Ali Waliyullahi

Daga wikishia

Ali Waliyullahi da (Lrabci: علي ولي الله) Harshen Farisanci ana nufi Ali ne Shugaba da Allah ya nada shi, wannan jumla wani Take ne na `Yan Shi'a kan asasin imaninsu da Imamanci da Wilayar Imam Ali (A.S) hakika `Yan Shi'a sun yi Imani kan cewa Halifancin Ali (A.S) bayan wafatin Annabi (S.A.W) ya kasance da umarnin Allah Subhanahu wa-Ta'ala.

Ali Waliyullahi a cikin salon rubutun madubi, a cikin rubutun hannun Mahmoud Ibrahim. Mai alaƙa da karni na 18 AD.

Hakika `Yan Shi'a cikin Kiran sallah da Ikama bayan sun ambaci shaidawa da Manzanci Annabi (S.A.W) da kuma bayan Kalmar shahada guda biyu suna fadin shaida da (Ali Waliyullah) duk da cewa ba su yi imani da hakan matsayin wani bangare daga kiran sallah da Ikama ba.

Mirza Ƙummi Babban Malamin Shi'a a karni na sha uku kamari, ya ce fadin (Ali Waliyullah) bayan (La ilaha Illallah Muhammadan Rasulullahi) Mustahabbi ne, haka Sayyid Muhammad Husaini Husaini Tahrani wanda ya tafi kan cewa ba za a raba wannan jumloli da juna ba, tare da kafa dalili da wannan a farkon ranar da Annabi ya fara kiran Mutanensa zuwa ga Muslunci ya umarce su da biyayyar Imam Ali (A.S) Akwai Sulalla da aka buga su da tambarin jumlar (Ali Waliyullahi) a lokacin Daulolin Shi'a a zamanin Alu Bawaihi, Isma'iliyya, Fatimiya, da kuma Safawiyya, wadannan sulalla suna nan har yanzu, tarihi mafi tsufansu suna danganewa da rabin karni na hudu kamari, haka kuma an rubuta wannan jumla a jikin gine-ginen Daular Fatimiyya, daga cikin Jumlarsu akwai Mihrabi na da yake danganewa da shekara 478 hijira kamari wanda ya yi daidai da 1094 Miladi wannan Mihrabi yana cikin Masallacin Ibn Tulun a Alkahira kasar Misra.

Matsayi da Sanin Mafhumi

Tutar Ali Waliyullahi a cikin Haramin Imam Ali (A.S)

Ali waliyullah wani bayyanannen Take na `Yan Shi'a da yake kunshe da Imani da Imamanci da wilayar Imam Ali (A.S) wanda an ciro ne daga Ayar Wilaya da Hadisai misalin Hadis Ghadir da Hudubar Ghadir[1] hakika `Yan Shi'a suna fassara Ali Waliyullah da ma'anar Shugaba[2] da umarnin Allah[3] kuma sun yi Imani da cewa Halifancin Ali (A.S) bayan wafatin Annabi (S.A.W) ya kasance da umarnin Allah[4] sabanin Ahlus-Sunna da suke ganin Halifancinsa yana kasancewa bayan Halifofi guda uku[5] kuma Halifancinsa ba shi da banbanci da Halifancin sauran Halifofi[6] Kalmar (Ali Waliyullah) tsakankanin Kutubul Arba'a na Shi'a, an ambace ta cikin Alkafi,[7] da Man La Yahduruhul Alfakihu,[8] haka kuma ta zo cikin Ziyarori da aka nakalto cikin wadannan litattafan, an kirayi Imam Ali (A.S) da taken (Waliyullahi)[9] a ba'arin wasu riwayoyi cikin littafan Shi'a bayan jumlar (Ali Waliyullah) jumlar (Wasiyyu Rasulillahi)[10] ta biyo bayanta, wacce a harshen Farisanci take nufin Halifan Manzon Allah[11] wasu ba'arin Sufaye na Ahlus-Sunna sun kawo jumlar (Ali Waliyullahi) cikin rubuce-rubucensu[12] Hakika `Yan Shi'a suna shirya bikin Idil Ghadir suna kafa Manyan Alluna da Tutoci da suke dauke da rubutun Ali Waliyullah[13] haka zaka samun wannan jumlar kan saman Dutsen Zobe da suke sawa a hannu.[14] haka zaka samu wasu suna rubuita wannan kalma a bayan Motar da suke hawa[15]

Shahadatu Salisa (Kalmar Shahada ta uku cikin kiran Sallah)

Asalin Makala: Shahadatus Salisa

`Yan Shi'a cikin kiran Sallah da Ikama bayan Shaidawa da Manzancin Annabi (S.A.W) suna fadin (Ali Waliyullahi)[16] Malaman Fikhun Shi'a sun bayyana cewa wannan kalma ba bangare ce ba cikin kiran Sallah da Ikama[17] amma da yawa daga cikin Malamai sun tafi kan halascin sanya ta shi cikin kiran sallah da niyyar neman samun lada[18]haka kuma cikin fadin Kalmar shahada don muslunta bayan shaidawa da Tauhidi da Manzanci Annabi (S.A.W) suna Shaidawa da (Ali Waliyullah)[19] duk da cewa Malaman Fikhu basa ganin larurar shaidawa da Wilayar Ali cikin karbar Muslunta[20] A cikin wata riwaya daga Masadir din Shi'a bayan jumlar:

«لا اِلٰهَ اِلّا الله، محمدٌ رسولُ الله»،

Ana fadin Ali Waliyullah[21] kuma fadinta yana sanyawa a yafe zunubai[22] Mirza Qummi Malamin Fikhun Shi'a a karni na 13 kan asasin riwayoyi yana ganin fadin Mustahabbanci Fadin Ali Waliyullah[23] Sayyid Muhammad Husaini Husaini Tahrani Babban Malamin Shi'a wanda ya bar duniya shekara 1374 yana ganin jumlar

«لا اله الا الله، محمد رسول الله، علی ولی الله»

Ba za a iya raba su da juna ba, ya kafa dalili da Hadis yaumu Dari kuma kan asasinsa rana ta farko da Annabi ya fara kiran mutanensa zuwa ga muslunci ya umarce su da biyayya da Imam Ali (A.S)[24] Kan asasin ba'arin wasu riwayoyi hakika a Ranar Kiyama kan saman kambun[25]sarauta da yake kan Annabi (S.A.W)[26]da Imam Ali (A.S) an rubuta

«لا اله الا الله، محمد رسول الله، علی ولی الله»

Sannan akwai kwatankwacin wannan siffantawar a wasu masadir din Shi'a da suka nakalto.[27] [yadahst]

«بسم الله الرحمن الرحیم، لا اله الا الله محمد رسول الله علی ولی الله»

Wannan jumla da aka rubutata a kan Kyalle a lokacin Daular Fatimiya[28]

Kirar Sulalla da suke Dauke da Kalmar (Ali Waliyullah)

Kalmar Ali Waliyullah akan dinari da aka fi sani da Mostansarih dinar, wanda Arslan Basassiri ya yi a shekara ta 450 miladiyya.

Kalmar Ali Waliyullahi a kan Sulallan Dinare wanda akafi sani da DInaren Muntasiriyya wanda ya kasance a shekara 450 hijiri Kamari[29] Wasu ba'arin Sarakunan Daulolin `Yan Shi'a misalin Isma'iliya[30] Fatimiya[31] sun buga Sulallansu dauke da Kalmar Ali Waliyullah. Wani adadi daga cikinsu sun kasance kamar haka:

  • Bawandiyan cikin Tabaristan a rabin karni na hudu Kamari[32]
  • Dailamiyan a Gilan[33]
  • Alu Babawaihi bayan zuwan Hukumar Basasiri wanda ya mutu 451 kamari[34]
  • Uljayitu, Sarkin na Takwas na Elakhi bayan canja Mazhaba zuwa Shi'anci[35]
  • Sarbardaran wanda suka yi sarauta daga shekara 736-788.[36]
  • Isma'iliya Alamut wanda suka yi hukuma daga 483-654.[37]
  • Safawiyan wanda suka yi hukuma shakaru 907-1135.[38]

Sanya Kalmar (Ali Waliyullahi) a kan Sulalla daga hannun wasu sarakuna da ban Shi'a ba misalin Aregun sarki na hudu a jerin Sarakunan Elakhi da sukayi hukuma a Shekaru 683-690.[39] sai dai cewa wasu masu zurfafa bincike[40]sun bayyana cewa haka ya faru ne sakamakon karkatarsu zuwa ga Mazhabar Shi'anci[41]

Kalmar Ali Waliyullahi a jikin Gine-ginen Tarihi da Addini

Kalmar Ali Waliyulah, akan daya daga cikin ginin masallacin Ibn Tulun da ke birnin Alkahira, wanda aka gina a zamanin Fatimid na Moaz Mostanser (mulkin 427-487H), Imami na 18 na Isma'iliyya.

Hakika an rubuta Kalmar (Ali Waliyullah) a jikin daya daga Mihrabi na Masallacin Ibn Tulun a cikin garin Alkahira da yake kasar Misra hakan ta faru ne tun zamanin hukumar Isma'iliya a shekara 427-487.[42]

Kalmar a jikin Gine-Ginen Shi'a na tarihi[43] a zaman Daular Fatimiya[44] Alal misali Mihrabin da ya kasance a shekara 478 hijiri Kamari wanda ya yi daidai da 1094 hijiri milady a Masallacin Ibn Tulun[45] wannan Mihrabi ya kasance a lokacin Halifancin Mu'az Muntasir Imami na sha takwas cikin jerin Imam Isma'illiya[46] Haka kuma an rubuta Kalmar (Ali Waliyullah) a kan saman Hasumiya da take garin Suldaniyeh da yake a Zanjan wanda yake danganewa da shekara 710 hijiri Kamari bayan Uljayitu Sarkin na Takwas a jerin sarkunan Elakhi ya karbi Mazhabar Shi'a kuma da Umarninsa ne aka gina wannan Hasumiya[47] haka kuma zaka sami wannan Kalmar a jikin katangar Masallacin Kabud Tabriz a zamanin Jahansha daya daga cikin Sarakunan Karakunilu a shekara 870 haka a Mihrabin Imamzadeh Habibu Bn Musa da yake a garin Kashan wanda yake danganewa da shekara 770 shima yana dauke da Kalmar[48]

«لا اله الا الله، محمد رسول الله، علی ولی الله

Haka kuma akwai Kalmar (Ali Waliyullahi) a jikin ba'arin wasu Haraman Imamai da Imamzadegan, daga cikinsu a saman Haramin Imam Ali (A.S)[49]da saman Hubbaren Imam Rida (A.S) da jikin Manarar Haramin Hazrat Abul Fadlil Abbas (A.S).[50]

Gallery

Sulalla da aka yi a zamanin Shah Isma'il I, wanda a cikinsa aka rubuta kalmar "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" akan Muhammad Rasulullah Ali Waliyullah. (929 AH
Zobe dauke da zanen Ali Waliyullahi

Bayanin kula

  1. Mohaddisi, Farhang Ghadir, 2006, shafi na 422 da 423
  2. Misali, duba Hosseini Milani, Jawaher Al-Kalam fi Marefah Al-Imama wa Al-Imam, 2009, juzu'i na 2, shafi na 294.
  3. Tabatabai da Shahi, Barasihaye Islami, 2008, juzu'i na 1, shafi 150
  4. Misali duba Tabari Saghir, Dala'il Al-Imamah, 1413H, shafi na 18.
  5. Misali, duba Abdullahi bin Ahmad bin Hanbal, Sunna, 1408H, juzu’i na 2, shafi na 573; Qairvani, Aqeedah al-Salaf, Dar al-Dashimik, shafi na 61.
  6. Agee, Almawakif fi Ilmil Al-Kalam, Alam Al-Kitab, shafi na 395.
  7. Kulaini, Al-Kafi, 1429 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 99.
  8. Sheikh Sadouq, Man La Yahzara al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 2, shafi na 604.
  9. Misali, duba Kulaini, Al-Kafi, 1429 AH, juzu'i na 9, shafi na 295 da 296; Sheikh Sadouq, Man La Yahzara Al-Faqih, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 586, 589, 590, 592; Sheikh Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 26, 27, 28.
  10. Misali duba Rawandi, Al-Dawat, 1407H, shafi na 211.
  11. Qommi, Tafsir Qummi, 1404H, juzu’i na 2, shafi na 208.
  12. Misali, duba Kashfi Tarmezi, Manaqib Mortazavi, 2013, shafi na 140 da 319; Mazhari, al-Tafsir al-Ahnathani, 1412 AH, juzu'i na 7, shafi na 256; Qandourzi, Yanabi Al Mouda, 1422 AH, Juzu'i na 1, shafi na 250, 288 da 249.
  13. «حضور میلیونی مردم تهران در مهمانی ۱۰ کیلومتری غدیر»،
  14. «انگشتر عقیق خطی علی ولی الله»،
  15. «شابلون پشت‌نویسی ماشین طرح علی ولی الله»،
  16. Sarawi, Al-Qatuf Al-Daniyya fi Al-Masha’il Al-Tham’a’ah, 1997 AD, juzu’i na 1, shafi na 55.
  17. Sobhani, Shi'e Shinakht, 1397, shafi 352; Yazdi, Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghti, 1429 AH, Mujalladi na 1, shafi na 532.
  18. Ghazi, Shahatu Assalisa Almukaddasa, 1423 BC, shafi na 341-384.
  19. Misali, duba Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 AH, Mujalladi na 2, shafi na 52; Ibn Shazan, al-Rawda fi Fadael Amir al-Mu’minin (AS), 1423 AH, shafi na 196.
  20. Misali, duba Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu’i na 41, shafi.630; Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham al-Tankih Shar'e al-Islam, Qum, Al-Ma'arif al-Islami Foundation, juzu'i na 15, 36
  21. Misali, duba Qommi, Tafsirin Qummi, 1404H, juzu’i na 2, shafi na 325; Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 670.
  22. Ibn Shazan Qomi, Al-Rawdah fi Fada’il Amir al-Mu’minin, 1423 AH, shafi na 23.
  23. Mirzai Qomi, Ghanaim Al-Alayam, 1375, juzu'i na 2, shafi na 423.
  24. Hosseini Tehrani, Imam-Shinasi, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 95.
  25. Qommi, Tafsir Qummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 325.
  26. Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 670.
  27. Misali, duba Kulaini, al-Kafi, 1429 AH, juzu'i na 8, shafi.99; Sheikh Sadouq, Al-Khesal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 324; Tabari Amoli Saghir, Dala'il Al-imamah, 1413 AH, shafi na 413; Ibn Shazan, Me’at Manaqba Man Manaqib Amir al-Mu’minin wa Al-Aima, 1407H, shafi na 49.
  28. «المنسوجات الاسلامیةالمصریة و معرض جوبلان بباریس»،
  29. Misali, duba Ibn Jozi, Al-Muntazem Fi Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1412 AH, Mujalladi na 16, shafi na 37; Fasai, Farsnameh Naseri, 1382, juzu'i na 1, shafi na 288.
  30. Serafrazi, "Sha'ir shi'i bar Sikkahaye Islami ta Shakali Giri hukumati Safawiyan", shafi na 13.
  31. Oudi, "Kawashe Nawin dar Tarikh Fatimiyat Masar", shafi na 35
  32. Maudet, "Binciken Tahlil bar Rawandi Darbi ibarat'Ali Wali Allah' bar sikkehaye Bavandian Kiyosiya", shafi na 219.
  33. Jafarian, Tarihin tashayyu dar Iran, 2007, shafi na 361.
  34. Ibn Jozi, Al-Muntazem Fi Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1412 AH, Mujalladi na 16, shafi na 37.
  35. Fasai, Farsnameh Naseri, 1382, juzu'i na 1, shafi na 288.
  36. John Mason, Kuruj wa Uruj Sarbadaran, 1361, shafi 83.
  37. Serafrazi, "Sha'ir shi'i bar Sikkahaye Islami ta Shakali Giri hukumati Safawiyan", shafi na 13
  38. Andami da Soleimani, "Bargi aza Sikkeshinasi (Rawandi Tashayyu dar Iran)", shafi na 83 da 84.1
  39. Jafarian, Tarikh Tashayyu dar Iran, 2007, shafi na 691.
  40. Serafrazi, "Sha'ir shi'i bar Sikkahaye Islami ta Shakali Giri hukumati Safawiyan", shafi na 23
  41. John Mason, Kuruj wa Uruj Sarbadaran, 1361, shafi na 83; Jafarian, Tarihin Shi'anci a Iran, 2007, shafi na 361.
  42. Serafrazi, "Sha'ir shi'i bar Sikkahaye Islami ta Shakali Giri hukumati Safawiyan", shafi na 45
  43. Muhaddi, Farhang Ghadir, 2006, shafi na 423.
  44. برای نمونه نگاه کنید به «Molana Imam Mustansirbillah»، The Bohras.
  45. Fouad Sayed, “Alkahira”, shafi na 8044.
  46. «Molana Imam Mustansirbillah»، The Bohras.
  47. Jafarian, Tarilh Tashayyu dar Iran, 2007, shafi na 737.
  48. Jafarian, Tarikh Tashayyu dar Iran, 2007, shafi na 850.
  49. «الضریح المقدس»، شبکة الامام علی(ع) میدیا
  50. «گنبد حرم حضرت عباس(ع)»،

Nassoshi