Maganar Da Annabi Isa Ya yi Yana Jariri

Daga wikishia

Magana da Annabi Isa Ya yi Yana Jariri, (Larabci: تكلم النبي عيسى في المهد) magana ta mu'ujiza Annabi Isa (A.S) ya yi lokacin da yake jariri a shimfiɗar haihuwa domin kawar da tuhumar aikata alfasha daga mahaifiyarsa Sayyida Maryam (S), da kuma shelanta muƙamin annabtarsa a gaban malaman yahudawa.[1] cikin ayoyi guda uku daga kur'ani aya ta 46 suratul alu imran, aya ta 110 suratul ma'ida da aya ta 29 suratul maryam an yi ishara kan buɗa bakin Annabi Isa tun yana kan zanin haihuwa.[2] a cewar marubutan tafsirul al-amsal, mutane biyu daga masu dandaƙe bincike daga malaman tafsiri sun tafi kan cewa abin nufi daga kalmar “mahdi” shi ne shimfiɗa ko wani lokaci da galibi jariri yake kasance cikin kulawar mahaifiyarsa.[3] kishiyar wannan magana, Muhammad Hadi Marifat cikin littafin Al-tamhid ya yi amanna cewa bayan shuɗewar wasu adadin shekaru bayan ta haihu ne ta dawo cikin gari , sannan ma'anar “mahdi” shek arun yarintarsa Isa.[4] haka nan Sayyid Ahmad Khani Hindi, malamin tafsirin kur'ani, ya yi amnanni maganar da Annabi Isa ya yi ta kasance a farko-farkon yarintarsa bawai lokacin da yake jariri ba.[5]

Abul Fatuh Razi, malamin tafsiri da hadisi ɗan shi'a a ƙarni na shida ƙamari, tare da jingina da wani hadisi daga Annabin muslunci, ya tafi kan cewa Annabi Isa ya kasance ɗaya daga cikin mutum biyar da suka yi magana a lokacin da suke jarirai.[6] Jafar Subhani da Ibrahim Amini daga malaman shi'a, daga maganar da Annabi Isa ya yi sun fitar da cewa hakan dalili ne kan yiwuwar samun hankali da tantancewa ta wajibi ga imamanci a shekarun yarinta.[7]

bisa Abin da ya zo cikin aya ta 30 suratul maryam, Isa cikin wannan magana da ya yi ya kira yi kansa da bawan Allah, annabin Allah da aka bashi littafi da kuma kasancewarsa mai alabrka. haka nan ya yi bayani shi bai kasance mai takurawa ba, kuma Allah ya umarce shi da kiyaye sallah da bada zakka da biyayya ga babarsa, bisa abin da ayoyin kur'ani suka kawo, hakika wannan magana ya yi sallama uku ga kansa, aminci kaina ranar da aka haifeni, ranar da zan mutu da kuma ranar da za a tashe ni a raye a wata duniya.[8]

Ba'arin malaman tafsiri sun tafi kan cewa maganar da Annabi Isa ya yi mu'ujiza ce tasa, wasu kuma suna ganin matsayin karama ce ta Sayyida Maryam.[9] Muhammad Hadi marifat, malamin tafsiri a shi'a, ya tafi kan cewa asalin maganar tasa ba ta alaƙa da ko wace irin mu'ujiza, saboda a imanin malamin Annabi Isa ya yi magana ne bayan girmnsa kuma dama yawanci yara suna fara magana ne a wannan lokaci, a cewar Hadi Marifat nau'in maganarsa ta kasance ne da wani ma'auni da hankali na musamman wanda cikinsa ya tabbatar da cewa mahaifiyarsa tya haife shi ta hanyar mu'ujiza kuma ta kasance tsarkakakkiya daga duk wata tuhumar aikata alfasha.[10]

Fakhrur Razi, malamin tafsiri da hadisi ahlus-sunna a ƙarni na shida, a cikin littafin tafirul al-kabir ya yi amanna cewa wannan waƙi'a tsantsar abin al'ajabi ne. Ya yi amanna da cewa akwai bambanci tsakanin mu'ujizar da take faruwa daga Annabi da kuma faruwar wani abin al'ajabi da ya same shi, ya yi amanna da cewa al'amura misalin haihuwar Annabi Isa ba tare da uba ba da maganar da ya yi a shimfiɗar jariri tana da bambanci da mu'ujizozi misalin raya matattu da ya yi a zamaninsa.[11]

Bayanin Kula

  1. Sadeghi Tehrani, "Sharhe Sakhnan Issa Masih Dur Ghawarah," na Muhammad Sadeghi Tehran.
  2. Alqur'ani mai girma. ↑
  3. Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1371 AH, juzu'i na 13, shafi na 52; Mansouri da Shorgashti, “Parssi Didgah Hai Tafsir, Mufassirun darbaraye Ayat takallum Hazrat Isa, (A.S), dar Mahd”, shafi na 209-210.
  4. Mansouri da Shorgashti, “Parse didGahaye Tafsir, Mufassirun Ayat Takallum Hazrat Isa, (A.S), Dar Mahd” shafi na 210.
  5. Kazemi, “Naqdi Bar Andisheh Hai Sayyid Ahmadkhan Hindi Pyramun Ijaz,” shafi na 138.
  6. Razi, Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan fi Tafsir Qur’an, 1408 AH, juzu’i na 13, shafi na 78.
  7. Sobhani, “Imamate dar kodaki?”, shafi na 46; Amini, “Aya Kodake panje sale Imam mishawad?”, Ibrahim Amini Ittila rasani.
  8. Makarem Shirazi, Tarjameh qur'an, 1373, shafi na 307.
  9. Fakhr Razi, al-Tafseer al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 21, shafi na 534.
  10. Mansouri da Shorgashti, “Parssi Didgah Hai Tafsir, Mufassirun darbaraye Ayat takallum Hazrat Isa, (A.S), dar Mahd”, shafi na 212
  11. Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 23, shafi na 280.

Nassoshi