Jump to content

Huɗubar Ashbahu

Daga wikishia
Huɗuba Ashbahu
Maudu'iSiffanta Allah. Mala'iku
Ya Fito DagaImam Ali (A.S)
Asalin MarawaiciMas'ada Bin Sadaƙa
Ingancin IsnadiIngantacce
Madogaran Shi'aAt-Tauhid. Nahjul Balaga
Madogaran Ahlus-sunnaRabi'ul Abrar. Al-Iƙdul Farid
Hadis Silsilatuz ZahabHadis SaƙlainiMaƙbulatu Umar Bin HanzalaHadis Ƙurbu NawafilHadis Mi'irajHadis WilayaHadis WisayaHadis Junud Aƙli Wa JahalHadis Shajara


Huɗubar Ashbahu (Larabci: خطبةالأشباح) Tana ɗaya daga jerin huɗubobin cikin nahajul balaga da suke Magana game da batun sanin Allah, Ibn Abil Al-Hadid cikin bayaninsa game da irin ƙima da muhimmancin da wannan huɗuba take da shi yana cewa: Misalin bambancin da yake tsakanin wannan huɗuba da misalin zancen Larabawa mai cike da fasaha kamar misalin bambancin da yake tsakanin ƙasa da zinare ne, Sayyid Ibn Ɗawus bisa lura da ƙimar matanin wannan huɗuba, ya ce babu kokwanto ko kaɗan game da ingancin wannan huɗuba.

Wannan huɗuba baya ga nahajul balaga ta zo cikin sauran madogaran Shi'a da Ahlus-sunna, ba'ari daga cikin bahasosi da aka bijiro da su a wannan huɗuba su ne kamar haka: Siffofin Allah, kasancewar kur'ani ma'auni cikin sanin sunayen Allah da siffofinsa, rashin tsinkayen mutum kan zatin Allah da siffofinsa, halittar mala'iku, siffofi da halayensu, tsinkayen ubangiji kan bakiɗayan sirrikan ɗan Adam.

An rubuta litattafai daban-daban game da wannan huɗuba, daga jumlarsu: Ali (A.S) Wa Salikin Rahe Shaiɗan (Faujul Muƙtaham), talifin Abdul-Ali Guyasti.

Gabatarwa

Huɗubar Ashbahu ɗaya ce daga jerin huɗubobin cikin nahajul balaga da suke cike da maɗaukakan ma'anoni.[1] Ibn Abil Al-hadid ɗaya daga cikin waɗanda suka rubuta sharhi kan nahajul balaga, cikin bayanin balaga da fasahar wannan huɗuba ya ƙiyastata da zancen larabawa da yake cike da fasaha , ya ce misalin wannan huɗuba da misalin zancen larabawa da yake cike da fasaha kamar misalin ƙasa da zallan zinare ne.[2]

Bisa naƙalin Sayyid Radiyu wanda ya haɗa littafin nahajul balaga, Imam Ali (A.S) ya yi bayanin wannan huɗuba ne lokacin da wani mutum ya buƙaci ya siffanta masa Allah, an ce yana so Imam ya siffanta masa Allah kamar yana ganinsa a gaban idanunsa, kan asasin wannan naƙali Imam Ali (A.S) wannan buƙata da wannan mutumi ya yi daga gare shi ta fusata shi matuƙa, ya tara mutane yah au mimbarin masallacin kufa ya yi wannan huɗuba.[3] game da mene ne ya fusata shi daga roƙonsa da wannan mutumi ya yi, an bijiro da uzurori daban-daban, daga jumlarsu akwai tsammanin cewa wannan mutumi yana jira Imam ya yi siffanta masa Allah da siffofin halittu domin ya samu damar ganin Allah ko suranta shi a kwakwalwarsa,[4] da kuma cewa ta yiwu duk da cewa musulmi sun ɗau dogon lokaci suna rayuwa kan fahimtar addinin muslunci amma tare da haka har zuwa yanzu ba su fahimci siffofin Allah ba.[5]

Lambobin jerin wannan huɗuba cikin mabambantan kwafi-kwafin na nahajul balaga:[6]

Sunan Kwafi Lambar Huduba
Al-mujam Al-mufahras, Subhi salihu 91
Faizul Al-islam, Sharhu Khuui, Mulla Salihu Mazandarani, Ibn Abil Al-hadid 90
Ibn Maisam 88
Abduhu 87
Mulla Fatahullahi 97
Fi Zilal 89

Sanya Suna

An ambaci bayanan da za su a ƙasa game da dalilin sanyawa huɗubar suna Ashbahu:

  • "Ashbahu" kinaya ce kan mala'iku kuma wani sashi daga huɗubar ya ƙunshi wannan batu;[7]
  • Kalmar “Ashbahu” da aka yi amfani da ita cikin wannan huɗuba ta zo daga ba'arin naƙali,[8] ba daga nahajul balaga ba,[9]
  • Ashbahu ma'ana duk wani da ake hango inuwarsa daga nesa ba tare da tantance haƙiƙaninsa ba; sakamakon cikin wannan huɗuba an kawo abubuwa da ba su bayyanu ba sosai ga mai sauraro aka kirata da suna Ashbahu.[10]

Abin da Yake Ciki

Ba'arin bahasosi da aka yi bayaninsu cikin wannan huɗuba, sun kasance kamar haka:

  • Ambato ba'arin siffofin Allah,
  • Kasancewar kur'ani ma'auni cikin sanin sunaye da siffofin Allah,
  • Rashin tsinkaye ɗan Adam kan haƙiƙanin zati da siffofin Allah,
  • Hikimar Allah cikin halittar duniya
  • Halittar sammai tare da ɗaukaka,
  • Halittar mala'iku da ke ɓantattun siffofinsu,
  • Halittar ƙasa, halittar Annabi Adam (A.S) da aiko da Annabawa;
  • Tsinkayen Allah kan bakiɗayan sirrikan ɗan Adam.[11]

Inganci

A imanin Sayyid Ibn Ɗawus marubucin Farajul Al-mahmum, cikin auna ingancin wannan huɗuba babu buƙatar bahasi da bincike game da isnadinta, saboda matanin wannan huɗuba ya girmama da babu wanda zai iya bayanin waɗannan l, afuzza sai wanda ya kasance ma'asumi.[12] Huɗuba ashbahu tana cikin shahararrun huɗubobin Imam Ali (A.S) da suka shahara tun kafin Sayyid Radiyu ya haɗa littafin nahajul balaga.[13] wannan huɗuba ƙari kan naƙalto ta cikin madogaran shi'a misalin Kitabul At-tauhid na Shaik Saduƙ,[14] da Taisiru Al-maɗalib na Yahaya ɗan Husaini Haruni daga malaman zaidiyya,[15] an naƙalto a litattafan Ahlus-sunna misalin Al-iƙdul Al-farid,[16] da Rabi'ul Al-abrar.[17]

A cewar Sayyid Abdul-Zahra Al-husaini Al-khaɗib marubucin littafin Masadir Nahji Al-balaga, Sayyid Radiyu ya naƙalto wannan huɗaba ne daga littafin Khuɗab Amiril Al-muminin (A.S), talifin Mas'adatu ɗan Sadaƙa; saboda a wani ɓangare, Sayyid Radiyu a farkon wannan ya yi bayani ƙarara a fili cewa ya naƙalto ta ne daga Mas'adatu ɗan Sadaƙa daga Imam Sadiƙ (A.S), a wani ɓangare daban kuma Mas'adatu an ce Mas'adatu yana littafi mai suna “Khuɗab Amiril Al-muminin, wannan littafi yana nan har zuwa zamanin Sayyid Hashim Bahrani marubucin Kitabul Al-burhan.[18]

Nazari

Littafin Tabi'at Dar Kutbe Ashba, Na Muh'sin Sitaregi

An rubuta litattafai daban-daban game da huɗuba Ashbahu, daga jumlarsu za a iya ishara da sunaye wanda za su a ƙasa:

  • Ali (A.S) Wa Salikine Rahe Shaiɗan (Fauju Muƙtaham), talifin Abdul-Ali Guya: kamfanin Dalilima suka buga shi a shekara ta 2007 m, littafi ne da yake ɗauke da shafuka 424.[19]
  • Ɗabi'at Dar Khuɗbeh Ashbahu Nahje Al-balaga, na Muhsin Sataregi, kamfanin Intisharat Desara a garin Rashti suka buga wannan littafi mai ɗauke da shafi 160.[20]

Bayanin kula

  1. Makarem Shirazi, Payame Imam Amirul Muminin (AS), 1386 Hijira Shamsiyya, Jild na 4, Shafi na 16
  2. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahjul Balagha, 1404 Hijira Kamariyya, Jild na 6, Shafi na 425
  3. Nahjul Balagha, wanda Subhi Salih ya gyara, yana dauke da jawabai, wasiku, da hikimomin Imam Ali (AS). A cikin khutba ta 91, Imam Ali yana bayani kan adalci, hikima, da halin shugabanci.
  4. Hashimi Khuyi, Minhaj al-Bala'a, 1400 Hijira Kamariyya, Jild na 6, Shafi na 287
  5. Makarem Shirazi, Payame Imam Amirul Muminin (AS), 1386 Hijira Shamsiyya, Jild na 4, Shafi na 19
  6. Dashti da Kazem Mohammadi, Al-Mu'jam Al-Mufahras li-Alfaz Nahj al-Balagha, 1375 Hijira Shamsiyya
  7. Makarem Shirazi, Payame Imam Amirul Muminin (AS), 1386 Hijira Shamsiyya, Jild na 4, Shafi na 18
  8. Al-Tawhid na Sheikh Saduq An rubuta shi a shekara ta 1398 Hijira Kamariyya Shafi na 79
  9. Makarem Shirazi, Payame Imam Amirul Muminin (AS), 1386 Hijira Shamsiyya, Jild na 4, Shafi na 18
  10. Shahidi, Tarjame Nahjul Balagha, 1378 Hijira Shamsiyya, Shafi na 471
  11. Subhi Salih, 1414 Hijira Kamariyya, Khutba ta 91, Shafuka 124-136
  12. Faraj al-Mahmum" na Sayyid Ibn Tawus , shekara ta 1368 Hijira Kamariyya shafi na 56
  13. Al-Husayni Al-Khatib, Masadir Nahjul Balagha, 1409 Hijira Kamariyya, Jild na 2, Shafi na 164
  14. Littafin "Al-Tawhid" na Sheikh Saduq A cikin shafuka 48-56
  15. Littafin "Taysir al-Matalib" , A cikin shafuka 287-289, shekara ta 1407 Hijira Kamariyya
  16. Littafin "Al-'Aqd al-Farid" na Ibn Abd Rabbih. A cikin jild na 4, shafuka 196-198,
  17. Littafin "Rabi' al-Abrar" na Zamakhshari, A cikin jild na 1, shafuka 310-312
  18. Littafin "Masadir Nahjul Balagha" na Al-Husayni Al-Khatib, A cikin jild na 2, shafi na 164,
  19. Goya, Ali Wa Salikin Rahe Shaitan, 1386, shafi na Shaidar dan kasa
  20. Mohsen Stergi
    Littafin "Tabi'a a cikin Khutba Ashbah na Nahjul Balagha

Nassoshi

  • Ibn Abd Rabbihi, Ahmad bin Muhammad, Al-'Iqd al-Farid, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, 1407H.
  • Al-Husayni Al-Khatib, Sayyid Abdul Zahra, Masadir Nahj al-Balagha wa Asanidihi, Beirut, Dar al-Zahra, 1409H.
  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatu-llah, Sharh Nahj al-Balagha, bincike: Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Qom, Laburaren Ayatollah Mar'ashi Najafi, 1404H.
  • Dashti, Muhammad, da Kazim Muhammadi, Al-Mu'jam al-Mufahras li-Alfaz Nahj al-Balagha, Qom, Cibiyar Al'adu da Bincike ta Amir al-Mu’minin (A), 1375 SH.
  • Zamakhshari, Mahmud bin Umar, Rabī‘ al-Abrār wa Nusūs al-Akhbār, Beirut, Mu'assasat al-A‘lamī lil-Matbū‘āt, 1412H.
  • Sutargi, Mohsen, Yanayi a cikin Khutbar Ashbah na Nahjul Balagha, Rasht, Dahsara, 1392SH.
  • Sayyid Ibn Tawus, Faraj al-Mahmum fi Tarikh Ulama' al-Nujum, Qom, Dar al-Dhakha'ir, 1368H.
  • Sayyid Radi, Muhammad bin Husayn, Nahj al-Balagha, fassara: Sayyid Ja‘far Shahidi, Tehran, Kamfanin Buga Littattafai na Ilimi da Al’adu, 1377SH.
  • Sayyid Radi, Muhammad bin Husayn, Nahj al-Balagha, fassara: Nasir Makarim Shirazi, Qom, Madrasar Imam Ali bin Abi Talib (A), 1384SH.
  • Sayyid Radi, Muhammad bin Husayn, Nahj al-Balagha, gyara: Subhi Salih, Qom, Hijrat, 1414H.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Al-Tawhid, Qom, Ofishin Bugawa na Islamic Publications, 1398H.
  • Guya, Abdul Ali, Ali (A) da Masu Bin Hanyar Shaitan, Qom, Dalil Ma, 1386SH.
  • Makarim Shirazi, Nasir, Payan Imam Amir al-Mu’minin (A), Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1386SH.
  • Haruni, Yahya bin Husayn, Taysir al-Matalib fi Amali Abi Talib, Sana'a, Mu'assasat al-Imam Zaid bin Ali al-Thaqafiyya, 1422H.
  • Hashimi Khuyi, Mirza Habibullah, Minhaj al-Balaghah fi Sharh Nahj al-Balagha, Tehran, Maktabat al-Islamiyya,