Nasibi

Daga wikishia

Nasibi (Larabci: ناصبي) shi ne wanda yake Kiyayya da Imam Ali (A.S) ko kiyaya da daya daga Ahlil-Baiti (A.S) kuma yake bayyanar da kiyayyarsa gare su, ko inkarin Falalolinsu, haka ana kidaya Zagi da La’antar A’imma da `Yan Shi’arsu a Matsayin Misdakan Nasibanci. A ra’ayin Malaman Fikihu na Shi’a Nasibawa Najasa ne kuma ana musu hukunci daya da Kafirai, da wannan dalili baya halasta cin Naman Abinda suka yanka da basu Sadaka da auratayya da su, kuma basu da hakkin yin Gado, a cewar ba’arin wasu Malamai masu zurfafa bincike a wannan zamani, Nasibanci ya fa bullowa ne da Kashe Usman Bn Affan sannan a lokacin Daular banu Umayya ya samu gatan hukuma, hana yaduwar Falalolin Ahlil-Baiti, kashe `Yan Shi’a da Zagin Imam Ali (A.S) a kan Mimbarori suna daka cikin Sakonni Nasibanci a lokacin Daular Banu Umayya, Mu’waiya Bn Abi Sufyan, Kawarijawa Usmaniyyawa, da Hariz Bn Usman suna daga bayyanannun Nasibawa. Malaman Shi’a sun yi rubuce-rubuce daban-daban dangane da Nasibawa da Nasibanci, daga jumlarsu akwai misalin littafin (An-nasbu wan-Nawasibu) talifin Muhsin Mu’allim, Risalar (Ash-Shihabus As-Sakibu fi Bayani Ma’anal An-Nawasib) talifin Muhaddis Bahrani, da Risalar (Malun An-nawasibi wa Annahu Laisa Kulli Mukalif Nasiban) talifin Sayyid Abdullahi Jaza’iri.

Sanin Mafhumi

Nasabu yana nufin yin kiyayya da Ahlil-Baiti ko kiyayya da Masoyansu da bayyanar da kiyayyar, [1] da wannan ne kiyayya da `Yan Shi'a Masoyan Ahlil-Baiti [2] da `Yan Shi’a [3] ana kirga shi cikin Nasibanci kadai cikin kasancewa ana kinsu saboda suna son Ahlil-Baiti [4] da da’a gare su [5] Mashhur din Malaman Musulmi kadai suna ganin Nasibi cikin Mutumin da yake kiyayya da Ahlil-Baiti kuma ya bayyana kiyayyarsa gare su [6] a cewar wasu wanda ya riki Gaba da Imam (A.S) wani yanki na addininsa [7] Mutumin da yake imani da cewa Imam Ali (A.S) ya Kafirta ko a matsayin Fasiki [8] imani da fifita wasu kansa [9] tare da zagi da la’antar Ahlil-Baiti [10] da inkarin Falalolin Ahlil-baiti, [11] da kuma jin baya son a ambace su ko yada darajojinsu [12] Hassan Bn Farhan Maliki daga Malaman Ahlus-Sunna yana ganin kowanne irin nau’in karkata daga barin Imam (A.S) da Ahlil-Baiti a matsayin Misdakin Nasibanci [13] haka kuma raunana ingantattun Hadisai na yabon Imam Ali (A.S) Ahlil-baiti , Imani da kuskuren Imam Ali (A.S) cikin Yakokin da ya yi a lokacin Halifanci da ya yi da wuce gona da iri cikin yabon Makiyansa da shakka da kokwanto cikin Halifancinsa da kin yi masa Mubaya’a duka suna daga Misdakan Nasibanci da kiyayya da Imam Ali (A.S) [14] kari kan wannan Muhaddis Bahrani daga Malaman Fikihu na Shi’a yana ganin Gabatar da wasu Mutane kan Imam Ali (A.S) cikin Imamanci da yarda da Imanancinsu ba komai bane illa tsantsar kiyayya da Ali da Nasibanci [15]

Rashin Tabbatuwar Nasibancin Ahlus-sunna

Mashhur din Malaman Fikihu na Shi’a, suna ganin Nasibi shi ne mutumin da yake kiyayya da gaba da Ahlil-Baiti kuma ya bayyanar da kiyayyarsa a fili, da wannan dalili ne basa hukunta Ahlus-sunna da suke bayyana soyayya ga Ahlil-Baiti da cewa Nasibawa [16] amma Muhaddis Bahrani ya tafi kan cewa Nasibi shi ne wanda ya fifita wasu mutane kan Imam Ali kuma yake Imani da Imamanci wadannan da fifita kansa [17] Madogar Malamin wata riwaya ce da ta kunshi bayanin cewa Imani da Imamanci sabanin na A’imma (A.S) Nasibanci ne [18] Mawallafin littafin Jawahir Kalam yana ganin wannan Magana ta sabawa Sira da aikin `Yan Shi’a [19] sannan ya yi shakku kan ingancin Isnadi da Ma’anar Riwayar [20] akwai Risala me suna (Malun An-nawasibi wa Annahu Laisa Kulli MUkalif Nasibi) da aka danganta ta da Sayyid Abdullahi Jaza’iri Malamin Shi’a da cikin wannan Risala aka hakaito rashin amincewarsa kan hukunta Ahlus-sunna da Nasibanci [21]

Hukuncin Nasibi

A ra’ayin Malaman Fikihun Shi’a Nasibawa Najasa ne [22] kuma suna cikin hukuncin Kafirai, [23] cikin litattafan fikihu akwai bahasi mai taken Najasantuwar Kafirai wanda ya hada da Magana kan Nasibanci da Nasibi, [24] ba’arin hukunce-hukuncen Nasibawa sun kasance kamar yanda bayani zai zo a kasa:

Bayyanar Nasibanci

Wasu ba’arin masu zurfafa bincike sun yi Imani da cewa Nasibanci ya fara bayyane bayan Kashe Usman Bn Affan ya kuma samu Lasisi a lokacin Gwamnatin Banu Umayya [33] a rahotan da Masadir din Tarihi suka kawo, Mu’awiya Bn Abi Sufyan lokacin da da yana Mugiratu Bn Shu’uba Gwamna a Kufa Shekara ta 41 h kamari ya bashi umarni da ya zagi Imam Ali (A.S) sannan ya bata sunan Sahabban Imam (A.S) [34] bayan Mu’awiya Halifofin Banu Umayyawa sun cigaba da zagin Imam Ali (A.S) a kan MImbarori [35] har zuwa lokacin Halifancin Umar Bn Abdul-Aziz [36] Hakim Naishaburi Malamin Ahlus-sunna ya siffanta karni na hudu h kamari da Karni da ya Gurbata da Kiyayyar Imam Ali (A.S) da wannan dalili ne ma ya mike ya rubuta littafin Fada’il Fatima Zahara domin kishiyanta da yakar mummunar al’adar gaba da Ahlil-Baiti (A.S) cikin siffanta halin karni na hudu ya rubuta cewa: Allah ya jarrabce mu da wasu Shugabanni da Mutane suke samun kusanci wurinsu da Kiyayya da Iyalan Manzon Allah (S.A.W) da kaskantar da su [37]

Sakonni

Cikin ba’arin Sakonni da Nasibanci a daurorin Hukumar Banu Umayya:

  • shigo da Kirkirarrun Riwayoyi cikin litattafan Ahlus-sunna da nufin raunana Ahlil-Baiti da Inkarin Falalolinsu ta hannun Nasiban Marawaitan Hadisi. [38]
  • Hana sanya sunayen Ahlil-Baiti kan `ya`yan da aka Haifa, da kashe duk wanda aka sa masa suna da Ali [39]
  • Hukunta Mutanen da suke yada Falalolin Imam Ali (A.S) da bayaninsu ko kuma kin yarda su yi kiyayya da shi, da kin yarda su nakalci wata Falala ga Mu’awiya, wani lokacin tana kaiwa ga kashe su, Misali Hajjaju Bn Yusuf Sakafi [40] ya bada umarnci An yiwa Adiyya Bn Sa’ad Bulala wanda ya kasance daga `Yan Shi’ar Imam (A.S) da kuma Kashe Ahmad Bn Ali Nasa’i daya daga cikin Marubutan Sihahu Sitta na Ahlus-Sunna [41] duka suna daga misalsalan wannan fage. [42]

Sanannun Nasibawa

Cikin Masadir akwai wasu ba’arin muane da suka shahara da Nasibanci;

  • Mu’awiya Bn Abi Sufyan, Sarki na Farko daga Umayyawa wanda ya yi Mulki kusan tsawon shekaru 20 a garin Dimashk (Siriya) [43] Ibn Abil Al-Hadid Mu’utazili wanda ya yi sharhin Nahjul Balaga, ya nakalto daga Jahiz cewa Mu’awiya yana La’antar Ali (A.S) a karshen hudubarsa ta Sallar Juma’a yana cewa wajibi ayi ta yada la’antarsa har ta kai ga babu wanda zai nakalto wata Falala da darajarsa [44]
  • Usmaniyyawa, mutane ne masu tuhumar Imam Ali da Hannu cikin Kashe Usman Bn Affan [45] da wannan dalili ne suka ki yi masa Mubaya’a [46] Ibn Hajar Askalani Masanin Ilimin Rijal na Ahlus-Sunna a karni na tara h kamari, ya bayyana Nasibawa matsayin wasu jama’a da suka yi Imani da cewa Imam Ali (A.S) ya taimaka cikin Kashe Usman Bn Affan [47] wadannan Jama’a sakamakon wuce gona da iri cikin soyayyarsu ga Usman Bn Affan sun karkata zuwa ga Sukan Imam Ali [48]
  • Kawarijawa, wasu jama’a ne da suka kasance daga cikin Sojojin Imam Ali (A.S) a lokacin Yakin Siffin da suka dawo suna tuhumar Ali Bn Abi Talib da Kafirta suka kuma yi masa Bore da tawaye, sakamakon kiyayyarsu da shi suma ana kiransu da Nasibawa ko Nasiba [49]
  • Hajjaj Bn Yusuf Sakafi wanda ya mutu a shekara ta 95, a cewar Mas’udi marubucin tarihi a karni na hudu hakika Hajjaju ya kasance yana kiyayya da Ahlil-Baiti [50] ya kasance yana kashe wadanda suka ki barranta daga Imam Ali da Sahabbansa [51] ya kasance yana kama `Yan Shi’a da kashe su da mafi kankantar zargi da tuhuma, a lokacinsa yafi sauki a zargeka da kafirta da Zindikanci daga a zargeka da kasancewa cikin `Yan Shi’ar Hazrat Ali (A.S), [52] Hajjaju da farko a lokacin Mulkin Abdul-Malik Bn Marwan an nada shi Gwamna a HIjaz daga baya kuma a ka dawo da shi Irak [53]
  • Hariz Bn Usman, mutumin da ya kasance yana La’antar Imam Ali (A.S) a kan Mimbari [54] shi ne Mutumin da ya kasance yana canja Lafazin Hadisin Falalar Imam Ali (A.S)
انت منی بمنزلة هارون من موسی

Sai ya canja shi da lafazin:

انت منی بمنزلة قارون من موسی

[55]

A cewar Ibn Hibban daya daga Masana Ilimin Rijal wurin Ahlus-Sunna, Hariz Bn Usman ya kasance a kowacce rana yana La’antar Ali Bn Abi Talib (A.S) sau saba’in Safe da Yamma [56]

  • Mugira Bn Shu’uba, lokacin da Mu’awiya ya nada shi Gwamna a garin Kufa ya kasance yana zagin Imam Ali da `Yan Shi’arsa a kan Mimbari [57] Mugira ya kasance daga cikin Sahabban Annabi ya bayyana gudummawar da ya bayar a kai hari kan gidan Hazrat Zahara (A.S) [58]
  • Mutawakkil, Mutum ne da kasance yana tsananin kiyayya da Imam Ali (A.S) kuma Masoyi ne ga Makiyan Imam Ali (A.S) [59] mutum ne da ya kasance yana kwace dukiyar `Yan Shi’a da kuma Kashe su, [60] kiyayyar Mutawakkil ga Ahlil-Baiti (A.S) ta kai haddin da a shekara ta 236 ya bada umarnin ruguje Kabarin Husaini Bn Ali (A.S) da wannan dalili ne gidajen da suke kusa da Kabari da wadanda suke kewaye da shi duk suka ruguje ya sakar musu ruwa ya mayar da wurin wajen Noma da shuka [61]
  • Ibn Taimiyya, daya daga Masu yiwa Salafiyya Tunani, wasu ba’ari daga masu zurfafa binciken ilimi daga Shi’a kan tabbatar da Nasibanci Ibn Taimiyya sun jingina da tare da kafa Hujja kan raunata Hadisan falalar Imam Ali (A.S0 da ya yi misalin Hadis Raddu Shamsi, [62] Hadis Ghadir [63]da kuma kiyayarsa ga `Yan Shi’a, [64] haka kuma Ibn Hajar Askalani ya ce wasu ba’arin Malamai sun jingina Munafunci ga Ibn Taimiyya sakamakon Maganganun da ya yi kan Hazrat Ali, Ibn Taimiyya yayi Imani da cewa Imam Ali (A.S) ya tafka kuskure a wurare goma sha bakwai cikin Tafsirin Kur’ani [65]

Litattfai

Malamai da Masu zurfafa bincike na Shi’a sun yi rubuce-rubuce kan Ma’anar Nasibanci [66] Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418H, shafi na 588-590.daga cikinsu akwai:

  • An-Nasabu wan-Nawasibu, talifin Muhsin Mu’allim an rubuta shi cikin Harshen Larabci, wannan littafi ya kunshi bayani kan ma’anar Nasibanci da Misdakansa [67] Hukunce-hukuncensa [68] da kufaifayin Nasibanci [69] marubucin ya bayyana Gaba da kiyayya da Imam Ali (A.S) su ne Sikelin na gane wane ne Nasibi [70] ya kawo sunayen Mutane fiye da 200 wanda ake tuhuma da Nasibanci [71] haka kuma ya kawo sunayen Yankuna da Nasibawa suka rayu a Tarihi [72] cibiyar Intiharatul Darul Huda ta buga wannan littafi a shekara 1418 h kamari Bairut [73]
  • Ashhihabus As-Sakib fi Bayan Ma’anal An-Nawasib, talifin Muhaddis Bahrani [74] haka kuma Risalar (Usulul Islami wal-Imani wa Hukmil An-Nasibi wa-ma yata’allaku Bihi) talfin Wahidul Bahbahani [75] duka suna daka litattafan da aka wallafa kan Nasibanci da Nasibi.

Haka kuma cikin rubuce-rubuce da aka yi don Raddi kan Talifofin Masu sabani da Shi’a an yi amfani da Kalmar Nasibawa [76] misalin: Almasa’ibul An-nawasib fi Raddi Alan Nawakidil Ar-Rawafid, Talifin Khadi Nurullahi Shushtari [77] da kuma littafin Ba’adul Masalibil An-Nawasib fi Nakadi Ba’adi Fada’ihil Arrawafid, Abdul-Jalil Kazwini [78] haka kuma cikin littafin An-Nasbu wan-Nawasibu an ambaci talifi 29 da aka cikin wannan fage [79]

Bayanin kula

  1. Turaihi, Majma Al-Bahraini, 1416 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 174.
  2. Shahid Sani, Rouz Al-Janan, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 420.
  3. Ibn Idris Hali,Ajwiba Rasa'il wa masa'il, 1429H, shafi na 227; Najafi, Jawaharlal Kalam, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 64.
  4. Shahid Sani, Rouz Al-Janan, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 420.
  5. Turaihi, Majma Al-Bahraini, 1416 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 174.
  6. Misali, duba: Shahid Sani, Rouz Al-Janan, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 420; Bahrani, Al-Hada'eq Al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 5, shafi na 186, juzu'i na 24, shafi na 60; Sobhani, Al-Khumusu, 1420 AH, shafi na 60.
  7. Ibn Taimiyyah,Majumu'atu Al-Fatawa, bugun Abd al-Rahman bin Qasim, juzu'i na 4, shafi na 429; Firouzabadi, Qamoos Al-Muhit, labarin shigarwa, Tarihi ya nakalto, Majma al-Baharin, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 173.
  8. Ibn Taimiyyah, Majmu'atu Al-Fatawa, bugun Abd al-Rahman bin Qasim, juzu'i na 4, shafi na 429.
  9. Fazel Moqdad, Al-Tanqih Al-Ra'e, 1404 AH, Juzu'i na 2, shafi na 421.
  10. Fazel Moqdad, Al-Tanqih Al-Ra'e, 1404 AH, Juzu'i na 2, shafi na 421.
  11. Fazel Moqdad, Al-Tanqih Al-Ra'e, 1404 AH, Juzu'i na 2, shafi na 421.
  12. Shahid Sani, Rouzul Al-Janan, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 420.
  13. Maliki, Enqaz Al-Tarikh Al-Islami, 1418H, shafi na 298.
  14. Maliki, Enqaz Al-Tarikh al-Islami, 1418H, shafi na 298.
  15. Bahrani, Al-Hada'eq Al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 24, shafi na 60.
  16. Misali, duba: Sadouq, Man la Yahdrah al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi:408; Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 64.
  17. Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 24, shafi na 60.
  18. Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 18, shafi na 157
  19. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 64.
  20. Tolayi, “Malak Nasiba Angari, Ahkam wa Asar Murattab bar Nasabi dar fikihi Imamiyya”, shafi na 52.
  21. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Mujalladi na 19, shafi na 76.
  22. Sadr, Ma wara'a Al-fikh, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 145.
  23. Misali duba: Tusi, Al-Nehaya, 1400H, shafi na 5.
  24. Misali, duba: Najafi, Jawaherul Kalam, 1404 AH, juzu’i na 6, shafi 63-65; Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 5, shafi na 185-177.
  25. Tusi, Tahzib Al-Ahkam, juzu'i na 9, shafi na 71; Imam Khumaini, Risalah Al-Najat, 2005, shafi na 325.
  26. Sadouq, Man Laihdrah al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 408; Mohaghegh Karki, Jame al-Maqassed, 1414 AH, juzu'i na 13, shafi na 15.
  27. Ibn Baraj, al-Mahazzab, 1406 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 129.
  28. Tusi, Al-Nehaya, 1400 AH, shafi na 112.
  29. Mohaghegh Hilli, Al-Mu'utabar, 1407 AH, Mujalladi na 2, shafi na 766.
  30. Behjat, Jami'u Al-Masa'il, 1426 AH, juzu'i na 6, shafi na 156.
  31. Imam Khumaini, Rasal Al-Najat, 2005, shafi na 309.
  32. Tusi, Al-Nehaya, 1400 AH, shafi na 570.
  33. Kothari,"Barasi Rishahaye Tariki Nasibigeri", shafi na 99
  34. Balazri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 5, shafi na 243; Tabari, Tarikh al-umAm Wa al-Muluk, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 254.
  35. Zamakhshari, Rabi'ul Al-Abrar, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 335.
  36. Ibn Athir, Al Kamil, 1385 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 42.
  37. Mai mulkin Nishaburi, Fadael Fatima al-Zahra, 1429H, shafi na 30.
  38. Kothari, "Barasi Rishehaye Tariki Nasibgeri", shafi na 104.
  39. Mezi, Tahdhib Al-Kamil, 1413 AH, juzu'i na 20, shafi na 429.
  40. Ibn Sa’ad, Tabaqat Al-Kubra, 1410H, juzu’i na 6, shafi na 305.
  41. Ibn Kathir, Al-Bedaya wa Al-Nehaya, 1407H, juzu'i na 11, shafi na 124.
  42. Kothari, "Barasi Rishehaye Tariki NasibGeri", shafi na 104-105.
  43. Ibn Abd al-Barr, Al-Isti'yab, 1412 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 1418.
  44. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 4, shafi na 56-57.
  45. Muallem, Al-Nasb wa Al-Nawasib, 1418H, shafi na 591.
  46. Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1387H, juzu'i na 4, shafi na 430.
  47. Ibn Hajar, Tahdhib al-Tahdhib, Dar Saddir, juzu'i na 8, shafi na 458.
  48. Ibn Hajar, Fathul Bari, 1408H, juzu'i na 7, shafi na 13.
  49. Muqrizi, Al-Mowa'iz wa Al-Etebar, 1425-1422 AH, juzu'i na 4, kashi na 1, shafi na 428.
  50. Duba Masoudi, Moruj al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 144.
  51. Mughniyeh, Al-Shia wal Al-Hakimun, 2000 AD, shafi na 94-96.
  52. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 11, shafi na 44.
  53. Ibn Kathir, al-Bedaya wa al-Nehaya, 1407H, juzu'i na 9, shafi na 117.
  54. Samani, Al-Ansab, 1382 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 95.
  55. Ibn Hajar, Tahzeeb al-Tahzib, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 239
  56. Ibn Hajar, Tahzeeb al-Tahzib, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 240.
  57. Ibn Kathir, al-Bedaya wa al-Nehaya, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 50.
  58. Mufid, Al-Jamal, 1413 AH, shafi na 117.
  59. Khuzari, Jihar Al-Abbasiya, 1422H, shafi na 248.
  60. Khuzari, Daulatu Al-Abbasiya, 1422H, shafi na 248.
  61. Khuzari, Daulatu Al-Abbasiya, 1422H, shafi na 248.
  62. Ibnu Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah, 1406 Hijira, Juzu'i na 8, shafi na 165, Al Mujaddad ya nakalto, "Nashanahaye Nasibgeri Ibn Taimiyya", shafi na 17.
  63. Ibnu Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah, 1406 Hijira, Juzu'i na 7, shafi na 319-320, an karbo daga "Nashanahaye Nasibgeri Ibn Taimiyya", shafi na 19.
  64. Al Mujaddad, “Nashanahaye Nasibgeri Ibn Taimiyya”, shafi na 17-25.
  65. Ibn Hajar, Al-Durarul Al-Kamenatu, 1392 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 155 da 181
  66. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418H, shafi na 588-590.
  67. Moalem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418 AH, shafi na 31-38
  68. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418 AH, shafi na 624-605.
  69. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418H, shafi na 588-590.
  70. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418H, shafi na 37.
  71. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418 AH, shafi na 528-261.
  72. Muallem, Al-Nasb da Al-Nawasb, 1418H, shafi na 229-244.
  73. <a class="external text" href="http://pdf.lib.eshia.ir/94626/1/1">«النصب و النواصب».</a>
  74. Bahrani, al-Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 3, shafi na 405.
  75. Agha Bozor Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 176.
  76. Muallem, Al-Nasb da Al-Nasbi, 1418H, shafi na 588-590.
  77. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Mujalladi na 19, shafi na 76.
  78. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, juzu'i na 3, shafi na 130.
  79. Muallem, Al-Nasb da Al-Nasbi, 1418H, shafi na 588-590.

Nassoshi

  • Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'a al-Tsanif al-Shia, Qum and Tehran, Ismailian Islamic Library na Tehran, 1408H.
  • Alu MUjaddid Sayyid Hassan «نشانه‌هایی از ناصبی‌گری ابن‌تیمیه»،
  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharh Nahj al-Balaghah, wanda: Ibrahim Muhammad Abul Fazl, Qum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, ya inganta shi, 1404H.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Al-Kamil fi Al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir, 1385H/1965 Miladiyya.
  • Ibn Idris Hilli, Muhammad bin Mansour, Ajwibatul Rasa'il wa Masa'il, editan Seyyed Mohammad Mahdi bin Seyyid Hasan Mousavi Khorsan, Qum, Dilil Ma, 1429H.
  • Ibn Baraj Tripolisi, Abdul Aziz, Al-Mahazzab, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary Society of Teachers, 1406H.
  • Ibn Taimiyyah, Ahmed bin Abdul Halim,Majmu'u Al-Fatawi, edition of Abdul Rahman bin Qasim, B.
  • Ibn Taimiyyah, Ahmed bn Abdul Halim, Minhaj Sunna Nabawi fi Nakadi ala Kalam Rafida Alkadariyya Al-Qadariyyah, Bincike: Muhammad Rashad Salem, Imam Muhammad Bin Saud Islamic University, 1406 AH/1986 AD.
  • Ibn Hajar Askalani, Ahmad Bn Aliالدرر الکامنه فی اعیان المائة الثامنه، بیروت، دار الجیل.
  • IBn Hajar Askalani, Ahmad Bn Aliتهذیب التهذیب، بیروت، دار صادر، بی‌‎تا.
  • Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Tabaqat al-Kubari, bincike: Muhammad Abdulkadir Atta, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1410 AH/1990 AD.
  • Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiyab fi Marafah al-Ashab, bincike: Ali Muhammad Bejawi, Beirut, Dar al-Jubeil, 1412 AH/1992 Miladiyya.
  • Ibn Kathir Damaschi, Ismail Ibn Umar, Al-Bedayah da Al-Nehayah, Beirut, Darul Fikr, 1407 AH/1986 Miladiyya.
  • Imam Khumaini, Ruhollah, Risala Najat al-Abad, Tehran, Imam Khumaini Editing and Publishing Institute, 1385.
  • Bahrani, Yusuf bin Ahmad, al-Hadaiq al-Nadrah fi Hakam al-Utrah al-Tahirah, edita: Mohammad Irwani da Seyyed Abd al-Razzaq Mokaram, Kum, gidan buga littattafai na Musulunci mai alaka da al'ummar hauza ta Kum, shekara ta 1405 bayan hijira. .
  • Balazri, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf (Juzu'i na 5), ​​Bincike: Ehsan Abbas, Beirut, Jamiat Al-Mustareqin al-Almaniyeh, 1400 AH/1979 Miladiyya.
  • Behjat, Mohammad Taqi, Jame'i Al-Masail, Qum, ofishin Ayatullahi Behjat, 1426H.
  • تولایی، رحمت، نقیبی، سید ابوالقاسم، «ملاک ناصب‌انگاری، احکام و آثار مترتب بر نصب در فقه امامیه»، در مجله فقه و اصول، بهار ۱۳۹۶ش.]
  • Hakim Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, Fada'el Fatima Al-Zahra, bincike: Alireza bin Abdullah, Alkahira, Darul Furqan, 1429H.
  • Khuzari, Muhammad, Daulatu Al-Abbasiya, Beirut, Alam al-Katb, 1422H.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Rabi'ul Al-Abrar da Nasus al-Akhbar, Research: Mehna Abdul Amir, Beirut, Scientific Institute for Press, 1412 AH.
  • Sobhani, Ja'afar, al-Khumsu fi Al-Shari'a Al-Islamiya al-Ghara, Qum, Imam Sadiq Institute, 1420H.
  • Samaani, Abdul Karim bin Muhammad, Al-Ansab, bincike: Abdul Rahman bin Yahya Maalami Yamani, Hyderabad, Majlis Al-Ma'arif al-Othmaniyah, 1382/1962 miladiyya.
  • Shaheed Thani, Zain al-Din bin Ali, Rauzul Al-Janan fi Sharh Irshad al-Azhan, Qum, gidan buga littattafai na Musulunci mai alaka da al'ummar Qum Seminary, 1402H.
  • Sadr, Seyyed Muhammad, Ma Wara'a Fiqhu, Jafar Hadi Djili, Beirut, Darul-Azwa Lalprinta da Al-Nashar da al-Tuziya, 1420H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Man Lai Hazara Al-Faqih, Qum, ofishin da'a na Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, 1413 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-umam wa Al-Muluk, bincike: Muhammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, Darul-Tarath, 1387H/1967 Miladiyya.
  • Turaahi, Fakhreddin, Majma Al-Baharaini, editan Seyyed Ahmad Hosseini, Tehran, kantin sayar da littattafai na Mortazavi, 1416H.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Nehaya fi Magdar Lafiqah wa al-Fatawi, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1400H.
  • Fazil Moqdad, Moqdad bn Abdullah, Al-Tanqeeh Al-Ra'e f al-Makhtasar al-Sharia, gyara daga Seyyed Abdul Latif Hosseini Koh-Kamri, Qum, Ayatollah Murashi Najafi Library Publications, 1404 AH.
  • Kausari Ahmad «بررسی ریشه‌های تاریخی ناصبی‌گری»،
  • Maliki, Enqaz al-Tarikh al-Islami, Jordan, Al-Imamah Al-Hafiya Foundation, 1418H.
  • Mohagheq Hilli, Jafar bin Hossein, al-Mu'utabar fi Sharh al-Mukhtasar, editan: Muhammad Ali Heydari da sauransu, Qum, Cibiyar Sayyid al-Shahada, 1407H.
  • Mohagheg Karki, Ali bin Hossein, Jame al-Maqasad fi Sharh Al-Qasas, Qom, Al-Bayt Institute, 1414 AH.
  • Mezi, Yusuf bin Abdurrahman, Tahzeeb al-Kamaal fi Asma al-Rajal, Research: Bashar Awad Ma'rouf, Beirut, Al-Rasalah Institute, 1413 AH/1992 AD.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Murujul Al-Dahab wa Maaden Al-Jawhar, bincike: Asad Daghar, Qum, Dar Al-Hijrah, 1409H.
  • Muallem, Mohsen, Al-Nasb da Al-Nawasb, Beirut, Dar Al-Hadi, 1418 AH/1977 Miladiyya.
  • Mugniyya Muhammad Jawad الشیعه و الحاکمون،
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Jamal wa al-Nusra na Sayyid al-Utrah fi Harb al-Basra, editan: Ali Mirshrifi, Kum, Sheikh Mofid Congress, 1413H.
  • Moghrizi, Ahmed bin Ali, Al-Mo'a'az da Al-Lagham fi Zikr Al-Shat'ar da Al-Anqir, Bincike: Ayman Fouad Seyed, London, 1422-1425 AH/2002-2004 AD.
  • Najafi, Mohammad Hassan, Jawaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, ya gyara shi: Abbas Quchani, Ali Akhundi, Beirut, Darahiya al-Tarath al-Arabi, 1404H.