Al-hadid ya naƙalto cewa duk inda ƴan shi'a suka samu kansu ko dai su fuskanci kisa ko kuma a yayyanke musu ƙafafuwa ko kwace musu dukiya da jefa su cikin gidan kurkuku.[9]
A daran 21 ga ramadan wanda ake tsammanin kasancewarsa daren lailatul ƙadri[10] ƴan shi'a suna zaman makokin domin tunawa da shahadar Imam Ali (A.S)[11] wasu sassan yankuna cikin ƙasar Iran ana shirya ta'aziyya wacce ake kira da tga'aziyyar ƙanbar da Sayyidina Ali (A.S)[12] haka nan ba'arin ƴan shi'a a wannan dare suna raba bakance da abincin buɗa baki da sahur,[13] maimaita zikirin «اللّهمَّ العَن قَتلَةَ اَميرالمُومِنين» ma'ana (Allahumma Il'an Ƙatalata Amirul Muminin) yana daga cikin ayyukan cikin wannan dare.[14]
Shin Imam Ali yana da Labarin Shahadarsa?
- Asalin Maƙala: Tsinkayen Imamai Game da Shahadarsu
Bisa dogara da ba'arin riwayoyi, haƙiƙa Imam Ali (A.S) yana da labari game da yaya zai yi shahada, misalin a cikin wanne lokaci ne da kuma yaya zata kasance duka yana da labari.[15] cikin littafin Al-Kafi ɗaya daga Kutubul Arba'a na shi'a, akwai wani sashe ɗauke da taken “Imamai suna da labarin wanne lokaci ne za su mutu”[16] Shaik Mufid, Allama Hilli da Sayyid Murtada suma sun yi rubutu game da mas'ala,[17] a cewar Shaik Mufid (wafati:413.ƙ) Masanin Kalam a shi'a ya bayyana cewa riwayoyin da suka zo game da wannan mas'ala riwayoyi ne mutawatirai.[18] cikin amsa kan wannan mas'ala ta cewa: idan har Imamai suna da labari kan zamanin da za su shahada to menene ya sanya basu kare kansu ba, lallai akwai tsammani biyu cikin hakan:
- Me yiwuwa suna da labari ne a dunkule game da shahadarsu da makasansu da lokacin duka a bawai filla-filla a faifaice ba.
- Idan suna da labari filla-filla game da shahadarsu, ta yi wu taklifinsu ya kasance su yi haƙuri kan haka.[19]
Sayyid Murtada (wafati:436.ƙ) wanda shi ma ya kasance daga malaman kalam na shi'a shima ya yi bayani game da ta yaya Imam Ali (A.S) ya kasance yana da labari game da shahadarsa da makasansa; sai dai cewa bai kasance yana san a wanne lokaci ne zai yi shahadar ba; saboda idna ya zama ya sani to dole ne ya kare kansa daga kisa.[20]
A cewar marubucin ƙasidar “Tsinkayen Imam kan shahadarsa da shubuhar rashin dacewar hakan tare da Isma” haƙiƙa Imamai cikin wuraren da suka miƙa kansu ga shahada yin hakan baya cin karo da hukunci kare rai, a ra'ayin marubucin iliminsu da tsinkayensu kan shahadarsu bai samu ta hanyar da aka saba da ita ba, da wannan dalili ne ma misalin wannan ilimi da tsinkaye tana iya yi wuwa babu taklifi cikinsa, idan ma mun ƙaddara yana da taklifi, tana iya yi wuwa Imamai domin kiyaye farin cikin da zaman lafiyar al'umma su kasance a irin wannan hali an keɓance su da taklifi na musammam,[21] an naƙalto daga Imam Rida (A.S) cewa a darewn 19 ga watan Ramadan haƙiƙa Imam Ali (A.S) ya miƙa wuya ga ƙaddarar Allah,[22] Mulla Salihu Mazandarani daga masu sharhi kan littafin Usulul Al-Kafi cikin sharhin wannan gaɓa daga zancen Imam Rida (A.S) game da Amirul Muminin (A.S):
an bashi zaɓi daga zama ko haɗuwa da Allah, sai ya zaɓi haɗuwa da Allah domin ƙaddarar Allah ta'ala ta gudana. Ya rubuta cewa Imam Ali Ali (A.S) a cikin daren 19 ga ramadan ya zaɓi saduwa da Allah domin tabbatar da ƙaddarar Allah, idan wannan lamari ya kasance ƙarƙashin umarnin Allah kuma tare da yardarsa to bawai kaɗai halal bane bari dai ya kasance wajibi, kamar dai yadda Imam Husaini (A.S) ya yi, mu ma a lokacin Jihadi haka muke yi tare da mun san babu komai ciki sai miƙa wuya ga mutuwa.[23]
Rawar da ƙaɗɗam ta Taka a Shahadar Imam Ali (A.S)
Kan asasin rahotannin tarihi, ƙaɗɗam ɗiyar Shajana ta bada gudummawa cikin shahadantar da Imam Ali (A.S) lokacin da Ibn Muljam ya nemi aurenta ta sanya masa sharaɗi cewa zai bata sadaki dirhami dubu ɗaya, baiwa guda ɗaya, bawa ɗaya da kuma kashe Imam Ali (A.S)[24] sai Ibn Muljam (L.A) ya karɓi wannan sharuɗɗa ya aureta.[25] mahaifi da ƴan'uwan[26] ƙaɗɗam duka sun kasance daga Khawarijawa[27] da aka kashe su a lokacin yaƙin Naharawan.
A lokacin taron aikin hajji shekara 39 bayan hijira an samu saɓanin tsakanin wakilan Imam Ali (A.S) da wakilan Mu'awiya. Bayan kammala aikin hajji wasu jama'a daga Khawarijawa sun taru a garin Makka sun bayyana cewa waɗannan mutane basu kiyaye alfarmar Ka'aba ba,[28] sannan suka tunano irin kisan da aka yi musu a lokacin yaƙin naharawan,[29] daga ƙarshe dai suka zaɓi mutane uku daga cikinsu Ibn Muljam (L.A) ya ɗau alƙawarin kashe Imam Ali (A.S), ɗaya ya yi rantsuwa kan kashe Mu'awiya na karshensu kuma ya ɗauki nauyin kashe Amru ɗan Asi,[30] a ranar 20 ga watan sha'aban Ibn Muljam ya shiga garin Kufa,[31] a nan ne ya haɗu da ƙaɗɗam suka san juna.[32]
Saran da Aka yi wa Imam Ali (A.S)
A daren 19 ga watan ramadan Imam Ali (A.S) ya tafi gidan ɗiyarsa Ummu Kulsum[33] Malam Jafariyan ɗan shi'a masanin tarihi ya naƙalto cewa akwai tarin riwayoyi daga Ahlul-Baiti (A.S) da ma Ahlus-sunna da suke labarta keɓantaccen halin da Imam Ali (A.S) ya samu kansa a wannan dare daga ma'anawiyya,[34] bisa naƙalin Ibn Asir malamin tarihi daga Ahlus-sunna cikin littafin Al-Kamil[35] da kuma riwayar littafin Al-kafi[36] haƙiƙa a daren da aka sari kan Imam yayin da Imam yake halin fitowa daga gida an samu wasu agwagi sun tare gabansa lokacin da suka ƙi bada hanya ya wuce sai yace ku kyale su suna kukan baƙin ciki ne da juyayi ne, Allama majlisi ya tai kan raunana wannan riwaya ta cikin littafin Al-kafi.[37]
Bisa naƙalin Allama Majlisi cikin littafin Biharul Al-anwar, Imam Ali (A.S) ya tafi masallaci kuma shi da kansa ne ya yi kiran sallah[38] sannan ya tayar da mutane da suke bacci cikin masallaci, hatta Ibn Muljam da yake kwance ruf da ciki wanda aka yi hani kansa a shari'a shima Imam ya tashe shi ya yi sallah[39] bayan nan sai ya tafi ya tsaya wurin sallarsa, lokacin da Imam yake sujjada[40] ko kuma yana ɗagowa daga sujjada,[41] sai Ibn Muljam ya zare takobi ya sara masa a ka,[42] kan asasin ba'arin riwayoyi an bayyana cewa an sare shi lokacin da yake halin shiga masallaci[43] Ibn Muljam,[44] Shabibu ɗan Bajara Ashja'i da Wardanu,[45] sun kasance suna tare da shi, bayan Ibn Muljam ya sari Imam sai yace: Hukunci na Allah ne ba naka bane ko na yaranka,[46] akwai riwaya da take bayyana cewa bayan saran Imam Ali (A.S) Jibrilu ya yi rantsuwa cewa lallai tabbas turakun shiriya sun ruguje, kuma taurarin sama da alamomin taƙawa sun dushe sun ɓace.[47] sai dai cewa babu wannan riwaya a madogaran da suka gabata, kaɗai ana samunta ne cikin madogarai da suka zo daga baya.[48][Tsokaci 1]
- Ku duba: Daren Saran Imam Ali (A.S)
Fuztu Wa Rabbil Ka'aba
- Asalin Maƙala: Fuztu Wa Rabbil Ka'aba
Kan asasin rahotan Ibn ƙutaiba Dinuri malamin tarihi a ƙarni na uku bayan hijira, haƙiƙa Imam Ali (A.S) saransa da aka yi ya furta kalmar “Fuztu wa Rabbil Ka'aba) ina rantsuwa da ubangijin ɗakin ka'aba tabbas na rabauta,[49] malaman shi'a misalin Sayyid Radiyyu[50] Ibn Shahre Ashub[51] sannan daga malaman Ahlus-sunna akwai misalin Ibn Asir[52] Balazri[53] sun naƙalto wannan magana.
A cewar Ibn Abil Al-hadid, bayan saran Imam an tara likitocin kufa domin yi masa magani[54] Asiru ɗan Amru bayan ya gama duba mikin da yake kan Imam ya gano cewa saran da aka yi masa ya gangara kwakwalwa, don haka ne ma yace Imam ya yi duk wasiyyar da zai yi saboda ba zai jima a raye ba.[55] Wasiyyoyin Imam Bayan Saransa da Aka yi.
Wasiyyar Imam Bayan Saransa
An naƙalto bayan saransa ya ɗau lokaci baya cikin hayyaci,[56] ya kasance yana yin sallah a tsugune sannan ya gayawa ƴaƴansa wasiyyarsa,[57] akwai keɓantacciyar wasiyyarsa zuwa ga ɗansa Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) wacce aka naƙalto a littafin Nahjul Al-Balaga[58] cikin bayaninsa ya bijiro da batun mutuwa[59] a ranar 21 ga watan ramadan ne shekara 40 bayan hijira ya yi shahada[60] ba'arin masadir sun ambaci wani zamani daban game da shahadarsa.[61]
Wasiyyarsa Game da Hukuncin ƙisasi kan Ibn Muljam
Imam Ali (A.S) ya yi wasiyya da cewa ayi Sara guda ɗaya kan wuyan Ibn Muljam[62] idan wannan sara ya kashe shi to kada a yi musla kan gawarsa,[63] kan asasin ba'arin masadir an naƙalto cewa Imam ya bada umarni da a kiyae baiwa Ibn Muljma abin ci da ruwa da kuma kyautata mu'amala da shi,[64] na'am a wasu masadir ɗin an naƙalto cewa bayan zartar da ƙisasi kan Ibn Muljma da Imam Hassan (A.S) ya yi.[65] mutane sun ƙona gawarsa[66] haka nan wasu masadir sun yi nuni da yin musla kan gawar Ibn Muljam.[67]
Rakiyar Jana'iza da Binne Imam
Imam Hassan (A.S), Imam Husaini (A.S), Muhammad Hanafiyya da Abdullahi ɗan jafar su ne suka yi masa wankan gawa,[68] bayan nan Imam Hassan (A.S) ya yi masa sallah,[69] aka binne shi cikin dare, sai dai cewa an shirya ƙaburbura a wurare daban-daban domin ɓoye kabarinsa,[70] da kuma hana tone shgi daga maƙiya daga Khawarijawa[71] da maƙiyansa Bani Umayya[72] wasu ƴan tsiraru kaɗai daga ƴan shi'a ne kaɗai suka san haƙiƙanin inda aka binne shi a wancan lokaci, har zuwa zamanin gwamnatin Bani Abbbas, bayan Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyanar da Kabarin,[73] haƙiƙa kabarin Imam Ali (A.S) ya kasance a birnin najaf, wannan kabari an ambace shi da sunaye daban-daban cikin madogaran tarihi[74] wanda ƴan shi'a sun yi ittifaƙi kansu.[75]
Nazari
• Maƙtalu Al-Imam Amirul Muminin Ali bin Abi ɗalib, littafin ne da harshen larabci wanda Ibn Abil dunya (wafati 281:ƙ) ya rubuta shi ɗaya ne daga Malaman hadisi na Ahlus-sunna.[76] cikin wannan littafi ya kawo labarurruka game da shahadar Imam Ali (A.S).[77] • Shahidu Tanha(Maƙtalu Amirul Muminin Ali Alaihi Salam) wanda Sayyid Muhammad Rida Muɗlaƙ ya rubutu.[78]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Kathir, al-Bidaiya wa al-Nihaiya, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 130.
- ↑ Ibn Kathir, al-Bidaiya wa al-Nihaiya, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 323.
- ↑ Jafar, hayatu Siyasi wa fikri Imaman Shi'a, 2008, shafi na 53-54.
- ↑ Jafar, hayatu Siyasi wa fikri Imaman Shi'a, 2008, shafi na 110
- ↑ Nahj al-Balaghah, 1414 AH, shafi na 264.
- ↑ Nasiri Razi, Tarikh tahlili Sadre Islam, 1384, shafi na 191.
- ↑ Sobhani, Al-Shia fi Maukib al-Tarikh, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 22.
- ↑ Nasiri Razi, Tariikh Tahlili Sadr Islam, 1384, shafi na 135.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharhi Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 11, shafi na 43.
- ↑ Majlesi, Mir'ah al-Aqol, 1404 AH, juzu'i na 16, shafi 381.
- ↑ Majidi Khamene, "Shabhaye Kadre dar Iran", shafi na 19.
- ↑ Majidi Khamene, "Shabhaye Kadre dar Iran", shafi na 20.
- ↑ Majidi Khamene, "Shabhaye Kadre dar Iran", shafi na 21.
- ↑ Qomi, Mufatih al-Janan, Aswah, shafi na 226.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 530.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 258-260.
- ↑ Duba Rabbani Golpaygani wa Rahmanizadeh, "Ilim Imam be Shahadat wa shubuhe nasazigare ba Ismat", shafi na 105.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 319.
- ↑ Sheikh Mufid, al-Masa'il al-Akbariya, 1413 AH, shafi na 69-72.
- ↑ Seyed Mortaza, Rasaila al-Sharif al-Mortaza, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 131. ↑
- ↑ Rabbani Golpayegani wa Rahmanizadeh, "Ilim Imam beh Shahadat wa shubuhe nasazigare ba Ismat", shafi na 111.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 259.
- ↑ Mazandarani, Sharh Usul Kafi,Publisher: Islamic Library, juzu'i na 6, shafi na 37.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 18-19
- ↑ Ibn Qutaiba, Al- Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 180.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 18.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 180.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 179.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 113.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1409 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 607.
- ↑ Yaqoubi, Tarikh Eliaqoubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 212.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 18.
- ↑ Hosseini Mutlaq, Shahid Tanha, 1386 AH, shafi 114
- ↑ Jafarian,Hayatu Fikri wa Siyasi Imamane Shi'a, 2013, shafi na 111.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 388
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 259.
- ↑ Majlisi, Mir'ah al-Aqool, 1404 AH, juzu'i na 3, shafi na 122.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 281.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 281.
- ↑ Sheikh Tusi, Amali, 1414H, shafi na 365.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 281.
- ↑ Ibn Atham Kufi, al-Futuh, juzu'i na 4, shafi na 278.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 AH, juzu'i na 5, shafi 145.
- ↑ Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, 1418 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 25-28
- ↑ Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408, Juzu'i na 2, shafi na 646.
- ↑ Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408, Juzu'i na 2, shafi na 646.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 282.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 282.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 180.
- ↑ Sayyid Razi Khasa'is Imamai, 1406H, shafi na 63.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 119.
- ↑ Ibn Athir, Usud al-Ghabah, 1409H, juzu'i na 3, shafi na 618.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 488.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 119.
- ↑ Madani Shirazi, aldaraz al-Awwal, 2004, juzu'i na 7, shafi na 14.>
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 289.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 290.
- ↑ Nahj al-Balaghah, 1414 AH, shafi na 421-422.
- ↑ Nahj al-Balaghah, 1414 AH, hadisi na 149, shafi na 207.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1428H, juzu'i na 1, shafi na 9.
- ↑ Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408, Juzu'i na 2, shafi na 645.
- ↑ Moghdisi, Al-bad'u wa al-Tarikh, Bursa'id, juzu'i na 5, shafi na 233.
- ↑ Nahj al-Balaghah, 1414 AH, shafi 422.
- ↑ Fatal Nishaburi, Rauzatu Al-Waezin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 137.
- ↑ Khazaz Razi, Kefayat Athar, 1401 AH, shafi 162.
- ↑ Khazaz Razi, Kefayat Athar, 1401 AH, shafi 162.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 181.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 181.
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 181.
- ↑ Qaidan, Atbat Aliya Iraq, 1383, juzu'i na 1, shafi na 30
- ↑ Ibn Qutaiba, Al-Imama wa Al-Siyasah, 1410H, Juzu'i na 1, shafi na 181.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 10.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1410 AH, juzu'i na 42, shafi na 338.
- ↑ Qaidan, Atbat Aliya Iraq, 1383, juzu'i na 1, shafi na 32.
- ↑ Ibn Abi al-Duniya, Maqtale Amirul Muminin (AS), 1379, shafi na 12-23.
- ↑ Ibn Abi al-Duniya, Maqtale Amirul Muminin (AS), 1379, shafi na 12-23.
- ↑ Ibn Abi al-Duniya, Maqtale Amirul Muminin (AS), 1379, shafi na 23.
- ↑ «مقتل علی (ع): شهید تنها»، خانه کتاب و ادبیات ایران.
Tsokaci
- ↑ Wallahi an ruguza ginshikan shiriya, kuma wallahi Taurarin sama da ayoyin Taqawa sun shafe. Kuma wallahi karfaffiyar ta karye, An kashe dan uwan Muhammad Al-Mustafa, an kashe wasiyyi Al-Mujtaba. An kashe Ali Al-Murtada, wallahi an kashe shugaban wasiyyai, mafi tsiyatar matsiyatav ne ya kashe shi.
Nassoshi
- Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarikh al-Islam, bincike: Omar Abdus Salam Tadmari, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na biyu, 1409H.
- Fatal Nishabouri, Muhammad bin Ahmad, Rawda al-Waaziin da Basira al-Mutaezin, Kum, Razi Publications, bugun farko, 1375.
- Ibn Abi al-Daniya, Abdullah, Maktal Ali, Mahdavi Damghani ya fassara, Mashhad, Tasu'a, 1379.
- Ibn Abi al-Duniya, Abdullah, Maqtale Amir al-Muminin, Qum, Dandalin Farfado da Al'adun Musulunci, 1411H.
- Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Heba Allah, Sharh Nahj al-Balaghah, gyara: Muhammad Abul Fazl Ibrahim, Kum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, bugu na farko, 1404H.
- Ibn Atham Kufi, Ahmad Ibn Atham, al-Futuh, bincike: Ali Shiri, Beirut, Darul-Azwa, 1411H.
- Ibn Athir, Ali bin Muhammad, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir, 2005.
- Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, al-Bidaya wa al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
- Ibn Khaldun, Abd al-Rahman bin Muhammad, Tarikh Ibn Khaldun (Diwan al-Mubatada da al-Khobar), bincike: Khalil Shahada, Beirut, Dar al-Fikr, bugu na biyu, 1408H.
- Ibn Qutaiba, Abdullahi bin Muslim, Al-Imamah wa Al-Siyasah, bincike: Ali Shiri, Beirut, Darul Awtah, bugun farko, 1410H.
- Jafar, Rasulu, Ilimi da Siyasa na Imaman Shi'a, Qum, Ansari, 2001.
- Khazaz Razi, Ali bin Muhammad, Kifaytul Asar, mai bincike kuma mai bincike: Abdul Latif Hosseini Kohkamari, Qom, Bidar, 1401H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, mai bincike kuma mai karantawa: Ali Akbar Ghafari, Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
- Madani Shirazi, Ali Khan bin Ahmed, al-taraz al-Awwal da al-Kanaz al-Lama al-Ali Man linghi al-Arab al-Maawl, Mashhad, Al-Al-Bait Foundation for Revival of Tradition, first edition, 1384.
- Majidi Khamene, Farideh, "Shabhaye Qadr dar Iran", Mujallar Golestan Qur'an, No. 37, Disamba 1379.
- Majlesi, Mohammad Baqir, Mir'ah al-Aqool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, mai bincike kuma mai karantawa: Seyed Hashim Rasouli, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islami, bugu na biyu, 1404H.
- Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Tabb da Al-Nashar Est., bugun farko, 1410H.
- Moghadsi, Motaher bin Taher, al-]bad'u wa al-Tarikh, Makarantar Al'adu Al-Diniya, Bur Saeed, Bita.
- Nahj al-Balaghah, bincike: Sobhi Saleh, Kum, Hijira, bugun farko, 1414H.
- Nasiri Razi, Muhammad, Tarikh Tahlil, Qum, Maarif Publishing House, 2004.
- Qomi, Abbas, Mofatih al-Jannan, Kum, Aswah, Bita.
- Sayyid Mortaza, Ali bin Hossein, Rasaila al-Sharif al-Mortaza, Mehdi Rajaei da Ahmad Hosseini Ashkuri, Kum Darul Qur'an al-Karim, 1415H.
- Sheikh Mofid, Al-Arshad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, Qum, Sheikh Mofid Congress, bugu na farko, 1413 AH.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Masail al-Akbariya, Ali Akbar Elahi Khorasani, Kum, Al-Khangir al-Alami na Alfiya Al-Shaykh Al-Mofid, 1413H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, al-Amali, Kum, Darul Taqwa, bugun farko, 1414H.
- Sobhani, Ja'afar, Al-Shi'a fi Maukab al-Tarikh, Qum, mataimakin shugaban harkokin ilimi da bincike, 1413H.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Tabari's (History of the Nations and Al-Muluk), bincike: Muhammad Abolfazl Ebrahim, Beirut, Dar al-Tarath, bugu na biyu, 1387H.
- Yaqoubi, Ahmad bin Abi Yaqoob, Tarikh Al-Yaqoubi, Beirut, Dar Sadir, bugun farko, BTA.
- «علی آن شیر خدا شاه عرب»، سایت حوزه نت، تاریخ بازدید:۲۶ آذر ۱۴۰۲ش.
- «مقتل علی (ع): شهید تنها»، خانه کتاب و ادبیات ایران، تاریخ بازدید: ۳ دی ۱۴۰۲ش.
- ربانی گلپایگانی، علی و محسن رحمانیزاده، «علم امام به شهادت و شبهه ناسازگاری آن با عصمت»، در مجله کلام اسلامی، شماره ۱۱۰، تیر ۱۳۹۸ش.