Jump to content

Sallah

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne game da siffanta wani mafhumi na fiƙihu, kuma ba zai iya zama ma'aunin ayyukan addini ba. domin ayyukan addini a koma zuwa ga wasu madogaran daban.
Risala Ilmiyya

Sallah (Larabci: الصلاة) ita ce mafi muhimmancin ayyukan ibada da ta tattaro zikiri da keɓantaccen motsi. a cikin riwaya an siffantata da "Ginshiƙin addini" kuma "Sharaɗin karɓar sauran ayyuka" sallah ta na da keɓantattun ladubba da hukunce-hukunce, daga jumlarsu akwai gabatar da alwala da fuskantar alƙibla, haka nan kuma ana yin sallah cikin shakali biyu ko dai cikin sallar jam'i ko ɗaiɗaiku, sai dai cewa kuma an yi wasicci da yin sallah cikin jam'i.

Sallah ta kasu gida biyu, sallolin wajibi da na mustahabbi: sallolin wajibi su ne: sallolin farilla na yau da gobe, sallar ayoyi, sallar ɗawafi, sallar gawa, sallolin ƙara'i na iyaye da sallar bisa sababin bakance, alƙawari da rantsuwa, duka su na daga sallolin wajibai. nafilolin yau da gobe su ma su na daga sallolin mustahabbi.

Cikin riwayoyin an yi bayanin illolin da barin sallah da sakaci da ita suke haifarwa daga jumlarsu akwai haramtuwa daga samun ceton Ahlil-Baiti, jinkirta sallah daga farkon lokacinta da yin sallah ba tare da ƙanƙan da kai da kai da kuma kushu'i ana ƙidaya su daga misdaƙin sakaci da kuma wulaƙanta sallah, haka nan kuma an bayyana tunawa da Allah, fito na fito da shirka da bautar gumaka, ƙauracewa fasadi da ɓarna matsayin hikimomin wajabta sallah. Hatta cikin sauran addinai akwai sallah sai dai cewa kawai yanda ake yinta a kowanne addini yana biye da koyarwar wannan addini.

Matsayi Da Muhimmanci

[1] an ambaci sallah cikin Kur'ani [2] ɗaiɗai har karo 98. Bisa ayoyin Kur'ani haƙiƙa sallah ta na hana mutum aikata zunubi,[3] tsanin masu gaskiya, [4] taimakon mutum cikin matsaloli, [5] ta na daga muhimman wasiyyoyin Allah ga Annabawa,[6] kuma ta na daga abubuwan da Annabawa suka himmatu kansu musammam kan iyalansu.[7] Sallah ta na daga laruran addinin muslunci[8] wata ibada ce bisa fatawar malaman fiƙihu bai halasta a barta ba cikin kowanne irin hali[9] barin sallah ya na daga manya-manyan zunubai[10] kuma alama ce ta kafirci da munafunci[11]. Cikin litattafan Wasa'ilul Ash-Shi'a da Al-Mustadrak an naƙalto hadisai fiye da 11600 game da sallah.[12] cikin litattafan fiƙihu akwai sashe da aka keɓance wanda ya tattaro hukunce-hukunce da ladubban sallah. [13]

Akwai rubuce-rubuce na musammam da aka yi su game da sallah waɗanda zuwa shekara 1998 m, ƙididdigarsu sun kai adadin 2000 daga risaloli litattafai da ma waƙoƙi.[14] zuwa shekara 2019 m, an gina masallaci miliyan uku da dubu ɗari shida a faɗin duniya domin yin sallah.[15] haka nan kuma akwai wurare da aka keɓance su domin sallah a kan hanyoyi da wuraren taron mutane daga kasuwanni da makarantu DSS. A cewar Muhammadi Raishahri wanda ya rasu shekara 2022 m, a farkon muslunci sallah ta fara wajaba ne a garin makka.[16] kan asasin wata riwaya daga littafin Biharul Al-Anwar, an naƙalto cewa, kwana ɗaya bayan aiko Annabi (S.A.W) ya yi sallah tare da Imam Ali (A.S) Hazrat Khadija da wasu mutane.[17]

Jumlolin Da Aka Yi Amfani Da Su Cikin Riwayoyi Game da Sallah

Kyakkyawab zanen rubutun Hadisin الصَّلوَةُ عِمَادُ الدِّين na Abdur-Rahim Kahya

Yanda Ake Yin Sallah

Halin daidaituwar jiki a ruku'u
Raka'ar Farko

Yanayin Daidaituwar Jiki A Halin Ruku'u Da farko mu na farawa da yin alwala, bayan nan sai mu tsaya mu fuskanci alƙibla tare da yin niyya, bayan nan sai kabbarar harama: ma'ana mu ɗaga hannuwanmu zuwa kusa da saman kunnuwa mu ce "Allahu Akbar" bayan nan sai mu fara da karanta suratul Fatiha da wata surar daban, bayan mun gama sai mu rankwafa ruku'u mu karanta zikirin ruku'u sai mu ɗago sama mu miƙe tsaye sannan mu durkusa sujjada mu yi zikirin sujjada, sannan mu ɗago daga sujjada mu zauna sannan mu ƙara tafiya sujjada ta biyu nan ma mu yi zikirin sujjada.[32] zikirin ruku'u shi ne "Subhana rabbiyal Al-Azim wa bihamdihi" zikirin Sujjada kuma "Subhana rabbiyal Al-A'ala wa bihamdihi" ko kuma mu karanta "Subhanallahi" ƙafa uku-uku cikin ko wace sujjada da ruku'u.

Raka'a Ta Biyu
Halin daidaituar jiki a sujjada

Halin Daidaituwar Jiki A Halin Sujjada Bayan ɗagowa daga sujjada ta biyu za mu miƙe tsaye mu daidaita a tsaye kamar dai raka'a ta farko mu karanta suratul hamdi da wata surar daban, sannan sai mu yi alƙunut, mu na ɗaga tafin hannunmu ya na kallon sama, bayan gama alƙunut sai mu rankwafa zuwa ruku'u mu yi zikirin ruku'u, bayan ɗagowa daga ruku'u za mu tsaya a tsaye kamar dai raka'a ta farko sannan mu durƙusa zuwa sujjada mu yi sujjada ta biyu.[33] cikin alƙunut za mu karanta addu'ar:

«رَبَّنا آتِنا فِی الدُّنْیا حَسَنَةً وَ فِی الْآخِرَةِ حَسَنَةً وَ قِنا عَذابَ النَّار»

[Tsokaci 1]

Ko wata addu'a da zikiri na daban ba wannan ba.[34]

Tashahhud
Halin daidaitar jiki a zaman tashahhud da sallama

Halin Daidaituwar Jiki A Tashahhud Cikin Sallah Bayan sujjada ta biyu za mu zauna kan gwiwowinmu biyu mu yi tashahhud kamar haka:

(«اَشْهَدُ اَنْ لااِلهَ اِلاَّ الله وَحْدَهُ لاشَرِیكَ لَهُ، وَاَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَداً عَبْدُهُ وَ رَسُولُه، اَلّلهُمَّ صَلِّ عَلی مُحَمَّد وَ آلِ مُحَمَّد)[Tsokaci 2] .[[35]]
Sallama

Cikin Sallolin masu raka'a biyu bayan tashahhud za mu sallama mu idar da sallah kamar haka:

(«اَلسَّلامُ عَلَیْكَ اَیُّهَا النَّبِیُّ وَ رَحْمَةُ الله وَ بَرَکاتُهُ، اَلسَّلامُ عَلَیْنا وَ عَلی عِبادِ الله الصّالِحینَ، اَلسَّلامُ عَلَیكُمْ وَ رَحْمَةُ الله وَ بَرَکاتُهُ)[Tsokaci 3].[[36]]
Raka'a Ta Uku Da Ta Huɗu

Bayan karanta tashahhud sai mu miƙe tsaye mu yi tasbihohi huɗu kamar haka:

(سُبْحانَ الله وَ الْحَمْدُ لِله وَ لا اِلهَ اِلّا الله وَ الله أكْبَر)

[Tsokaci 4]

Bayan gamawa, sai mu rankwafa ruku'u mu ɗago mu ta fi sujjada bayan ɗagowa daga sujjada ta biyu a cikin sallar mai raka'a uku zamu zauna zaman tashahhud bayan tashahhud sai mu yi sallama. sannan cikin sallar mai raka'o'i huɗu bayan ɗagowa daga sujjada ta biyu cikin raka'a ta uku za mu miƙe tsaye mu karanta tasibihatul arba'a (tasbihohi guda huɗu ) kamar haka: (سُبْحانَ الله وَ الْحَمْدُ لِله وَ لا اِلهَ اِلّا الله وَ الله أكْبَر), [Tsokaci 5] sannan mu rankwafa ruku'u bayan ɗagowa daga ruku'u mu ta fi sujjada bayan ɗagowa daga sujjada ta biyu sai mu zauna zaman tashahhud bayan tashahhud sai mu yi sallama.[37]

Hukunce-hukunce Da Ladubban Sallah

Wajiban Sallah
Asalin Maƙala: Wajiban Sallah
Hotan turba da ake dora goshi a kanta yayin sujjada

Wajiban sallah wasu sasannin asalin sallah ne waɗanda a bisa ra'ayin mashhur ɗin malaman fiƙihu sun kasance kamar haka: niyya, tsayuwa, kabbarar harama, ruku'u, sujjada, karatun fatiha da sura, zikiri (misalin zikirin ruku'u ko na sujjada), tashahhud (zaman tahiyya), sallama, tartibi (jerantawa) da muwalat (rashin dogon jinkiri) (ma'ana kawo sassan sallah daki-daki ba tare da jinkirtawa ba).[38] wajiban sallah sun kasu gida biyu daga wajibai na rukuni da wanda ba na rukuni ba, wajiban sallah biyar na farko sun kasance daga rukunan sallah waɗanda idan aka yi ƙari cikinsu ko ragi da ganganci ko mantuwa sallah ta na ɓaci, sai sauran wajibai shida wanda ba na rukuni ba waɗanda ƙari ko ragi cikinsu yana ɓata sallah idan ya kasance bisa ganganci.[39]

Abubuwan Da Suke Ɓata Sallah

Koyar da sallah daga littafin Hadiyye Asiman na `yan makarantar primary

Sallah ta na ɓaci da ɗaya daga Abubuwan da za su zo a ƙasa:

  • Hadasul Akbar (Abin da yake sa yin wanka) ko kuma hadasul asgar (Abin da yake warware alwala).
  • Ganganci yin magana.
  • Kyakyacewa da dariya bisa ganganci.
  • Takattuf: (ɗora hannu kan hannu).
  • Kuka da gangan tare da ɗaga sauti saboda sabgogin duniya.[40]
  • Faɗin Amin bayan karatun Fatiha.
  • Duk wani aiki da zai rusa fuskar sallah, misalin wasan miƙe hannuwa sama da sauke su ƙasa ko yin tafi.
  • Ci da sha.
  • Yin Shakka cikin raka'o'in da aka gama yinsu cikin salloli masu biyu da raka'a uku, ko cikin raka'a ta farko a sallah mai raka'o'i huɗu.
  • ƙari ko ragi cikin wajibai na rukuni da gangan ko bisa rafkanwa, ko kuma ƙari da ragi cikin wajiban da ba na rukuni ba bisa ganganci.[41]

Sauran Hukunce-hukunce

Sallar Jam'i tare da jagoracin Ayatullahi Mar'ashi Najafi a Haramin Hazrat Ma'asuma (S)
  • Alwala: wajibi ne yin alwala domin sallolin wajibi.[42] a wasu wuraren maimakon alwala ana yin taimama, kamar lokacin da aka rasa ruwan yin alwala, ko kuma amfani da ruwa zai iya cutarwa ko kuma ƙurewar lokaci.[43]
  • Wurin Sallah: an yi bayani wasu adadin sharuɗɗa game da wurin da za a yi sallah; daga jumlarsu dole ya kasance halastaccen wuri ba na kwace ba, dole ya kasance tabbatacce baya motsawa, tsarkakakke ba najasa ba, wurin da za a ɗora goshi kada ya fi inda za a ɗora gwiwowi tudu fiye da tudun yatsu huɗu ko zurfinsa ya zurfafa fiye da gwargwadon yatsu huɗu.[44]
  • Tufafin mai sallah: wajibi namiji ya lulluɓe al'aurarsa guda biyu, mace kuma wajibi ne ta lulluɓe baki ɗayan jikinta, na'am ba wajibi ba ne lulluɓe zagayen fuskarta da tsintsiyar hannuwanta.[45]
  • Sallar ƙasaru: wajibi matafiyi ya wadatu da yin raka'a biyu maimakon raka'a huɗu cikin salloli masu raka'o'i huɗu.[47] domin tabbatuwatar tafiya ta shari'a akwai buƙatar cika wasu adadin sharuɗɗa, daga jumlarsu dole nisan tafiya da dawowa ya kai farsakin shari'a (tsakanin kilo mita 40 zuwa 45).[48]

ladubban Sallah

ladubba da mustahabbai da aka yi bayani cikin sallah sun kasance cikin sharhin da zai zo kamar haka: yin sallah a farkon lokacinta, yin ado yayin sallah, yin sallah a masallaci cikin jam'i, addu'a a farkon sallah, halarto da zuciya tare da khushu'i,[49] bayan sallah akwai wasu ayyuka da ake yi bayan idar da sallah da ake kiransu da sunan ta'aƙibat; misalin karanta ayatul kursiyyu, karanta tasbihin Hazrat Zahra (A.S) sujudul shukri.[50] ba'arin wannan ayyuka sun zo cikin littafin Mafatihul Al-Jinan.[51]

Sallolin Wajibi Da Na Mustahabbi

Rubutun Hannu na Sayyid Ali Khazi
Asalin Maƙala: Sallolin Wajibi

Sallolin wajibi salloli ne da yin su ya zama tilas, idan ya zamana ba a yi su ba har lokacinsu ya fita, wajibi ne a rama su, waɗannan salloli su ne kamar haka:

  • Sallolin yau da gobe: raka'o'i goma sha bakwai cikin mabambantan lokuta guda biyar Asubahi, azuhur, la'asar, magariba da isha'i).
  • Salatul ayat: sallah ce da ake yin ta lokacin afkuwar bala'o'in ɗabi'a misalin girgizar ƙasa, kisfewar rana ko wata.
  • Sallar gawa: sallah ce da ake yi kafin binne gawa, ana yinta kan gawar mamaci musulmi, haka nan bai halasta ba a binne musulmi kafin yi masa sallah.

Sallolin Mustahabbi

Asalin Maƙala: Sallolin Mustahabbi

Sallolin mustahabbi ko nafila, salloli ne da ba wajibi ba ne a yi su, tare da haka an yi umarni da wasicci kan yin su; misalin nafilolin yau da gobe.[53] sallolin mustahabbi dukkaninsu raka'a biyu-biyu ne in banda sallar witiri.[54]

Illolin Sakaci Da Sallah

Tushen Kasida: Sakaci Da Sallah

Imam Sadik (A.S)

«إِنَّ شَفَاعَتَنَا لَا تَنَالُ مُسْتَخِفّاً بِالصَّلَاة؛

mai sakaci da sallah ba zai samu cetonmu ba

Shaik Saduk, Amali, bugun shekara ta 1376. h.shamsi. shafi na 484

Annabi (S.A.W)

«مَن اَحسَنَ صَلاتَه حتّى تَراها الناس، وَ أساءَها حينَ يَخلو، فَتِلکَ استهانة؛

duk wanda yake kyaunta sallarsa a gaban idon mutane, sannan yake munanata a bayan idon mutane, lallai wannan abun da yake yi wulaƙanta sallah ne.

Nuri, Mustadrakul Alwasa'il, bugun shkeara ta 1408,h,ƙ. juzu'i na 3 shafi na 26

  • Jarrabtuwa da wahalhalu da halaye goma sha biyar: bisa dogara da riwaya daga Annabi da yake magana da Hazrat Fatima (S) an naƙalto daga gare shi cewa: duk wanda yake wasa tare da sakaci da sallah, Allah zai jarrabce shi da wahalhalu goma sha biyar.

1. Rashin albarkar rayuwa; 2. Rashin albarkar dukiya; 3. Rashin hasken fuska; 4. Rashin samun ladan ayyuka; 5. Rashin amsa addu'a;[57] 6. Rashin amfanuwa da addu'ar mutane; 7. Mutuwa a wulaƙance; 8. Mutuwa cikin yunwa; 9. Mutuwa cikin ƙishi, cikin yanayin duk yanda ya kai da shan ruwa ba zai gushe ba cikin ƙishi; 10. Mala'ika zai dinga yi masa azaba cikin ƙabarinsa; 11. Duhun ƙabari; 12. Matsar ƙabari; 13. Ranar alƙiyama Mala'ika zai jashi kan fuskarsa sauran halittu suna kallo; 14. Fuskantar hisabi mai tsanani ranar alƙiyama; 15. Allah ba zai masa kallon rahama ba, kuma zai fuskanci azaba mai raɗaɗi;[58] Jinkirta yin sallah a kan lokacinta bisa ganganci[59] da kuma yin sallah ba tare da ƙanƙan da kai da kushu'i ba ana ƙidaya hakan daga misdaƙan sakaci da sallah.[60]


Domin neman ƙarin bayani ku duba wannan Maƙala: Tarikul Salati.

Bambance Bambance cikin Sallah Tsakanin Mazhabar Shi'a da Mazhabar Ahlus-sunna

Bambance Bambance tsakanin sallah a mazhabar Shi'a da mazhabobin Ahlus-sunna
Take Shi'a Maliki Shafi'i Hanafi Hanbali
Karatun suratul Hamdi wajibi ce cikin raka'a ta farko da ta biyu wajibi ce cikin bakidayan raka'o'in sallolin farilla da mustahabbi wajibi ce cikin bakidayan raka'o'in sallolin farilla da mustahabbi wajibi ce cikin raka'a ta farko da ta biyu wajibi ce cikin bakidayan raka'o'i.[61]
Karanta bismilla a farkon sura bangare ce daga sura da karatunta wajibi ne rashin karanta ta mustahabbi ne bangare ce daga sura da karatunta wajibi ne rashin karanta ta halas ne bangare ce daga sura karatunta wajibi ne.[62]
Ƙunut mustahabbi ne cikin bakidayan salloli a iya sallar asuba ya halasta a iya sallar asuba ya halasta a iya sallar witiri yake halas a iya sallar wutiri yake halas.[63]
Jaharu da Ikfat cikin bangarorin sallah yin jaharu cikin sallolin asuba da magariba da isha, da kuma ikfat cikin sallolin azuhur da la'asar wajibi ne Jaharu cikin sallolin asuba, magariba da isha, mustahabbi ne jaharu cikin sallolin asuba, magariba da isha, ikfat cikin sallolin azuhur da la'asar mustahabbi wajibi ne babu wajabcin yin jaharu ko ikfat a dukkanin sallolin wajibi da mustahabbi jaharu wajibi ne cikin sallolin asuba magariba da isha.[64]
Takattuf (Ɗora hannun dama a kan na hagu) Haramun ne, a ra'ayin mashhur yana bata sallah ya halasta amma ba wajibi bane ko mustahabbi mustahabbi ne kuma sunna ne mustahabbi ne kuma sunna ne mustahabbi ne kuma sunna ne[65]
Faɗin Amin bayan karatun suratul hamdi haramun ne kuma yana bata sallah mustahabbi ne mustahabbi ne mustahabbi ne mustahabbi ne.[66]
Ruku'u da ɗumanina; nutsuwa cikin ruku'u rankwafawa gwargwadon yanda hannun zai isa gwiwar ƙafa ɗumanina cikin ruku'u rankwafawa gwargwadon yanda hannu zai kai ga gwiwar ƙafa wajibi ne haka ɗumanina cikin ruku'u rankwafawa gwargwadon yanda hannu zai kai ga gwiwar ƙafa wajibi ne haka ɗumanina cikin ruku'u rankwafawa kaɗai ta waatar sannan ba dole bane ayi ɗumanina rankwafawa gwargwadon yanda hannu zai kai ga gwiwar ƙafa wajibi ne haka ɗumanina cikin ruku'u.[67]
Zikirin ruku'u wajibi ne ba wajibi bane mustahabbi ne ba wajibi bane mustahabbi ne ba wajibi bane mustahabbi ne wajibi ne.[68]
Miƙewa tsaye bayan ruku'u wajibi ne wajibi ne wajibi ne ba wajibi ne ba wajibi ne.[69]
Gaɓoɓin sujjada yayin yin sujjada, goshi, tafukan hannaye da ƙafafuwa, gwiwowin ƙafafu da yatsu biyu na ƙafafu wajibi ne ya zamana sun taɓa ƙasa wajibi ne goshi ya taɓa ƙasa amma sauran Gaɓoɓin su mustahabbi ne wajibi ne goshi ya taɓa ƙasa amma sauran Gaɓoɓin su mustahabbi ne wajibi ne goshi ya taɓa ƙasa amma sauran Gaɓoɓin su mustahabbi ne wajibi ne Gaɓoɓi bakwai tare da hanci su taɓa ƙasa.[70]
Ɗumanina cikin sujjada wajibi ne wajibi ne wajibi ne ba wajibi bane wajibi ne.[71]
Zikirin sujjada wajibi ne mustahabbi ne mustahabbi ne mustahabbi ne mustahabbi ne.[72]
Tashahhud wajibi ne a tsakiyar sallah da ƙarshen sallah mustahabbi ne a tsakiyar sallah da ƙarshen sallah mustahabbi ne a tsakiyar sallah, wajibi ne a ƙarshen sallah mustahabbi ne a tsakiyar sallah da ƙarshen sallah wajibi ne a tsakiyar sallah da ƙarshen sallah.[73]
Sallama bisa fatawar mashhur daga malaman baya wajibi ce wajibi ce wajibi ce mustahabbi ce wajibi ce.[74]
Shakka cikin adadin raka'o'in sallah cikin shakka bayan raka'a ta biyu cikin sallah mai raka'o'i huɗu, za ayi gini kan raka'a mafi yawa, sannan yi sallar ihtiyaɗi cikin sallolin farilla za yi gini kan mafi ƙaranci tare da cigaba da sallah cikin sallolin farilla, za ayi gini kan mafi ƙaranci tare da cigaba da sallah cikin sallolin farilla idan ya zamana karon farko muka yi shakka, to zamu sake sallah, idan ta sake faruwa to za mu yi gini kan mafi ƙaranci cikin bakiɗayan sallolin farilla za a yi gina kan mafi ƙaranci tare da cigaba da sallah.[75]
Sallar matafiyi salloli masu raka'o'i huɗu wajibi a yi su raka'a biyu biyu akwai zaɓi cikin cika sallah da yin ƙasaru akwai zaɓi cikin cika sallah da yin ƙasaru wajibi ne yin ƙasaru akwai zaɓi cikin cika sallah da yin ƙasaru.[76]
Haɗe salloli biyu a lokaci guda ya halasta ya halasta a lokacin tafiya baya halasta ya halasta a halin tafiya.[77]

Hikimar Wajabta Sallah

Kur'an:

«وَأَقِمِ الصَّلَاةَ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ

kuma ku tsayar da sallah lallai sallah tana hana alfasha da munkari.

Suratul Ankabut aya ta 45

Cikin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Rida (A.S), hikima da falsafar wajabta sallah ya kasance daga iƙrarin Ubangijintakar Ubangiji, fito na fito da shirka da bautar gumaka, bayyanar da ƙasƙantar bawa a gaban girman Ubangiji, tunawa da Allah, katanguwa daga ɓarna da zunubi da girman kai.[78] cikin tafsirul amsal nan ma an bijiro da batun cewa ƙarfafuwar ruhi da daidaituwarsa, da'awa zuwa ga gyara kai, horar da kyawawan ɗabi'u, ƙimanta sauran ayyuka da gafarta zunubai suna daga hikimomin da aka yi bayani game da wajabta sallah.[79] Haka nan kuma cikin ayar (ku tsayar da sallah domin tunawa da ni)[80] an bayyana cewa hadafi daga sallah shi ne tunawa da Allah.[81] an naƙalto daga Hazrat Fatima (S) cewa Allah ya wajabta sallah saboda nesanta bayinsa daga girman kai.[82] cikin Nahjul Balaga ya zo cewa sallah ta na rusa girman kai da jiji da kai.[83]

Sallah A Cikin Sauran Addinai

Akwai sallah a cikin bakiɗayan addinai, duk da cewa yanayinta yana bambanta cikin ko wane addini,[84] a addinin yahudawa su na kiran sallah da sunan "Tifila" a sigar jam'i kuma "Tifilim" ko kuma "Tifiliyot" sannan hukunce-hukuncenta sun zo a sashen "Mishana" (Litattafan gargajiya na addu'a a wurin yahudawa) cikin ƙasidar "Bincike kan yanayin sallah a addinan Ibrahimiyya" ya zo cewa yahudawa suna sallah sau uku a kowacce rana, a ranar Shabat (Asabar) da sauran ranaku masu tsarki, firƙoƙin Ortodoksi masu ra'ayin ƴan mazan jiya su na da wata sallah da suke kira da sunan Mosaf.[85] Sallah a wurion kiristoci suna yinta ne domin alaƙa da Allah (Uba) ko sauran mutanen tiriniti (Trinity) ma'ana (Ɗa ko Ruhi mai tsarki), tsakankanin mabambantan firƙoƙi a kiristanci, su na yin sallah cikin mabambantan yanayi, ana iya yin sallah cikin surar jam'i (addu'ar sarayi) misalin taron addu'ar daren Ubangiji ko kuma kowa ya yi tasa shi kaɗai.[86]

Fihirisar Littafi

Littafin Adabus As-Salati na Imam Khomaini

An yi rubuce-rubuce da tarjamomi daban-daban game da sallah.[87] ba'arinsu sun kasance kamar haka:

  • Adabus As-Salati, na Imam Khomaini: wannan littafi ne da ya tattaro magana kan ladubba na zuciya da sirrikan baɗiini dangane da sallah, littafi ne da yake da muƙaddima wacce marubucin littafin ya yi ta domin ɗansa.

Asrar Salat, na Imam Khomaini: wani tafsiri ne na Irfani game da sallah, daga kiran sallah zuwa sallama. As-Salatu fil Al-Kitab wa Al-Sunna, na Muhammad Muhammadi Raishahari: littafi ne da ya tattaro ayoyi da hadisai daga Shi'a da Ahlus-sunna kan wajabcin sallah, hikima, sallah kafin muslunci, fifikon sallah, hususiyoyin sallah, lokutan sallah, ladubban sallah da sauransu.

Bayanin kula

  1. Norouzi, Mukaddimeh bar Falsafeh Namaz, Intisharat Yadavaran, shafi na 116.
  2. Misali, dubi Suratul Hajj, aya ta 41; Suratul Baqarah, aya ta 3; Suratul Nisa 103 da 162; Suratul Ma'edah 6; Suratul Anfal aya ta 2, 3 da 4; Suratul Ibrahim aya ta 31; Suratul Muminun aya ta 2; Suratul Namal aya ta 2 da ta 3.
  3. Suratul Ankabut, aya ta 45.
  4. Suratul Ankabut, aya ta 45.
  5. suratul nakara aya tab 45
  6. Misali, dubi Suratu Maryam, aya ta 31.
  7. Duba suratu Maryam, aya ta 55.
  8. Vazirifard, “Barasi Inkarin Zaruri dini wa Asar An dar Fiqhu”, shafi na 183.
  9. Mudarrasi, Mukaddimeh Namaz, 1387, shafi na 61.
  10. Tayyeb, Atyeb al-Bayan, 1378, juzu'i na 14, shafi na 168.
  11. Payandeh, Nahj al-Fasaha, 2007, p. 279.
  12. duba Hurrul Amili, Wasa'il al-Shi'a, 1409 AH, vol. 4, pp. 6-8, p. 539; Nuri, Mustadrak al-Wasa'il, 1408 AH, vol. 3, pp. 5-6, p. 548
  13. Misali, duba Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 7, shafi na 2 zuwa gaba.
  14. Sehati Sardroudi, "lKItabe Shinasi Guzineshi wa tausifi Namaz", shafi na 42.
  15. <a class="external text" href="https://mawdoo3.com/كم_عدد_المساجد_في_العالم">«كم عدد المساجد في العالم»</a>اکبر موقع عربی بالعالم.
  16. Mohammadi Rayshahri,Shenaktnameh Namaz, 1392, juzu'i na 1, shafi na 58.
  17. Duba Majlesi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 18, shafi na 179-180.
  18. Hurrul Ameli, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 27
  19. Motaghi, Kanz al-Umal, 1364 AH, juzu'i na 7, H18851.
  20. Motaghi, Kanz al-Umal, 1364 AH, juzu'i na 7, H18851.
  21. Majlisi, Raudatul Al-Mutaqiin, 1406 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 6, 17, 220 da 283.
  22. Qotb Rawandi, Shahab al-Akhbar, 1388, p. 59.
  23. Ibn Shu'bah, Tuhfat al-Aqul, 1363 AH, shafi. 455.
  24. Paindeh, Nahj Al-Fasahah, 1387, Hadith 1588.
  25. Sadooq, Al-Khisal, 1362 AH, juz. 1, shafi na. 103.
  26. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH,juz . 82, shafi na. 232.
  27. Muttaqi, Kanz al-Ummal, 1364 AH, juz. 7, shafi na 291.
  28. Amadi, Ghorar al-Hikam, University of Tehran, p. 56.
  29. Abu Al-Futuh Razi, Rawd al-Janan, 1376 AH, vol. 1, p. 248.
  30. Amadi, Ghurar Al-Hikam, University of Tehran, vol. 2 p. 166.
  31. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, Juz. 82,shafi na. 232.
  32. Duba Sazimane Pajuhesh wa Barn ameh rizi Amuzeshi wezarat Amuzesh wa Parwaresh. Hadiyye Asiman , 1401, shafi 53-54.
  33. Duba Ƙungiyar Bincike da Tsare-Tsare na Ilimi na Ma'aikatar Ilimi, Hadiyye Asimani, 1401, shafi 54-55
  34. Khomeini, Tawdih Al-Masail, 1387 AH, pp. 161-163.
  35. نگاه کنید به سازمان پژوهش و برنامه‌ریزی آموزشی وزارت آموزش و پرورش، هدیه‌های آسمانی، ۱۴۰۱ش، ص۵۵.
  36. نگاه کنید به سازمان پژوهش و برنامه‌ریزی آموزشی وزارت آموزش و پرورش، هدیه‌های آسمانی، ۱۴۰۱ش، ص۵۵.
  37. Malik Pourafshar, Amuzeshi Naman wa Wuzu, 1396, shafi na 11-10.
  38. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa (Mahshi), 1419 AH, Vol. 2, p. 433.
  39. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa (Mahshi), 1419 AH, Vol. 2, p. 433.
  40. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwat al-Wuthqa (al-Mahshi), 1419 AH, vol. 2, pp. 5-29; Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Towzih al-Masa'il Maraje', 1424 AH, vol. 1, pp. 614-627.
  41. Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Towzih al-Masa'il Maraje, 1424 AH, vol. 1, pp. 628-630.
  42. Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Towzih al-Masael Maraje, 1424 AH, juz. 1, shafi na 185.
  43. Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Towzih al-Masail Maraje, 1424 AH, juz. 1, shafi na. 365
  44. duba: Tabatabai Yazdi, Al-Urwat al-Wuthqa (Mahashy), 1419 AH, juz. 2,shafi na 362-385.
  45. Khomeini, Tawdih al-Masail (Resalah), 1424 AH, juz. 1,shafi na. 441-442.
  46. Bani Hashemi Khomeini, Resaleh Towzih al-Masael Maraje, 1424 AH, juz. 1, shafi na 431.
  47. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1419 AH, juz. 3, shafi na 414
  48. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1419 AH, juz. 3,shafi na. 414
  49. duba Mohammad Reishahri's "Al-Salat fi al-Kitab wa al-Sunnah", 1377 AH, juz. 1, shafi na. 49-63.
  50. "duba Mohammadi Reyshahri, Al-Salat in the Quran and Sunnah, 1377, juz. 1, shafi na 140-144."
  51. Look at Qomi, Mafatih al-Janan, bakhshi Takqibat Namaz Shafi na. 12-19.
  52. Tabatabai Yazdi, Al-'Urwah al-Wuthqa (Mahshi), 1419 AH, juz 2, shafi na 244.
  53. Tabatabaee Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthqa (Mahshi), 1419 AH, juz 2, shafi na 244-245.
  54. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa (Mahshi), 1419 AH, juz. 2, shafi na. 246.
  55. Sheikh Saduq, Man La Yahduruhu al-Faqih, 1367 AH, juz . 1, shafi na 206.
  56. Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 484
  57. Ibnu Tawoos, Falalar Qa'il, 1406H, shafi na 22.
  58. Ibnu Tawoos, Falalar Qa'il, 1406H, shafi na 22.
  59. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 80, shafi na 6
  60. <a class="external text" href="https://hawzah.net/fa/LifeStyle/View/52184">«سبک شمردن نماز»</a>
  61. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 109.
  62. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 110.
  63. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 110.
  64. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 110.
  65. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 110.
  66. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 110-111
  67. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 111.
  68. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 111
  69. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 111
  70. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 112.
  71. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 112.
  72. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 112.
  73. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 112-113
  74. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 114.
  75. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 114.
  76. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 139.
  77. Mughniyeh, Fiqhu Ala al-Mazahib al-Khamsa, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 142.
  78. Har Ameli, Vasal al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 4
  79. Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1374, juzu'i na 16, shafi 290-294
  80. Suratul Taha, aya ta 14.
  81. Dubi Motahari, “Falsafeh ibadat”, shafi na 15-17.
  82. Tabarsi, Al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 107
  83. Nahj al-Balagheh, Sahih Sobhi Saleh, Aphoriss 252, shafi na 512.
  84. Rajeb Esfahani, Mufrsdat, 1412H, shafi na 491.
  85. Bagharian, "Barasi Cegunagi Namaz dar Adyan Elahi", shafi na 219.
  86. <a class="external text" href="http://intjz.net/maqalat/ak-namaz.htm#_Toc280784367">«نگاهی به اشکال مختلف نماز در برخی ادیان الهی»</a>
  87. Duba Kitabe Shinasi Namaz", shafi na 57 da 58.

Tsokaci

  1. ya ka bamu alheri da kyakkyawa a gidan duniya da lahira sannan ka tseratar da mu daga azabar wuta
  2. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai ALlah, kadai yake ba shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa muhammad bawansa manzonsa ne, ya Allah kayi dadin tsira da aminci ga muhammad da mutanen gidansa
  3. Amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan annabi da rahamarsa da albarkokinsa, amincin Allah ya tabbata ga bayin Allah nagargaru, amincin Allah ya tabbata gareku da albarkarsa
  4. tsarkin ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah shi ne mafi girma
  5. Tsarki ya tabbata ga Allah kuma goidaya ta tabbata a gareshi, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah akbar

Nassoshi

  • Motaghi Handi, Ali bin Hossamuddin, Kanzal-Amal, Ottoman Encyclopedia, hedkwatar Hyderabad, 1364H.
  • Abulfatuh Razi, Hossein bin Ali, Ruz al-Jinnan wa Ruh al-Jinan fi Tafsir al-Qur'an, Mashhad, Astan Quds Razavi Islamic Research Foundation, 1376.
  • Amadi, Abdulwahid bin Mohammad, Gharar al-Hakm da Darr al-Kalam, Tehran, Jami'ar Tehran.
  • Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hossein, Tauzihul Almasa'il Maraji , Qum, ofishin yada labaran Musulunci, bugu na 8, 1424H.
  • Hurru Amili, Muhammad bin Hasan, Al-Wasa'il al-Shia, Kum, Al-Bait (AS), 1409H.
  • Ibn Sha'bah, Hassan bin Ali, Tohf al-Aqool, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1363.
  • Ibn Tawoos, Ali Ibn Musa, Fallah Al-Saqi da Najah Al-Masail, Kum, Bostan Kitab, 1406H.
  • Imam Khumaini, Bayanin Al'amura, Cibiyar Edita da Buga Imam Khumaini (A.S) Tehran, bugu na 7,1387.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, Tehran, Dar Al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Madrasi, Sayyid Muhammad Taqi, Hukunce-hukuncen Sallah, Qum, Mohiban Al-Hussein (a.s.) Bugawa, bugu na 4, 1387.
  • Majlesi, Mohammad Taqi, Ruzda al-Mutaqeen fi Sharh Man la Yahzara al-Faqih, Kum, Kushanbur Islamic Cultural Institute, bugu na biyu, 1406H.
  • Majlisi, Mohammad Bagher, Bihar al-Anwar, Al-Wafa Foundation, 1403 AH.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Nashon, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 32, 1374.
  • Malekpour Afshar, Ibrahim, Koyarwar Sallah da Alwala, Pourafshar Publications, Qum, bugun 19, 1396.
  • Mohammadi Rishahri, Mohammad, Certificate of Prayer, Dar al-Hadith Scientific and Cultural Institute, 1392.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad, Salat fi al-Kitab wa Sunnah, wanda Abdul Hadi Masoudi ya fassara, Qum, Dar al-Hadith, bugun farko, 1377.
  • Motahari, Morteza, "Philosophy of Ibadat", in Tamashaghe Raz Quarterly, Lamba 2, Summer 2013.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, Fiqh Ali al-Mahabh al-Khamsa, Beirut, Dar al-Tiyar al-Jadid-Dar al-Jawad, bugu na 10, 1421H.
  • Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Kum, Hijira, bugun farko, 1414H.
  • Najafi, Mohammad Hassan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, bincike da gyara na Abbas Qavachani da Ali Akhundi, Beirut, Dar Ehiya al-Trath Al-Arabi, bugu na 7, 1362.
  • Norouzi, Mohammad Masoud, Gabatarwa ga Falsafar Addu'a, Yadavaran International Publications.
  • Nouri, Mirzahosein, Mostadrak Al-Wasail, Qom, Al-Bait Institute (AS), bugu na farko, 1408H.
  • Payandeh, Abul Qasim, Nahj al-Fasaha (Tarin Nasihar Annabi (SAW), Darul Alam, 1387).
  • Qomi, Sheikh Abbas, Mofatih al-Jinan, Kum, Aswah, Bita.
  • Qutb Ravandi, Saeed bin Hibatullah, Shahab Al-Akhbar, Qom, Dar al-Hadith, 2008.
  • Ragheb Esfahani, Hossein bin Muhammad, Al-Mufardat fi Gharib al-Qur'an, bincike da gyarawa na Safwan Adnan Dawudi, Beirut-Damascus, Dar al-Qalam - Al-Dar al-Shamiya, bugu na farko, 1412H.
  • Sazimane Fajuhesh Barname rizi Amuzehsi wezarat Amuzesh Farwareshi Hadiyyae Asimani, Tehran, Kamfanin Offset, bugun 11, 1401.
  • Sheikh Sadouq, Mohammad Bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Khasal Sadouq, Jamia Modaresin, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Lay Hazara Al-Faqih, Sadouq Publishing House, 1367
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtjaj Ali Ahl al-Jajj, Mohammad Baqer Khorsan, Mashhad, Mawallafin Morteza, bugun farko, 1403H.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Wathaghi (Mohshi), bincike da gyara na Ahmad Mohseni Sabzevari, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1419 Hijira.
  • Tayeb, Seyyed Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam Publications, bugu na biyu, 1378.
  • Vazirifard, Mohammad Javad, barasi Inkari Zaruri dini wa Asare An dar Fiqh", a cikin Allameh Quarterly, No. 39, Spring and Summer 2011.