Huɗubar Hazrat Zahra (S) A Taron Matan Madina
Huɗubar Hazrat Fatima (S) cikin taron matan garin Madina (arabic: خطبة السيدة فاطمة في نساء المدينة) ko Huɗubar duban mara lafiya, wani bayani ne na Hazrat Zahra (S) ƴar Annabi (S.A.W) da ta yi shi a taron matan Madina kan nuna rashin amincewarta da kwace halifanci, wannan ta yi shi ne tana kan shimfiɗar jinyar da ta yi daga rashin lafiya wacce cikinta ne ta yi shahada, wannan bayani ya ƙunshi zayyana halin da ake cikin bayan wafatin Annabi (S.A.W) da kuma gargaɗi kan makomar al’ummar musulmi, haka kuma bayani ne da yake tattare da fasaha da balaga da muhimmancin gaske. Hazrat Fatima (S) cikin Huɗubar duban mara lafiya cikin shelanta barranta daga masu karya alƙawari da kuma yin Allah wadai da masu karya alƙawari ta bayyana halin da ake ciki cikin wurare da dama, hasashen makoma mara daɗi ga musulmi, Siffofin mulkin Alawiyyawa, raunin tunani da sabanin ra'ayoyin mutanen Madina, nauyin da yake kan Musulmi cikin ƙalubalantar lalacewar hukuma, da kuma suranta haƙiƙanin fusƙar Saƙifa, cikin wannan huɗuba ta jingina da wasu adadin ayoyin Alkur’ani daga jumlarsu aya ta 80 suratul Ma’ida game da ƙarshen biyewa son rai, da kuma aya ta 96 suratul A’araf da aya ta 51 suratul Zumar dangane da zargin waɗanda basa ɗa’a ga gaskiya, da aya ta 35 suratul Yunus game da mutanen da suka cancanci jagoranci da shugabanci. Huɗubar Hazrat Zahra (S) cikin taron matan Muhajirun da Ansar ta zo ta hanyoyi daban-daban a litattafan riwaya na Shi’a da Ahlus-sunna, wannan huɗuba ta samu sharhi daban-daban daga masu bincike da nazarin addini cikin litattafan da aka wallafa dangane da rayuwar Hazrat Fatima (S).
Gabatarwa Da Muhimmanci
Huɗubar Hazrat Fatima (S) cikin taron matan Madina yayin da suka zo dubata, wata Magana ce ta Fatima (S) daga shimfiɗar jinyar da ta yi wacce ta kai ta ga shahada, ta yi wannan Magana ne gare su lokacin zuwa dubata. [1] dangane da su wanene suka zo dubata babu cikakken rahoto a kai, [2] na’am cikin littafin Balagatul An-Nisa’i, [3] da kuma Sharh Ibn Abi Al-Hadid kan Nahjul Balaga, [4] ya zo cewa wasu adadi daga matan Muhajirun da Ansar sun je gidan Fatima (S) duba ta, a Tarikh Yaƙubi an ambaci cewa matan Annabi (S.A.W) da wasu adadin Matan ƙuraishawa sun je duba ta. [5] Wasu ba’ari masu bincike, sun bayyana cewa bayanin da Fatima (S) ta yi ga taron matan da suka je duba ta, bayani ne da yake ɗauke da fasaha da balaga ya kuma ƙunshi ma’ana mai gigita tunani. [6] A cewarsu, saboda ilimin da Sayyida Fatima take da shi game da ci gaban al'ummar Musulunci na asali, kuma don samun tasiri ga masu saurarenta, ta yi amfani da jawabai da dama da suka hada, bayyanai masu gamsarwa da rarrashi a cikin wannan hudubar.[7] wannan matani yana hakaito tsinkaya da ilimin da Fatima take da shi dangane da abubuwan da suke faruwa a garin Madina. [8] Makarim Shirazi daga Maraji’an taƙlidi yana ganin wannan huɗuba daidai da huɗubar Fadak huɗuba ce da take tattare da ƙarfaffan sauti mai isar da saƙo da kuma jarumta, na’am wannan huɗuba tana da murya ta baƙin ciki da takaici, [9] a cewar Malamin duk da cewa Hazrat Zahra ta fuskanci zalunci mai yawa daga Azzalumai wanda sakamakon ciwo da suka jimata ne ma ta yi shahada, amma tare da haka cikin wannan huɗuba bata faɗi komai ba dangane da halin da take ciki ba, gabaɗayan bayanin cikin huɗubar ya karkata ne kan kwacen halifancin da aka yi wa Ali (A.S) da kuma gargaɗi da jan kunne kan hatsarin da yake fuskanto Al’ummar Musulmai daga karkacewa gaskiya, wannan alama ce ta irin yanda take fifita maslahar Muslunci da kuma muƙamin yarda da sallamawarta ga Allah. [10]
Muhallin Da Aka Koro Huɗubar
Hazrat Fatima cikin ƙarshen rayuwarta bayan harin da aka kai kan gidanta ta kwanta jinyar ciwon da suka jimata, sai matan Muhajirun da Ansar suka je dubata [11] dangane da dalilin da ya sa suka je dubata an ce mazajensu daga Muhajirun da Ansar sun zargi kawukansu kan abubuwan da suka faru bayan wafatin Annabi (S.A.W) a kanta, da wannan dalili suka tura matansu su je su dubata domin sassauta nauyin zunubin da suka aikata da kuma samun sauki a zukatansu. [12] haka kuma wasu sun tafi kan cewa hadafinsu ya kasance hadafi na siyasa da gyara dangantakarsu da Iyalan Annabi (S.A.W) tare da masu Mulki a lokaci da kuma sassauta damuwa a garin Madina, sun kasance daga haduffan ziyarar. [13]
Abin da Huɗubar Take ƙunshe Da Shi
Hazrat Zahra (S)
Hazrat Zahra (S): “na barranta da duniyarku, ina ƙiyayya da mazajenku, na jarraba halinsu da zancensu kuma daga abin da suka aikata na ji ba daɗi, na ajiye su a gefe guda.
cikin huɗubar ziyarar dubiya, cikin shelanta barranta daga masu karya alƙawari da yarjejeniya, [15] tare da Allah wadai kan mutanen da suka ƙi cika alƙawari da suranta abin da suka aikata daga saɓawa alƙawari, [16] sannan ta yi bayanin yanayin da ake ciki, tana mai hasashen makomar mara dadi ga Musulmi, da sifofin gwamnatin Alawiyya, raunin tunani da rarrabuwar ra'ayoyi da irin nauyin da ke wuyan mutane a kan fasadi da gwamnati take yi, da kuma fayya ce fuskar Mutanen Saƙeefa. [17] cikin wannan huɗuba ta jingina da ayoyin Alkur’ani daga jumlarsu aya ta 80 suratul Ma’ida dangane da makomar biyewa son rai, da kuma aya ta 96 suratul A’araf da aya ta 51 suratul Zumar cikin zargin rashin ɗa’a ga gaskiya da aya ta 35 suratul Yunus game da mutanen da suke da cancantar. jagoranci da shugabanci. [18]
Allah Wadai Da Mutane
Fatima Zahra (S) a farkon huɗubar ta fara da Allah wadai da Muhajirun da Ansar kan dalilin kasancewa tare da Masu Mulki cikin abubuwan da suka faru, [19] haka kuma da yin shirunsa kan karkacewa gaskiya da kuma kasancewarsu tare da masu mulki, [20] ta kwatanta su da misalin karyayyar Takobi da tsagaggun Masu, [21] a cewar Husaini Ali Muntazari wannan kwatantawa alama ce ta raunin tunani da rarabuwar ra’ayoyin musulmai kan abubuwan da suka faru bayan wafatin Annabi (S.A.W), [22] Hazrat Zahra (S) ta ɗora lefin kwace halifancin Imam Ali (A.S) kan wuyan Muhajirun da Ansar, saboda a kan idonsu aka yi komai amma sai suka biyewa ra’ayin Abi Yarima asha kiɗa da kuma hukuma, [23] kuma wannan abin kunyar zai ta binsu har abada,. [24]
Bayyana Dalilai Da Illolin Da Suka Sanya Imam Ali (A.S) Barin Halifanci
A gaɓa ta biyu cikin Huɗubar Fatima tana ganin hadafin da ya sanya Imam Ali (A.S) barin Halifanci shi ne ƙin yadda ya sallama da kuma jaraumtarsa a fagen yaƙi da Maƙiyan Muslunci, ɗanɗanar raɗaɗin Takobi da rashin damuwa da mutuwa, fushinsa cikin tafarkin Allah da kuma rashin sulhu da Maƙiya Allah. [25]
Siffofin Hukumar Ali
Fatima (S) cikin wani ɓangare na Huɗubarta ta yi ƙarin bayani cewa idan Ali (A.S) ya zama shugaba zai mulki mutane, zai banbance ƙarya da gaskiya, zai hana hukumarsa zama hukumar ƴan kama karya a hannun ragowar Arna Mushrikai da suka tsira. tausayawa da fatan alheri shugaba ga Musulmai da kaucewa kausasawa musu cikin hanyar shiriya, shayar da masu ƙishin adalci daga idaniyar ruwan haƙiƙa, da rashin ɗanfaruwar Shugaba kan al’amuran duniya, banbance maƙaryaci daga mai gskiya, kwararuwar albarka ga al’umma idan ta kiyaye tsoran Allah, sune alamomin irin wannan hukuma. [26]
Siffofin Azzaluman Shugabanni ƴan Kwace
Hazrat Zahra (S) a gaɓa ta uku ta bayyana mamakinta daga ayyukan Musulmai, da wannan da dalili ne suka biyewa maƙaryata suka zaɓi shugabanni marasa cancanta, da wannan fata ne suka aika irin wannan zalunci da rashin adalci haka, [27] wasu ba’ari sun ce me yiwuwa abin da take nufi cikin wannan gaɓa shi ne da wanne ƙarfaffan dalili da hujja ne ya sanya su watsi da misalin Hazrat Ali da Ahlul-Baiti (A.S) suka ajiye su a gefe suka zaɓi wasu mutane daban, [28] a cewarta mutane sun bar kai sun maƙale ga wutsiya, sun karkata zuwa ga Amawa sun watsi da Malami sun ajiye shi a gefe, suna raya cewa miyagun lefukansu matsayin kyawawan ayyuka, Fatima (S) tana ganinsu matsayin maɓarnata da suke kallon ɓarnar da suke yi matsayin gyara. [29]
Hasashen Makoma Ta Rashin Kwanciyar Hankali
Gargaɗi dangane da sakamakon da zai biyon bayan zaɓen tumun dare, gaɓa ta ƙarshe cikin huɗubar Fatima (S) cikin wannan ganawa da Matan Madina, ta kuma gargaɗi mutane da jan kunnensu da su guji neman nasara ta hanyar Takubba, da gwamnatin masu ƙetare haddi da iyakoki Azzalumai mashaya jini, tashen-tashen hankula, da kuma gwamnatin yan kama karya da ta lalata dukiyar al’umma da warwatsa su, [30] Makarim Shirazi yana cewa mai yiwuwa Fatima (S) tana ishara ne da hukumar Banul Abbas da ɗaiɗaikun mutane misalin Hajjaj Bn Yusuf da kuma abubuwa da suka faru daga baya misalin Waƙi’atu Harrra. [31]
Martanin Muhajirun Da Ansar Kan Maganar Fatima (S)
A cewar Suwaidi Bn Gafla bayan matan Madina sun gayawa Mazajensu Maganar da Fatima (S) ta yi wasu jama’a daga cikinsu sun je wurin Fatima (S) domin neman bata haƙuri da kuma neman yafiya da kuma fakewa da cewa sun riga sun yiwa Abubakar Bai’a kuma a shari’ance ba za su iya karya bai’arsu ba, saboda haka suna ganin suna da uzuri daga rashin taimakawa Ahlul-Baiti (A.S) bayan ta saurari bayanansu, sai ta ce: ku ta shi ku bani waje kada ku gaya min wata Magana baku da wani uzuri kan ayyukanku, [32] baku da wani uzuri da zaku kare kanku da shi kan ƙin kare gaskiya daga abubuwa masu hatsari da za su faru nan gaba duka lefin yana kanku. [33]
Masadir ɗin Huɗubar
Huɗubar Hazrat Zahra (S) cikin taron matan Muhajirun da Ansar, huɗuba ce daga aka rawaitota a hanyar Marawaita Ma’asumai da waɗanda ba Ma’sumai ba cikin litattafan Shi’a da Ahlus-Sunna. [34]wannan huɗuba an naƙaltota da wasu adadin sanadai [35] daga jumlarsu:
- Shaik Saduƙ cikin littafin Ma’ani Akhbar ta hanyoyi biyu, ɗaya daga cikinsu da isnadinsa daga Imam Ali (A.S) ɗayan kuma ya naƙalto shi ta hanyar Abdullahi Bn Hassan Bn Hassan daga Mahaifiyarsa Fatima ƴar Imam Husaini. [36]
- ɗabari cikin littafin Dala’ilul Al-Imamati cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) daga Kakansa Imam Sajjad (A.S) ya naƙalto wannan huɗuba. [37]
- Ibn ɗaifur da Ibn Abil Al-Hadid daga Malam Ahluss-Sunna cikin littafinsa mai suna Balagat An-Nisa’i. [38] Ibn Abi Al-Hadi [39] Atiyah Kufi ya ruwaito wannan hadisin.daga Suwaidi Bn Gafla, Haka nan Ahmad bin Ali Tabarsi ya ruwaito wannan hudubar a cikin littafinsa Al-Ihtjaj, inda ya ruwaito Suwayd bin Ghafla.[40] Allama Hilli, ya gabatar da Suwaidi cikin jerin Sahabban Imam Ali (A.S) [41] Allama Majlisi shima ya naƙalto wannan huɗuba daga littafin Al-Ihtijaj a laittafinsa Bihar Al-Anwar, [42] a cewar Husaini Ali Muntazari ɗaya daga waɗanda suka yi sharhi wannan huɗuba, Suwaidi Bn Gafla wanda ya rawaito wannan huɗuba ya muslunta tun zamanin Manzon Allah (S.A.W) kuma ya kasance mutum mai iklasi wanda Malaman Ilimin Rijal na Shi’a da Ahlus-sunna suka wassaƙa shi (lissafa cikin masu amana a naƙalin hadisi), [43]
Sharhi
Huɗubar Zahra (S) a taron matan Madina an yi sharhi kan cikin surar littafi mai cin gashin kansa haka kuma cikin litattafai.
- Malake Islam, Sharhin Huɗubar Fadakiyya da Huɗubar Hazrat Zahra (S) cikin taron matan Madina. Talifin Mirza Khalil Kamra’i. [44]
- Ranje Nameh Kausar Afrinesh-sharhi khuɗbe Dobom, Iyadat Zanane Muhajir wa Ansar Az Hazrat Zahra (S) Rubutun Sayyid Mujtaba Burhani.
- Sharh Khuɗbeh Hazrat Zahra (S) wa Majaraye Fadak, rubutun Husaini Ali Muntazari. [45] (Sharhe Do Fadakiyya wa Khuɗbe Iyadat).
- Bartari Banuye Jahan, talifin Nasir Makarim Shirazi, [46] Sharhe Do Khuɗbeh Fadakiyya a Iyadat, cikin rubutun tarihin rayuwar Hazrat Fatima tun daga haihuwarta har zuwa wafatin Annabi (S.A.W) da bayansa.
- Sireh wa Simaye Raihaneh Payambar (S.A.W) rubutun Ali Karami Faridani, [47] Sharhe Khuɗbehaye Hazrat Zahra dar Zimne tabyin Zindagi wa fada’il Hazrat Zahra (S) cikin ɓangarori 22.
Bayanin kula
- ↑ Ɗabarasi, al-Ihtijaj, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 108.
- ↑ Khashawi, Zindigani Siyasi Hazrat Fatima Zahra (AS), 1378, p...
- ↑ Ibn Tafur, Balagat al-Nisa, shafi na 19.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balagha, juzu'i na 16, shafi na 233.
- ↑ Yaƙoubi, Tarikh Yaƙoubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 115.
- ↑ Kerami, Sireh wa Simaye Raihane Payambar, Rayhana, 1380, shafi na 734.
- ↑ Khazaei et al., " Tahlil Kuhɗbeh Iyadat bar Paye Nazriyeh Kunehse Guftari", shafi na 7-8.
- ↑ Fatahizadeh wa Rasouli, "Isnadi wa Shuruhu Kuhuɗbehhaye Hazrat Zahra, Smalullahi Alaiha", shafi na 17-18.
- ↑ Makarem Shirazi, Zahra Bartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 211.
- ↑ Makarem Shirazi, Zahra Bartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 212-215.
- ↑ Khazaei et al., "Tahlil Kuhuɗbe Iyadat bar paye nazariyeh kuneshe guftar", shafi na 16.
- ↑ Kerami, Sireh wa simaye Raihaneh Payambar, 1380, shafi na 734.
- ↑ Khazaei et al., "Tahlil Khuɗbe Iyadat bar paye nazariyeh kuneshe guftar", shafi na 16.
- ↑ Rouhani, Zindigani Hazrat Zahra (Tajumeh juzu'i na 43 Bihar al-Anwar), 1377, shafi na 583-580.
- ↑ Porsaid Aghaei, “Khuɗbehaye Fatimah (A.S)”, shafi na 60.
- ↑ Montazeri, Khuɗbehaye Fatima Zahra, salamullahi Alaiha, wa majaraye Fadak, 1374, shafi na 379.
- ↑ Montazeri, Khuɗbe Fatima Zahra, salamullahi Alaiha, wa Majaraye Fadak, 1374, shafi na 371; Dashti, Farhang Sukhnane Hazrat Fatimah (A.S), 2013, shafi na 90-96; Kerami, Sirehe wa Simaye Raihaneh Payambar, 2013, shafi na 745-737.
- ↑ Porsaid Aghaei, Khuɗbehaye Fatimah (A.S)”, shafi na 60.
- ↑ Kerami,Sireh wa Simaye Rayhana Payambar, 2013, shafi na 737.
- ↑ Makarem Shirazi, Zahra Bartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 221.
- ↑ Kerami, Sireh wa Simaye Raihaneh Payambar, 2013, shafi na 738.
- ↑ Montazeri,Khuɗbeh Hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, 1374, shafi na 383-384.
- ↑ Montazeri,Khuɗbeh Hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, 1374, shafi na 385.
- ↑ Makarem Shirazi, Zahra Bartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 222
- ↑ Dashti, Farhang Hazrat Fatimah (S), 2013, shafi na 92; Montazeri, Sharhe Kuhɗbeh Hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, 1374, shafi na 393-395.
- ↑ Makarem Shirazi, ZahraBartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 227-228; Montazeri, Sharhe Khuɗbeh Hazrat Zahra, salamullahi Alaiha, 1374, shafi na 402-410; Kerami, Sireh wa Simaye Raihaneh Payambar, 2013, shafi na 741.
- ↑ Kerami,Sireh wa Samaye Raihaneh Payambar, 1380, shafi na 742-743;
- ↑ Montazeri, Sharhe khuɗbeh hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, 1374, shafi na 414.
- ↑ Dashti,Farhang Sukhnane Hazrat Fatimah (AS), 2013, shafi na 94-95.
- ↑ Kerami, Sireh wa Simaye Raihaneh Payambar, 1380, shafi na 744-745; Dashti, Farhang Sukhnane Hazrat Fatima (AS), 2001, shafi na 95.
- ↑ Makarem Shirazi, ZahraBartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 241-238.
- ↑ Montazeri, Sharhe Khuɗbeh Hazrat Fatima, Salamujllahi Alaiha, wa Majaraye Fadak, 1374, shafi na 424-426.
- ↑ Kerami, Sireh wa Simaye Raihaneh payambar, Rayhana, 2000, shafi na 748-749.
- ↑ Fatahizadeh da Rasouli, "Isnadi wa Shuruh Khuɗbehaye Hazrat Zahra", shafi na 18.
- ↑ Makarem Shirazi, ZahraBartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 215.
- ↑ Sheikh Sadouƙ, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 354-356.
- ↑ Tabari, Dala'ilul Al-Imamah, 1413 AH, shafi na 125.
- ↑ Ibn Tafur, Balagat al-Nisa, shafi na 19
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balagha, juzu'i na 16, shafi na 233.
- ↑ Tabarsi, al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 108.
- ↑ Allameh Hilli, Khulasatul Al-Akwal, 1417H, shafi na 163.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 43, shafi na 159.
- ↑ Montazeri, Kuhɗbeh Hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, wa Majaraye Fadak, 1374, shafi na 376-377.
- ↑ <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.erfan.ir/farsi/90949.html?search=ملکه%20اسلام#searchItem">نگاهی به کتاب «ملکه اسلام»، کتابی در شرح خطبه های حضرت زهرا(س)</a>
- ↑ Montazeri, Kuhɗbeh Hazrat Zahra, Salamullahi Alaiha, wa Majaraye Fadak, 1374, shafi na 371-428
- ↑ Makarem Shirazi, Zahra Bartarin Banuye Jahan, 1379, shafi na 211-247.
- ↑ Kerami, Sireh wa Simaye raihane Payambar (S.A.W), 1380, shafi na 733-749.
Nassoshi
- Ibn Abi al-Hadid, Abd al-Hamid bin Hebatullah, Sharhin Nahj al-Balaghah, ƙum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, 1404H.
- Ibn Tayfur, Abi al-Fazl Ahmed bin Abi Tahir, Balaghat al-Nisa, School of Insight, Bita.
- Burhani, Seyyed Mojtabi, Ranjnameh Kausar, Sharhe Khuɗbeh dobom wa Iyadat zanane Muhajir wa Ansar az hazrat Zahra, salamullahi Alaiha, ƙom, Hamasa ƙalam, 1399.
- Porsaid Aghaei, Seyyed Masoud, "Khuɗbehaye Fatimah (A.S), dar Daneshnameh,Fatemi karkashin kulawar Ali Akbar Rashad, juzu'i na 3, Tehran, Kungiyar Binciken Al'adun Musulunci da Tunani, 2013.
- خزاعی، محبوبه؛ خاکپور، حسین؛ حسومی، ولیالله <a class="eɗternal teɗt" href="http://hiƙ.bou.ac.ir/article_68781_fdeb5208ececfe0c66a1121bb4116486.pdf">تحلیل خطبه عیادت حضرت زهرا(س) بر پایه نظریه کنش گفتاری</a>
- Khashawi, Shaheen, Zindigani siyasi Hazrat Fatima Zahra Salamullah Alaiha, Tehran, Abid Publishing House, 1378.
- Dashti, Mohammad, Farhnag Sukhnane Fatima Zahra Salam Allah Alaiha, ƙum, Cibiyar Bincike ta Amirul Mominin, 2013.
- Rouhani, Mohammad, Zindigani Hazrat Zahra, salamullahi Alaiha, Tarjumeh Juzu'i na 43 na Bihar al-Anwar, Tehran, Mahammad Publishing House, 1377.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Ma'ani Al-Akhbar, ƙum, ofishin buga littattafan musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Kum, 1403H.
- Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtjaj Ala Ahli Al-laJajj, Mashhad, Morteza Publishing House, 1403H.
- Tabari Amoli Saghir, Muhammad bin Jarir bin Rostam, Dala'ilul Al-Imamah, ƙum, bugun Ba'ath, 1413H.
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Khulasatul Al-Aƙwal fi ilimil Al-Rijal, ƙum, Al-Fiƙahah Publication Institute, 1417H.
- فتاحیزاده، فتحیه، رسولی راوندی، محمدرضا<a class="eɗternal teɗt" href="http://ensani.ir/file/download/article/20150922133110-9849-180.pdf">«اسناد و شروح خطبههای حضرت زهرا سلام الله علیها»</a>
- Karmi Faridni, Ali, Sireh wa Simaye Raihane Payambar (S.A.W) da bayyanarsa, ƙum, Dail Mawallafi, 1380.
- Majlesi, Mohammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Makarem Shirazi, Nasser, Zahra (s) Bartarin Banuye jahan, ƙom, Sarwar Publishing House, 1379.
- Montazeri, Hossein Ali, Sharhe Khuɗbeh Hazrat Zahra wa Majaraye Fadak, ƙum, ofishin Sayyid Ayatullah Uzma Montazeri, 1374.
- Yaƙoubi, Ahmed bin Ishaƙ, Tarikh Yaƙoubi, Beirut, Dar Sadir, B.