Annabawa

Daga wikishia
wannan wata ƙasida ce da aka yi ta dangane da adadin annabawa, mu'ujiza, muƙami da shari'ar da aka aiko musu. Domin sanin sauran bahasosi da suke da dangantaka da annabta ku duba: annabta

Annabawa wasu mutane ne waɗanda ta hanyarsu ne Allah yake kiran mutane zuwa gare shi, Allah ya na alaƙa da annabawansa ta hanyar wahayi.

Isma, tsinkaye kan ilimin gaibu, mu'ujiza, karɓar wahayi (Wahayin shari'a da wahayin bayani) suna daga cikin siffofin annabawa. Cikin kur'ani an ambaci wasu ba'arin mu'ujizojin annabawa misalin sanyayar wuta ga annabi ibrahim (a.s) canja sandar musa zuwa ga macizai, raya matattu ta hannun annabi isa (a.s), kur'ani mai girma da tsaga wata da ta faru ta hannun annabin muslunci (s.a.w).

Kur'ani ya tabbatar da fifitar ba'arin annabawa kan wasu ba'ari, wasu annabawa ƙari kan muƙamin annabta sun kasance manzanni ma'abota shari'a, wasu kuma sun kasance tare da muƙamin imamanci. Kan asasin abin da ya zo daga riwayoyi haƙiƙa annabawa ulul azmi ma'ana annabi nuhu (a.s), annabi ibrahim (a.s), annabi musa (a.s), annabi isa (a.s) da annabi muhammad (s.a.w) sun fifita kan dukkanin annabawa, sannan kuma shi annabi muhammad (s.a.w) yana da fifiko kan bakiɗayan annabawa. Haka nan cikin annabawa, annabi shisu (a.s), annabi idrisu (a.s), annabi musa (a.s) annabi isa (a.s) annabi muhammad (s.a.w) annabawa ne da suke aka saukar musu da littafi daga sama, haka zalika annabawa ulul azmi suma annabawa ne da aka saukar musu da shari'a.

Kan asasin mahangar mashhur ɗin malaman muslunci, adadin annabawa ya kai dubu ɗari da ashirin da huɗu. Sunayen annabawa 26 ne ya zo cikin kur'ani, annabi adam (a.s) shi ne annabi na farko, sannan annabi muhammad (s.a.w) shi ne annabi na ƙarshe da babu wani annabi da zai zo a bayansa. Malaman shi'a sun yi rubuce-rubuce dangane da tarihin annabawa, tare da wallafa litattafai masu zaman kansu kan wannan maudu'i. An-nurul mubin fi ƙisasul al-anbiya'i wal-mursalina, na sayyid ni'imatullahi jaza'iri, ƙisasul al-anbiya'i na rawandi, tanzihul al-anbiya'i na sayyid murtada da hayatul al-ƙulubi na allama majlisi, suna daga cikin litattafai da aka wallafa game da tarihin rayuwar annabawa.

Annabawa

Tushen ƙasida: Annbata

Annabi shi ne mutumin da yake samun saƙo daga Allah ba tare da tsanantuwa da wani mutum ba.[1] shi annabi shi ne tsani na kasancewa tsakanin Allah da halittunsa, kuma shi ne wanda yake kiran halittu zuwa ga Allah.[2]

Karɓar saƙon wahayi, ilimin gaibu,[3] da isma,[4] samun amsa addu'a[5] suna daga cikin siffofin annabawa, galibin malaman kalam na muslunci sun yi amanna da cewa su annabawa mutane ne ma'asumai katangaggu daga aikata duk wani nau'in zunubi a cikin bakiɗayan marhalolin rayuwarsu,[6] da wannan dalili wurare daga kur'ani da maganar istigfari da gafarar Allah kan wasu annabawa ta zo kan wani aiki da suka aikata,[7] misalin kisan bamisre da annabi musa (a.s) ya yi,[8] aje saƙo da annabi yunus (a.s),[9] ya yi, da cin ɗan itaciya da annabi adam (a.s) ya yi bayan an hana shi ci,[10] malamai sun fassara wannan ayyuka da tarkul aula (barin aikata abin da yafi dacewa ace an aikata) kishiyar wannan magana, wasu ba'arin malaman kalam, suna ganin cewa annabawa ma'asumai kaɗai cikin abubuwan da suke da alaƙa da dangantaka da annabtarsu, amma cikin fagen rayuwar ta bil'adama ta yau da kullum lallai suna iya aikata kuskure da rafkana.[11]

Sunayen Annabawa Da Adadinsu

Dangane da adadin annabawa akwai riwayoyi daban-daban, allama ɗabaɗaba'i bisa dogara da shahararriyar riwaya ya naƙalto cewa adadin annabawa ya kai dubu ɗari da ashirin da huɗu,[12] kan asasin wannan riwaya annabawa 313 sun kasance manzanni, sannan kuma 600 sun kasance annabawan da aka aiko ga bani isra'il, huɗu daga cikinsu watau annabi hudu (a.s), annabi salihu (a.s), annabi shu'aibu (a.s) da annabi muhammad (s.a.w) sun kasance daga larabawa,[13] cikin wata riwaya an ambaci cewa adadin annabawa mutum dubu takwas,[14] wata kuma ɗari uku ashirin,[15] a wani ƙaulin kuma an ambaci dubu ɗari da arba'in da huɗu.[16] allama majlisi yana tsammani adadin dubu takwas yana da alaƙa ne manyan annabawa,[17] na farkonsu annabi adam (a.s),[18] na ƙarshensu kuma shi ne annabi muhammad.[19]

Kur'ani ya kawo sunayen ba'arin annabawa,[20] adam (a.s), nuhu (as.) idrisu (a.s), hudu (a.s), salihu (a.s), ibrahim (a.s) luɗ (a.s), isma'il (a.s), alyasa'u (a.s), zul kifili (a.s) ilyasu (a.s), yunus (a.s) is'haƙ (a.s), yaƙub (a.s), yusuf (a.s), shu'aibu (a.s), musa (a.s) haruna (a.s), dawud (a.s), sulaiman (a.s), ayyub (a.s), zakariyya (a.s), yahaya (a.s), isa (a.s) da muhammad (s.a.w) annabawa ne da sunayensu ya zo cikin kur'ani.[21] ba'arin malaman tafsiri sun yi amanna kan cewa sunan isma'il ɗan hizƙilu. [Tsokaci 1]. shima ya zo a cikin kur'ani.[22]

Wasu ba'ari sun tafi kan cewa haƙiƙa kur'ani ya ambaci ba'arin siffofin wasu annabawa misalin armaya'u (a.s) da shamu'il (a.s), sai dai cewa bai ambaci sunayensu ba.[23] a cikin kur'ani akwai sura sukutun ɗauke da sunan suratul anbiya da wasu adadin surori ɗauke da sunan yunus, hudu, yusuf, ibrahim, muhammad da nuhu.

Cikin riwayoyi an kawo sunayen wasu annabawa daga shisu,[24] hizƙilu,[25] habaƙuƙ,[26] daniyal,[27] jirjisu,[28] Uzairu,[29] hanzalatu,[30] armaya'u,[31] akwai saɓani cikin annabawa akwai mutane misalin khidir,[32] khalid ɗan sinan,[33] zul ƙarnaini,[34] a cewar allama ɗabaɗaba'i Uzairu yana cikin mutane da babu cikakken bayani kan kasancewarsa annabi.[35] kan asasin bayanan kur'an, ba'arin annabawa sun rayu tare a zamani ɗaya; daga jumlarsu musa da [[Haruna (A.S)|haruna][36] ibrahim da luɗ[37] duka sun kasance a zamani ɗaya. Haka nan a rahotannin ba'arin riwayoyi za a fahimci cewa wasu annabawa sun rayu tare a zamani ɗaya, alal misali sayyid bin ɗawus cikin littafin Alluhuf ya naƙalto riwaya daga imam hassan (a.s) lokacin da yake niyyar fita daga garin makka zuwa kufa daidai lokacin da yake magana da abdullahi ɗan umar ya ce: shin ka san cewa bani isra'il ya kai ga cewa daga hudowar rana zuwa faɗuwarta suna kashe annabawa ɗaiɗai har guda saba'in, sannan suna cigaba da harkon rayuwarsu ba tare da jin sun aikata wani abu mai mugun muni ba; kai kace babu wani mummunan abu da ya faru?!.[38] a wata riwaya a d ata zo a littafin majma'ul al-bayan an naƙalto daga annabi (s.a.w) ya cewa abu ubaida jarra: ya abu ubaida! Bani isra'ila cikin yini guda sun kasance suna kashe annabawa ɗaidai har guda 43 a lokaci ɗaya, bayan nan sai aka samu adadin mutane guda 112 sun miƙe gaban makasan annabawa domin umarni da kyakkyawa da hani da munkari, sai dai cewa suma waɗannan bayin Allah ba su tsira ba daga ƙarshe su ma kashe su suka yi.[39]


Annabawa A Cikin Kur'ani
Suna Maimaituwa Zamani Annabi Manzo Ulul Azmi Imami Littafi Mutane Kabari Ma'abocin Shari'a
Adam 17 Adam Majaf wurin kabarin amirul Muminin (A.S)
Idris 2 Enoch Annabi[40] An kaishi sama[41]
Nuhu 43 Noah Annabi[42] Manzo[43] Ulul azmi Najaf wurin kabarin amirul muminin Na'am
Hudu 7[44] Eber Manzo[45] Adawa[46] Najaf wadi salam
Salihu 9 Manzo[47] Samudawa[48] Najaf wadi salam
Ibrahim 69 Abraham Annabi[49] Manzo[50] Ulul azmi Imami[51] Suhuf[52] Khalil (Palasɗin) Na'am[53]
Luɗ 27 Lot Annabi[54] Manzo[55] Khalil (Palasɗin)
Isma'il 11 Ishamael Annabi[56] Masallacin harami/hijri isma'il kusa da kabarin hajara mahaifiyarsa
Uzairu 1[57] Bani isra'il Palasɗin
Is'haƙ 17 Isaac Annabi[58] Imami[59] Khalil (Palasɗin)
Yaƙub 16 Jacob Annabi[60] Imami[61] Jami'u khalil (Palasɗin)
Yusuf 27 Joseph Annabi[62] Bani isra'il Jami'u khalil (Palasɗin)
Ayyub 4 Job Annabi[63] Huran
Shu'aibu 11 Jethro, Reuel, Hobab Manzo[64] Madyana[65] Baitul muƙaddas
Musa 136 Moses Annabi[66] Manzo[67] Ulul azmi Attaura[68] Fir'aunonin bani isra'il Gefanbaitul muƙaddas
Haruna 19 Aaron Annabi[69] Manzo[70] Fir'aunonin bani isra'il[71] Gefan ɗuru sina
Zulƙiflu 2 Ezekiel Tsakanin garin kufa da hilla
Dawud 16 David Annabi[72] Manzo[73] Zabura[74] Baitul muƙaddas
Sulaiman 17 Solomon Annabi[75] Baitul muƙaddas
Ilyas 2 Elijah Annabi[76] Manzo[77] An kaishi sama
Alyasa'u 2 Elisha Annabi[78] Damshƙ
Yunus Jonah Annabi[79] Manzo[80] Kufa
Zakariyya 7 Zechariah Annabi[81] Baitul muƙaddas
Yahaya 5 John the baptist Annabi[82] Masallacin bani umayya damashƙ
Isa 25 Jesus Annabi[83] Manzo[84] Ulul azmi Imami Linjila[85] Bani isra'il[86] An kaishi sama Na'am[87]
Muhammad 4 Annabi[88] Manzo[89] Ulul azmi Imami Kur'ani[90] Bakiɗayan mutane Madina Na'am[91]

Darajoji Da Martabobi

Kan asasin ayar (وَلَقَدْ فَضَّلْنَا بَعْضَ النَّبِيِّينَ عَلَىٰ بَعْضٍ) (haƙiƙa mun fifita ba'arin annabawa kan ba'ari)[92] ta bayyana cewa muƙami da matsayin annabawa bai kasance bai ɗaya ba, wasu ba'arin daga cikinsu sun fifita kan ba'ari, cikin hadisai ya zo cewa muƙamin annabi akram (s.a.w) ya fifita daga na sauran annabawa.[93] [Tsokaci 2] a aƙidar yahudawa annabawan bani isra'il suna da fifiko kan sauran annabawa, sannan kuma annabi musa (a.s) yana da fifiko kan annabawan bani isra'il.[94]

Ulul Azmi

Tushen ƙasida: Ulul Azmi

A cewar allama ɗabaɗaba'i abin da ake nufi da azmi a cikin aya ta 35 suratul ahƙaf, shi ne shari'a, sannan abin da ake nufi daga ulul azmi annabawa ma'abota shari'a. A ra'ayin malamin annabawan da aka basu shari'a sune nuhu (a.s), ibrahim (a.s), musa (a.s) isa (a.s) da muhammad (s.a.w) su ne dai ake kira da ulul azmi[95] wasu malamai sun tafi kan cewa ulul azmi bai kaɗaita cikin annabawan da aka basu shari'a ba..[96]] kan asasin wata riwaya, annabawa ulul azmi suna da fifiko kan sauran annabawa.[97]

Muƙamin Risala

Kan dogara da magana mashhur ɗin malama, "Nabiyyu" wata ma'ana ce gamammiya daga "Rasul" kowanne rasul (Manzo) annabi ne amma ba kowanne annabi ne manzo ba.[98] kan asasin wani hadisi, annabawa 313 sun kasance manzanni.[99] ba'arin bambance-bambance tsakanin annabi da manzo sun kasance kamar haka:

  • Manzo ana masa wahayi cikin mafarki da faɗake, amma shi annabi kaɗai cikin mafarki yake samun wahayi.[100]
  • Manzo shi ne wanda aka bawa shari'a kuma shi ne wanda yake sanya hukunce-hukunce, amma shi annabi yana gadi da kulawa ne da shari'ar wani annabin daban. ɗabarsi ya danganta wannan magana zuwa ga jahiz.[103] na'am ba'arin malaman tafsiri misalin ɗabarsi, suna ganin nabiyyu da rasul lafuzza guda biyu masu ma'anoni biyu makusantan juna.[104]

Annabawan Shari'a Da Annabawan Isar Da Saƙo

Kan asasin wani tsarin rarrabawa annabawa sun rabu gida biyu, annabawan shari'a da kuma annabawa masu isar da saƙon shari'a.[105] wazifar da take wuyan annabawan isar da saƙo, shi ne yaɗa saƙo da tabligi, zartarwa da kuma tafsiri da bayanin shari'a da kasance zamanin wannan annabi, saɓanin annabawan shari'a, misalin nuhu, ibrahim, musa da isa[106] da su kansu an aiko musu da shari'a[107]] sun zo da sabon addini, adadin nau'in waɗannan annabawa ƴan kaɗan ne.[108]

Muƙamin Imamanci

Kan asasin ayar ibtila'in ibrahim, ba'arin annabawa da sum kasance tare da muƙamin imamanci,[109] cikin ba'arin riwayoyi muƙamin imamanci ya fifita kan muƙamin annabta, saboda wanann muƙami an baiwa ibrahim (a.s)shi ne a ƙarshen rayuwarsa bayan aiko shi annabi.[110]. [Tsokaci 3] cikin suratul anbiya annabi ibrahim (a.s), annabi is'haƙ (a.s), annabi yaƙub (a.s) da annabi luɗ (a.s) an gabatar da su matsayin imamai[111] a cikin wani hadisi daga imam sadiƙ (a.s), bakiɗayan annabawa ulul azmi sun kasance tare da muƙamin ulul azmi.[112]

Fifikonsu Kan Mala'iku

A cewar shaik mufid, imamiyya da ahlul-hadis daga ahlus-sunna suna ganin fifikon muƙamin annabawa kan mala'iku, sai dai kuma galibin mu'utazilawa daga ahlus-sunna sun yi imani da fifikon mala'iku kan annabawa.[113] cikin ba'ari daga hadisai haƙiƙa muƙamin annabin muslunci (s.a.w) da muƙamin imamai goma sha biyu ya fifita kan mala'iku.[114]

Annabawan Ma'abota Littafi

Adadin annabawa da aka saukar musu littafi daga sama; bisa dogara abin da ya zo a ayoyin kur'ani, zabura ita ce littafin annabi dawud (a.s) attaura annabi musa (a.s). [Tsokaci 4]. linjila (bible) annabi isa (a.s)[115]kur'ani kuma annabi muhammad (s.a.w), kur'ani littafi bai ambaci littafin da aka saukarwa annabi ibrahim (a.s) ba, sai dai ya ambaci "Suhuf" gareshi.[116] haka nan kan asasin abin da ya zo a wani hadisi, Allah ya aikowa da annabi shisu (a.s) sahifa guda 50, annabi idrisu (a.s) guda 30, annabi ibrahim (a.s) guda 20.[117]

Malaman tafsiri tare da jingina da ayar: “Abin da aka yi wa nuhu wasiyya da shi daga addini, an shar'anta muku shi, da abin da aka maka wahayinsa, abin da muka yi wasicci da shi ga ibrahim, musa da isa”[118] annabi nuhu (a.s) annabi ibrahim (a.s), annabi musa (a.s), annabi isa (a.s) da annabi muhammad (s.a.w) annabawa ne da aka aiko musu da shari'a.[119] cikin ba'arin riwayoyi, dalilin gabatar da waɗannan annabawa matsayin ulul azmi ya faru ne saboda shari'ar da take tare da su.[120]

Allama ɗabaɗaba'i ya ce kowanne mutum ɗaya daga cikin annabawa ulul azmi ya kasance yana da shari'a tasa mai cin gashin kanta.[121] kuma litattafan sauran annabawa waɗanda ba ulul azmi ba misalin dawud (a.s)[122] annabi shisu (a.s) da annabi idrisu (a.s),[123] litattafai ne da basa cin karo da keaɓantuwar shari'ar litattafan da aka saukarwa da annabawa ulul azmi; su litattafan annabawa da ba ulul azmi ba basu ƙunshi hukunce-hukuncen shari'a ba.[124]

Mujizoji

Mu'ujiza, ɗaya daga hanyoyin bambance annabawa na gaskiya daga masu da'awar annabta bisa ƙarya, ita mujiza wani aiki da ya shallake abin da aka saba da shi da Allah yake gudanar da ita ta hannun annabi tana kasancewa ne tare da da'awar annabta da kuma yin ƙalubale.[125] kur'ani ya ambaci ba'arin mujizojin annabawa, taguwar annabi salihu,[126] sanyayar wuta kan ibrahim,[127] raya matattun kaji guda huɗu ta hannun ibrahim.[128] mujizoji guda tara na musa (a.s) misalin canja sandarsa zuwa macizai.[129] gangarar idanuwar ruwa ga asbaɗu bani isra'il,[130] tsaga kogi gida biyu da buɗe hanya domin tseratar da bani isra'il,[131] farin hannu,[132] mujizojin isa (a.s) misalin warkar da marasa lafiya, raya matattu, canja yunɓu zuwa tsuntsaye,[133] mu'ujizojin annabi akram (s.a.w) misalin kur'ani,[134] da tsaga wata[135] suna daga cikin shahararrun mu'ujizozjin annabawa da aka yi ishara da nuni zuwa kansu, ibn jauzi ya naƙalto mu'ujizoji ɗai-ɗai har guda 1000 na annabi (s.a.w) daga madogaran da aka yi magana kansu.[136]

Bambantuwar mu'ujizoji ya faru ne daaga bambantuwar ilimi da buƙatun mutane cikin mabambantan zamani da lokuta, hikimar Allah tana hukunta mu'ujizar kowanne annabi ta zama ta dace da buƙatun mutanensa, alal misali a zamanin annabi musa (a.s) sihiri da tsafi wani abu da ya yi matuƙar yaɗuwa da bazuwa cikin mutanen wannan zamani, sai Allah ya sanya sandar musa matsayin mu'ujiza a gareshi da abokan jayayya z asu gaza kawo wani abu kwatankwacinta, kuma ta zama itmam hujjat (hujjar yanke duk wani uzuri) kan sauran mutane.[137]

Irhasat (Alamomi)

Tushen ƙasida: Irhasat

Abubuwan da suke faruwa gabanin aiko da annabawa da manufar samar da yanayi da tanadi ga mutane da zai taimaka musu cikin karɓa da yarda da da'awar annabawa za su yi daga baya,[138] cikin isɗilahin malaman kalam ana kiran wannan abu da sunan irhasat. tseratar da annabi musa (a.s) daga kogin nilu, maganar annabi isa (a.s) yana jinjiri kan shimfiɗar haihuwa,[139] bushewar ƙaramar ƙoramar garin sawa, girgzar katangar kisra, kashe wutar farisa da sauran abubuwa da suka faru a shekarar da aka haifi annabi akram (s.a.w),[140] suna daga cikin irhasat annabawa.

Fihirisar Littafi

Malaman hadisi, malaman tafsiri da malaman ilimin kalam na muslunci cikin rubuce-rubucensu sun yi talifi batutuwa game da annabawa, allama majlisi ya keɓance mujalladai huɗu cikin biharul al-anwar da ya tattaro riwayoyi da suke da alaƙa da maudu'in annabawa,[141] sannan ya rubuta mujalladai ɗai-ɗai har guda tara game da tarihin annabi akram (s.a.w),[142] haka nan dangane da annabawa akwai litattafai masu zaman kansu da aka rubuta, galibinsu suna ɗauke da taken ƙissoshin annabawa, mafi yawansu suna sharhi ne kan halayen annabawa, a wani lokaci kumaana bahasi na aƙida da suke dangantaka da su, ba'ain waɗannan litattafai sun kasance kamar haka:

  • Nurul al-mubin fi ƙisasi al-anbiya'i wal-mursalina: na sayyid ni'imatullahi jaza'iri wanda ya rayu tsakanin shekaru 1050-1112 bayan hijira, wannan littafi ya tattare da tarihin rayuwar annabawa waɗanda sunayensu ya zo cikin riwayoyin shi'a, marubucin wannan littafi cikin muƙaddima ya yi bahasosi misalin adadin annabawa, tarayyarsu da juna, annabawa ulul azmi da kuma bambanci da yake tsakanin annabi da imami, ya rubuta wannan littafi ne da harshen larabci, amma an tarjama zuwa harshen farisanci cikin taken “Dastan payambaran ya ƙissahaye kur'an az adam ta khatam”.
  • Tanzihul anbiya wal a'imma: na sayyid murtada wanda ya rayu tsakanin shekaru 355-436 bayan hijira, ya wallafa wannan littafi domin tabbatar da ismar annabawa ya rubuta wannan littafi ne cikin harshen larabci. Marubucin cikin wannan littafi nasa ya tabbatar da isma ga annabawa tare da kore duk wani nau'in kuskure da zunubi babba da ƙarami daga gare su.[143]
  • Waƙa'iƙus as-sinin wal-a'awam, na sayyid abdul-husaini khatun abadi (Wafati:1105.h.ƙ) littafi ne cikin sashe guda uku. Sashe na farko bahasi ne game da tarihin annabawwa, marubucin ya kawo sunayen annabawa, shekarunsu da ba'arin halayen wasu adadin annabawa, cikin sauran sashe guda biyu ya yi Magana game da abubuwan da suke faru a zamaninsu, an rubuta asalin wannan littafi cikin harshen farisanci.

Haka nan kuma litattafan ƙisasul al-anbiya wanda ake kira da ara'isul almajalis na ahmad ɗan Muhammad salabi, da ƙisasul al-anbiya na ibn kasir da ƙisasul anbiya na abu is'haƙ naishaburi daga malaman ahlus-sunna, duka litattafai ne aka wallafa dangane da wannan maudu'i.

Bayanin kula

  1. Tareehi, Majma Al-Baharin, 1375, juzu'i na 1, shafi na 375.
  2. Mustafawi, Attahƙiƙ kalemat Kur’an, 1368, juzu’i na 12, shafi na 55.
  3. Tusi, Al-Tabayan, Darahiya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 2, shafi na 459.
  4. Mufid, Adamul sahawin Annabiyyi, 1413 AH, shafi na 29 da 30; Sayyed Morteza, Tanziyeh al-Anbia, 2007, shafi na 34.
  5. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 72, shafi na 116.
  6. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 72, shafi na 116.
  7. Misali, duba: Suratul ƙasas, aya ta 16; Suratul Anbiya, aya ta 87; Suratul Taha, aya ta 121.
  8. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 16, shafi na 42, 43.
  9. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 14, shafi 315.
  10. Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 7, shafi 56; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 13, shafi na 323.
  11. Sadouƙ, Man la Yahdrah al-Faƙih, 1413 AH, Juzu’i na 1, shafi na 360.
  12. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 144.
  13. Don nazarin ruwayar, duba: Sadouƙ, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi:524; Sadouƙ, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi 333; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 32, juzu'i na 74, shafi na 71.
  14. Tusi, al-Amali, 1414 AH, shafi na 397; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 31.
  15. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 60.
  16. Mofid, Al-EKhtisas, 1413 AH, shafi na 263; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 16, shafi na 352.
  17. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, 31.
  18. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 32.
  19. Suratul Ahzab, aya ta 40.
  20. Suratul Nisa’i, aya ta 164.
  21. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  22. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 14, shafi na 63.
  23. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 313.
  24. Sadouƙ, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 524.
  25. ƙutb Raɓandi, Kisas Anbiya, 1409 Hijira, shafi na 242-2541.
  26. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 14, shafi na 163.
  27. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 13, shafi 448.
  28. ƙutb Raɓandi, ƙasas al-anbiya, 1409 AH, shafi 238.
  29. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 13, shafi 448.
  30. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 14, shafi 156.
  31. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 14, shafi na 373; ƙutb Raɓandi, Kissoshin Annabawa, 1409H, shafi na 224.
  32. Duba: Tusi, Al-Tabayan, darul Al-Arabi, juzu'i na 7, shafi.82.
  33. Duba: Tusi, Al-Tabayan, darulAl-Arabi, juzu'i na 7, shafi.82.
  34. Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 21, shafi na 495.
  35. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  36. Suratul Maryam, aya ta:53.
  37. Suratul Hud, aya ta 74.
  38. Sayyid Ibn Tawus, Al-Mahhouf Ali ƙatali al-Tafouf, shafi na 102
  39. Tabarsi, Majalisar Al-Bayan cikin Tafsirin Kur’ani, Mawallafi: Dar al-Marafah, juzu’i na 2, shafi na 720.
  40. (وَاذْكُرْ فِی الْكِتَابِ إِدْرِیسَ ۚ إِنَّهُ كَانَ صِدِّیقًا نَّبِیا.) مریم/۵۶
  41. روایات ذیل آیه وَ رَفَعْناهُ مَكاناً عَلِيًّا (مریم/57)
  42. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  43. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۰۷
  44. سوره اعراف، آیه ۶۵؛ سوره هود، آیات ۵۰، ۵۳، ۵۸، ۶۰، ۸۹؛ سوره شعراء، آیه ۱۲۴؛ النجار، قصص‌الانبیاء، ۱۴۰۶ق، ص۴۹.
  45. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۲۵
  46. (وَإِلَیٰ عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا.) اعراف/۶۵
  47. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۴۳
  48. قرآن ۷:۷۳
  49. (وَاذْكُرْ فِی الْكِتَابِ إِبْرَاهِیمَ ۚ إِنَّهُ كَانَ صِدِّیقًا نَّبِیا.) مریم/۴۱
  50. (أَتَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَینَاتِ.) توبه/۷۰
  51. (وَإِذِ ابْتَلَیٰ إِبْرَاهِیمَ رَبُّهُ بِكَلِمَاتٍ فَأَتَمَّهُنَّ ۖ قَالَ إِنِّی جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامًا ۖ قَالَ وَمِن ذُرِّیتِی ۖ قَالَ لاینَالُ عَهْدِی الظَّالِمِینَ.) بقره/۱۲۴
  52. (صُحُفِ إِبْرَاهِیمَ وَمُوسَیٰ.) اعلی/۱۹
  53. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۶۲
  54. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ.) انعام/۸۹
  55. (صُحُفِ إِبْرَاهِیمَ وَمُوسَیٰ.) اعلی/۱۹
  56. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ.) انعام/۸۹
  57. (وَ قالَتِ الْيَهُودُ عُزَيْرٌ ابْنُ اللَّهِ وَ قالَتِ النَّصارى‏ الْمَسيحُ ابْنُ اللَّه.) توبه/۳۰
  58. (فَلَمَّا اعْتزََلهَُمْ وَ مَا یعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ وَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَ یعْقُوبَ وَ كلاًُّ جَعَلْنَا نَبِیا.) مریم/۴۹
  59. (وَ جَعَلْنَاهُمْ أَئمَّةً یهْدُونَ بِأَمْرِنَا.) انبیاء/۷۳
  60. (فَلَمَّا اعْتزََلهَُمْ وَ مَا یعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ وَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَ یعْقُوبَ وَ كلاًُّ جَعَلْنَا نَبِیا.) مریم/۴۹
  61. (وَ جَعَلْنَاهُمْ أَئمَّةً یهْدُونَ بِأَمْرِنَا.) انبیاء/۷۳
  62. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  63. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  64. (إِنی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِین.) شعراء/۱۷۸
  65. (وَ إِلی مَدْینَ أَخَاهُمْ شُعَیبًا.) اعراف/۸۵
  66. (وَ اذْكُرْ فی الْكِتَابِ مُوسی إِنَّهُ كاَنَ مخُْلَصًا وَ كاَنَ رَسُولًا نَّبِیا.) سوره مریم، آیه۵۱.
  67. (وَ اذْكُرْ فی الْكِتَابِ مُوسی إِنَّهُ كاَنَ مخُْلَصًا وَ كاَنَ رَسُولًا نَّبِیا.) سوره مریم، آیه۵۱.
  68. (إِنَّا أَنْزَلْنَا التَّوْراةَ فیها هُدی وَ نُورٌ.) مائده/۴۴
  69. (وَ وَهَبْنا لَهُ مِنْ رَحْمَتِنا أَخاهُ هارُونَ نَبِيًّا .) مریم/۵۳
  70. ثُمَّ أَرْسَلْنا مُوسی وَ أَخاهُ هارُونَ بِآیاتِنا وَ سُلْطانٍ مُبین.) مؤمنون/۴۵
  71. ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَیٰ وَهَارُونَ إِلَیٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ بِآیاتِنَا فَاسْتَكْبَرُوا وَكَانُوا قَوْمًا مُّجْرِمِینَ.) یونس/۷۵
  72. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  73. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۰۷
  74. (وَ ءَاتَینَا دَاوُدَ زَبُورًا.) اسراء/۵۵
  75. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  76. (إِنِّی لَكُمْ رَسُولٌ أَمِینٌ.) شعراء/۱۰۷
  77. (وَ إِنَّ إِلْیاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِین.) صافات/۱۲۳
  78. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  79. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  80. (وَ إِنَّ یونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِین.) صافات/۱۳۹
  81. (أُولَـٰئِكَ الَّذِینَ آتَینَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ). انعام/۸۹
  82. (فَنَادَتْهُ الْمَلَئكَةُ وَ هُوَ قَائمٌ یصَلی فی الْمِحْرَابِ أَنَّ اللَّهَ یبَشِّرُكَ بِیحْیی مُصَدِّقَا بِكلَِمَةٍ مِّنَ اللَّهِ وَ سَیدًا وَ حَصُورًا وَ نَبِیا مِّنَ الصَّلِحِین.) آل عمران/۳۹
  83. (قَالَ إِنی عَبْدُ اللَّهِ ءَاتَئنی الْكِتَابَ وَ جَعَلَنی نَبِیا.) مریم/۳۰
  84. (إِنَّمَا الْمَسِیحُ عِیسی ابْنُ مَرْیمَ رَسُولُ اللَّهِ وَ كَلِمَتُهُ أَلْقَئهَا إِلی مَرْیم.) نساء/۱۷۱
  85. (وَ قَفَّینَا بِعِیسی ابْنِ مَرْیمَ وَ ءَاتَینَهُ الْانجِیلَ.) حدید/۲۷
  86. (وَإِذْ قَالَ عِیسَی ابْنُ مَرْیمَ یا بَنِی إِسْرَائِیلَ إِنِّی رَسُولُ اللَّـهِ إِلَیكُم مُّصَدِّقًا لِّمَا بَینَ یدَی مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرًا بِرَسُولٍ یأْتِی مِن بَعْدِی اسْمُهُ أَحْمَدُ.) صف/۶
  87. (شَرَعَ لَكُم مِّنَ الدِّینِ مَا وَصَّیٰ بِهِ نُوحًا وَالَّذِی أَوْحَینَا إِلَیكَ وَمَا وَصَّینَا بِهِ إِبْرَاهِیمَ وَمُوسَیٰ وَعِیسَیٰ.)
  88. (ما كاَنَ محُمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِّن رِّجَالِكُمْ وَ لَكِن رَّسُولَ اللَّهِ وَ خَاتَمَ النَّبِینَ.) احزاب/۴۴
  89. (ما كاَنَ محَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِّن رِّجَالِكُمْ وَ لَكِن رَّسُولَ اللَّهِ وَ خَاتَمَ النَّبِینَ.) احزاب/۴۰
  90. (وَ كَذَالِكَ أَوْحَینَا إِلَیكَ قُرْءَانًا عَرَبِیا لِّتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَی وَ مَنْ حَوْلهَا.) شوری/۷
  91. (شَرَعَ لَكُم مِّنَ الدِّینِ مَا وَصَّیٰ بِهِ نُوحًا وَالَّذِی أَوْحَینَا إِلَیكَ وَمَا وَصَّینَا بِهِ إِبْرَاهِیمَ وَمُوسَیٰ وَعِیسَیٰ.) شوری/۱۳
  92. Suratul Isra, aya ta 55
  93. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 254.
  94. Taheri Akerdi, Yahudiyyat, 1390, shafi na 173.
  95. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  96. مصباح یزدی، راه و راهنماشناسی، ۱۳۹۳ش، ص۴۰۴.
  97. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 145.
  98. Mofid, Aoel Al-Makalat, 1413 AH, shafi na 45.
  99. Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 524; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 32, juzu'i na 74, shafi na 71.
  100. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 176-177.
  101. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 176-177
  102. مصباح یزدی، راه و راهنماشناسی، ۱۳۹۳ش، ص۵۵.
  103. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 7, shafi na 144.
  104. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 7, shafi na 144.
  105. Motahari, Majumu Asar, juzu'i na 2, shafi na 183.
  106. Motahari, Majmu Asar, juzu'i na 2, shafi na 183.
  107. Motahari, majumu asar, juzu'i na 3, shafi na 173.
  108. Motahari, majmu asar, juzu'i na 2, shafi na 183.
  109. Suratul Baqarah, aya ta:124
  110. Bahrani, al-Barhan, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 323.
  111. Suratul Anbiya, aya ta 69 zuwa ta 73.
  112. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 1, shafi na 175.
  113. Mofid, Aoel Al-Makalat, 1413 AH, shafi na 49-50.
  114. Sadouq, Kamaluddin, juzu'i na 1, shafi na 254.
  115. Suratul Hadid, aya ta 27
  116. Suratul Ala, aya ta 19.
  117. Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 524.
  118. Suratul Shura, aya ta 13.
  119. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  120. Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 80.
  121. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  122. Suratul Nisa’i, aya ta 163.
  123. Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 524.
  124. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 141.
  125. Mufid, Al-Naqt al-Ithaqadiyyah, 1413H, shafi na 35.
  126. Suratul A'araf, aya ta 73.
  127. Suratul Anbiya, aya ta 69
  128. Suratul Baqarah, aya ta:260.
  129. Suratul Shu'ara, aya ta 32.
  130. Suratul Baqarah aya ta 60.
  131. Suratul Shuara, aya ta 63.
  132. Suratul A'araf: aya ta 108; Suratul Taha, aya ta 22; Suratul Shaara', aya ta 33; Suratul Namal, aya ta 12; Suratul Qass, aya ta 32.
  133. Suratul Al-Imran, aya ta 49; Suratul Ma’edah, aya ta:110.
  134. Suratul Toor, aya ta 34.
  135. Suratul Qamar, aya ta 1.
  136. Ibn Juzi, al-Muntazem, 1412 AH, juzu'i na 15, shafi na 129.
  137. Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 1, shafi na 42.
  138. Tahanavi, Mausuatu kashaf istilaht, Maktabat Lebanon, Juzu'i 1, shafi 141..
  139. Jafari, Tafsir Kausar, 1377, juzu'i na 3, shafi na 300.
  140. Ibn Kathir, Al-Bidaya Wal-Nihaya, 1407H, Juzu'i na 2, shafi na 268; Yaqoubi, Tarikh Al-Yaqoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 8.
  141. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11-15.
  142. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 15-24.
  143. Sayyed Morteza, Tanziyeh al-Anbia, 2007, shafi na 34.

Tsokaci

  1. Isma'in bin hizƙilu yana daga cikin abbanawan bani isra'il. allama ɗabaɗaba'i ya yi amanna kan cewa isma'il da ya zo cikin kur'ani a ayar «واذكُر فِى الكِتبِ اِسمعيلَ اِنَّهُ كانَ صادِقَ الوَعدِ و كانَ رَسولاً نَبيـّا» (سوره مریم، آیه۵۴). shi ne dai isma'il ɗan hizƙilu,. almizan, bugun shalara ta 1417 hijiri. j 14 shafi na 63
  2. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Allah bai halicci wata halitta mafi falala daga gareni ba, kuma babu wata halitta mafi karamci kansa fuey da ni,, sai Ali (A.S) ya ce: sai na ce ya manzon Allah shin kai ne mafi falala ko Jibrilu? sai ya ce: ya Ali! lallai Allah tabaraka wa ta'ala ya fifita annabawa da manzanni kan mala'iku makusantan, sannan ya fifita ni kan bakiɗayan annabawa da manzann. kamlaud-dini, bugun shekara ta 1395, j 1 shafi na 254.
  3. cikin wata shahararriyar riwaya daga imam sadik (a.s) an lissafa martabobin da ibrahim ya samu kafin imamanci kamar haka: 1-annabata 2-ibada 3-manzanci 4-khulla (badaɗaye) 5-imamanci, lallai Allah ta'ala ya riƙi ibrahim matsayin bawansa kafin zaɓarsa annabi, kuma ya zaɓe shi annabi kafin ya zaɓe shi manzo, lallai Allah ya zaɓe shi manzo kafin zaɓarsa badaɗaye, kuma lallai ya zaɓe shi badaɗaye kafin ya sanya shi imami, yayin da ya tattara masa waɗannan muƙamai sai yace, "lallai ina sanyaka imami ga mutane..." imam sadiƙ (a.s): Allah ta'ala ya zaɓi ibrahim bawansa gabanin zaɓarsa da annabta, kuma ya zaɓe da annabta gabanin zaɓarsa da manzanci, ya zaɓe shi manzanci gabanin saɓarsa da badaɗaye, kuma ya zaɓe shi badaɗaye gabanin zaɓarsa da imamanci, sakamakon bashi dukkanin waɗanan muƙamai, sai ya ce: na sanyaka imami ga mutane. kulaini, alkafi j 1 shafi na 175
  4. kur'ani bai kawoi bayani ƙarara ba game da saukar da attaura ga musa (a.s) sai dai kuma ya tabbatar da cewa attaura littafi ne daga Allah(suratul ma'ida aya ta 44) haka ya tabbatatar da saukar da alluna ga musa (a.s) (suratul a'araf aya 154). wasu ba'arin malaman tafsiri suna tafi kan cewa alluna sune dai attaura(ɗabaɗaba'i, almizan, bugun shekara ta 1417 hijiri, j 8 shafi na 250).

Nassoshi

  • Ibn Juzi, Abd al-Rahman bin Ali, al-Muntazem fi Tarikh al-Umms wa al-Muluk, bincike: Muhammad Abd al-Qader Atta da Mostafa Abd al-Qader Atta, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1412 AH/1992 AD.
  • Bahrani, Sayyid Hashem, Al-Barhan Fi Tafsiril Qur'an, Tehran, Ba'ath Foundation, 1416 Hijira.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Jafari, Yaqub, Tafsirin Kausar, Kum, Hijira, 1377.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, edita: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, 1407H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403H.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, Rahi wa Raheshinasi, wanda: Mostafa Karimi, Qum, Buga Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, 2013.
  • Motahari, Morteza, tarin ayyuka, Tehran, Sadra Publishing Hou
  • Mustafavi, Hassan, At-Tahaqiq fi kalamat al-Qur'an al-Karim, Tehran, Ministry of Culture and Islamic Guidance, 1368.
  • Qutb Rawandi, Saeed bin Hibatullah, Qasases al-Anbiya, edited by: Gholamreza Irfanian Yazdi, Mashhad, Islamic Research Center, 1409 A.H.
  • Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ya gyara shi: Mehdi Lajordi, Tehran, Nash Jahan, 1378H.
  • Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdara al-Faqih, Edited by: Ali Akbar Ghafari, Qum, Islamic Publication Office mai alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary Society, 1413 AH.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Al-Khasal, editan: Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Modaresin, 1362.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din wa Tamam al-Neema, editan: Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, 1395H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, gyara daga: Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary Society, 1403 AH.
  • Seyyed Morteza Alam Al-Hadi, Tanzihul Anbiya wa A'Immai, Bincike: Fars Hassoun Karim, Kum, Bostan Kitab, 1380/1422 Hijira.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na al'ummar Seminary Qum, 1417H.
  • Tahanwi, Mohammad Ali bin Ali, Mausu'atu Kashaf istilahat. bincike: Ali Farid Dahrouj, Beirut, Makarantar Mawallafa ta Lebanon, Beta.
  • Taheri Akerdi, Mohammad Hossein, Yahudiyyat, Al-Mustafa International Translation and Publishing Center (AS), 1390/1432 AH.
  • Tareehi, Fakhreddin bin Mohammad, Majma Al-Bahraini, Ahmad Hosseini Ashkuri, Tehran, Mortazavi, 1375 ya gyara.
  • Tayeb, Seyyed Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam, 1378.
  • Tousi, Muhammad bin Hasan, al-Mali, wanda: Mu’assasar Al-Baath, Qom, Dar al-Thaqafa, 1414H.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, bincike: Ahmed Qasir Ameli, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Bita.se.