Ayar Sadiƙin

Daga wikishia
Ayar Sadikin

Ayar sadiƙin, (Larabci: آية الصادقين) suratul tauba aya ta 119 an umarci muminai da su kasance cikin sadiƙin (ma'abota gaskiya) su yi ɗa'a gare su. Malaman tafsiri game da su wane ne ma'abota gaskiya, sun gabatar mabambantan fassarori tare da dogara da wasu ayoyi daga kur'ani; daga jumlarsu akwai Shaik Ɗusi tare da jingina da aya ta 23 suratul ahzab ya tafi kan cewa waɗanda ake nufi da sadiƙin cikin wannan aya su ne mutanen da suka yi aiki da gaskiya cikin alƙawarin da suka yiwa ubangiji.

Akwai riwayoyi da aka naƙalto daga jawami'u riwaya na ahlus-sunna da shi'a kan asasinsu Ali ɗan Abi ɗalib shi kaɗai ko tare da iyalansa da sahabbansa, ko Annabi da iyalansa su ne mutanen da ake nufi da sadiƙin (Ma'abota gaskiya), riwayoyi masu tarin yawa sun fassara Ahlul-baiti matsayin sadiƙin.

Allama Hilli yana ɗaukar wannan aya ɗaya daga cikin dalilan imamancin Imam Ali (A.S) kuma Ahlul-baiti su ne kaɗai misdaƙin wannan aya. A cewar Nasir Makarim shirazi ma'anar aya shi ne cewa mu kasance tare da Muhammad da iyalansa. Fakhrur Razi ya tafi kan kasancewar wannan aya dalili kan ismar sadiƙin, amma kuma ya ce dukkanin al'umma su ne misdaƙin sadiƙin.

Matani Da Misdaƙin Ayar Sadiƙin

﴾يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ ﴿١١٩ ﴾﴿
Ya ku wadanda kuka bada imani ku ji tsoran Allah kuma ku kasance tare da ma'abota gaskiya.



(Quran: Tauba: 119)


Ma'ana Da Misdaƙin Ayar Sadiƙin

Kalmar «صادقین» jam'i ne na «صادق».[1] a cewar Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i cikin tafsirul al-mizan , duk mutumin da aƙidar ta dace da haƙiƙa ko zahirinsa ya yi daidai da baɗininsa shi ɗin sadiƙ ne (Ma'abocin gaskiya).[2] Zamakhshari daga malaman tafsiri ahlus-sunna shima ya tafi kan cewa sadiƙin su ne mutanen da cikin addninsu ta fuskanin aƙida suka kasance masu gaskiya cikin zantukansu da ayyukansu.[3]

Tare da haka, malaman tafsiri game da misdaƙin da siffofin sadiƙin sun samu saɓanin ra'ayoyi. Ɗabarsi cikin tafsirin majma'ul al-abayan ya ce abin nufi daga sadiƙin su ne mutanen da aka ambaci siffofinsu{{tsokaci| Bai kyautu ka juyar da fuskarka wajen gabas ko yamma ba. Kyautatawa shi ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littãfi. Kuma ya yi imani da annabawa, tare da cewa yana son dukiyarsa, ya bayar da dukiyarsa ga dangi, marayu, mabuƙata, marasa gida, maroƙa, da bayi. ya tsayar da sallaha ya ba da zakka, Kuma waɗanda idan suka ƙulla alkawari, suka yi imani da alkawarinsu, kuma suka yi haƙuri ga tsanani da hasara, kuma a lokacin yaƙi, waɗannan su ne suka faɗi gaskiya, kuma su ne masu taƙawa.] a cikin aya ta 177 suratul baƙara.[4]

Shaik Ɗusi yana ganin misdaƙin sadiƙin su ne waɗanda aka yi bayanin siffofinsu a aya ta 23 suratul ahzab[Tsokaci 1] ma'ana waɗanda suka yi sauke alƙawarinsu da Allah cikin gaskiya.[5]

Daga cikin malaman tafsiri na ahlus-sunna, Ƙurɗubi ya tafi kan cewa muhajirun su ne sadiƙin su ne mutanen da a cikin aya ta 8 suratul hashar[Tsokaci 2] aka kira su da sadiƙun.[6]

Cikin hadisan da aka naƙalto a litattafan hadisi na shi'a da ahlus-sunna, akwai wasu riwayoyi wanda cikinsu aka ambaci Ali (A.S) ko kuma shi da iyalansa[7] ko Muhammad (S.A.W) da iyalansa matsayin misdaƙin sadiƙin.[8] Tare da haka da yawa-yawan riwayoyi sun fassara Ahlul-baiti (A.S) da misdaƙin sadiƙin.[9]

Shiryarwar Kan Isma Da Imamancin Sadiƙin

A cewar wasu adadi daga malaman shi'a, ayar sadiƙin tana shiryarwa kan imamanci da ismar Imam Ali (A.S). Allama Hilli cikin sharhin kalamin muhaƙƙiƙ ɗusi da yake ganin ayar “ Ku Kasance tare da ma'abota gaskiya” ɗaya daga dalilan imamancin Imam Ali (A.S), ya ce abin da ake nufi daga ma'abota gaskiya su ne mutanen da gaskiyarsu ta kasance a bayyane kuma babu inda ake samun haka sai cikin ma'asumi; saboda ba za a iya gano gaskiyar wanda ba ma'asumi ba, bisa ijma'in musulmi cikin dukkanin sahabbai babu wanda ya kasance ma'asumi in banda Imam Ali (A.S).[10]

Haka nan Nasir Makarim Shirazi, marja'in taƙlidi kuma malamin tafsiri na shi'a, yana cewa ma'anar ku kasance tare da ma'abota gaskiya shi ne ku kasance tare da Muhammad da iyalansa, saboda idan mutum bai kasance ma'asumi ba ta ƙaƙa ba tare da ƙaidi da sharaɗi Allah zai fitar da umarni ɗa'a da kuma kasancewa tare da shi cikin kowanne hali da yanayi?[11] Daga cikin malaman ahlus-sunna Fakhrur Razi, yana ganin wannan aya matsayin dalili kan ismar sadiƙin, ya ce daga wannan jumla za a fahimci cewa muminai ba ku kasance ma'asumai ba domin tsira daga kuskure wajibi ne su yi ɗa'a da biyayya daga mutanen da basa aikata kuskure waɗanda su ne sadiƙin.[12] na'am shi yana ganin misdaƙin sadiƙin su ne bakiɗayan al'ummar musulmi.[13]

Nazari

  • Li'akuna Ma'a Al-sadiƙin, rubutun Tijjani Al-samawi, bugun farko, shekara 1374, muassaseh ansariyan.
  • Kunu Ma'a Al-sadiƙin, talifin Sayyid Murtada Al-husaini Al-Shirazi.

Bayanin Kula

  1. Jurjani, Al-Tarifat, 1419 AH, shafi na 95.
  2. Tabatabaei, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i na 9, shafi na 402.
  3. Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 220.
  4. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1379, juzu'i na 3, shafi na 81.
  5. Tusi, al-Tabayan, 1401 AH, juzu'i na 5, shafi na 318. ↑
  6. ƙortubi, Al-Jamae ahkam Al-ƙur'an, 1423 AH, Juzu'i na 8, shafi na 288.
  7. Siyuti, Al-Dar al-Manthor, 1421 AH, juzu'i na 4, shafi.287; Amadi, Ghaya Al-Maram, 1391 AH, juzu'i na 3, shafi 51-50; Amini, Al-Ghadir, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 306.
  8. Hakim Haskani, Shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, Juzu’i na 1, shafi na 262.
  9. Kulayni, Usul Kafi, 1401 BC, juzu'i na 1, shafi na 208; Amidi, Ghayat al-Maram, 1391 BC, juzu'i na 3, shafi na 52.
  10. Hilli, Kashf Al-Murad, 1419 AH, shafi 503.
  11. «دلالت آیه (کونوا مع الصادقین) بر وجود معصوم، در هر عصری»، سایت آیین رحمت.
  12. Fakhr Razi, Mafatih al-Ghayb, 1420 AH, juzu'i na 16, shafi 166.
  13. Fakhr Razi, Mafatih al-Ghayb, 1420 AH, juzu'i na 16, shafi 166.

Tsokaci

  1. Wasu daga cikin muminai maza ne da suka yi imani da Allah, wasu sun yi shahada, wasu kuma suna jiran shahada kuma ba su canja alkawarinsu da Allah ba.
  2. لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللهِ وَرِضْوَانًا وَيَنْصُرُونَ اللهَ وَرَسُولَهُ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ

Nassoshi

  • Jurjani, Sayyid Sharif Ali bin Muhammad, Al-tarifat, Beirut, Dar Al-Fikr, 1419 BC.
  • Hakim Hasakani, Abdullahi bin Ahmad, Shawahid Al-tanzil, Tehran, Cibiyar Buga da Bugawa, 1411 BC.
  • Hilli, Hasan bin Yusuf, Kashf al-Murad, Qum, Islamic Publishing Institute, 1419 BC.
  • «دلالت آیه کونوا مع الصادقین بر وجود معصوم، در هر عصری»، سایت آیین رحمت، تاریخ بازدید: ۲۲ مرداد ۱۴۰۳.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Al-Kashshaf fi Haqiqat, Sirrin Wahayi, da Idon Fassara, bugun: Mustafa Hussein Ahmad, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Arabi, 1407 BC.
  • Suyuti, Jalaluddin, Al-Durr Al-Manthur, Beirut, Dar Ihya’ al-Arabi al-Tarath, 1421 BC.
  • Tabatabai, Sayyid Muhammad Hussein, Al-Mizan, Beirut, Al-Alami Foundation, 1393 BC.
  • Tabarsi, Fadl bin Hassan, Majma'ul Al-Bayan Tafsir Al-Qur'ani, Beirut, Dar Farfaɗo Gadon Larabawa, 1379 Hijira.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tibyan fi Tafsiril Al-Qur’an, Qom, Ofishin Watsa Labarai na Musulunci, 1401 BC.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mafatiful Al-Gaibi (Babban Tafsiri), Beirut, Gidan Farfaɗo na Gadon Larabawa, Afirka ta Kudu, 1420H.
  • Qurtubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jami’ fi Ahkam Al-Ahkam Al-Qur’an Al-Arabi, bugun Abdul-Razzaq Al-Mahdi, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Arabi, 1423 BC.
  • Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Usul Kafi, Beirut, Dar Al-Ta’arif, 1401 BC.

{{end}]