Huɗuba Garra
Huɗuba garra, (Larabci: خطبة الغراء) tana cikin sanannun huɗubobi a cikin littafin nahajul balaga.[1] sakamakon fasaha da balaga da wannan huɗuba ta tattaro ne ake kiranta da huɗubar garra (huɗuba mai matuƙar haskakawa).[2] Ibn Abil Al-hadid ya kira wannan huɗuba da mu'ujizar Imam Ali. (A.S)[3] cikin wannan huɗuba anyi amfani da sauƙaƙan kalmomi sannan kuma huɗuba ce da ta ƙunshi fannin bayani da badi'u misalin tamsili da saja'u , isti'ara da kinaya.[4] daidai da abin da Sayyid Radiyu ya naƙalto, bayan mutane sun gama sauraren wannan huɗuba sai da suka jijjiga suka zubara da hawaye saboda tsananin tsoro.[5]
Wannan huɗuba ta tatttara kan maudu'ai guda huɗu: 1.ɗan Adam da tarihinsa 2. Zargin kan ɗamfaruwar zukata kan duniya 3. Wasicci da jin tsoran Allah da bayanin siffofin masu taƙawa 4. Siffanta abubuwa da za su faru bayan mutuwa. Cikin bahasi da yake da alaƙa da ɗan Adam da tarihinsa wanda shi ne mafi muhimmanci maudu'in da yake cikin wannan huɗuba, ya yi bayanin batutuwa misalin mutuwar mutum, ni'imomin da Allah ya ba shi, gafala, rayuwar duniya, wa'aztuwa da kuma kasancewa duniya ƙararriya.[6] a cewar Abu Na'im Isfahani cikin littafinsa Hilyatul Al-auliya Wa ɗabaƙatul Al-asfiya, Imam Ali (A.S) ya yi bayanin wannan huɗuba a daidai lokacin da aka sanya jana'izar wani mutum cikin ƙabari iyalansa sun a ta rusa kuka da ƙaraji da kukan rabuwa da shi.[7]
Sayyid Abduz-Zahara Husaini Khaɗib, marubucin littafin Masadir Nahjil Balaga Wa Asaniduhu, ya yi Imani da cewa cikin auna ingancin wannan huɗuba ba a buƙatar bincike isnadinta, saboda matanin wannan huɗuba ya kasance tare da balaga da fasahar da babu wanda zai iya yin wannan huɗuba sai ma'asumi.[8] bayan littafin nahajul balaga sauran litattafai misalin tuhaful al-uƙul,[9] da Hilyatul Al-auliya Wa Ɗabaƙatul Al-asfiya[10] sun kawo naƙalto wannan huɗuba[11] A cewar Abduz-Zahra Husaini Khaɗib cikin littafin Al-iƙdul Al-farid[12] bisa kuskure mai littafin ya kira wata huɗuba daban da sunan huɗuba garra;[13] kamar yadda cikin littafin Taisiru Al-maɗalib shi ma ya kira huɗuba mai labata 185 cikin nahjul balaga da suna huɗuba garra.[14] Sayyid Sadiƙ Musawi cikin littafin Tamamu Nahji Al-balaga, huɗuba mai lamba 237 a nahajul balaga yana ganin matsayin wani sashe daga wannan huɗuba.[15]
Jerin lambobin wannan huɗuba a cikin kwafi-kwafin nahajul balaga tare da bambance-bambance da aka samu.[16]
Sunan Kwafi | Lambar Huɗuba |
---|---|
Al-mujam Al-mufahras, Subhi Salihu | 83 |
Faizul Al-islam, Mulla Salihu, Ibn Abil Al-hadid | 83 |
Ibn Maisam | 82 |
Abduhu | 80 |
Mulla Fatahullahi | 84 |
Fi Zilal | 81 |
Bayanin Kula
- ↑ Hosseini Khatib, masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 103.
- ↑ Makarem Shirazi, Payame Imam Amirul Momineen (AS), 2006, juzu'i na 3, shafi na 459.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 243.
- ↑ Hosseini Khatib, masadir Nahj al-Balagheh, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 104.
- ↑ Nahj al-Balagha, Tas'hihu Sobhi Saleh, 1414 AH, Huduba ta 83, shafi na 114.
- ↑ Amin Naji wa Zahra Amini Armaki, “Barsi mabani inzar wa tabshir dar kutbeh garra,” shafi na 81.
- ↑ Hosseini Khatib, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 107.
- ↑ Hosseini Khatib, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 107.
- ↑ Ibn Shu'bah Harrani, Tuhaf al-Uqul, 1404 BC, shafi na 210.
- ↑ Isfahani, Hilyat al-Awliya’, Dar Umm al-Qura’, juzu’i na 1, shafi na 77-78.
- ↑ Don ganin sauran tushen wannan hadisin, duba: Dashti, takardu da takardun Nahj al-Balagha, 1378, shafi na 137-138.
- ↑ Duba: Ibn Abd Rabbah, al-Iqd al-Farid, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 163.
- ↑ Hosseini Khatib, Masadir Nahj al-Balagha, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 107.
- ↑ Harouni, Taisir al-Matalib, 1422H, shafi na 273.
- ↑ Mousavi, Tammam Nahj al-Balagheh, 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 367.
- ↑ Dashti, wa Kazem Mohammadi, Al-Mujam al-Mufahras Li alfaz Nahj al-Balagheh, 1375, shafi na 509.
Nassoshi
- Ibn Shu'ba Harrani, Hasan bin Ali, Tohaf al-uqool on Al-Rasul (SAW), Qum, Islamic Publications Office, 1404H.
- Ibn Abd Rabbah, Ahmed Ibn Muhammad, Al-Aqdo Al-Farid, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Ulamiya, 1407H. * Esfahani, Ahmad bin Abdullah, Hilya al-Awliya wa Tabaqat al-Asfiya, Alkahira, Dar Umm al-Qara, Bita.
- امین ناجی، محمدهادی، و زهرا امینی ارمکی، «بررسی مبانی انذار و تبشیر در خطبه غراء»، در مجله پژوهشهای اخلاقی، شماره ۵۲، تابستان ۱۴۰۲ش.
- Ansarrian, Hossein, Nahj al-Balagheh, Tehran, Payam Azadi, ya fassara, 2006.
- Ibn Abi al-Hadid, Abd al-Hamid bin Heba Allah, Sharhin Nahj al-Balagheh, bincike: Muhammad Abul Fazl Ibrahim, Kum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, 1404H.
- Hosseini Khatib, Sayyid Abdul Zahra, Masadir Nahj al-Balaghah wa Asanidah, Beirut, Dar al-Zahra, 1409H.
- Dashti, Mohammad, takardu da takardu na Nahj al-Balagheh, Qom, Amir al-Momenin (AS) Cibiyar Nazarin Al'adu, 1378.
- Dashti, Mohammad, da Kazem Mohammadi, Al-Mu'jajm Al-Mufars Lalfaz Nahj al-Balagheh, Qom, Amirul Mominin (AS) Cibiyar Nazarin Al'adu, 1375.
- Sayyed Razi, Muhammad bin Hossein, Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Kum, Hijira, 1414 H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Sakon Imam Amirul Momineen (AS), Tehran, Darul Katb al-Islamiya, 1386.
- Mousavi, Seyyed Sadegh, Tammam Nahj al-Balagheh, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1426 AH.
- Harouni, Yahya bin Saeed, Taysir al-Matlib fi Amali Abi Talib, Sana'a, Imam Zaid bin Ali al-Thaqfiyyah Foundation, 1422H.